Showing 57001 words to 60000 words out of 168255 words
da Anty Harira.
Sai wajen sha daya na safe ta kashe T.Vn ta leka kicin, Harira ba ta nan ta wuce dakinta. Nan ta hau hada kayan girkin da za ta bukata.
Kafin karfe biyu na rana gidan ya gauraye da niimtaccen kamshin tsiren mutanen Turkiya. Ta kwashe shi daga oven ta zauna a nan dining din cikin kicin tana ci. Bayan ta dibarwa Harira.
Kwana biyu ta sake yi don na farko yayi mata dadi,Harira ma wuni tayi tana santin tsiren, tana zaune a kicin tanaci tana tunani. Tunda ta zo yau kwana biyu ba ta yi magana da Mammah da su Ismaeel ba, sosai ta ke cikin kewarsu. Ga shi ba ta da waya, ko sanda ta ke gida ba ta rike waya ko da wa za ta yi magana da wayar Mammah ta ke yi. Tana wannan tunanin tana kai lomar adana kebab dinta ba ta ankara ba sai ganin giftawar mutum ta yi har ta so ta tsorata. Da sauri ta waiwaya, Abdulazeez ne.
Kai tsaye ya wuce ga firji ya bude ya dauko gorar ruwan Faromai sanyi ya bincire murfin ya kafa a bakinsa ya ringa kwankwada, sanyi da gardin ruwan na ratsawa har cikin kwakwalwarsa yana wanke gajiya da zafin da kwakwalwar ta kwaso. Ta dauke kai daga kallonsa yayin da ta sauke wata siririyar ajiyar zuciya, ina ma za ta iya? Da ta roke shi ya ara mata wayarsa ta kira Mammah da Baba Azumi da Yayanta Ismael Dakata mazaunin kasar Amurka ko ta ji dadin zuciyarta daga matsewar da ta yi mata wuri guda sabida kewarsu.
Wannan aure jinsa ta ke tamkar an kawo ta kurkuku, ya yanke alakarta da kowa nata, Mamanta ba ta kara bi ta kanta ba, miji kamar malaika kullum fuska babu walwala, in yasa kafa ya fice sai goshin maghriba yake shigowa gidan daga nan bata karaganinsa sai wayewar gari in ya fito don tafiya office, in sun bashi abinci yana karba, in ta gaishe shi zai amsa, bayan wannan ba wata kalma dake kara hadasu, da alama ba ya son bude ido ya ga fuskarta, watakila bayan rashin so ita mummuna ce. Ita ma ba so ta ke ya so ta ba, amma akalla ya bude kofar da aurensa ya rufe mata na datse alaka tsakaninta da kowa nata.
Ji ta yi idanunta sun cicciko da kwalla kafin ta yi aune kwallar ta zubo, sharr! Da sauri ta sa bayan hannunta tana sharewa. Har ya wuce ya bar kicin din yana mamakin me ya yi mata ya sanya ta kuka? Daga kawai ya shigo kitchen? Watakila ba ta son ganinsa ne, in ba haka ba shi bai ga laifin da ya yi mata ba. Alkawururrukan da ya daukar mata tun a yau har ya fara kokarin cika su.
Ci gaba ta yi da cin abincinta tana hawaye, a haka Harira ta cimmata. Wai Abdulazeez ya ce a sanya mishi abinci a mota zai koma ofis. Nuna mata inda ta zuba masa abincin ta yi da hannunta, har tsiren ta zuba masa mai yawa, ba ta so ta yi magana Harira ta gane kuka ta ke yi. Ta manta cewa gaba take da ita. Murmushi Harira ta yi, ta ce.
Ki kai masa da kanki Hansatu, ki yi hakuri kin ji?
Wannan Hansatun da Harira ke kiranta da shi dariya yake bata, amma yau haushi ya ba ta. Ba ta ce komai ba ta mike ta dauki basket din ta fita.
