Showing 138001 words to 141000 words out of 168255 words
ta bude sakon saboda ta gane lambar da Abdulazeez ya kira ta jiya ce. Hannunta har rawa yake yi, ko me ya rubuto? Ga mamakinta, fatan alkhairi ne a kan jarrabawarta.
As you strive hard to achieve this goal, heres hoping that you excel in every course,with hope in yourself and this strong determination of yours,with me In mind.. and the assurance of my inexpressible love to you I believed that success will surely come your way.
-Abdulazeez.
Ita kadai ta hau blushingtun daga baki har kunne. Sakon waya mafi daraja data taba karba a rayuwarta. Sakon waya da ya sata farin cikin da wani sako bai taba sata ba. Ya goge gabadaya memories na wancan black sakon data taba karba a rubuce. Ta kusa yin tuntube da za ta shiga motar. Haleem ya ce.
Tsohuwa yi a hankali, doguwa, hankalinki a gwiwa!. Ta harareshi, amma farin cikin data ke ciki ya hanata ramawa. Suna hanya banda maimaita karanta sakon ba abin da ta ke yi. Haleem na ta mata hira bata san me yake cewa ba. Hatta Mammah ta lura Hafsat yau cikin farin ciki take. Ta san ta canka daidai in ta ce waya na aiki. Addua ta ke yi a zuciyarta wadda ita kadai ta san me ta ke roka musu, wanda ba zai wuce zaman lafiya da zuria mai albarka, da soyayya mai dorewa har abada ba.
Ta riga kowa shigewa daki bayan cin abincin dare, manne ta ke da wayarta tana jiran Abdulazeez ko zai kira? Ko karatun paper din gobe ta ki yi, ba ta da nutsuwar yinsa. Haka ta yi ta zaman jiran gawon shanu amma hudubar jan ajinmu na mata da zuciyarta ke ta yi mata ya hana ta yin sadaukantaka ita ta kira shi. Sai karfe hudu na asubah kamar jiya tana bisa sallayarta ta ga shigowar kiransa kamar a mafarki. Ba ta iya ta jinkirta ba ko na minti daya wannan karon wajen amsawa.
Tana iya jiyo ajiyar zuciyarsa, ita ma ajiyar zuciyar ta yi ba da saninta ba. Hafsat bazaki kira ni ba, in ni ban kira ki ba? Ya fada da dukkan concern da muryarshi ke iya badawa, haka kawai yake ji a zuciyarsa abubuwan da yake mata bai kyauta ba, shi kuma yana yi ne don ya nuna mata fushinsa na abin da ta yi masa rannan duk da ya san ta fi shi gaskiya.
Yaya Azeez na ga text, na gode!.
Abin da ta iya furtawa kenan cikin kankanuwar murya,cike da tsoron kada yau ma ya katse maganar tasu irin jiya, ya barta da shaukin da ita kadai tasan adadinsa. Ba tare da ta bashi amsar tambayarsa ba, don ita kanta bata da amsarta.
Fadan namu ya kare ne?
Ya tambaya da yanayin da ke nuna yana tsananin son jin amsarta wannan karon.
Murmushi ta yi ta kwanta sosai a kan sallayarta maimakon zaman sallar da ta yi akan kafafunta. Sannan tace.
Its inconclusive!”.
Dariya ta ba shi sosai. What made itinconclusive bayan gashi na karbi laifin bakidayansa yanzu?
Saboda ni har gobe ban san laifin da na yi maka ba ka ke hora ni haka Yaya Azeez,zuciya ta a kanka mai rauni ce, idan nace rauni ina nufin rauni; ba komai ta ke iya dauka ba musamman fushin ka, tun daga ranar da ta soma son k........
