Showing 87001 words to 90000 words out of 168255 words
*****
WASHEGARI
An tara maza da mata, babba da yaro na nesa da na kusa, na zuriar Malam Hashim Babba Jimeta. Da zuriar Dr. Bashar Mai-jamaa Numan, wanda shi ma dan nan asalin Yola ne daga karamar hukumar NUMAN. Kamar yadda Malam Babba da Dada suka bada umarni; duk wani jininsu ya hallara an ga Habibah.
Tunda Sagir ya shigo da bakin falon ganawar wannan family kowa yake raba ido ya ga ta inda Habiba za ta billo, tunda an gaya musu wadanda suka rike ta ne suka kawo ta. Tun fitowarsu Mammah ta ja mayafin Hafsat ta rufe mata rabin fuska, ta ce ta rufe fuskarta ta kalli gabanta, sai ta ce ta bude za ta bude.
Ita dai Addah mamaki ya hana ta cewa komai, saboda ita dai tun tasowarta ba ta san suna da yan uwa a Yola ba. Jikin tsohuwa Dada da Malam Babba ya yi sanyi ganin har wadannan baki suka gama shigowa suka zazzauna babu Habiba babu alamunta.
Gaggaisawa aka fara yi, sannan Malam ya bude taron da addua. Daddy ya gabatar da kansu su ma suka gabatar da kansu a matsayin iyayen Habiba da yan uwanta, ga kuma mijin aurenta Prof. Bashar Mai-jamaa, karshe Malam ya tambaye su wane labari suke dauke da shi game da yarsa Habiba? Sannan ina ta ke yanzu? Dr. Bashar ya kara da cewa,
Lafiya nake zaune da maidakina Habiba tun ina matsayin Malamin makarantar sakandire. Rana daya na tsiri karo aure sakamakon kowa da rubutacciyar kaddararsa ta aure, amma ba don Habiba ta gaza da ni ta kowanne bangare ba.
Yaranmu uku, Modibbo (Ridhwan), da Abdurrahman sai auta Imamu a lokacin da na auro Hajara. Tun zuwan Hajara gidan ya ki zama lafiya, fitintinu iri-iri kullum da tashin hankalin da zan dawo na taras. Amma duk sanda na yi bincike a kan rikicin zan tadda Hajara ce ta tado shi. Zaman lafiyan ya kara tabarbarewa a gidan lokacin da Habiba ta samu ciki na hudu, Hajara kuma ta kwashe shekaru uku a gidan kenan babu ciki ba dalilinsa. Wannan ciki ya kara daga hankalin Hajara ta fiddo ainahin kalarta a fili, ta mace mai tsananin hassada akan abinda Allah bai bata ba.
Na sha ji tana fadi wa Habiba wannan cikin ba dai ki haife shi a gidan nan ba, ko dai ya bi rariya ko ki haife shi akan titi.Sai in tsawatar da kakkausan harshe, in kuma gaya mata Allah ya fi ta. Mugun bakinta ya kare a kanta. Saboda Habiba ba ta da fus, bata iya tashin hankali ba,rashin katabus dinta yayi yawa, shi ya sa Hajara ke mata duk cin kashin da ta ga dama. Ido wannan Habiba bazata daga ta dube ta ba. A karshe ni na koma kishiyar, saboda ni nake tare wa Habiba fadan in ina nan, in bana nan kuwa tana shan ukuba a hannun Hajara. Sabida haka ne na ga gara in sauwakewa Hajara auren nan ko ma samu kwanciyar hankali ni da iyalina.
Na saki Hajara saki daya, amma ta ki tafiya, ta ce gara ma in barta ta zauna a dakinta, don in ta tafi biyu-babu zan yi, don kuwa ta sha alwashin Habiba ba za ta haife cikinta cikin gidan nan ba.
A karshe ta karfi na fidda Hajara daga gidana, na watso mata kayanta waje, wannan shi ne dalilin rabuwata da Hajara na farko.
Na maida hankali ga kula da Habiba duk da cikin ba mai matsala bane sam kamar haihuwarta na baya, ji nakeyi kamar wannan ne karo na farko da zaa yimin haihuwa bansan dalili ba. Muka ci gaba da kula da yaranmu da zamanmu cikin rufin asiri da kwanciyar hankali.