Yana cikin motar har ya kunnata ya rufe kofar da alama ita yake jira, ba ta yi masa magana ba ta bude kujerar gaba ta ajiye kwandon ta rufe kofar. Ya ja motarsa da hanzari ya bar harabar gidan, daman mantuwa ya yi ya dawo, amma ba aladarsa ba ce dawowa gida cin abincin rana ba. Abin da ya tarar tana ci ne ya ba shi shaawa har ya ce a ba shi abincin.
Rayuwar amarya Hafsat-Suhaana da Abdulazeez kenan a gidan aurensu har tsayin sati biyu. Za ta yi girki sau uku a rana, kuma babu wanda ba ya ci, na safe zai fita da shi, na rana da ba ya samun sukunin dawowa zai turo direban ofishinsu ya daukar masa, na dare kuma in ya dawo masallacin unguwarsu sallar ishai zai ganshi a diningya zauna ya ci. Weakness dinsa kenan (abinci) kuma da a ce Hafsat na da wayo da ta dade da gane hakan. Ba ya son abincin sayarwa sai ta kama dole. Sanda yake (schooling) shi yake dafawa kansa. Da ya tafi Law-school daga gidansu Muazatu ake ba shi. Da ya gama ya dawo gida mahaifiyarshi ta sangarce shi da dadadan girke-girkenta wadanda dandanonsu yanzu ya yi masa daidai da wanda Addarta ke ba shi, wanda ke nuna ko dai ta koya ne a wajenta, ko kuma tare suke yi.
Kallon farko da yake yi mata na sangartacciya, ya soma gogewa.
SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI
07030137870
*Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama*
Ta dago ta dube shi kamar za ta ce, aah, ya tsare gida sosai. Ya sanya layin etisalat a ciki ya yi charging wayar sosai. Kamar yadda ta haddace karatun sallahr farillarta haka ta haddace lambobin uwarta da na Baba Azumi. Da sauri ta shigar da lambobin ta kasa danna call don ba ta san karbar da Mammah za ta yi wa kiran nata ba, sai gani ta yi Abdulazeez ya danna mata. Runtse idanunta ta yi lokacin da ta ji tattausar muryar Hajiya Maryam na fadin,
Assalamu alaikum.
Wasu hawayen dadi suka sauko mata, ta kasa amsawa. Daga can bangaren Mammah ta ji shiru, ta ce, Wa ke magana ne?
Bude idonta ta yi suka sauka cikin na Abdulazeez, ya daga mata gira cikin karfafawa.
Muryarta ta yi rauni sosai, ta ce, Mommah. Sai kuka.
Duk duniya babu mai kiranta haka sai Addarta, murmushi ta yi, ta ce, At last ya sayi wayar?
Abdulazeez juyawa ya yi ya fita don ya basu dama suyi maganarsu, ya dauki jakar system,wig da gown dinsa ya bar gidan yana mamakin irin wannan soyayya da ke tsakanin mahaifiyarsa da Suhaana. Zai iya rantsuwa shi bai samu rabin-rabinta ba. Ya ya za ta ji ranar da ya dawo mata da Suhaana da takardar saki? Zuciyarsa ya ji ta birkice, kwakwalwarsa ta daina aiki. Sai dai no matter what ba zai iya jure rashin Muazatu ba. Uwarsa ce dole watarana za ta yafe masa. Kuma zai san yadda ya yi Suhaana ta wanke shi tunda ita ce (apple of her eyes),his love to Muazatu is estimable, and hence; inevitable. Tunda ya yi biyayya ya yi abin da suke so, shi ma sai a ba shi hakkinsa. Fisabilillahi ya yi kokari da ya kawo wannan lokacin bai mallaki abar sonsa ba. Amma a kwanakin nan sosai yake jin tausayin Hafsah image dinta kuma na yawan gilmawa a idanunsa. Ya kara samun kwarin gwiwar son taimakon rayuwarta ta kowanne fanni.
Mammah da yarta a waya ana shan hira.
Tunda ya yi hankalin saya miki wayar alhamdu lillahi. Na sa masa ido ne ai in ga kamun ludayinsa. Waadin da na diba na zuwa gidanku ya kusa cika ai ko ba ki kira ba Adda...