Hannu ta kai ta toshe bakinta jin sakin layin da ta keyi. How sure she is yanzun yana sonta baka da zuci kamar yadda Mammah ta ce da za ta fara gaya masa sirrin zuciyarta? Wanda daga ita sai Ubangijin ta suka sani duk da cewa ya furta mata kalmomin dake nuna soyayyar? Ta ji kamar ta dawo da abin da ta fada cikin bakinta, inda hali ta bi bakin da zare da allura. A can bangaren Abdulazeez wayar ya canza wa position daga dama zuwa hagu yana jin wani kududu da ya dade da tsayawa a makogaronsa na melting gradually (narkewaahankali). Zuciyarsa ta shigaimaginatingHafsat a gabansa, da shi kadai ya san da me zai yi tukwicin wannan kalaman da bai taba jin mafi gardinsu daga gare ta ba.
Ina jinki Hafsah, ki karasa don Allah... Ya fada da wata kankanuwar murya, muryar sa har rawa takeyi.
Yaya Azeez, alamarin na zuci ne, sirri ne irin na zuciyar mutum, da ba lallai a zahiri ya zama hakan ba. Zuciyar mutum,Birnin sa.(Sunan wani littafin TAKORI ).
Ina so in san wannan alamarin sosai, don in tantance ko irin wanda na ke fama da shi ne? Ni tawa zuciyar wani irin radadi ta ke mini in na tuno bana tare da HAFSAT-SUHAANAH, in na shafa na ji babu ita a gadon barci na. Daga sanda ta tafi Jimeta na koma gidan ni kadai, ni da zararre ba mu da maraba. A dakinta nake kwana a kan gadonta in lulluba da duvets dinta. Wadannan lausasan duvets din nata kala-kala. A kan Hafsah na san so na hakika, a kan Hafsah na san mutum na iya bada komai da ya mallaka don ya dawo da abin da ya rasa guda daya!
Hafsah youare special. I love that your tender heart and everything of you, and be rest assured that Abdulazeez lovesyou so much, to an extent Hafsah ......Nayi rantsuwa ki yarda da ni!Kada ki tambaye ni yaushe hakan ta faru, ni kaina ban sani ba. Wannan fushin da ki ka ce ina yi kuwa Hafsah? Let me put it in concret and tangible example for you; fushi ne irin wanda yaron da ke tsananin jin yunwa ke yi in an raba shi da jikin uwarsa ba tare da ya koshi ba. Kina tunanin wannan yaron zai karbi wani uzuri ne a kan uwar da ya riga ya san cewa tasa ce,bai da wata uwar sai ita,bai taba samun sukunin rabarta ba ne da niimomin da Allah ya mallaka masa tattare da ita?
Abdulazeez ya mance Hafsat ba ta gane wahalalliyar Hausa, she didnt get him right to where he wants to, cewa ta yi.
Ni bana jin hausain disguise, kuma ni ban haihu ba.
Ya ce Za ma ki ji ne. Kuma zaki haihun. Dole ki bude kwanyarki ki gane abunda nake nufi yau. Ni ma bana jin Dutch, not even Flemishballe in yi miki bayanin dana ke so ki fahimta.Shiyasa na yi miki da yaren dana iya kuma dole ki gane. Girl,bari in miki dallah-dallah toh. Ni Abdulazeez mijinki ne, miji kuma na aure, wanda Ubangiji ya dora miki nauyin dukkan hakkokinsa,amma Hafsat guduna kikeyi, a dalilin ki da ban sani ba, kina min rowar abin da ya zam halalina. Hafsat banda wata matar sai ke, ban iya neman mata ba kullum kuma ina rokon Allah kada ya dora mini. Tun a Sun-city ki ke min wannan azabar. Hafsah in ban zo wajenki ba ki gayamin wajen wa zan je? Shekaruna kusan talatin da hudu ban taba hutawa daga wannan ukubar ba. Ko babu soyayya ina da wannan hakkin a kanki. Hafsa ko kina so in kara kallo wata yar kwalisar in makale mata, in ce ina so in ba ita ba sai rijiya?
