Showing 42001 words to 45000 words out of 168255 words
ta kama shi rike da macen da ba tashi ba, rike da macen da ba su halatta mashi ba. Bayan ture Mu’azatu da ya yi daga jikinsa har dada ja baya ya yi ya sanya rata sosai a tsakaninsu. Hannunsa na kyarma ya amsa wayar Mammah.
“Kana ina?”
Ta tambaya cikin muryarta mai sanyi. Kunuwanta na zuko mata kukan Mu’azatu.
“Ina... ina... office Mam....mah...”
“Idan ka gama da ita, to ka zo ka gana da ita wannan ita ma. I think is high time ku fara fahimtar juna lokaci yana kurewa”. Ta kashe wayarta tare da sakin tsaki, “Me ake da matan bariki? Bin namiji har ofis don rashin mafadi?” Ta fadi cikin bacin rai da tafasar zuciya.
Anya wannan yarinyar ba za ta zame wa Hafsat barazana ba in an yi auren nan? Anya da gaske Abdul’azeez yake zai iya rabuwa da ita? Tunanin da ya cunkushe zuciyar Hajiya Maryam kenan.
Shi kuwa Abdul’azeez a sanyaye ya ajiye wayar, kalaman Mammah tas! A kunnen Mu’azatu, kamar da gayya ma Maman nashi ta fada don ta ji, kamar ta bugo da gayya ne don sanin cewa suna tare a lokacin, ta tabbatar mata da abin da ya gaya mata. Kafin ya ankara sai ganin Mu’azatu ya yi ta kai bakin kofa ta kama ‘handle’ za ta murda. Yunkurawa daya ya yi, Mu’azatu ta ganshi gabanta ya kare kofar, ya sha gabanta. Kokari yake su hada idanu, amma ta ki. Kuka kawai ta ke yi. Ta gama gane irin auren da ake son yi masa, irin na yarinya (sweet 16) din nan da (Proffessional) wanda ya gama mallakar hankalin kansa, to ita zai rainawa hankali? Kamar shi za a yi wa auren dole idan ba yana so ba? Ko macen da ta yi karatu irin nasa ana yi wa auren dole balle shi namiji? Shi ne ya zauna yana tsarata yana jawo mata ayoyi shi ga Ustazu? Da wata makirar Mammansa mai muryar karuwai.
Cikin tsananin fusata ta dube shi, “Ka ba ni hanya in wuce Malam, lest you regret knowing me (don kada ka yi nadamar sanina”.
“Minti goma za ki kara min kacal, zan ba ki hanyar...”
Cikin gunjin kuka ta ce, “Bana son kara jin kowacce kalma daga gare ka, Allah ya hada kowa da rabonsa.....”
Ya runtse ido. Ji ya yi saukar kalaman tamkar digar dalma a zuciyarsa.
“Duk kokarin da na yi da wanda nake yi da wanda zan yi DOMINKI abin da za ki ce min kenan Mu’azatu? A halaka fa zan saka kaina don in tsira da ke Mu’azatu...”
Ta zame kasa, kan gwiwoyinta ta kifa kai tana kuka. Shi ma ya bi ta ya durkushe.
“Wallahi zan aure ki Mu’azatu komai rintsi. Ki barni in yi auren don in zauna lafiya da iyayena. Na yi miki alkawarin na SHEKARA DAYA ne da wasu watanni, lokacin kin kammala BL dinki”.
Ta dago rinannun idanunta jike da hawaye, ta dube shi. Bai iya karya don ya burge ba! Wannan halinsa ne da ta dade da sani. Ba ya yi maka karya don ya faranta maka, kai shi kwata-kwata a halayyarsa babu karya, yana fadin abin da ke zuciyarsa ne kawai ba tare da tunanin zai yi maka dadi ko akasinsa ba. Tana son Abdul’azeez, tana son komai nasa, in ta ce za ta iya barinsa ga wata mace ‘yar uwarta, mai halitta irin tata data tabbata da cewa ba ta fita da komai ba ta fadi ba nauyi. Abin da ba za ta iya ba shi ne, tarayya da wata a son nasa, ko mallakarshi tare da wata.