Wata rana cikin Habiba nada wata biyu ba kadan na wayi gari na tafi wajen aiki inda nake koyarwa a makarantar yammata ta (GGSS YOLA). Na dawo na tadda su Abdurrahman zugum-zugum a gida su kadai. Na kama Imamu da ke ta kuka na aza bisa cinyana ina tambayarsu ina Mamansu ta je ba ta gaya min ba, ba ta kuma tafi da Imamu ba? Suka ce ai ta tafi unguwa tun kan su dawo makaranta, shi ma Imamu shi kadai suka same shi a kofar gida.
Haka na shiga kicin na shiga nema musu abin da za su ci, muka ci gaba da zaman jiran dawowar Habiba, ina cike da mamakin abinda tayi don bata taba yin haka ba koda wasa, ba inda take zuwa bata nemi izni na ba, sannan wai ta bar karamin yaro kamar Imamu a kofar gida. Har rana ta fadi ba ta dawo ba.
Ban kawo komai a raina ba na sanya a raina cewa, babbar lalura ce ta fidda ita tunda ba ta taba yin hakan ba. Da na ga dare ya yi ne hankalina ya soma tashi, ga Abdurrahman da Imamu sun ishe ni da kuka. Don haka na sako su a gaba muka taho gidan Dada nan Demsawo, mu muna (Upper Luggere) a lokacin.
Tafiyar da har yau ba ta dawo ba kenan, ga yayanta duk sun zama maza, ban da Modibbo babu wanda zai iya tuna ta sai a hoto. Mun dukufa addua muna rokon Allah ya bayyana ta ba dare ba rana, mahaifinta kun ganshi nan ya yi shekaru ba ya bacci, ya kuma ce a duk istikharar da yake yi a kan Habiba Allah ba ya nuna masa komai a kanta. Dada ce ta ci gaba da rainon su Imamu ta ki bai wa kowa a gidannan su ko nawa dangin.
Rana daya na tsinci kaina ba abinda nake so sai dawo da Hajara gidana, na dawo da ita muka ci gaba da zama, amma Dada ta hana ta jikokinta.
Watanni shidda da bacewar Habiba malamai babu adadi Malam Babba ya baza, shima baa barshi a baya ba, suka mike suna addua dare da rana a kan kowanne boyayyen alamari ne tattare da Habiba Allah ya bayyana mana, Ya kuma maido ta gida lafiya cikin iyalinta.
Rannan na dawo aiki na tadda cincirindon mutane a kofar gidana. Ana hango ni aka shiga darewa ana bani hanya. Hajara ce ta ke hauka tuburan a tsakiyar unguwa, ta kekketa sutturar jikinta duk da yadda matan makwabta ke kokarin rufe mata tsiraici abu ya ci tura, da an saka za ta yage su, tana fadin duk irin sharrin da ta rinka shukawa a zamanta da Habiba. Wallahi wasu ko da wasa ban sansu ba, Habiba ba ta taba fada min ba. A karshe ta ke fadin, ita ta yi wa Habiba kurciya ta bar Yola, kuma ko za ta mutu a haukace Habiba ta tafi kenan ba za ta dawo ba. Gidana ma da ta dawo asiri ta yi min ta dawo, kuma ban isa in karya shi ba saboda a kogin Niger-Delta ta jefa.
A sanda ya zo nan hawaye sun jika fuskarsa, ya sanya gefen babbar rigarsa yana sharewa. Hafsat-Suhaanah, wadda zuwa yanzu ta fahimci ko a ina suke, da kuma dalilin zuwansu, da ko wane ne wannan farin bafillacen maabocin zati da kamala. Jikinta tsuma ya hau yi, tsigogin jikinta suka shiga tashi, ta kura masa ido ba ta ko kiftawa.
Wani irin feeling ta ke ji yana fizgar zuciyarta irin wanda ba ta taba ji a kan kowa ba. Ci gaba ta yi da kallonsa, wannan feeling na kara cika kowanne sako na zuciyarta. Shin ko wannan shi ne abin da kowanne Da ya ke ji a kan mahaifansa, su ma mahaifan suke ji a kan yayansu wanda Daddy ya kasa ji a kanta a baya???
