Showing 147001 words to 150000 words out of 168255 words

Chapter 50 - Auren Kwangila Book 4 Hausa Novel Complete

Takori   

12 Dec 2024

327

wasu ababen dabe kewa da dalibin Yale zai buka. (New Haven Towers) yana nan a Downtown na birnin NewHaven County. Idan aka ce Downtown ana nufin mahada ko cibiya ta kasuwanci, aladu da tarihi, siyasa da Geographical heart. Sau tari downtown’ synoymous ne da (CBD) na kowanne gari, wato Central Business District ko kuma a kira downtown da city-center ya fi saukin fahimta.
Abdulazeez Dakata na zaune a two bedrooms apartment a cikin New Haven Towers’. Daga (New Haven Towers) a kafa yake takawa zuwa makaranta kullum sabida bauchi nisa (trackable distance) ne. Da taxidin ta sauke su a daidai kofar shiga ginin TOWERS din shi ya dauki jakar ta har handbag dake hannunta suka hau ta lifter. A kofar apartment dinsa ya ciro makulli a aljihunsa ya bude, jakarta ya fara shigarwa sannan ya ba ta hanya. Sai wani dauke kai yake yi ya ki yarda su hada ido. Wucewa ta yi ciki ta samu lallausar kujerar wadataccen falon ta zauna, sannan ta warware lullubin kanta ta shiga karewa falon kallo. Matuka tsarinsa ya ba ta shaawa, komai neatandclassycikin tsari irin na bature, a can gefe study-table ne, manya-manyan littattafan law sun cinye filin tebirin sai inda zaa aje littafi ayi rubutu kadai suka bari. Ga study light mai ban shaawa komai na falon har labulaye brown da milk ne (ruwan kasa da ruwan madara). Akwai talabijin ta jikin bango, amma da alama ba’a kunnata sam. Kujerun wasu yan gujib-gujib na leathermasu tsananin taushi kalar su ruwan madara zallah. Daya daga cikin dakunan barcin guda biyu ya shiga bata kara ganinsa ba.
Ranta ya soma baci da wannan tarba da Abdulazeez ke mata, a kalla ya nuna mata dakin da za ta shiga ta sauke lalurorinta, ko ba zai yi mata magana ba. Idonta ta ji ya kawo ruwa da ta tuna salloli uku ne a kanta, ta taho tun daga Nigeria har America saboda shi, amma daga sannu da zuwa ko sannu ba ta kara samu ba. Tana wannan tunanin ya fito daga dakin da alama wanka ya yi, ya yi sallar magriba da isha a gefe duk tana zaune. Sannan ya sake komawa dakin ya sauya kaya ya fitohar da takalmi a kafarsa alamar fita zai yi. Kallonta ya yi da mamakin har yanzu tana a inda ya barta? Kamar ya wuce ta, sai kuma ya iso gabanta ya tsaya, sanyin turaren wankan sa na dunhillduk ya cika mata hanci.
Dakin ma sai na ce ki shiga za ki shige shi? Ai kuwa kina da aiki kuma zaki kwana anan wajen tunda ba ni na gayyato ki ba. Ya sa kai ya fice abinsa.
Ci gaba da zaman ta yi tana shaqar bacin rai, daga bisani ta ji fitsari na neman kwace mata. Dole ta mike ta suri jakarta ta murda dakin da ke daura da wanda ya fito. A nan ta lura ya ajiye mata trolley da tun shigowarsu ba ta ga inda ta yi ba. Kofa daya ce tal a cikin dan kyakkyawan dakin barcin wadda ta san toilet ce. Can ta nufa da hanzarinta, fitsari na barazanar zubo mata.
Sai da ta yi shi ta samu saida. A gurguje ta daura alwala ta fito ta kintaci gabas ta nada mayafinta ta tada sallah. Sai da ta rama sallolinta a nutse sannan ta kara da shafaI da wutiri ta mike ta soma rage kayan jikinta don ta shiga wanka. Wanka ta yi sosai da ruwa mai dumi don garin akwai sanyi duk da bai yi nisa ba, nisan da zai soma zubar da kankara. Tana wankan ta ji motsinsa a dakin da rufe kofarsa.
