Showing 12001 words to 15000 words out of 168255 words
ban da ya dauko shi ya kawo cikin family dinsa. Ita kuma Hajiya Maryam tana matukar son Habibah, son ne ya shafi abin da ta haifa, sannan tana tunanin in ba ta rike yarinyar nan ba ina za ta kai ta? Ba ta san komai da ya dangaci Habibah ba ba ta san daga inda ta fito ba, sannan in ta kai ta gidan marayu tana tausayin rayuwar da za ta taso a ciki. Za ta taso ne a shegance, a shegantata bayan ita ta yarda yarinyar nan ba shegiya ba ce da ubanta, akwai abin da ya rabo Habiba da mahaifinta. Me ya sa Daddy ba zai yi mata alfarma ba?
Hantsi na dagawa ta samu wayar Anti Safiyyah ta daga suka gaisa da tambayar lafiyar yara. Anti Safiyya ta ce, “Mai aikin babba ki ke so ko yarinya, ko budurwa?”
“Babba dai, wadda ta san ciwon kanta. Ban da wadda ba ta kai shekaru hamsin ba”.
Safiyyah ta ce, “To alhamdu lillahi an samu. Sunanta Azumi, ‘yar Sakoto ce, zan kawo ta ranar juma’a insha Allahu. Za a dinga biyanta Riyal dari biyu duk wata, duk irin hidimar da ki ke so ta yi miki za ta yi miki, ku dai tattauna a tsakaninku”.
“Na gode Safiyyah sosai. Na gode Allah ya kara zumunci”. In ji Mammah. Da haka suka ajiye wayar.
A cikin wannan hali na zaman doya da manja, zuciya ba dadi, Hajiya Maryam ta ci gaba da zama da mijinta a dalilin ‘yar mai aikinta. Ana i’gobe za su cika kwana bakwai da baro asibiti tunanin ragon suna (haqiqa) ya dame ta. A yadda Daddy ke kumbure-kumburen nan za ta doshe shi da zancen yanka ragon suna? Ta yi tunanin ta bai wa Salah ya sayo da kudinta kamar yadda ta yi amfani da kudinta wajen siya mata suttura, madara kam ya saya katan-katan kamar yadda ya furta, sai dai wani (positive) tunani ya shige ta. Bai kamata tun yanzu ta soma yin gaban kanta a kan yarinyar ba, dole ta ba shi hakkin da yake cewa tana ‘forcing’ dinshi na zaman uban yarinyar yana so ko ba ya so, in ta sayi rago ta yanka mata ya tabbata ita ce uwarta, ita ce ubanta kenan,
“You must be the father you don’t want to be Daddy!”. Ta fada a fili.
A daren ranar ta cancada kwalliya, turare kala-kala ta feshe jikinta da shi, a gobe ta ke sa ran za a kawo mata sabuwar mai aikin. Ba za ta iya barin Baby ita kadai ba, don haka ta kira Usman da Isma’eel da Halim ta jere su a gadonta ta ce su kwana a nan.
“Isma’el ba ka da nauyin barci, ka kula da baby in ta motsa. Ga madararta, ga ruwan zam-zam dinta ka duba pampers akai-akai”.
“Dont worry Mammah, je ki lallasar mana Daddy ya daina fushi da ke. Mammah tausayinki nake ji, ya ce wai wata sabuwar mata zai kawo mana ke kin daina sonsa sabida jaririya”.
Murmushi ta yi, ta ce, “Isma’el Allah ne ya halatta masa auren mata har hudu in yana da iko. Ba saboda jaririyarmu ba ne. Kuma ba saboda ita yake fushin da yake yi ba, ni ce na yi masa laifi”. Ta fadi hakan ne don kada su fassara mahaifin nasu a matsayin mutum mara tausayi da adalci. Wanda tuni hakan ya fara darsuwa a zuciyar Isma’el tunda ya fi Usman da Halim wayo. Amma yanzun ya yarda da abin da Mammah ta ce, sai dai ko kusa ba ya son Daddy da wata macen bayan mahaifiyarsu. Akwai abokinsa a makaranta a Abuja da yake ba shi labarin cewa Mamansa ta rasu wajen haihuwarsa a hannun (step-mother) dinsa yake, kullum sai ta dake shi ta sa babansa ya dake shi, kuma ba ta bashi abinci sai mai aikinsu ce ta ke ba shi. Wannan labari da Salim ya ba shi ya tsaya masa a zuci, ba ya so ya ji an ce za a kara aure.
