Showing 96001 words to 99000 words out of 168255 words
ganin yadda ita da Azumi suka zubo mata ido. Mikewa ta yi ta nufi daki, kafin ta isa da gudu-gudu ta karasa ta shige, kuka ya kufce mata, karshen tika-tika-tik! Me kuma za ta ce wa uwar tasu? Za ta ci gaba da boye sakin ne kuma? A dauke ta a maida ita gidanta bayan kuma auren babu shi, ya mutu?
Tambayoyin da ta ke ta jero wa kanta kenan ta rasa amsar ko daya.
Bayan tashinta da kulewarta Hajiya Maryam da Baba Azumi suka bi bayanta da kallo sannan suka dubi juna, an rasa mai magana a cikinsu.
******
ABDULAZEEZ DAKATA
Shi kadai ya san yadda rayuwar ta kasance masa a tsayin sati biyun nan da Hafsat tayi a Jimeta. Zai iya kiransu kwana goma sha hudu mafiya tsayi da fadi a renakun rayuwarsa. Abin da ya sani kawai shi ne; ba ya iya zaman gidan, barci kadai ke kawo shi cikinsa. Da safe zai yi wanka ya tafi office babu tunanin karin kumallo, sai ya je can dinhanjin cikinsa ya hana shi sukuni yake samu ya sha coffee ya cika wa kansa aiki duk don ya hana kansa tunanin komai. Haka zai zauna babu ko tunanin abinci sai lodawa kansa aiki, sallah kadai ke tayar da shi.Ba shi zai baro office ba sai karfe shidda na yamma. Daga nan kuma kai tsaye gidansu zai wuce, a can zai yi sallar maghriba da isha tare da Daddy, su ci abinci tare har Mammah ya zauna ya ki tashi har sai Daddy ya ce da shi dare ya yi, watarana har ya tsokane shi ko zai koma Jimeta ne a yi sati biyun tare da shi?
Daga Daddy har Hajiya Maryam sun fahimci yana cikin damuwa wadda cikinsu babu wanda tunaninsa bai ce da shi ta rashin maidakinsa a kusa ba ce. Don haka babu wanda ya bashi hankalinsa. Babu daren da zai zo ya wuce a tsayin kwanaki goma sha hudun nan da bai gwada kiran wayar Hafsat ba sama da sau hamsin a rana, amsar dai a kullum iri daya ce; wayar a kashe ta ke. Ya kasa amsa wayar Muazatu ko guda daya daga ranar da ya saki Hafsat! Abinda shi kansa bai san dalili ba; wadda ke can gidan su a birnin Lagos hakan ya dugunzuma nata hankalin. A ganinta yanzu lokacin farin cikinsu ne, lokacin cikar burinsu, me yake nufi da kin amsa wayarta idan shi ya kasa kiranta?
Kwanansa bakwai da baro Hafsat a Jimeta ya yanke wa zuciyarsa komawa. Wannan ne kadai mafita a gare shi, ya koma ya samu Hafsat ya gyara dingimemen kuskurensa ko rayuwarshi ta koma daidai, zai lallaba ta ya karbe takardar... ya yayyagata kafin kowa ya gani, zai maida ita dakinta kafin kowa ya ji. Ya godewa Allah ya yi sakin da addini ke so zuciya bata kaishi ta baro bakidaya ba! Idan ya samu ya dawo da Hafsat sai kuma ya san ya zai yi da Muazatu. A wannan gejin yana jin zai iya karya alkadarinsa ya zauna da su su biyun. Ya fahimci abin da yake kin fahimta da gangan; Hafsat ba ta shigo rayuwarsa don ta fita ba, ba ta shigo zuciyarsa don ta yi KWANGILA ta wuce ba... Ba mata irinta ne ake aura a saki a lokacin da ake so ba. Ba mata irinta ake saki don a samo wasu ba. Ba mata irinta ke barin gidan auren su na farko zuwa wani, ba tareda kwakkwaran dalili ba. Irin Hafsat saidai wata kaddararta daban mai karfi ta raba su da gidansu na farko (mutuwa) amma ba common saki irin wannan ba. Ya yarda ya amince a cikin mata akwai virtuousones;Their prices is per above rubies! Baa amfani da su don cimma wata manufa sai don biyan bukatar rai kadai! Ya yarda ya amince zuciyarsa SOYAYYAh ta ke wa Hafsat ba irin wadda ta ke yi wa Muazatu ba... Idan abinda yake ji a kan Hafsat shi ne soyayyah zai so wani masanin ilmin zuciya ya taimaka mishi, ya fada mishi wanda yake ji a kan Muazatu kuma mene ne shi???