Da ta gama wankan sai da ta leko da kanta ta tabbatar ba ya dakin, sannan ta fito gaba-gadi. Ledoji ta gani ya ajiye mata guda biyu wanda ko ba ta bude ba bata raba daya biyun abinci ne. Ga lafiyayyen kamshi na tashi. Kwalliya ta tsaya ta yi sosai da daya daga cikin dinkunan da Mammah ta yi mata na wani material light bluemai santsi, an yi masa doguwar riga fitted gownda aikin duwatsu a gaban rigar sosai, ta murza daurin kai kamar mai shirin zuwa dinnerparty. Ta sa dankunne da sarka deep colour na material din na dutsen (cubic zirconia). Ba ta shafa jambaki ba, sai ta yi amfani da wet-lips mai taushi da kamshi. Har za ta zauna ta ci abincin ta ga gara ta je falo ta ci a can?Na me za ta kunshe kanta a daki don maigidan ba ya maraba da ita? Ai gara ta je ya yi ta ganinta tana harkokinta, in zamanta ya takura masa ya maida ita gaban iyayenta.
Falon ta fito rike da ledojinta, akwai dining table a gefe mai cin kananan kujeru uku, amma ba ta hau ba, tsakiyar rug ta baje ta fiddo kazar Kentucky Fried Chicken da chips da gwangwanin pepsi mai sanyi har guda biyu ta hau cin kayanta hankali kwance.
Zaune yake a study-table yana rubutu, wando ne three quarter a jikinsa da farar singlet ko sanyi ba ya ji. Tun fitowarta yana hankalce da ita ta gefen idanunsa, yana kuma ci gaba da hada assignment dinsa duk a lokaci daya. Ganin alamarin yake kamar a mafarki, yau ga shi ga Hafsat matsayin cikakkun maaurata a KARO NA BIYU! Its indeed a day in history wadda ba zai taba mantawa ba. Godiyarsa ga Ubangijin halitta wanda ya halatta AURE ya kuma halicci SOYAYAYAH ba za ta taba gushewa ba. Sosai yake enjoyingsharetan da yake yi musamman ganinyadda damuwarta a kan hakan ta fito karara. Dazu yana kallonta har kananan hawaye ta yi saboda bai nuna mata dakin kwana ba. A ransa ya ce.
Ashe babu dadi?
Da ta gama cin abincin ta nufi kofar da ta gane kitchen za ta kai ta, murmushi ta yi tana bin madafin da kallo. He still cooks. Ta fadi in a whisper (cikin rada).A shara ta zuba ledoji da kasusuwan kazar da ta ci ta wanke hannunta a sink da sabulun wanke hannu.Kawai sai ta hau gyara kitchen din. Kitchen ne na zamani, amma ya hadu da girkin namiji. Komaiout of order sai dai babu kofi ko kwanon da bai wanke ya killace ba ya rufa farin tawul akansu. Ta bude firji da freezer yana da kayan abinci daidai cikinsa. Da gani ba kullum yake yi ba, sai a (leisure time) dinsa.
Falon ta dawo ta nemi kujera ta zauna ta zuba tagumi. Wannan karon ya gama rubutun ya koma typing dinsa cikin laptop dinsa. Kamar bai san da zaman mutum a falon ba, zuciya ta soma zo wa Hafsat wuya duk kuwa da cewa ba halinta ne fushi ba. Ta ga in ta ce kuka za ta yi ta yi kan wulakancin Abdulazeez ta fadi ba nauyi. Gara ta dinga damunsa yadda zai yi gaggawar maida ita gaban masu kaunarta.
Mikewa ta yi ta isa ga T.V ta hau kokarin jona ta, ko banza ta samu abokin hira kada bakinta ya soma ciwo.