Sai ta yi shiru da kukan tana goge hawaye, tana hadiyar zuciya.
“Kin amince da abin da na fada Mu’azatu? Zan yi auren, zan rabu da ita a lokacin da iyayenki suka shirya aura min ke, zan aure ki”.
Kallonsa ta yi cikin ido, tana kara jin wutar sonsa na fizgarta, losing him easily is not easy (rasa shi cikin sauki ba abu ne mai sauki ba). Ta samu muryarta na fita cikin tangardar harshe,
“Amma... amma..... ka san ba zan iya hada ka da wata ba ko? Ba zan iya zama da kishiya ba...!”
Girgiza kai ya yi, “Ni ma ba zan iya zama da mata biyu ba. I know... na ce miki rabuwa da ita zan yi in lokaci ya yi, ki yarda da ni, ki amince da kalamaina. Bana magana don in bata lokacin ki da nawa. Ungo hannuna mu kulla alkawari...”. Ya mika mata karamin yatsansa, yana kallon cikin idanunta da yanayin da ta ke masifar so.
Wani tattausan murmushi ya subuce mata. Ta mika nata karamin yatsan, suka sarke su suna jifan juna da wani mayataccen murmushin SO. Sun amince an halicce su ne domin junansu. Don su zama abokan rayuwar juna, babu wata SUHAANAH da ta isa ta shiga tsakanin wannan soyayyar.
*****
To mai karatu, kai ka yarda da hakan? Anya kaddarorin rayuwa suna tafiya yadda muka tsara su ne? Anya Abdul’azeez bai yi kuskure ba? Abin da yake shirin yi me sunansa? Bravity ga Mu’azatu? Dishonestness ga Mammah? Unfairness ga Suhaanah? Ko ko me yake nufi???
****
Mu karasa a littafi na 2, kada ku damu, tare suke. Taku har abada
Sumayyah Abdulkadir
Buk 2
SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI
07030137870
*Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama*
Sanin cewa Mammah na jiransa a gida ya sa ya ki shiga gidan da wuri. Bayan rabuwarsa da Muazatu ya tuko mota a hankali kamar wanda kwai ya fashewa a ciki, ya taho gida. Da ya zo kofar gidan bai karaso ba ya kashe motar daga nesa, ya kifa kai a kan sitiyarin motar ya rufe idonsa. A wannan dan lokacin ya tsara komai, ya tsara kalaman da zai yi wa Suhaana amfani da su. Ya yayyafa wa zuciyarsa ruwan sanyi a kan ta rage tsanar yarinyar, ta sake da ita yadda za ta fahimci duk abin da yake nufi. A kananan shekarunta yana da tabbacin shawo kanta ta yarda da tsarinsa ba zai yi masa wuya ba.
Sai da ya tabbatar ya shirya kalaman a kan harshensa ya yi bitarsu sun zauna sosai, sannan ya tashi motar a hankali ya karasa gida.
Mammah da ke dokon shigowarsa tana jin sanda maigadi ya bude masa get ya shigo ya adana motar a mazauninta. Ya tattaro wayoyinsa da brief-case hadi da kamfutar laptop ya fito. Yana rataye da falmaran din bakar suit din jikinsa a kafadunsa. Bai yi tsammanin ganinta a falon ba, don ya san karfe tara ta ke shiga barci, yanzu kuma tara har da rabi.
Ya sanya a ransa Baba Azumi zai sa ta yi masa magana da Addar, don haka ya shigo kansa tsaye.
Ta cika ta yi fam a kan kushin din falon, ya ja ya yi turus! Da suka hada ido, ta sassauta fushin da ke kan fuskarta, cikin sanyin murya ta ce, Na dauka ba ka kai wa magriba a waje in ba da wani muhimmin case a hannunka ba?
Ya nisa a hankali, Yi hakuri Mammah wallahi baki na yi suka tsayar da ni, sai yanzun na samu kaina.
Ta so ta ce da shi, Baki ko budurwar banzarka? Ta ga cewa shiga personal-lifedinshi ba girmanta ba ne, sai kawai ta mike ta nufi hanyar turakar maigidanta tana fadin,
Ka je study room Addar za ta zo yanzu.