Mammah ta lura da jikin Hafsat rawa yake yi, kuma ta bude idonta daga lullubin dolen da ta saka ta tana ta kallon Dr. Bashar Mai-jamaa Numan. Jawo ta jikinta ta yi, ta kwantar da kanta a cinyoyinta. Hafsat ta rufe idanunta hawayen farin ciki suka shiga kwaranyo mata. Farfesa Bashar ya ci gaba da bada labarinsa bayan ya tsane hawayen idanunsa da hannun babbar rigarsa.
Cuta ta karshe Hajara ta yi min, ba ni kadai ba, har iyayen da suka tsugunna suka haifi Habiba. Tunda duk son da nake mata ban kai su ba. A lokacin na damka ta hannun iyayenta na sake ta saki uku. Ni da su, (Malam Babba da Dada) da sauran yan uwanta na ciki daya da yayan da ta haifa muka rungumi kaddara. Domin a shekarar farko in Malam ya yi istikhara yana gaya mana ya ganta lafiya cikin kwanciyar hankali a duk inda ta ke. Amma a shekaru na gaba sai ya ce ba ya ganin komai a kanta sai duhu. Allah ya rufe masa alamarinta.
Yaya Tijjani babban Yayansu, kasancewar maaikacin gidan talabijin ne na jihar Yola, ya yi hobbasa iri-iri wajen neman Habiba a kafafen yada labarai har yau ba amo ba labari, babu ko wanda ya ce ya taba ganinta sai a wannan shekarar da dan wajenku, abokin Sagir ya zo daurin auren Modibbo ya ce mana yana da labarinta, ya san inda ta ke, zai dawo mana da cikakken bayani a kanta bayan watanni hudu.
Ya gaya musu cewa, shekaru takwas ya kwashe bai kara aure ba, kasancewar matan bakidaya tsoro suke ba shi, kuma yana sanya ran zai ga Habiba komai daren dadewa bai taba fidda rai ba.
Kuka Hafsat ta fara yi cikin mayafinta lokacin da Dr. Bashar ya dasa ayah. Mammah ma kukan ne ya ci karfinta. Da fari tausayin iyayen Habiba ta ke ji, amma yanzu Dr. Bashar yafi bata tausayi. Da ace Habiba ta yi tsawon rai zai fi kowa bukatarta a yanzu ko mata ukku gare shi. A hankali ta ke jijjiga Hafsat da ke kuka a kan cinyarta. Daddy da Abdulazeez hankalinsu na kan Mammah da Addah wadanda kukansu ya soma fitowa fili har aka soma maida hankali gare su duk da dai fuskar Hafsat na rufe cikin mayafinta. Wani iri Abdulazeez ke ji a ransa da kukan Hafsat, yadda shi kansa ba zai iya fassarawa ba. Mammah ta share hawayenta cikin murya mai sanyi ta soma ba su labari.
Tun daga sanda aminiyarta Hajiya Halima matar Controller ta kawo mata Habiba da kuma bayanin da Haliman ta yi mata a kan Habiban na yadda ta same ta, zuwa yi mata fasfo da visa da tafiyarsu Jeddah, yadda ta gane Habiba na da ciki bayan tsautsayi ya sameta sun je asibitihaihuwar gaggawa ta sameta. A nan ne ta dago ido ta dubi ahalin Habiba sun zubo mata na mujiya caaa! Kamar idanunsu sa fado.
Russunar da kwayar idonta ta yi kasa, muryarta cike da alhini ta ce.
Im sorry, ina mai baku hakurin sanar da ku cewa, Habibah ta rasu a wurin haihuwar diyarta Hafsat-Suhaanah...!!!
Ta yaye lullubin kan Hafsat ta ce,
Je ki ga mahaifinki Hafsat!.
Hawaye ne suke bulbula daga idanunsu bakidaya, in ka dauke yara-yaran matasa da aka haifa a bayan batan Habiban. Hatta Yaya Tijjani kuka yake yi, Fusam, Saade mai binta da Haladu, sun ko kasa kallon Hafsat din.