Cikin saa kuwa ta hada ta, ta dauki remote tana neman tashoshi, ta dire a bollywood wato tashar fina-finan India ta saka murya sosai suna ta raye-rayensu. Duk yadda ya kai da son ci gaba da abin da yake yi, hakan ya faskara. Hayaniyar ta dame shi, shi tunda ya zo bai taba jona T.V ba. Tsaki ya yi ya daga murya yadda za ta ji ya ce.
Please ki kashe. Banza ta yi amsa kamar ba ta ji ba. Tasowa ya yi a fusace ya je ya kashe ya koma ya ci gaba. Mikewa ta yi ta je ta sake kunnawa ta dawo ta zauna. Ba ta gama zaman ba ta ganshi a gabanta, cikin bacin rai ya ce.
“Are you here to disturb me (kin zo ne don ki dame ni)?
Hafsat ba ta taso ta ga ana tsiwa a gidansu ba, sannan ba ta cikin halayenta, amma yau ta yadda komai hali yake yi, kuma in ka ce ba za ka iya abu ba, to tabbata condition din bai same ka ba. Domin samun kanta ta yi da mayarwa Abdulazeez martani cikin launin nata bacin ran.
Kana iya mayar da ni inda na fito, tunda zama na takura ne a gare ka!.
Da sauri ya amsa.
Da ni na kawo ki? And I think you have your return tickets in your handbag?(Na yi zaton kina da tikitin komawarki a jakar ki?)”
Duk dauriyarta sai da hawaye suka silalo ta mike ta nufi daki. Kayanta ta jawo ta soma dannawa da ma ba ta jera su a wardrove ba suna cikin trolley din. Wadanda ta fitar da ta yi wanka ta ke dannawa, ta zuge ta saka hijabin sallarta. Keeeeeeeyyyy! Haka ta janyo jakarta ta tadda shi a falon yana ci gaba da aikinsa. Gabansa ta isa ta tsaya fuskarta babu ko digon hawaye ta goge su tsaf a daki.
Na fito Yaya Azeez, kai ni airport.
Da farko ko dagowa bai yi ba. Shi kansa ya san yanzu kam ba daidai yake typing dinsa ba. Yana yi ne kawai kada tasan ta birkita nutsuwarsa. Dagowa ya yi ya dube ta cikin ido da shanyayyun idanunsa.
Ki ka taho tun daga Nigeria ke kadai sai zuwa Airport ne zai gagare ki???”
Dauke idanunta ta yi daga kallon cikin idonsa sakamakon wani maganadisu da ke fita daga tsakiyar idonsa, yana shiga natamiraculously. Ba abin da za ta iya karantawa cikinsu a wannan lokacin ban da rashin damuwa da lamarinta. Gefen hijabinta ta kai ta rufe fuskarta ta soma kuka. Tashi ya yi tsam da takardunsa da laptop dinsa ya shige dakin kwanansa.
Sai da ta yi mai isarta sannan ta bai wa kanta hakuri ta koma dakin da kayanta. Ba ta da kudi a hannu, amma tana da credit cards’ har biyu. To amma ta koma gida ta ce wa Mammah me bayan ta gama gargadinta gidanta ba space na yaji? Babu kawo kara, su je su zauna su yi HAKURI da juna, to ko wannan shi ne hakurin da ta ke ikirari?
Haka ta kwana bacin rai da sake-sake. Amma da yake akwai gajiya sosai a tare da ita ba ta san yaushe wani wahalallen bacci ya yi awon gaba da ita ba, har sai da ta makara sallar asubahi.











SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI
07030137870

*Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama*


Washegari ba ta tashi ta tadda shi a gidan ba, ya wuce makaranta tun bakwai na safe. A gefen filonta ta ji motsin takarda. Zarota ta yi ta duba,
“You can use thekitchen.
Jefar da takardar ta yi a fusace ta mike ta yi toilet.