A ransa ya ce, Ai a bari na ajiye kayan hannuna, na ba wa cikina hakkinsa, na dan yi freshen up kada ta ganni a jigace haka ta san cewa ta shigo rayuwata, ta takura ta da yawa.
Ita dai Mamma ta yi wucewarta, shi kuma ya nufi dakinsa.
Sai da ya gama duk abin da zai yi, ya yi wanka ya shirya cikin T. Shirt mara nauyi (black colour), an yi rubutu da farin fenti dara-dara (ARMANI). Ya hada da bakin wandon (jeans), ya taje sumar kansa, ya feshe jikinsa da turaren Eternity Moment.Zuciyarsa ma na hango masa EternityMoment dinsa da Muazatu kamar yau ne, in har yarinyar nan ta yarda su rufa wa juna asiri.
Ganin karfe goma na dare ya sa shi yin saurin fitowa ya janyo kofar dakin. Ya karasa cikin gidan ya shiga dakin Baba Azumi da zummar ya tura ta ta kira Suhaanar. Ya yi sallama daga bakin kofar, ta amsa tare da yi masa izinin shigowa. Lekawa ya yi kadan yana fadin, Ba ki yi bacci ba?
Sai ya ga Suhaanar kwance bisa cinyoyinta tana lallabe mata sassalkan gashin kanta.
Ba mu yi ba, muna dakon dawowarka ne, sai kuma Adda ta ce in yi mata kalba kafin ka dawo.
To ga ni na dawo, kuma ina jin barci. Ku yi hakuri da kalbar nan haka.
Suhaanah ta mike ta lalubi dankwalinta ta daura. Ya wuce study room din da Mamma ta yi umarni, ya zauna yana jiranta yana kuma duba agogon hannunsa.
Hafsat ta dubi Baba Azumi cikin damuwa, Idan na je bayan ina wuni sai me zan ce masa?
Baba Azumi ta juya kai cikin murmushi, Ni ma ban sani ba.
Haba Baba Azumi, ba ku koya min abin da zan ce ba za ku tura ni in yi hira da shi? Ta fada kamar za ta yi kuka.
Baba Azumi ta kafe ta da ido, Ni da wa kenan?
Ta yi shiru, ta sunkuyar da kai. Jikinta ya bata tayi rashin kunya.
Ita me ya sa ba ki yi mata wannan tambayar ba, sai ni marainiyar wayonki ko?
Yi hakuri.
Toh, tashi ki je yana jiranki, kin ji ya ce bacci yake ji.
Ta mike a kasalce ta yafa mayafin abayar Oman ruwan makuba da ke jikinta, kusan shigarta kenan dogayen riguna kala kala da wuya ka ganta da atamfa ko leshi sai in zasu Kano, a cewarta zani yana mata wahalar daurawa shikuma lace nauyi yake mata, ta nufi dakin karatun nasu.
Kanta a kasa ta yi sallama ta shiga. Ya dago a hankali yana kare ma sigarta kallo. Doguwa ce, siririya, kamannin Habiba sun kara fitowa a jikinta, sai dai zaa kira ta mai kuruciya da gogaggen jiki fiye da Habiba sanda ta ke raye. Kuma Habiba ta fita kaurin jiki. Kwakwalwarsa ta soma daukan caji tana tuno masa wata hira ta karshe da ya yi da mahaifiyarta.....
Rai-rai-rai hirar ke dawo masa... anya tunaninsa a kan Addah gaskiya ne? Hafsat BA SHEGIYA BA CE... Inda amana shi zai gaya wa kowa cewa da ubanta. Sai dai me? He is not after that (ba wannan ne a gabansa ba), tashi rayuwar ce, ba ruwanshi da rayuwarta.
Ta dade da zama, ta gaishe shi bai ji ba. Ko ya ji bai amsa ba, ba za ta iya tantancewa ba.
Ba ki iya gaisuwa ba? Ya tambaye ta bayan ya dawo daga duniyar tunaninsa.