Amma Mommah wata hudu... babu ke babu Daddy ko Baba Azumi, babu ko su Haleem? Momma me na yi miki da zafi haka? Kada ki sa in ci gaba da yarda da kaina cewa; kin daina sona... Sai kuka.
Murmushi Hajiya Maryam ta yi, irin murmushin nan na UWA maabociyar kawaici da yakanah.
Me ya yi zafi na wannan kukan Addah? Ashe uwa na daina son danta? Akwai dalilai da yawa da suka sanya babu wayata kuma babu kafata a gidanku. Amma tunda kin dauka haka da zafi zan gaya miki wasu don in wanke kaina daga wannan zargin naki Addah.
Aurenku ba aure ne na soyayya irin sauran aurarraki ba. Ina da karfin iko a cikinsa, wanda in na sa za a yi, in na hana za a bari. Bana son wannan karfin ikon nawa ya ci gaba da tasiri a cikinsa. So nake ku shaku da juna, ku so junanku ba tare da sa hannuna ba. Idan na zo na ganki cikin wani hali, ko ki ka gaya min wani abu wanda zuciyata ba ta gamsu da shi ba, ba zan jure ba sai na murza wannan kambun nawa. Ki fahimce ni Addah, bana son ji ko ganin komai da ya shafe ku ba so da kaunar junanku ba.
Kuma na fara samun abin da nake so alhamdulillah. A jiya na fahimta. Duk da haka kuna bukatar karin lokaci ki gafarce ni, ki kara min watanni biyu a gaba kafin in tako kafafuna gidanku. Amma daga yanzu na amince ki kira ni duk yadda ki ke so, ko sau dari ne a rana.
Dariya ta yi, dadi har cikin ranta. Duk da in Hausa mai tsauri ce ba ta fahimtarta. Yanzun ma ba ta fahimci wani muhimmin abu cikin zantukan Mamarta ba. Ta dai fahimci ba daina sonta ta yi ba, tana da dalilinta na rashin zuwan da rashin kiran. Tana so sai sun shirya sun saba da juna sun kaunaci juna don kansu. Tausayin Hajiya Maryam ya tsirga a zuciyarta, shin ya ya za ta ji ranar da ta fahimci duk wannan hakilon nata a tutar babu zai tashi? Abdulazeez ba fara sonta zai yi ba? Kuma ba zai taba son nata ba, yana da wadda zuciyarsa ta riga ta mutu ta rube a kanta?
Hawayen tausayin Mammah suka zubo mata, don ta kawar da tunanin da ya addabi zuciyarta sai ta ce, Mommah ya cike min JAMB.
Fassara farin cikin zuciyar Hajiya Maryam ba zai rubutu ba, Na ji dadi sosai Hafsat, wane course ya sa ma ki?
Ban sani ba Mommah, kuma ba ni da zabi. Na bar mishi wuka da nama. Ni dai in yi karatu kowanne iri ne Mommah.
Murmushi Hajiya Maryam ta yi ta sanya wa Abdulazeez albarka cikin zuciyarta.
Ni na san me zai sa miki, tunda shi karatu in ba shariah ba (Bar and the Bench) to ba karatu ba ne.
Dariya Hafsat ta yi, Kuma Mommah duk sai mu taru mu tare a kotu?
Mammah ta ce, Eh toh!! Ku haifi yaya ma ku maka su a kotu.
Kunya ce ta lullube ta don haka ta sauya zancen.
Mommah ba ni Baba Azumi.
Ba ta nan, ta je Sokkoto auren babbar yar Harira, ta samu miji.
Murna sosai ta yi wa Harira, Kuma Mommah sai ki ka dandana mana Harira ki ka zo kuma ki ka kwace?
Ta yi dariya ta ce. Dandani haukaci kenan. Gani na yi gara ke ma ki dage kamar sauran mata ki nemo aljannarki da kanki ba tare da mataimaki ba. Ki zama (total housewife), ranar da ki ka haihu na yi miki alkawarin mai aiki don haka ki dage......
Rufe ido ta yi cikin jin kunya kamar Mommah din na kallonta.