Fuskar Dr. Bashar cikin tafukansa yana ta gunjin kuka, amma hakan bai hana shi dagowa ya mikowa Hafsat hannu ba. Wadda ita ma nata kukan ya tsananta, kanta ko kallabi babu. Wani ignition Abdulazeez ya samu zuciyarsa na yi da kallon Hafsat cikin wannan hali. Shi ba abun ya je ya mikar da ita tsaye ya rungume ta ba, komai ya kare a tsakaninsu. Ya riga ya yanke hukuncin da tun baa je koina ba ya soma shiga halin haulai akan ingancinsa.
Kasa jure ganin wannan abin tausayin ya yi, ya tashi ya fice zuciyarsa na wani irin zabalbala. Ga shi ya riga ya aiwatar da komai, tun a Abuja ya sanyawa Hafsat takardar sakin cikin handbag dinta a lokacin da ya sanyata ta koma daki wai ta canzo mayafi, tsabar shikansa yana jin kunyar bata takardar sakin a hannunta. Saboda shi ma ya san ko giyar wake ya sha ba zai iya fuskantarta ido cikin ido ya ba ta wannan takardar sakin ba, duk da abu ne da ta kwana da sanin kasancewarsa, to amma akwai KARAMCI da KYAUTATAWA a cikin zamansu, wanda ba zai taba gogewa daga tarihin rayuwarsa ba, kuma ba zai gushe yana kallon Hafsatu da su ba. Da sassarfa ya isa ga motarsu ya bude ya shige ya maida kofar ya rufe, ya kwantar da kai a kan sitiyarin ya kai hannu ya dafe kirjinsa daidai saitin da ke azabtar da shi. ME NA AIKATA??? Yake fadi a fili.
*****
Da rarrafe Hafsat ta rarrafa ta isa ga Dr. Bashar kafin ta karaso ya taso ya cimmata, ya sanya ta tsakiyar hannayensa ya rungume. Yanayin da Hafsat ta samu kanta a wannan lokacin ba ta taba tsintar kanta a kololuwar dadin irinsa ba. A tsaye suke tsakiyar taron nan kusan minti goma kafin Dada ta mike ta rabo ta da uban ta kamo hannunta.
War hadosabajoam Hafsatu (Zo nan kawata Hafsatu). In ji tsohuwa Dada.
“Sobirawo na malla launirawo? (Kawalli ce ko kishiya ce?) Daada ta sake fadi tana hawaye.
Duk da Hafsat ba ta san me ta ke fadi ba ta isa gare ta, ta rungume ta don ta fahimci ita ce mahaifiya ga Habiban, wato Kaka a gare ta.
Malam Hashim Babbah ya share nasa hawayen ya shiga baiwa kowa baki. Ya ce, Alhamdulillahi, Alhamdulillahi, Alhadulillahi har sau uku. Sannan ya cigaba da cewa Allah bai yi lamunin za mu sake ganawa da Habiba ba, amma bai barmu da kewarta mai yawa ba tunda ta ajiye Hafsu. Zuciyoyinmu yanzu sun samu nutsuwa daga taraddadin da kullum suke ciki.
Baiwar Allah!Ya dubi Hajiya Maryam.
Alkhairinki ya bi ki har yaya da jikokinki. Ba mu da kalaman da za mu furta godiya a gare ki. Muna rokon Ubangiji Ya fi mu godewa. Ba sai kin fadi irin rikon da ki ka yi wa yarinyar nan ba, ido ba mudu ba amma ya san kima, kowa ya dube ta ya san ta fi karfin komai na rayuwa. Allah ya zama gatanku ke da mijinki da zuriarku bakidaya.
Kowa ya amsa da, Amin-amin.
Hafsatu matso kusa da ni, ko ba kya aure da tsoho? Dube ni sosai, gemuna bai gama kodewa ba.
Murmushi ta yi ta matsa kusa da shi. Ya kama hannayenta biyu ya rike cikin nasa. Adda Hafsatu babar Hajiya maryam ta ce da shi.
Anya takwara tana auren nan da kai Malam? Dubi sardidin mijinta a gefe, gara ka rike Dadanka kada ka yi ba-wan-ba-kanin.
Ido ya koma ga inda Adda Hafsatu ta nuna, kowa na son ganin wane ne mijin dalleliyar baturiya Hafsat? Wayam! Babu kowa, babu wanda ya ankara da fitarsa saboda a lokacin sun rude da koke-koke.