Ba ta shiga kitchen din ba sai wajen sha daya na safe. Bakin shayi kawai ta dafa don ba ta jin za ta iya sanya wani abu a cikinta saboda haushin mai apartment din nan. Da rana ma kwai ta dafa guda biyu da indomie noodle guda daya ta ci jin hanjin cikinta na rawa da karkarwa. Ta yi niyyar dafa masa abinci ta tuna Abdulazeez fa in yana wannan fushin nasa maras dalili ba ya cin abincinta, wahalar banza za ta yi ya zo a kan idonta ya tsallake nata ya nemi abin da zai ci. Ba shi ya dawo gidan ba sai da yamma niki-niki da ledoji. A kitchen ya zube su ya wuce ta a falo tana kallo ya shige dakinsa.
Kwanan Hafsat uku kenan a America amma ba abin da ta gani sai bacin rai da damuwa. Abdulazeez ya zube mata komai na ci da na amfani, amma ban da kulawarsa wadda ita ta fi bukata fiye da komai. Duk ta wani rame sabida damuwa da rashin cin abincin kirki. Shi da kansa ya soma damuwa da ramar da ta ke yi din, wanda ya san shi ne sila. Ya soma saukowa ko ba komai ya san ya rama, ta dandani irin abin da ya ji a lokacin da ta yanke communication a tsakaninsu a lokacin da ba ya bukatar komai sai kulawarta.
A sanda ya soma saukowa a sannan ne ya lura ita ta hau ingarman dokin fushi. Sai ya janye saukowar suka ci gaba da zama a haka. Sai dai wannan karon in ta yi girki yana ci, ko ba komai ya yi kewar abincinta yadda ba zai iya bayyanawa ba.
A haka suka share sati daya, a karshen satin tafiya ta kama shi kan wani assignment dinsa zuwa Texas (The Supreme Court of Texas), ga shi ba ya so ya shiga sabgarta ganin yadda ta ke a kan tsininta. Abincin ma yau ba ta dafa da shi ba, daidai cikinta ta dafa ta shige daki. Ba zai kuma iya tafiya ba tare da ya sanar da ita ba, haka ya wuni da wannan damuwar. Tunda ta zo kuma bai hada mata layin waya ba, amma shi yana magana da su Mammah a Saudiyyah. Ya gaya musu ta zo lafiya bai san me ya sa ba ta kira waya ba tunda ta zo, amma lafiyarta lau. To su ma they are busy da ibadah ba wanda ya damu da rashin kiran nata tunda shi suna jinsa.
A daren ranar bayan ya hada yan kayan da zai yi amfani da su na kwana biyu, wato asabar da lahadi sai ya fito ya nufi dakin nata.
Sanda ya murda kofar ya shiga tana kwance a gadonta tana lazumi. Sosai ya tsaya yana kallonta, abu biyu ne ya dauki hankalinsa, ramar da ta yi da hawayen da ta ke zubarwa. Jikinsa ya ji ya yi wani irin sanyi, ya shigo dakin gabadayansa ba tare da ya zo da niyyar hakan ba. Lokaci na farko da ya soma zargin kansa da rashin kyautawa kan abin da yake yi tun zuwanta.An rabo ta da kowa nata an turo ta wajenshi, amma tukwicin da zai yi wa iyayensa kenan?Wadanda ba su bukaci ko kwandalarsa cikin tafiyarta ba sai don su faranta masa. Amma ita har yau ba ta yi hankalin ta yi wa mutum laifi ta san ta yi ba, har ta nemi sulhu kan laifinta? Sai ma nasa laifin ta ke gani, wannan shi ne a doke ka a hana ka kuka.
Haka ya daure duk wani bacin ransa da laifin da ta ke ganin nasa ne ya ya zauna a gefen gadon daura da kafafunta. Rana ta farko da ya shigo dakin har ya zauna tun zuwanta. Dauke idonta ta yi daga kansa ta juya bakidaya daya barin ta ci gaba da sharar hawayenta. Ya ji haushin abin da ta yin, amma ya hadiye ya ce.