Da haka Mammah ta wuce ta barshi yana tunani, yana kallon Baby da ke barcinta cikin kwanciyar hankali a cikin kyakkyawan gadonta da ke gefensu. Usman da Halim tuni sun yi barci.
Mammah ta yi sallama a kasaitaccen (bedroom) na Ambassador Hamza Dakata, tuni ya kashe fitila ya rufe kwamfuta yana azkar din barci, dole ya amsa sallamar don bai zaci ganinta a lokacin ba. Kwana shida kenan rabon da su hada makwanci, in ya ce ba ya kewar Maryam ya san ya yi babbar karya ya kwana da yunwa. Mace daya tamkar da dubu wadda ta mamaye filin mata goma a zuciya da ruhinsa, ta haifa masa sanyin idaniya ABDUL’AZEEZ HAMZAH ATIKU, in ya ce zai hada matsayinta da na wata mace da sunan aure ya san ya fada ne kawai don ya ji dadin bakinsa ko ya huce haushi amma Maryam ta wuce nan a zuciyarsa.
Jin ta ya yi ta kwanta a gadon bayansa ta sanya tausasan hannuwanta ta rungume shi, hawayenta na sauka saf-saf a kan kafadunsa. Runtse ido ya yi wani sanyi na ratsa zuciyarsa. Ta ja bargon da yake kokarin rufawa ta ajiye a gefe.
“Ka yi hakuri Daddy don Allah ka yi hakuri, na yarda laifina ne, na kasa hakura da tsarinka in yi maka biyayya. Na yi ne don neman lada a wurin Ubangiji ba don in bata maka rai ba Daddy”. Ta fadi cikin shesshekar kuka mai motsa zuciya balle zuciyar masoyi. Kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya dago ta ya juyo suka fuskanci juna.
“Why Maryam? Me ya sa ki ka zabi farin cikin wasu bare da ba ki hada alakar komai da su ba a kan nawa? Na dade ina mamaki, ina tambayar kaina anya Maryam dina ce? Ta bar ni kwana shidda ba tare da ta san halin da nake ciki ba? Ya ya nake rayuwa? Me nake ci nake rayuwar? Anya Maryam ke ce???”
Hawaye ta ke sharewa sosai,
“Tunda ka gaza fahimtata Daddy, ka kasa mara min baya mu ceci rai, mu yi jihadin rikon maraya tare, mu yi domin neman lada a wurin Ubangiji na amince ka fadi duk yadda ka ke so a yi da jaririyar nan na maka alkawarin zan bi, in har za mu koma rayuwarmu ta baya ka kuma fasa auren da ka ke cewa yara za ka yi. Ba zan iya hada ka da kowacce mace ba Daddy ‘depression’ zai kama ni”.
Bai san sanda dariya ta kwace masa ba, ya yi sosai sannan ya gintse fuska, “Ina nan fa ina jiyo laccar da ki ke wa Isma’el yaushe ki ka juya ta a baibai?
Kin ce Allah ya ba ni iko, yanzu kuma kin ce ‘depression’ zai kama ki, dole in yi aure Maryam don in samu mai kula da ni, ke kuma ki ji da ‘yar da ki ka fi so a kaina. Me ye laifina a nan?”
Ta share hawaye da tishu ta ce.
“Ai na ce ka fadi yadda ka ke so a yi, ko cewa ka yi in jefa ta a kwatami zan jefa tunda ba ka sonta”.
Ya hade fuska, “Ni na ce miki bana sonta? Me ta min? Kawai kin kasa fahimtata ne ke ma, amma a bar zancen haka, kowa ya zauna a kan ra’ayinsa. Amma abubuwan da ki ka dauko hanyar yinsu ba zan lamunce su ba, dole ki ba ni dukkan kulawar da ki ke ba ni a baya. Ban amince ki canza ko kwaya daya ba, bana son zama da masu aiki amma na amince ki daukar mata Nanny zan biya ko nawa ne. Ki daina hada lamarina da nata, daga sanda na dawo office karfe shidda na yamma har zuwa wayewar gari in fita (office) lokacinki nawa ne da yarana ki bar ‘yarki can wajen mai rainonta. Kuma ki ci gaba da bincike a kan danginta, duk ranar da suka bayyana za ki mayar musu da ‘yarsu”.
