Showing 90001 words to 93000 words out of 168255 words

Chapter 31 - Auren Kwangila Book 4 Hausa Novel Complete

Takori   

12 Dec 2024

332

UWA-MAHAIFIYA, ta amince ya auro Muazatu ya karo cikin gidan za ta zauna lafiya da ita, koda kuwa bazai iya adalci a tsakanin su ba zata jure ta zauna. Ta sa a ranta muddin ta samu damar kebewa da shi kafin barinsu Jimeta za ta shawarce shi a kan wannan hangen na zuciyarta. Za ta iya jure komai ban da rasa shi a yanzu. Yana da matsayi iri-iri cikin rayuwarta. Ya cika mata dukkan burirrikanta. Ya kawo dawwamammen farin ciki da kwanciyar hankali gare ta. Za ta so shi da makamancin hakan shi ma (Allah sarki Hafsat).
Kawunansu Malam Babba ya kama ya shiga kwararo musu addua. A karshe ya ce, Miji ake baiwa amanar matarshi, amma ni Hashim Babba Jimeta, ke Hafsu na baima amanar jikana Abdulazeez, ki kula min da shi, ki rike shi amana, Allah ya yi muku albarka bakidaya.
Abdulazeez ji ya yi idanunsa sun cicciko da kwalla. A haka ya dago su ya kalli Hafsat wadda kanta ke sunkuye, mayafinta ya zame ta baya. Manyan kitson kanta sai kyalli suke suna daukar idonsa. Da a ce bai yi azarbabin kuskuren sanya takardar nan a jakarta ba ya bari sai za su koma Kano ya bata hannu da hannu kamar yadda zuciyarsa ta shawarce shi da farko, da yayyagawa zai yi yanzu ba wanda ya ji ba wanda ya gani, ya yi fatali da wasu alkawurruka da ya san ya daukarwa Muazatu tunda ita ba Allah ba ce. In ya so ya yi kaffara ya ci gaba da zama da Hafsat har karshen rayuwarsa.
An ce ana barin halas ko don kunya! Ya tabbata zai iya mantawa da Muazatu cikin rayuwarsa, amma ba zai taba iya mantawa da Hafsat ba. Alamarinsa da ita ya fi gaban a kira shi soyayya irin tashi da Muazatu. Wani alamari ne daban beyondhis expectations. Wasu igiyoyi ties sun bi sun daddaure zuciyarsa tamau sun hanashi sukuni da jin dadin rayuwar ko ta yaya, daga jiya zuwa yau da bai kwana wuri guda da Hafsat ba.
Ya tabbata za su ci gaba da bibiyarsa suna kassara shi har karshen rayuwarsa in bai yi gaggawa ya gyara kuskurensa ba.
Kamar an ce da Hafsat dago. A hankali ta cira idonta suka sauka cikin na Abdulazeez. Sababbin alamura masu ban mamaki ta gani a cikinsu wadanda bata taba gani ba. Ji ta yi ba za ta iya jure kallon tsakiyar idanunsa ba domin sosai ta fahimci yana cikin wani hali da ta kasa ganewa. Sunkuyar da kanta ta yi ta zame hannunta daga cikin nasa ta koma jikin Dada ta zauna. A kusa da Malam ya ci gaba da zama ya kasa tashi. Don ya san muddin ya mike kafafunsa ba za su iya daukar nauyin gangar jikinsa ba. Ya tafka gundumemen kuskure wanda bai san ya ya zai yi ya gyara shi ba.
Hotunansu da Habiba a Jeddah Mammah ta fiddo kala-kala a ke ta gani. Duk cikin bakar abaya ta ke irin ta matan Saudiyya amma fuskarta a waje ta ke ta dage himar din sama dauke da murmushi mai keta zuciya da hakorin makkah na gwal a bakinta, yawanci duk tare ta ke da su Ismael a wuraren wasan yarababu Abdulazeez yana Nigeria a lokacin. Adduoi na musamman aka yi aka rufe taron, sannan jamaar gidan suka shiga fiddo da garar abinci kala-kala wanda aka tanada musamman dominsu. Rago guda aka kyafe aka gashe musu ko daddatsa shi baa yi ba. Abinciccikan na fulanin Jimeta ne irin su tuwon Alabo (nyiri gurka)da miyar kubewa, tuwon masara da miyar yakuwa da gyada wato (hako lauto), tuwon dawa da miyar zogale (hako kabije) tuwon shinkafa da miyar karkashi (hako gubudo). A fannin abin sha kunu ne guda uku; ga kunun shinkafa (garibasise), kunun gyada (gari biriji), kunun tsamiya (garijabberi) sannan ga soyayyar rama (saande). Kowa yaci abincin nan da matukar marmari yayi hanian hade da gasashshen naman rago.
Har dare suna gidan sai magriba maza suka fita sallah, suma matan suka yi a cikin gida. Bayan sallar ishai suka yi sallama da kowa za su wuce masauki. Mammah ta dubi Hafsat wadda ita ma ta mike tana son ta bi su saboda rashin sabo, ta ce ta zauna da Dada, gobe kafin su wuce Kano za su biyo su yi sallama, kuma ta sanya wayarta a caji za ta kira ta anjima.











SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI
07030137870

*Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama*

Ta zura hannu cikin jakartatana lalubo wayar, sai ta ji farar takardar cikin ambulan. Zaro ta ta yi ta juya ta a hannunta ganin an rubuta sunanta HAFSAT a jikin ambulan din. Sai dai abu daya ya ja hankalinta, handwriting din Abdulazeez ne wanda ya riga ya zauna a memory din ta sabida yawan duba takardunsa data ke yi in ya bari a falo. Ta maida ita inda ta dauko ta don ta ga bai kamata ta bude agaban Mammah ba batasan ko menene a ciki ba. Mammah ta ce.
Wasikar mene ne wannan kamar rubutun mijinki?
Cikin jin kunya irin nata ta sunkuyar da kai, ta ce, Ina jin shi ya saka.
Mammahbata ce komai ba ta yi musu sallama ta bi bayan su Adda Hafsatu, Suhaanah ta koma dakin Dada rike da jakarta.
Har karfe goma sha daya na dare Hafsat da kakarta Dada ba su kwanta ba. Hira suke yi tana ba ta labarin rayuwar mahaifiyarta. Da duk abin da ya kamata ta sani na zuriarsu. Ita kuma Hafsat na ba ta nata labarin rayuwar a gidan tsohon Ambasada Hamza Atiku har zuwa aurenta.
Dada ta ce, A duniya da ma akwai sauran mutane irin wadannan? Alherinsu ya bi su har yaya da jikoki.
A cikin labaran da ta ke baiwa Dada ba ta taba kuskuren cewa Daddy bai karbe ta a baya ba, ta riga ta shafe wannan daga tarihin rayuwarta, ko Daddy bai yi repenting kuskurensa ba ba za ta gushe tana mai yi masa uzuri ba da kallonsa matsayin uban da ya haife ta.
Suna shirin kwanciya tana kakkabe gadon bonon Dada da gefen zaninta don ta kwanta, Dada ta shimfida sallaya za ta dasa sallar daren da ta ke cinye rabin dare tana yi sannan ta kwanta. Ta bawa Dada baya tana ta kakkabe gadon, ta ji muryar Dada na zolayarta.
Tun ganina da shi na farko na ji ya kwanta min a zuciya kamar autana Nuru. Da Hajiya Mairamu ta sani ta barki kin bi mijinki kun yi kwanan sallama, tunda za ki kwana biyu a nan a kai ki ki ga sauran dangi da ba ki gani ba, kuma Babanki ya ce za ku je Numan ya kai ki wajen nashi yan uwan.
Murmushi ta yi ba tare da ta juyo ba, a ranta ta ce, Maaurata na hakika su suka damu da juna har in za su rabu na wani dan lokaci su damu da su yi sallama da juna ban da mu Dada! Mu namu auren suna ne kawai.
Ta shiga tunanin ita yaushe rabon ma ta kwana daki daya da Abdulazeez Dakata? Tun wani zamani can da suke cikin zama na aminci kafin ya rikide mata ya canza kamar wahainiya, har gobe in za a kashe ta ba ta san ina Abdulazeez ya sa gaba a aurenta ba. Idan ta yi kokarin fassarawa sai ya rikide ya canja wanda ya nuna shi kansa ba shi da direction. Tunowa ta yi da takardar dazu da ta ciro a jakarta har Mammah ta gani, ta yi mamakin yaushe ya sa takardar a jakarta ba ta sani ba? Ta kuma cika da dokin son ganin me takardar ta kunsa? Don haka da ta gama gyaran gadon, kayan barci ta sanya ta jona wayarta a caji, sannan ta dauko takardar ta bi lafiyar gadon audugar kakarta, ta rufe rabin jikinta da bargon Dadan ta bude takardar ta soma karantawa.