Na ce ina wuni tun dazu ba ka amsa ni ba. Ta fada fa accent dinta mai nuna har yanzu Hausar ba ta gama daidaito a bakinta ba, yaren Dutch (flemish) ya riga ya daddatsa harshenta.
Taushin muryarta kawai ya kara masa kwarin gwiwar za ta amince da duk abin da ya zo da shi, akwai innocence intonationa cikin muryarta.
Sake gaisuwar zan amsa yanzu.
Ta dan saci kallonsa don tabbatar da shi din ne Yayan su Halim din nan, ko ba shi din ba ne? Wancan ko a murya ba shi da kirki, wannan a cikin muryarsa akwai sassauci.
Ina wuni?
Lafiya lau, kun wuni lafiya?
lafiya alhamdulillah.
Ya yi dan jim kafin ya ce, Mammah ta sanar da ke aure za ta yi mana ko?
Ta sanar da ni. Ta amsa kamar cikin rada, ba don ya kasance cikin masu kyakkyawan ji ba, da ba zai ji ta ba.
To ke me ye raayinki?
Ba tare da ta dago ta dube shi ba, ta amsa. Hawaye nuna son ci kowa a idanunta.
Ni ba ni da wani raayi sai nata, ni abin ikonta ce, ni mai biyayya ce ga dukkan umarninta.
Sai ya ji yar kunyar kansa ta kama shi. Ba ta haife ta ba, shi ta haifa, ita a shirye ta ke da ta yi mata biyayyar, shi da ta haifa ya gaza.
Shiru ya ratsa, kafin ya kira ta a hankali, Hafsah!
Wani irin sauti ne mai taushi da ba wanda ya taba kiran sunanta da shi a duniya, don haka ta dago don ganin wanda ya kira ta da shi din. Abdulazeez Hamzah Dakata ne.
Like father like son.
Ta fada a zuciyarta. He looks so much like his Dad.
Ba ta zurfafa kallon nasa ba, ta sunkuyar da kanta, ba ta zaci yana da sassauci haka ba a yadda ta sanshi a baya, duk da dai ta fahimci a kanta ne kawai yake zama tough din a kan sauran kannenshi ba haka yake ba, shin ko hakan na da nasaba da cewa don ita ba jininsa ba ce, ba ta da mahaifi? Za ta so watarana ya amsa mata wannan tambayar.
Mene ne babban burinki a rayuwa? Ina nufin bayan auren da Mammanki ke son ki da shi, me ki ka fi so a rayuwarki?
Ta dan daga kanta sama alamar tunani, kafin kalaman su fito a nitse daga bakinta.
In ci gaba da karatuna, karatu mai yawa har PhD.
Ya tsaida idanunsa a kan ta.
Sai kuma me?
Ta dan yi nuku-nuku ta kasa fada sai motsa baki ta ke yi.
“Hafsah feel free with me, bayan matsayina na Yayanki ni din kuma yanzu mijinki ne in Allah ya yarda. Ina so ki saki jiki da ni ki gaya min me ki ke so a rayuwarki komai wahalarsa ko tsaurinsa?
Ta dan samu nutsuwa kadan, ta waiga ta tabbatar babu kowa cikin dakin karatun, daga su sai Allah! Ta saci kallonsa kadan, sannan ta ce, Ina so....inaso in nemo mahaifina a duk inda yake, na san mahaifiyata ta rasu, Halim ya taba gaya min ta rasu ne wajen haihuwata, amma shi baa sanshi ba, ba a san inda yake ba. Na sha tambayar Mommah sai ta ce in bar zancen sai na yi shekara goma sha takwas, yanzu kuma shekaru na sha bakwai.
Abdulazeez ya nutsu yana saurarenta, da ta gama, ya sarke yatsunsa cikin junansu, yana kallonta kanta a sunkuye. Da kyar yake gane abin da ta ke cewa da Belgian harshenta, amma duk da haka yana ganewa, ya ce.
Hafsa, na ji dukkan bayaninki, na kuma fahimta. Na farko na amince zan barki ki ci gaba da karatu, da kaina zan cike miki JAMB da ake yi a nan Nigeria, am sure za ki haye daga nan zan kai ki jamia ki zabi duk abin da ki ke so ki karanta. Burinki na biyu ganin mahaifinki ko?