Yadda yake maganar yanzun cikin wani irin lallashi ne da shi kansa bai taba zaton ya iya ba. A rayiwarsa bai taba lallashin Muazatu ba sai dai ya cedo and donts.To ko wannan shi ne bambancin matar sunnah da budurwar waje? Shi kansa bai sani ba. Hafsat ta yi shiru, ilahirin jikinta ya mutu, wani irin chemistry na bin gabban jikinta. Ta tabbatar yau da Abdulazeez a gabanta yake zai samu abin nan da ya dade yana burin samu daga gare ta whatever their contract! Saboda ya gama samun duk wani weakness dinta.Kawarda zancen ta yi saboda sosai ta ke jin kunya, wata irin kunya da bata taba ji ta Abdulazeez ba, ko sanda yake gabanta. Kuma ba ta son zancen wata din nan da ya soko suna cikin hirarsu mai dadi.
Yaya Azeez bari zancen watayar gayuka ji? Ka gaya min duk irin gayun da kake so I will be doing.Mammah ta hakura ne? A muryarta akwai trembling (gargada) sannan akwai kuruciya, sokonci da kishi a fili duka a lokaci daya.
Dadi ne ya kashe Abdulazeez a kwancen da yake.Dadin Hafsat na kishinsa, ko da yake da dade da sanin hakan tun ma kafin ita ta san soyayyar tasa na farautar ranta.Amma bai nuna ba don kada ta ji kunya ta fasa hirar. Rikon wayar ya canza daga kunnen damansa zuwa na hagu. Yana yawan yin hakan in yana waya. Na bari Hafsah tunda ba kya so, kuma nima fa na fada ne wai in miki misali. Banda haka ma ni idona ai ya dade da dusashewa akan ki Hafsah, in ya ga mata ma rufewa yake yi.Da ba ta hakura ba za ta sakar miki mara ne har ta baki waya? Wannan over-discplinedMaman taki! Hummm!
Keni fa yau hirar mata da miji nake so mu yi Hafsah, irin wadda bamu taba yi ba, hirar realAbdulazeez dareal Hafsatin theirreal self! Ki bude baki ki ba ni amsa. Are you feeling what Iam feeling?
Hafsat ta daburce, wata irin daburcewa mai cakudeda jin kunya, ta wara ido sosai daga lumshe sun data yi tana kallon dama da hagunta da bakin kofa ko wani yana jin abin da Yaya Azeez ke cewa??? Hijabinta ta janyo ta rufe fuskarta tana ji masa kunyar. A take ta tuno abubuwa da yawa, wasu da suka faru a ‘Sun-City’, wasu a Rockview da halin da ta ke samun kanta a irin wadannan ranakun. In haka ne kuwa ita ma tana da wani extraordinary feeling a kan Abdulazeez wanda daga ita sai Ubangijinta suka sani, amma wani alamarin tsakanin mutum da zuciyarsa ne, ta ya ya zai ce sai ya ji?
Hafsah!. Ya kira sunanta. Kafin ta samu sukunin amsawa ya dora.
In ba ki ba ni amsa ba na rantse gobe zan dawo Nigeria!.
Gabanta ya fadi, in Abdulazeez ya dawo ya ce da iyayensa me ya dawo da shi? Ya fasa karatun? Bayan makudan kudaden da aka narkar a kan tafiyar daga iyayensa har gwamnatin tarayya?After all ba ta bukatar dawowarsa a yanzu bata gama planningda fuskar da za ta karbe shi ba a matsayin tabbataccenmiji a karo na biyu, wanda babu yarjejeniyar komai a tsakaninsu sai auren sunnah tsurarsa. Aure na har abada! Rayayye wanda babu ranar macewarsa sai ranar da rayuwar dayan su ta kare.
In haka ne ta yi abin da yake so don a zauna lafiya.
Don Allahkayi hakuri Yaya Azeez,ba sai ka dawo ba zan fada Allah.Ina jinki Ya fada a gajarce exhaustedly. Hafsat ta ja numfashi sannan ta runtse ido tace.
“I really have it for you alsoI mean the feelings.... and its just..just unexpressable!.
Ta fadi kowacce kalma dallah-dallah, daban daga jikin yar uwarta kamar mai koyon vocabulary.
Murmushi ya yi cikin mamakin yau Hafsat ke magana haka.