Ga abin da Abdulazeez Dakata ya rubuta wa matarsa Hafsat-Suhaana.

‘A zaman da muka yi na tsawon watanni goma sha biyar, in na ce akwai wata rana da ki ka bata min ko kika yi min abin da raina ba ya so ba bisa kuskure ba, na zalunce ki. Ta nawa bangaren ne akwai babban gibi da ya sa ni kasa ci gaba da zama da ke Hafsah, amma ba don ba ki cancanci a so ki ba, ko a ci gaba da zaman aure da ke ba. You are a darling (ke abar so ce) ga duk wanda Allah ya yi wa alfarmar samunki a matsayin mahadin rayuwa. Rauni na guda daya ne; INA SON MUAZATU! Na yi duk iya tunanina don nema wa aurenmu mafita na rasa Hafsat don shinge ne (barrier) a gare ni ga samun Muazatu, amma ba don ina kin ki ba. A bisa hakan, da wasu dalilai da dama na yanke igiyar aurenmu guda daya kamar yadda muka yi YARJEJENIYA. Allah ya ba mu mafita ta alkhairi ni da ke bakidaya.
Sa-hannu
ESQ Abdulazeez Dakata.

A hankali Hafsat ta lumshe idanunta, zuciyarta ta yi wani irin bugu sau uku; fat-fat-fat, a jere a lokaci daya. Ta shaki iska don ta fesar amma iskar ta makale ta ki fitowa daga huhunta. Kokawa ta shiga yi da numfashinta daga huhu zuwa makogaro amma iskar ta ki fita wanda hakan ya maida ita unconscious na lokaci mai tsawo. Sai numfarfashi ta ke ta baka kamar mai ciwon asthma da ta samu attack.
Dada ta yi sallama kenan daga sallar da ta idar ta ji numfarfashin Hafsa kamar na fitar rai. Da sauri ta yaye mayafinta ta wurgar ta yo kanta. Bakinta ta sanya cikin bakinta ta shiga ba ta taimakon farko irin wanda ake badawa mouth-to-mouth idan numfashi ya yi gardama.
Sun dauki mintuna biyar a haka kafin ta ji numfashin Hafsan na daidaita. Dago ta ta yi ta kwantar a kan kirjinta ta rungume ta.
Ko da Hafsat ta samu kanta runtse idanunta ta yi hawaye suka soma sauka wani na bin wani. A ganinta bai kamata sakin ya fitar da ita hayyacinta har haka ba tunda akalla ta san da wanzuwarsa. Lokacin karbarsa ne ba ta sani ba. Ya zo mata ne awkwardly(bagatatan) kamar fadowar aradu. Abdulazeez ya shammace ta, ya kuma tafi da dukkan farin cikin da ta ke ciki a yau wanda shi ne silarsa. Bai kamata ta ce ya karya zuciyarta ba, amma ya karya din. Rokon Allah ta ke ya sa mafarki ta ke yi, ire-iren mafarkanta na ranakun KWANGILA sun cika Abdulazeez ya sake ta. Ta farka ta ganshi yana shirin (office) a gefenta ko yana kumbing kanshi yana feso mata ruwan jikakkiyar sumar sa a fuska, amma ta yi duk wani kokari da za ta iya don ta farka daga mafarkin yau, wasu hujjoji masu yawa sun tabbatar mata na yaureality ne.