Gyada kai ta yi cikin hadiyar zuciya, “Na amince Daddy, wallahi na amince. Na gode, Allah ya kara rufa maka asiri duniya da lahira. Alfarma ta karshe da nake nema ka yi mata haqiqa, ka sanya mata sunan duk da ka zaba, ka yi mata khutbah gobe da safe kafin ka wuce office, already na nemi Nanny din wallahi, gobe Safiyyah za ta kawo ta........”.
Ta cika shi da surutu, bayan shi kuma cike yake da wata irin kewarta, janyo ta ya yi kawai ya sanya cikin kirjinsa, ya rufe su ruf da bargon mai tsananin taushi da kamshi. Can kusan makoshinsa ya ce,
“Ke don Allah ya ishe ni haka, gobe zan yanka mata ragon...”
Da haka hirar ta kare, ta koma mai ma’ana da kara dankon kauna. Hakika ta yi kewar mijinta, shi ma Daddyn ya yi kewarta yadda harshensa ba zai iya fassarawa ba, sai dai ‘emotions’ dinsa a daren ranar bakidayanta sun nuna mata hakan.
“Daddy kenan! Zuma, ga zaki ga harbi”.
Maryam Dakata ta fadi cikin zuciyarta cike da shaukin mijinnata, dan uwanta, uban ‘ya’yanta.
*****
Washegari da Salah ya sauke shi a office ya ba shi umarnin ya sayo babban rago a yanka da sunan ‘yar Mammah, da ta ce ta ba shi zabin sunan da za a saka wa jaririyar, cewa ya yi shi fa babu ruwansa. Ta sa wa ‘yarta sunan da ta ke so idan kuma haqiqar da ya yi mata ma ba ta gode ba, to don Allah ta kyale shi haka. Da yake lallaba shi ta ke, sai ba ta ja da nisa ba. Ta mika masa bebin tana marairaicewa.
“To don Allah amshe ta ka yi mata khutbah da sunan Addah, wato Hafsatu”.
Harara ya dalla mata, “A dalilin me? Ga sunan uwarta za a ce na uwata zan saka? Ba gara ki sa mata Habiban ba don a gane danginta da sauri?”
A ranta ta ce, “Bakinka ya sari danyen kashi. Hmmm! Ko an gane ba wanda zan bawa, ‘ya ce Allah ya riga ya ba ni, iyayena da ‘yan uwana sun isa su zame mata dangin”.
Ta sake kwantar da murya, “Daddy, ba zan taba mance sunan uwarta ba, don Allah ka sa mata Addah, don ta biyo kyawawan halayenta”.
Yana cin magani ya amsa, ya zauna a bakin kujera ya kai bakinsa saitin kunnenta yana yi mata khutbar. Dadi ya kashe Mammah a zuci.
Bayan ya fita da awanni uku Anti Safiyya ta yi sallama, matar biye da ita. Kyakkyawar tarba Hajiya Maryam ta yi musu. Bayan sun ci abincin rana suka soma tattaunawa. Azumi ta amince za ta taya Hajiya Maryam ayyukan gida, za ta yi rainon Hafsat da amana. Shekarunta arba’in da biyar, nitsattsiyar mace sosai. Mamma ta miqa mata Hafsat din da ta yi wa lakabi da SUHAANAH kasancewar sunan mahaifiyarta ne, a take Azumi ta karbe ta ta goye. A gaban Anti Safiyyah Hajiya Maryam ta zaunar da Azumi a kan kilishi, ita da Anty Safiyya suna kan kujera ta soma magana cikin nutsuwar da Allah ya halicce ta da ita.