“Then let me come, and make itvivid to me, sai a banbance na wanda yafi tsanani tsakanin Abdulazeez da Suhaanah!. Ya fada cikin wata murya da ta kasa yarda ta Yaya Azeez ce.
Na yi alkawarin bayyanawar a duk ranar da muka hadu. Hafsat ta fada cikin jin kunya.
Yaushe ce wannan ranar Hafsa idan ba ki yarda na zo ba? Shekara daya ba nan kusa ba ce, Ive one year aheada gabana kafin na kammala. Jiranta zai zama kamar jiran ranar busa kaho a gare ni. Gaskiya bazan iya ba!.
Dauke wayar ta yi daga kunnenta na dan lokaci, tana mai karbar tasirin kalaman a cikin kowacce gaba ta gangar jikinta. Isthis what is calledLOVE? And the feeling of having it in return? In hakanshine soyayya ta hakika, to hakika ba abin da ya fi ta dadi da sanya nutsuwa a zuciyar dan Adam. Allah ya sani tana son Abdulazeez! Wayar ta mayar kunnenta, abin mamaki he is still onthe call.
Ya ce, Hafsa bude kunnenki ki ji
Kalaman da yake fada mata sun yi mata nauyi a cikin kwanyarta, wanda ya kai ta ga janyo hijabinta ta rufe fuskarta bakidaya kamar yana ganinta.
Mammah ta ba ta waya ne dama don Danta Abdulazeez ya kashe ta da dadadan kalamansa, ko don ya hana ta bacci da manyan maganganun sa? Ya yi formatting brain dinta ya zuba sababbin abubuwa da ba ta san da su ba a duniyarta?
Kin yi alkawarin duk ranar da muka hadu babu kunya? Kin yi alkawari it will bea day in history? In kin yi wannan alkawarin zan barki ki kwanta Hafsah kuma zan yarda in zauna!.
A yadda ta matsu da ta samu shakar numfashi yadda ya kamata, ba alkawarin da ba za ta iya yi masa ba yanzu. Don haka ta ce ta amince.
Ya ce, Then a good night kiss, irin na Rockview.
Wannan karon Hafsat ba ta da mafita banda ta kashe wayarta jin numfashi na neman fin karfinta. The Rockview memories overwhelmed her!Ita kadai ta ke murmushi mai zurfi bayan kashe wayar.
*****
Washegari sai da ta makara, makara ba yar kadan ba. Ana gab da rufe exam hall. Yau kam ta sa a ranta za ta kashe wayarta kafin ta kwanta. Abdulazeez a shirye yake da ya jawo mata dako (carry over) wanda ba zai taya ta wajen sauke shi ba. He is already what he wants to be in life! Ba ta tsammanin don ta zama mai (spill over) yana da damuwa. She is a goal oriented like him. After all zai iya jiranta ta gama su dora a inda suka tsaya tunda an sakar musu mara yanzu babu tunani da fargabar ranar karewar KWANGILA!
Kin kunna wayarta ta yi har bayan kwana biyu. Dawowarta kenan yau ta shiga dakin Mammah don ta sanar da ita ta dawo. Tana shiga ta ce. Kin ga Allah ki kunna wayarki ko wannan dan Anacen ya shafa man lafiya. Ina dalili zaabi a uzzire ni? Ni kuma ba zan ba ki tawa ba kamar yadda ya bukata, don ban ga dalili ba.
Murmushi ta yi ta juya ta fita a ranta tana fadin, Mammah kyale Yaya Azeez kawai. He just want to me to score zero, ko in cika musu answersheet da ABDULAZEEZ DAKATA .
Alhamdulillah! Yau Hafsat-Suhaana ta zana last paper dinta. Ta gama zangon farko na year 2, sun samu hutu na tsayin sati hudu, idan sun dawo za su shiga zango na biyu na (level two). Ta yi baccinta yau ta hantse har da munshari.
SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI
07030137870
*Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama*
Gaisawa suka fara yi ita da Hajiya Halima matar Controller, sannan Mammah ta fadi makasudin kiran nata, Ki turo min babarbariyar da ki ka turo ta yi wa Hafsat gyaran amarci Fannah takeko wa? Daga gobe zuwa jibi don Allah Maman Saadiyyah.