Ta daga kanta a hankali tana wasa da yatsun hannunta.
Na yi miki alkawari ni da kaina zan nemo miki shi insha Allahu. Na san garin da yake.
Ta dago kanta da sauri, ta ware manyan idanunta a kansa. Amma ta kasa magana.
Da gaske nake Hafsah. Har yayye ne da ke guda uku, amma ban san maza ne ko mata ne ba.
Kawai sai ya ga hawaye ya gangaro kan kundukukinta, masu dumi, wasu na korar wasu.
Mamaki ya kama shi ainun, amma bai bar hakan ya nuna a kan fuskarsa ba.
Na yi tunanin abin da za ki ji dadi ne, amma sai in ga kina kuka?
Ta sunkuyar da kanta, sannan ta share ambaliyar hawayen da bayan hannunta.
Ni ma ban san me ya sa ni kukan ba, amma watakila kukan farin ciki ne.
Ya ce, Yadda zan zama sanadin farin cikin nan naki, nake rokon ke ma ki zama sanadin nawa farin cikin da ba mai samar da shi gare ni sai KE!
Ta dago jikakkun idanunta ta kalle shi.
Ni me nake da shi da zan saka maka wannan farin cikin da za ka ba ni? Iya tunanina ba ni da komai.
Ya sauko daga kujerar da yake kai, ya zauna dabas a gabanta. Idonsa ya kai ga yatsun hannunta da suka sha adon jan lalle yan sirara da su. Ya dawo da kallonsa kan fuskarta cikin nutsuwa, ya ce.
Ba abin da za ki ba ni Hafsah, kawai amincewarki nake nema mu yi planning contract marriage (AUREN KWANGILA) tsakanina dake na tsawon shekara daya da wasuwatanni kadan.
Contract Marriage? Kana nufin auren da Mommah ke nufi mu yi, da ma (contract marriage) ne? Ta tambaye shi cikin yamutsa fuska na rashin fahimta.
Ba haka nake nufi ba. Bana so ko kadan Mammah ta san wannan zancen. Zai tsaya ne a tsakanina da ke kawai, zan cika miki manyan burikanki na rayuwa da izinin Allah kafin cikar waadin nan. Ke ma kuma za ki taimaka min wajen cikar nawa burin, ki samu farin cikinki, ni ma a karshe in samu nawa ba tare da kowa ya san me muke ciki ba har zuwa karshen waadin.
Ban gane ba har yanzu, mene ne waadin? Sannan ta ya ya za a yi hakan ba tare da wani ya sani ba? Mene ne ma naka burin? Meyasa Mammah bata gaya min hakan ba?
Ta fada cikin tsananin shiga duhu, fuskarta da yanayinta gabadaya sun nuna hakan, sun bayyana tsananin rudun da kalamansa suka jefa ta.
Gaskiya hausarta da shekarunta sun yi kadan su fahimci abin da yake nufi kai tsaye. Tana bukatar ayi mata gwari-gwari.
Hafsah ina da wadda nake so in aura ne, sunanta Muazatu. Mahaifinta Malamina ne shekarunmu biyu tare kenan, mun fahimci juna mun amincewa juna. Sannan mun yi wa juna alkawarin aure komai runtsi to the very end.
Amma Mammah ta ce ba ta amince ba, Daddy ya mara mata baya sun ce ke zan aura ba ita ba. Hafsah kamar yadda ki ka fada min burikanki a yanzu, da yadda ki ke matukar sonsu, da burin ganin cikarsu. Ni Muazatu ce burina a yanzu. Bayan ita duk wasu burirrikana na rayuwa zan iya ce miki Allah ya cika min su (Alhamdu lillah).
Za a yi mana aure kamar yadda Mammah ke so, mu zauna gida daya in sanya ki a makaranta, ki yi ta karatunki. Aurenmu babu takura, domin kowa zaman kansa zai yi kamar yadda dai ki ke zaune yanzu a gaban Mammah, gida kawai za mu canza bayan shi ina tabbatar miki ba abin da zai