“Azumi ga ni ga wadda ta kawo min ke, kawata Hajiya Safiyya, na daina zama da ‘yan aikin da ban san asalinsu ba. Tsakani da Allah ki gaya min daga ina ki ka fito a Nigeria, da inda iyalinki suke. Zan kuma yi bincike idan kin yi min karya”.
Anty Safiyya ta gyada mata kai, “Haka ne kwarai. Azumi muna sauraronki”.
Dattijiyar ta gyara zama cikin hankali ta ke magana.
“Daga jihar Sokoto na zo Saudiyyah, idan na yi miki karya Allah ya hukunta ni daidai da abin da na aikata na yaudara”.
Mammah ta ce, “Sokoto wace unguwa? Gidan wa?”
“Unguwar Mabera, gidan Malam Isuhu Maishanu, mun zo Saudiyyah ni da mijina muna neman na kanmu a Shari Mansur shekara biyar a baya, muna kawo goro da sauran abubuwan da mutanenmu ke bukata, an sha kama mu har sau biyu ana mayar da mu Najeriya muna dawowa, kamar yadda ki ka sani in ka dandani zaman saudiyyah ba ka iya bari da sauki, to hakan ce ta faru da mu ni da maigidana.
Shekarar baya ya rasu ya bar ni da ‘ya’ya biyar namiji daya hudu mata. Namijin Yusha’u ya jima da yin aure a Maishanu. Na aurar da mata biyu a can gida Sokoto, ta ukun wato Harira da autar Ladidi kuma suna hannun kanwata a Talata Mafara. Idan akwai karya cikin abin da na fada Allah ya hukunta ni da laifin yaudara da cin amana”.
Anty Safiyya ta dafa kirjinta da hannunta na dama ta dan fiddo mata ido ta ce,
“Ni ‘yar Sokoto ce gaba da baya, Iyayena da kakannina, don haka zan bincika abin da ki ka ce daga yau zuwa gobe. A unguwar Nakasari da unguwar rogo iyayena suke na san Mabera sosai”.
Azumi ta gyada kai alamar amincewa.
Hajiya Maryam ta nisa, sannan ta dubi Azumi, “Abin da ya sa na yi miki wannan titsiyen ba rashin yarda bane, mai aikina ta baya ce...........” Tiryan-tiryan ta ba su labarin tun kawo mata Habiba Abuja zuwa yau. Azumi ta sakko Hafsat ta kara rungume ta a jikinta, ta sa mayafinta ta kara rufe ta sosai daga ita har Anty Safiyya sai da suka yi hawaye. Safiyyah ta karbi Hafsat ita ma ta rungume tana kallon kyakkyawar fuskarta, ta ce da Hajiya Maryam.
“Na rantse da Allah na dauka haihuwa ki kai, ganin yarinyar nan fara tas kamar ‘ya’yanki. Kina da tsayi, kina da dan jiki ba a fiya ganewa ba idan irinku nada ciki. Allah ya ba ki ladan wannan jihadi na ceton ran maraya da sadaukarwa saboda Allah”.
Murmushi ta yi, ta ce, “Amin”. Amma ba ta gaya musu halin da ta ke ciki da maigidanta a kan lamarin ba. Ciki ba don tuwo kawai aka halicce shi ba, wani abun yana bukatar sirri.
Bayan tafiyar Safiyya, Azumi ta goye Hafsat wadda Mammah ta kira (Suhaana) suka ci gaba da ayyukan gida tana nuna wa Azumi kan komai na gidan. Ta nuna mata dakinta. Kwarai dattijuwar mai hikima da azanci ce, har girkin dare ita ta yi, kuma Hajiya Maryam ta yaba, tuwon shinkafa da miyar busasshiyar kubewa da ta ji naman ragon sunan Hafsatu. Sai Mammah ta yi na Daddy kawai, su Isma’el suna ta santin girkin Baba Azumi, yadda Mammah ta koya musu su dinga kiranta.SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI
07030137870
*Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama*
Auren kwangila
Page 3
Karfe shidda daidai na yamma Salah direba ya yi (parking) a cikin (gate) din gidan Ambasadan Najeriya a kasar Saudiyyah Professor Dr. Hamza Atiku Dakata, Hajiya Maryam ta fito rungume tsam da kyakkyawar bakwainin jaririyarta cikin farin shawul mai tsananin taushi. Salah ya biyo ta da jakar ‘shopping’ din kayan jarirai da abubuwan bukatar su da ta yo a kasuwar (Baaba Sheriff), ta karasa cikin falon bayan ta ture kofar gilashin (sliding door) da ta raba harabar gidan da tangamemen falon wanda ya ji kayan alatu da ababen more rayuwa iri-iri.