Mommah ki daina kira min haihuwa, Im still your baby!
You are still my baby Addah! Na daina.
Dariya suka yi tare.
Ki ka ce in kira ki sau dari a rana Mommah? Ai sai Daddy ya ce ba lafiya ba.
To ai ke ce Addah kin bi kin daga min hankali a kan abin da bai kai ya kawo ba, don na aurar da ke sai in yi ta zarya a gidanki? Kina so mijin ya ce surukar ba ta kwarai ba ce?
Dariya ta ke yi sosai wadda rabon da ta yi irinta har ta manta. Kwanaki da watanni sun shude sun tafiyar da farin cikinta na gida, sun dasa wata sabuwar rayuwa a gare ta a gidan Abdulazeez Dakata. Rayuwa mara dadi da ba ta ko son tunawa. Amma yau ta zo mata da farin ciki mai yawa a dalilai masu yawa;Theres compassion in him today (Abdulazeez), Mommahs love... Abu daya ya rage da zai cika wannan farin cikin... brothers love...!
Mommah ina Amerikawa? Ina Belgians?
Murmushi Mammah ta yi, Duk za su samu hutu lokaci daya. Watan April. Na yi miki alkawari ranar da zan zo gidanki, Usman da Ismaeel sune masu take min baya. Haleem ba yanzu ba.
Wani dan ihu ta saki, sai da Mammah ta toshe kunnenta ta kashe wayar tana murmushi.
Daddy ya shigo, fuskarta kawai ya kalla ya ga annurin da ta ke ciki, zuciyarsa ta gaya masa ta gaji da takunkumin da ta sanya wa kan nata ta yi magana da yarta. Dariya ya yi ya zauna yana fadin.
Har an shekara ne?
Cikin rashin fahimta ta ce, Da me fa?
Da kai Hafsa gidan aure.
Abin ya ba ta dariya sosai, ta ce, Ai da ma ban ce shekara ba, cewa na yi sai sun shirya kansu. Kuma ita ta kirawo ni tana ta kuka wai na daina sonta.
Cikinsa kamar ya fashe don dariya ya dora, Ke kuma dama a kan gwiwa ki ke, tana kira ki ka haife?
Harararsa ta yi, harara irin tasu ta manya, Aah ka manta nakudurta nake yi.
To ai da alama Hausa ba ta ishe ki ba, in aka ce mace na kan gwiwa ai nakuda ake nufi. Yau kin haihu kowa ya huta.
Dakin ta bar masa don ta lura yau zolaya yake ji, ta ce, In ka fito wanka table is ready
Ba fa abincin da zan ci sai kin ba ni labarin wayar nan.
Dakatawa ta yi a bakin kofa, ta juyo ta dube shi hannunta biyu harde a kirjinta.
To Daddy me ka ke so ka ji?
Sun shirya?
Su wa? Ta yi kamar ba ta gane ba.
Yayanki mana.
Danka dai, ni ba ni da wasu yaya bayan Suhaana.
To na ji, ina nufin da na da yarki, sun shirya?
Har ya saya mata waya da jamb form ya cike mata. Ta fada tana kada masa ido.
Tausayi ta ba shi sosai, don shi ya fi kowa sanin Abdulazeez da kyar in babu yaudarar mahaifiyarsa cikin alamarinsa. In zai so abu ba ya sonsa a lokaci guda sai ya gane yana da matukar amfani a gare shi. Tun sanda ya zo babu damuwa ya ce ya amince da auren Suhaana bayan da fari ya yi tawaye he didnt believe him! Ko zai so Hafsat not that soon, watakila har sai ta haifa masa yaya. Kuma shi a satin nan Attorney General Habib Rufai ya kai masa ziyara har Gwags karkashin rakiyar attorneys da yawa, bayan sun gaisa yake gaya masa shi ne Baban Muazatu yarinyar da yaron wajensa ke nema ya ce sai ta kare (Law-school), yanzu ta ci karfin karatun nata su zauna su tsayar da lokaci da ta kare sai a yi biki ba sai an kuma jan lokaci ba. Bai ce komai ba saboda kwarjinin mutumin da mutuncinsa hakan kuma ya ganar da shi cewa, Abdulazeez bai bar neman Muazatu ba.