Toh!Tantabara sarkin soyyyah! Tsohuwar zuma ce ta tashi za a yi wa formerAmbasada gyara?Ko kuwa Hafsat ce ta haihu har zata koma babu gayyatar suna?
Ko daya. Addar nake so a kara gyara min kawai, ta koma masha Allah fiye da gyaran farko.
Dariya sosai Anty Halima ta yi. Ka ji uwa, kuma surukar zamani, wato a gyare miki yarki Abdulazeez ya sha shagalinsa!”
Salati Mammah ta saka tare da runtse ido. Ni Hajiya Halima yaushe za ki girma ne? Yau in da ni na ce zan yi ki ce na addabi tsoho, na ce a yi wa yara shi ma ya zama abin magana?
Sosai Halima ke dariya, To ita Hafsat har yau ba bayani ne? Ana neman shekara ta biyu fa.
Ki sanya su a addua komai sai Allah ya nufa.
Haka ne. Inj Hajiya Halima, Kada ki damu, Hafsat sai ta koma tamkar jiya aka kai ta. Zan yi magana da wadda ta yi mata na aure goben nan zan sa a kawo ta, ta zo Abuja yi wa yar Captain Bakari, kin san auren ya zo.
Au abin ya zo? Zumunci na da Haj. Munira ya yi rauni ne, tun dawowarmu nan ban samu na ziyarce ta ba, kuma ba ni da lambar wayarta, bana jin ta san mun dawo ma, ta zo wajena a Belgium da suka kai dansu karatu can. Tun daga nan ba mu kara haduwa ba.
Haka suka yi ta hira irin tasu ta aminai, sai da Hafsat ta shigo ta gaya mata ta yi baki, sannan suka yi sallama.
Mammah ta yi shiri kamar yadda ta saba duk dare ta nufi turakar maigidanta. Prof. Dr. Hamzah Dakata, agogo sarkin aiki wanda a gida ma ba ya hutawa. Bautawa aikinsa yake da karfinsa, lafiyarsa da lokutansa har zuwa lokacin marking takardun dalibansa yake yi. Hajiya Maryam ta zauna a gefensa, sassanyan turarenta ya bugi hancinsa, dole ya aje biro ya dube ta da sassanyan kallo, Maryama Amarya, kuma uwargidan Hamza Atiku ya aka yi ne?
Dariya ta yi ta juya masa idanu, Zuwa na yi neman alfarma, a yi wa Addah visa ta tafi America.
Hannayenta biyu ya riko cikin jin dadi domin hakika ta yi masa ba-zata. Bai zaci za ta barta haka da wuri ba duk da ya san za ta barta din, Sun samu hutun ne?
Eh, na sati hudu. A yi da gaggawa don ta samu ta yi ko sati uku ne. Jikinshi ya janyo ta yana fadin, Mairo yar albarka, na gode, nagode!.
Hajiya Maryam ta san Ambassador yana son Abdulazeez tun yana karami, amma ba ta kara sakankancewa da kaunar ba sai yau. Tukwicin soyayya mai yawa ta karba, har da kujerar makkah. Ya ce dukkansu su je su yi umrah, Suhaana ta tafi wajen mijinta sun dade rabonsu da Saudiyyah.
Don haka gabadaya gidan ba wanda ba a hada da passport dinsa ba. Haleem ne ya kai Hafsat yin tata visar babu wani cikakken bayani, shi Daddy yasa yayi processing visa din kagin su mika, duk da shima bai san me iyayen nasu suke shiryawa ba, an umarce shi ne kawai da ya ciccikeapplication din ya hada da informations din Abdulazeez wandaDaddy ya shi ya kuma ya kaitathumbprint. Daga nan ya mika nasu wajen yin na Saudiyyah.
A ranar mai gyaran jikin ta zo da yamma ta fara yi mata. Ta soma ba ta wasu abubuwa na ci da