Ki juyo mu yi magana, tafiya zan yi ta kwana biyu Imgoing for some assingments to Texas.
Ai ba ta san lokacin da ta juyo ba ta mike zaune. Ni kuma in zauna da wa??”
Cikin tsakiyar idanunta ya dube ta kai tsaye. Da da wa ki ke zaune a gidan nan? Ban yi zaton kin san da mutum a cikin gidan ba?
Mikewa ta yi ta diro daga gadon ta nufi wardrove ta soma kwaso kayanta, cikin rishin kuka ta ce. Wallahi ba zan zauna ba, ko dai kafata kafarka, ko ka sa ni a jirgi in koma gida. Yanzu ne na yarda da duk abin da Mammah ta ke fada. How sure am I yanzun kana sona? Zuciyata ta zarme na ki yarda da ita, bayan na san duk duniya ba wanda ya kai ta sona! Na yarda da dadin bakinka, da kalaman ka na yaudara, na yarda duk abin da ka ke fada da zuciya daya. Da na san haka kake da ban zo ba.Kaicona! Da na yarda aka maida auren nan!! ..…Auren da tun fil azal nasan bani da gurbi a cikinsa..!!!”. Ta sulale a kan gwiwoyinta rungume da rigarta a hannu, ta sa kuka mai cin rai.
Ba ta san yaushe ya taso daga gefen gadon da yake zaune ba. Ta dai ganshi yana ciro wasu daga cikin kayanta wadanda ta ke watsawa a jaka. Fita ya yi da su bai ce mata komai ba. Wannan ya fi komai kara bakanta mata rai; shirun da ya yi mata. Zama ta yi a wurin ta saki kukan gabadaya. A can dakinsa shi kuma da ya hada kayanta da ya debo da nasa ya rufe jakar ci gaba ya yi da sabgoginsa, amma duk sai ya ji ya kasa sukuni, maganganunta sun taba shi, ya kuma yardar wa kansa hukuncin nasa ya yi tsauri fiye da laifin da yake ikirarin ta yi masa. Ga wata irin soyayya da ke cinsa a zuci. Yau Hafsat din ce matsayin matarsa ta hakika a dakin aurensa babu zancen yarjejeniya, amma ya tsaya yana wahalar da su dukkansu a banza. Ita ta kasa ganewa lallashi yake so. So yake ta lallashe shi, ta yi admittingda kanta ta yi masa laifi, amma ta ki yin hakan. She only insist on ba ya sonta. Murmushin takaici ya yi, ya tabbata in zai iya buda mata son ta gani ba ta da fadin zuciyar da za ta dauki nauyin rabin sa.
Duk yadda ya so ya yi bacci a wannan daren ya kasa. Hafsat ce a cikin apartment dinsa, amma wai ya raba daki ba ma makwanci da ita ba. Tana can tana kukan bakin cikinsa, yana nan soyayyarta na neman hallaka shi. Abin da ya dade yana jiran samun yancinsa shi ne a hannunsa amma ya jefar. Ya tuna yadda yake hana idonsa barci yana rokon Allah ya dawo da ita cikin rayuwarsa ya gyara kuskuren da ya yi, Ubangiji maji rokon bayinSa Ya amsa masa a lokacin da bai zata ba. Anya wannan gabar da ya kulla da ita don kawai ta kashe masa waya tana so ta yi jarrabawa ba butulci ya yi wa Ubangiji ba?
Wani irin tausayi da kauna suka taru suka dabaibaye shi. Soyayyar da ke dankare a zuciyarsa ta yi ta kawata su. Tsohuwar ajiya ta soma bankadowa tana fiddo kanta. Tsayawa ya yi yana karbar isowarsu daya bayan daya cikin zuciya da ruhinsa. Yayin da gangar jikinsa ke musu masauki a muhallin da ya dace da kowannensu. Kafin ya mike ya shiga toilet dinsa da zummar yin wankan da ya zame masa jiki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login