Ya tsaya, ya nutsu, ya kintata, ya yi estimating, sai ya samu cewa the feeling is totally different....Ba soyayyah kadai yake yi wa Hafsat-Suhaanah ba, har da wata boyayyar kauna yar usuli mai yawan kintace. Yana begen sake ganinta ko da sau daya ne, yana kewarta cikin gidansa... Har ila yau yana nadamar yin AUREN KWANGILA da ita... yana nadamar yin amfani da halitta mafi soyuwa a zuciyar mahaifiyarsa don son cimma wata manufa. Watakila Ubangiji ya canza zuciyarsa a kanta ne don Ya ganar da shi kuskurensa.
Duk ilmin addinin da yake da shi bai yi amfani da shi ba, ya sa kafa ya take saninsa saboda soyayyar Muazatu data rufe masa idanu. Sanin kansa ne babu wani aure na kwangila a cikin addini, kai duk wani aure da za a kafa shi a kan wasu sharudda ko a deba masa waadi bai inganta ba a addinin musulunci. Duk wani aure da za a yi shi ba ka kusanci iyalinka ba har tsayin watanni ukku ba tare da dalili ba, shi ma ba cikakken aure ba ne! Ya zauna ya cutar da Hafsat watanni goma sha biyar bai taba sauke nauyin auratayya da Allah ya dora a wuyansa ba ba tare da hujja wadda addini ne ya tsara ta ba. Babu mamaki don Allah ya hukunta shi da soyayyar Hafsat da ta hana shi nutsuwa a lokacin da ya haramtawa kansa ita. Ta tsayar da duk wasu daily activities na rayuwar cikakken mutum a gare shi. A tsayin kwanakin nan bakidaya a dakin Hafsat yake kwana a kan gadonta. Barci gwanin iya sata kadai shi ke sace shi, shi ma duk inda assalatun fari ta ke zai bar idanunshi. Zuciyarshi ta dora daga inda ta tsaya na tunanin hanyar da zai bi ya maido Hafsat cikin rayuwarsa ba tare da kowa ya ji ya gani ba. Babu mafita ban da komawa ya cimmata a Jimeta.
Bai kara fahimtar cewa ya fita daga saiti ba, sai da ESQ Ahmad Kutama ya kawo wasu manyan files ya ajiye a gabansa. Da mamaki yake dubansa kafin ya janyo kujera ya zauna a gabansa.
“Check these files for me properly,please.
Janyo su ya yi gabansa yana dubawa, shi ya rubuta clues na shariar da za su yi sati uku masu zuwa, amma me? Clues din ba su da alaka da wannan shariar na wadda za su yi kafin waccan ce. Lumshe idonsa ya yi ya bude a hankali, Im so sorry. Kawai ya iya cewa.
Ahmad ya bi shi da kallon tsaf! Ga shi dai ya yi shigarsa tsaf cikin suit kalar grey da ratsin fari ta ciki kamar yadda ya saba,but its obvious that he is definitely upset... alamu ma sun nuna kwana biyun nan he didnt shave his face, sannan gashin kan ya cukurkude alamar ba ya samun extra kulawar da yake samu a baya duk da shi ba maabocin yawan askin bane amma kula yake da sumar sa sosai. Ya san yana da aure don har da shi aka raka shi dakin matarsa balle ya ce rikicin soyayyah ya fada. To me aure ba ya iya fadawa soyayya for the second time? Ahmad ya tambayi kansa.