Daddy ne zaune a kan kilishi cikin ‘ya’yansa uku yana duba littattafansu na makaranta, don ganin halin da kwakwalwar kowannensu ke ciki. Halim yana kan cinyarsa da nashi (drawing book) din, a yadda ya fahimta Isma’el shi ne mai matsala, yana da rauni kwarai a kan darasin lissafi (mathematics). Nasiha yake masa sosai cikin hikima kan ya maida hankali ya iya lissafi domin shi ne kashin bayan ilimin boko. Mammah ta yi sallama suka mike da gudu suka yi kanta. Fadi ta ke,
“Ku yi a sannu kada ku kada kanwarku, kun ga ba ta da lafiya”.
A sannu Daddy ya daga ido ya dube su, ya soma dan yamutse fuska, suka hada ido da matar tasa. Ta fahimci ya canza fuska, gwiwoyinta suka yi sanyi, amma a haka ta karasa gare shi ta zauna dab da shi ta miqa masa jaririyar, kamar ba zai karba ba ko me ya tuna kuma ya karba, ganin Usman ya danne Isma’el duk a kokarinsu na kowanne so yake a bashi jaririyar ya dauka, sai ya karba don ya raba fadan, amma ba cikin dadin rai ba.
Sama-sama ya kalli ‘yar sai kuma ya mika mata, ya tambaye ta,
“To yanzu ya za ki yi da ita? Bana jin gidan marayu na Saudi-Arabia za su amshe ta, tunda mu ba ‘yan kasa ba ne”.
Mammah cikin mamakin sauyin da ta gani a tare da Daddy farad daya, ta ce da shi cikin kwantaccen sauti.
“Wai da so nake ka yi min izini in sha magani in samu ruwan nono in shayar da ita”.
Girgiza kai ya shiga yi,
“Wasa ne wannan, ki shayar da dan da ba nawa ba?”
Kamar za ta fashe da kuka ta ce, “Daddy........”
Ya dakatar da ita, “Please don’t argue with me Maryama. Ki maida ita wajen dangin mahaifiyarta, ba zan iya riqon dan da ba nawa ba balle in kasa yin adalci tsakaninsa da ‘ya’yana Allah ya tuhume ni, musamman rikon maraya. Na yi miki alkawarin zan dauki nauyin iliminta har zuwa digiri na kololuwa idan tana so a ko’ina ta ke cikin duniya. Amma ba zan hada ta da ‘ya’yana in rike ba”.
Hajiya maryam ta fashe da kuka, “Don Allah Daddy kada ka yi min haka... ina sonta, ina son uwarta ina son diya mace... Allah bai ba ni ba... don Allah Daddy ka yi min alfarma ka barni in rike ta koda wannan itace alfarma ta karshe da zaka yimin a rayuwa”.
Ta daga hannuwanta biyu gare shi tana kuka tana roko.
Dukkan yaran ma kuka suka sa suna rokonsa har Halim,
“Daddy ka bar mana don Allah, muna so, kada a kai ta wani waje ta mutu kamar yadda Mamanta ta mutu, do us a favour”. Inji Usman.
Suka kama babyn duka suka kankame, ita kuma da ta ji matsa ta canyara kuka da muryarta kamar gyare don zaki. Su biyar din duka kuka da hawaye share-share.
Sakin baki Ambasada ya yi yana kallonsu, kafin ya ce “Na shiga ukuna. Ku dakata, mu yi magana ta maslaha”. Ya fada yana daga hannu irin na saranda. Duk suka dakata suna share hawaye suna hadiyar zucci.
“Zan bi ra’ayinku tunda kun rinjaye ni, amma da sharadin ban yarda Mammah ta yi (breast-feeding) dinta ba, a nemi ‘alternative”.
Sai duk suka juya suna kallon Mammah don jin