Hujja ta farko jinta jikin dattijuwa Dadanta, tana shafa kwantaccen gashin kanta tana tambayarta, shin tana da ciwon asthma? Da hausarta da ba ta fita sosai, amma kwarai ta ke gane duk abin da ta ke fada.
Ba ni da asthmaDada, amma ina da nimoniya (pneumonia). Ta amsa cikin dusashshiyyar murya.
Amma abin da ki ka yi dazu, ya fi kama da na mai ciwon asthma.
Hannu ta kai tana share hawayen da ke yin ambaliya suna bulbulowa daga idanunta.
In ma ba ni da Asthma Abdulazeez ya saka mini. Abinda ta fadi kenan cikin zuciyarta.
Baccin da ba su yi ba ke nan, sai da aka yi kiran assalatu a kunnuwansu. Hafsat ta ga kuka da ciwon zuciya ba za su kare ta da komai ba tunda dai (he finally made his decision) ba ya bukatarta cikin rayuwarsa, bai boye ba ya gaya mata, ya kamata ta bude zuciyarta ta rungumi kaddararta da hannu bibbiyu...Ta karbi rayuwar a yadda tazo mata.
Ko wani bai fada mata ba ta fahimci zuciyarta ta dade da kamuwa da so da kaunar Abdulazeez... to idan so cuta ne ya kamata hakuri ya zamo maganin cutar nan tunda an ce babu cutar da ba ta da magani a duniya.
Da wannan tunanin Hafsat ta kwarara zuciyarta, ta karbi butar da Dada ta cika mata da ruwa ta zaga ta kuma dauro alwala. Kafin ta yi sallah sai da ta tabbatar ta yi wa takardar sakinta kyakkyawan boyo, ta yi alkawarin kame bakinta ba dai wani ya ji wannan maganar daga bakinta ba, shi da ya aikata ya yi musu bayani in sun nemi baasin rashin dawowarta. Ta zo Jimeta kenan! Ita da Abuja sai da ziyara, ziyarar ma daga shekara sai shekara.
Ta dauki rayuwar da ta yi da Abdulazeez Dakata ta sanya cikin wani kundi (littafi) mai dadin karantawa. A yau ta kawo karshen karatun wannan KUNDI wato littafi ta rufe shi ta adana cikin tsohon akwatin karfe ta tura karkashin gado tare da duk wani alamari da ya shafe shi. Tana tausayin kanta da sabon sunan da alumma za ta laka mata na bazawara(before the age of 20), amma ta fi tausaya wa Mammah.Wadda ta dauki duk wani buri ta dora a kan aurenta da danta. Dan da a wurinta ba nata ba ne, ita ce yarta. Idan kalaman Abdulazeez sun so su yi mata ciwo sai ta yi maza ta kawo uzuri... iyakar gaskiyarsa ya fada... ya fadi zahirin abin da ke zuciyarsa ne. Yana daga cikin halayensa da ta ke so; fadar gaskiya komai dacinta... Bata da abubuwan da Muazatu ke da su, shi ya sa ya kasa ba ta gurbin matar aure!!!
Sallah ta ke, amma kuka ta ke yi, hawayenta na bilbila a cikin sujjadarta. Rokon Allah ta ke ya ba ta juriya ta karbi sabuwar rayuwar nan da ta zo mata!!!