Bayan wannan shi dai ya san Abdulazeez bai da matsala, dan gata ne na karshe, gatan da ya sa duk ya riga su aure. Saboda Babansa ne ya gina masa gida. Su kuwa sai haya suka kama cikin Abuja. Shi nasa wata biyu kenan, na Abdallah wata hudu. To ko kuma ta gidan ce ta ke birkita shi haka? Duk zai iya yiwuwa. Ya san Abdulazeez da shegen zurfin ciki a kan abin da ya shafi matarsa. Bai taba zama yayi hirarta da wani a cikin su ba. Ko suna hirar yammatansu kafin suyi aure shi baya magana. Haka bayan sunyi aure suna zancen amaren nasu a gabansa irin sun makarar dasu ko makamancin haka ko kai baya dagawa balle ya tofa. Amma duk da haka ya samu kansa da son taimaka masa koda da shawara ne don bai taba ganinsa cikin wannan halin ba. Ga shi alamarin har yana so ya shafi aikinsa. Abdulazeez din da ba ya barinsu su yi kuskure ko kankani yau shi ake yi wa gyara mai girma haka.
Gyara zamansa ya yi ya fuskance shi sosai.
Me ye matsalarka Barrister?
Yau karo na farko a rayuwarsa neman wanda zai budawa cikinsa yake yi, ko zai samu wata shawara wadda ta fi tasa inganci. Ya yarda ya gama lalata rayuwarsa in bai je Jimeta a gobe ba har takardarsa ta je hannun mahaifiyarsa. Ba hukuncin da zata yi masa yake tsoro ba; bazata taba yarda da dawowar Suhaanah gareshi ba! Ta sha gaya musuopportunity comes only once in life (dama tana zuwarwa dan adam sau daya ne a rayuwa) kuyi amfani da ita a sanda kuka sameta. Yau ba yana son Hafsat-Suhaanah don Mammah ba ne, sonta yake a karan-kansa da soyayya mai azabtarwa. Bai san sanda ya buda baki ya ce da Ahmad.
In an yi saki, ya ake a gyara? In an yi alkawari aka kasa cikawa daga baya ya ake a yi kaffara?
Gaban Ahmad sai da ya fadi, bai san sanda ya ce a tsorace, You mean ka saki Hafsat? Auren shekara daya kacal?Kai kuwa me tayi maka haka da zafi?
Kamar zai kife shi da mari ya ce, Ya zan tambaye ka, kuma ka bi ni da tambaya?
Ai ban san sakin wane iri ba ne. Ya fada cikin sanyin jiki.
Abdulazeez ya kwantar da kansa a kan teburinsa. Murya a raunane ya ce. Thisis the deadly mistake ive ever made, na sake ta Ahmad, amma ina so in dawo da ita. Dubi yadda na zama cikin sati daya kacal da yin sakin. Da farko na yi zaton Muazatu nake so a kanta, yanzu da babu ita cikin gidan na gane Muazatun ba ta da matsayi mai yawa a tare da ni. Ka taimake ni Ahmad ba ni da idea.
So yake ya ce da shi. Ai mun gaya maka, watarana za ka so yarinyar nan ko da za ka yi mata kishiya. To amma tausayin Abdulazeez din ya hana shi fadin hakan, yanzu ba lokacin raddi ba ne. Lokacin neman mafita ne. Kuskure ne ya riga ya yi shi sai a nemi hanyar gyarawa in mai gyaruwar yayi. Bai nemi baasi ba, cike da fargaba ya ce.
Sakin guda nawa ne?