Modibbo ya fiddo ido cikin mamaki ya tambayi Adda Hafsatu, Ba dai Barrister abokin Kawu Sagir ba?
Shi kuwa. Jiya aurensu shekara guda da watanni uku. Aunty Luba ta ba da amsa.
Kuma Da yake a gare su, shi ne babba dansu. Aunty Mariya ta kara bayani.
Allahu akbar! Allahu Akbar!! Abinda Malam Babba da iyalinsa ke fadi kenan cikin jinjina halin GIRMA da karamci irin na Hajiya Maryam da mijinta tsohon Ambassador Hamza Atiku. Daddy ya ciro waya yana kiran Abdulazeez. Yana dagawa ya ce da shi, Ina ka tafi? Ka shigo yanzun nan. Ba tare da ya saurari amsa daga gare shi ba ya kashe wayarsa ya maida aljihu.
Falon ya rikice da tofin albarka da fatan alkhairi ga Hajiya Maryam Hamza Atiku. Sai da kowa ya gaji ya bari sannan ta gyara zama, ta ce.
Na yi zama da Habiba zama na amana, domin ta so yarana ta kaunace su, ta kula da su tsakani da Allah, musamman Abdulazeez na hannun damanta. A kan idonsa aka haifi Hafsat a asibiti can Jeddah. A tasowarsu kuma sai na fahimci yana shiri da uwa ba ya shiri da yarta, tun a wannan lokacin nake nazarinsu na fahimci sam ba sa ga maciji. Ni kuma na sa a raina tun a lokacin Abdulazeez ba shi da mata sai Suhaana. Mun yi musu aure ba tare da son ran kowannensu ba, su suka san yadda sukai suka shirya kansu.
Kalaman da ya tsinta kenan a shigowarsa falon wadanda suka kara tsinka masa zuciya. Wata juwa-juwa ya ji tana kwasarshi tana neman fyada shi da kasa jin kowa a falon na kiran sunansa cike da kauna da tsananinbegensa a zukata da fuskokinsu, Angon Hansatu!.Shine mijin nata? Wasucikinsu suka ceAbdulazeez na Hafsu. Allah ya yi albarka!. Kowanne da abin da yake cewa na nuna kauna da kulawa a gare shi.
Kusa da mahaifinsa ya lallaba ya zauna, amma sai Malam Babba ya ce ya taso ya zo kusa da shi. Da rarrafe ya yi hakan, sabida gwiwoyinsa sun kasa daukar sa. Malam ya yafito Addah da hannayensa. Cikin matsananciyar kunya ta tashi daga kusa da Dada ta tafi ta zube a gabansa. Hannun Abdulazeez ya dauka ya sanya cikin na Hafsat ya cure wuri guda. Daga Abdulazeez har Hafsat bugun zuciyarsu ya tsananta a wannan lokacin, sun kuma kasa duban junansu idanun kowannensu na kan kyawawan yatsun da Malam Hashim ya cure ya dunkule wuri guda,siraran zobunan danyen gold na hannunta guda biyu sun kawata yatsun. Yatsun kawai suke kallo sarke cikin najunansu da tunanuka masu nauyi a zukatansu. Abdulazeez na ji a ransa sallama yake yi da Hafsat, sallama irin ta SAI WATARANA...... Hafsat na tunani a zuciyarta, mene ne muhimmin aibunta da Abdulazeez ya kasa sonta???
In a da rashin asali ne, yanzu fa? Zai dubi Allah da girman UWA ya kaunace ta su ci gaba da kyakkyawar rayuwarsu ko kuwa? Ko kuwa zai rufe ido a karo na biyu ya zabi Muazatu a kan su su biyu ita da mahaifiyarsa? Yau ta tsayar da zuciyarta wuri guda ta fahimci kauna ce sak! Mai lullube da soyayya ta ke yi wa mijinta Abdulazeez Dakata ba wani abu daban ba. Ba za ta taba sonsa da abin Allah wadai ba. Fushin iyaye kuwa abin Allah wadai ne, tana rokon Allah ko ba zai so ta ba ya ci gaba da zama da ita don tsira daga fushin