Tun ranar yake jin tausayin Hajiya Maryam, yake kirkiro duk abin da zai sa ta farin ciki, ba abin da ya fi ka kasa juya Dan da ka haifa muni a zuciya. Ya kuma yi alkawarin ba zai yi mata zancen ba Abdulazeez din zai zuba wa ido ya ga iya gudun ruwansa.
Tun a ranar da hakan ta faru yake cewa su je su ga Suhaana tana cewa aah da sauran lokaci. Wayar da ta ce ya saya wa Suhaana da makaranta da zai maida ta, ya tabbata akwai dalilinsa amma ba SO ba, kamar yadda ita Maryam ta ke tsammani.
Ajiyar zuciya ya yi yana kallonta tana ta jera mishi abinci a dining ya mike ya isa gare ta ya rike hannunta. Dakatawa ta yi ta juyo ta dube shi, murmushin tausayi ya yi mata.
Ki bar abincin nan bana jin yunwa, mu je ki cuda ni a wanka.
A sanyaye ta ce, Toh. Don ta ga Daddyn shi ma a sanyaye yake.
Haka kawai sai ta ji nata jikin ma ya yi sanyi.
Saboda murnar maganar da ta yi da Mammah yau ko abinci ba ta girka ba (quaker oat) ta dauko ta dama cikin sayayyar da ya yo musu. Ta sha ta koshi ta shige daki sai barci cikin kwanciyar hankali.
Ba shi ya dawo gidan ba sai dare, akwai abin da yake yi wanda ya rike shi.Wani abun alajabi ne ya faru cikin kudurah da Iradar Ubangiji, yana shirin tafiya garin Adamawa a washegari don fara binciken alamarin Hafsat duk da cewa bai san kowa a garin ba. Wani sabon Lawyer ne aka kawo ofishinsu wanda haka kawai yake yi masa yanayi damatarsa, Barrister Sagir Babba. Ba halinsa ba ne shisshigi, amma sai da ya san yadda ya yi ya shigewa Sagir a bisa dalilai masu yawa. Da suka tashi suka fito ya tadda Sagir ya bude bannet din motarshi yana ta tabe-tabe. Kusa da shi ya yi parking ya bude motarsa ya watsa shirginsa ya rufe ya iso gare shi, ya ce, Ya ya dai Barrister? Magriba ta kawo kai muna nan.
Ya girgiza kai cikin takaici, Kai dai bari, karfen nasara ne da ba shi da tabbas. Jiya na karbo motar nan daga gareji, amma har ta kara kwafsa mani. Akwai (Mechanics) a nan kusa ne? Ka san ni bako ne a garin naku duka-duka yau satina biyu a cikin Abuja. Garejin da aka duba min ita can ne kusa da gidana a Kubwa.
Dadi ne ya kama Abdulazeez, ba abin da yake nema yanzu sai kusanci da bakon Barrister wanda ke sanya shi ayyana abubuwa da yawa a kansa a zuciyarsa tun ganinsa na farko da shi.
Ina ganin mu je yanzu na sauke ka a gida, Kubwa ba nan ba ce, in dare ya rufa maka a nan da kyar za ka samu abin hawa. Gobe sai in yi wa (mechanic) dina waya ya zo nan ya duba maka ita.
Sagir ya rufe bannet din yana fadin, Ai kuwa na gode da wannan taimako. Na gode sosai.
Ba damuwa. In ji Abdulazeez, ya fada yana bude masa gaban motarsa ya shiga suka tafi.
Suna tafe suna hira. Abdulazeez da mawuyaci ne ko shekara ku ka yi ya tsaya yana gaya maka abin da ba ka tambaye shi ba, yau sai ya bude ciki yana ta yi wa Sagir hira rututu, ya gaya amsa shi dan Kano ne yan unguwar Dakata, amma a nan aka haife su a nan suka girma. Last year ya yi aure.
Lawyer ake yi wa lauyanci, amma bai gane ba.