******
Da dai a ce ba daki daya ya kwana da kakansa Baffa Atiku ba da Allah kadai ya san irin halin da zai kasance. To Baffan kamar ya gane yana cikin wani hali, ya kasa ya tsare ya hana shi tunanin komai. Idan Allah ya yi maka alfarmar rayuwa da kakanninka, to ka gode masa duk girmanka. Suna da wani feeling a kan jikokinsu da son farin cikinsu wani lokacin fiye da iyayen da suka haife su. Bai titsiye shi a kan sai ya gaya masa damuwarsa ba, amma ya lura ana ta kiransa a waya ba ya dauka, karshe ma da aka ci gaba da kiran wayar ya kashe ta bakidaya ya sanya ta a caji. Baffa bai bar kunnuwansa sun huta ba sai da bacci ya soma fizgarsa. Wani azababben barci da babu komai sai mafarkin Hafsat-Suhaanah, da halin da ta ke ciki a daidai wannan lokacin domin ya tabbata zuwa yanzu kyakkyawan sakonsa ya isa gare ta.
Kowa ya kalle shi a washegari sai ya tambaye shi ko ba shi da lafiya ne? Musamman Daddy wanda ya fi kowa shiga damuwar halin da ya ga Abdulazeez din a ciki. Ya zabge ya fyade a dare daya kamarwanda ya yi wata yana jinya, ya ce in ya san bashi da lafiya ba zai iya tuki ba su je Airport su hau jirgi ragowar su taho a mota, ya ce zai iya, kuma lafiyarshi kalau bacci ne bai samu ba. Wani irin kallo Daddy ke binsa da shi na rashin yarda.
Demsawo suka nufo suka yi sallama da kowa na gidan, Mammah ta ce da Hafsat tunda hutu bai kare ba ta yi zamanta sai hutu ya kare Abdulazeez ya zo ya taho da ita. A karshe ta ce, ta je yana dakin Malam su yi sallama. Ta yi sallama da Dada da matan su Yaya Tijjani, da sauran kannenHabiba da basu koma gidajensu ba tun jiya, an hada musu tsarabar Jimeta rankatakaf! Yara suka yi ta kwasa suna kaiwa mota. Mammah ta fita ta shiga mota suna jiran Abdulazeez.
Kusa da dakin Malam dakin Nuru ne autan Dada, yana makarantar da yake koyarwa a lokacin da yake ranar aiki ce jumaa da safe. Hafsat ta tafi don cika umarnin Mammah, amma sai ta ratse ta shige dakin Nuru ta rufe har da saka sakata.
Ba ta son ganinsa, ba ta son wata alaka ko ta gaisuwa ce ta sake shiga tsakaninsu. Me ya saura a tsakaninsu? Babu for now! Sai yan uwantakar musulunci da zumuncin haihuwarsa da Maryam Dakata ta yi ya riga ya hada. Da ta san haka zafin saki yake a zuciyar diya mace da ba ta yarda da wannan yarjejeniyar ba. Da ta san haka zafin so yake, da ba ta yarda ko kusa Abdulazeez ya shiga rayuwarta ba. A sanda suke tare, the feeling is so sweet a yanzu da rabuwa ta zo, itspainful, very painful. Zuciya ta yi duhu, babu komai cikinta sai kunci mai azabtar da ruhi. Hawaye ke zuba daga idanunta suna sauka a kan tafukan hannayenta.
Abdulazeez Dakata zaune a dakin Malam Babba, Mammah ta ce da shi, ga Hafsat nan zuwa. Ji ya yi kamar ta dauke masa wani nannauyan dutse da ya danne zuciyarsa. Kokari zai yi ya karbe takardar daga hannunta tun wani bai ji ba bai gani ba, ya yi repenting. Ya san Hafsat na da sanyin zuciya, sannan tana girmamashi, tana yawan yi masa uzuri, kalamai kadan za su wanke wannan gundumemen laifin nasa (kamar yadda yake tsammani). Daga shekaranjiya zuwa yau ya nutsu ya tantance aya da tsakuwa, ya yarda rayuwarsa ba za ta taba komawa daidai ba, ba tare da dawowar Hafsat cikinta ba. He can do without Muazatu, but he cannot do without Hafsat, wannan wani abu ne da ya yarda da shi daga jiya zuwa yau kadai ganin yadda rayuwar ta birkice shi (upside-down) ta maida shi wani birkitacce susutacce. Rokon Allah yake ya sa Hafsat ba ta yi zancen wasikar nan da Mammah ba.
Kai ba ta yi ba... babu wani canji a tare da Mamman har ta shiga mota.
Don haka ya ci gaba da taraddadin jiran fitowar Hafsat ya maida hannun agogo baya. Amma har ya kwashe mintuna talatin a zaune babu Hafsat balle kamshin sanyayyan turarenta.
Hankalinsa ya soma tashi ne lokacin da Daddy da Mammah suka shiga kiran wayoyinsa da ke aljihun rigarsa, da fari kamar ba zai amsa ba amma suka ci gaba da kiran. Dole ya amsawa Daddy.
Har yanzu sallamar ba ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login