Ba tare da ya dago ba ya ce, I think daya ne. A gurguje ma na rubuta ina tsoron ta zo ta ganni ina rubutawa. Ahmad proffession dina bai kare ni da komai ba da na kasa gane ba hanyar samo Muazatu na bi ba, hanyar kara tsanarta a zuciyar mahaifiya ta na bi. Hanyar kara nesanta kaina da ita na bi. A karshe in kare da babu ko dayansu muddin zancen sakin ya je kunnen Mammah.
Ahmad ya dafe kai.
Yanzu ina Hafsat din?
Tana garinsu Jimeta.
Just call her now (kira ta yanzu) ka ce da ita na maida ke dakinki, shi ne muhimmi kafin komai. Ko ta yarda ko bata yarda ba; ta maidu.
Wayar ya janyo cikin kasala duk da ya san ba samun nata zai yi ba, amma haka ya yi ta gwada jera kiran yana katsewa. Ya dubi Ahmad cikin rauni.
Ta dade da yanke communication da ni, na tabbata ta dade da ganin takardar, da kyar in bata canza layin waya ba.
Ahmad dai haushin Abdulazeez kamar ya kashe shi. Wai a kan wata da yake hange a waje ya saki ta gida, ba dole hakki ya rikide masa zuwa soyayya ba?
Tunda gobe weekend ne za ka iya zuwa Jimetan, make sure ka kwace takardar ka kuma gaya mata ka maida ita ta ji da kunnenta. Ita kuma wannan Muazatun ajiye zancenta a gefe sai ka dawo da zabin mahaifiyarka. Abdulazeez kana tune da hakkin mahaifiya kuwa da karfin ikon da Allah ya ba ta cikin rayuwarka? Allah (S.W.A) Ya ce a bi ta, a bi ta, a bi ta kafin ya ce a bi uba. Amma budurwa??? Kana son ganin albarka cikin rayuwarka? Ta aura maka mace har mace mai daraja irin wannan ka saki? Inda hali mu tafi tare, mu hau jirgi don mu yi sauri. Ireallywant to help.
Daga office din kai tsaye gida ya wuce, ya samu Mammah da Daddy a falo suna cin abinci. Sun masa tayi, amma yau sam ya kasa cin abinci. Jiransu ya yi har suka kammala, Daddy ya dawo tsakiyar falo ya zauna a kujerun falon na alfarma. Budar bakin Daddy sai cewa ya yi.
Za ka wakilce ni a graduation din Ismael da Usman a America da Brussels jibi, zaka fara halartar na Ismael first,sai ku wuce Brussels na Usman tare dashi, ni ayyuka sun min yawa, passport dinka daka bani na sabunta maka watannin baya ya jima a wajena don haka tuni na gama maka shirin komai, thumb print kawai zakaje kayi da safe namaka bookingma, sai ka zaba tsakanin jirgin safe ko na dare. Na gayawa shugabanku dazu ya baka leave na sati daya na tura ka wakilci kuma ya amince, zakayi sati daya sai ku dawo tare da su duka. In an kwana biyu kuma ni sai in je wa Haleem visit a Sweden.
Dukkansu babu wanda bai lura da yanayin canzawar fuskarshi ba. Wata irin canzawa kamar an aiko masa da sakon mutuwa, fuskar har wani brown ta koma. Da kyar ya iya hadiyar miyau, cikin damuwa ya ce.
Daddy Jimeta za ni gobe.
Mammah ta ceJimeta kuma? Cikin mamaki sosai, ta cigaba da cewa. Dan zaman da za ta yi cikin yan uwanta na sati biyu kacal za ka haramta mata karashe shi? Ina ce next week za ta dawo? To ban yarda ba, wannan rashin hakuri da rashin kawaici har ina?.
Daddy ma yana bayan Mammah, ya ce, Ba za ka je Jimeta ba sai ka dawo daga graduation din nan sai kaje ku taho tare.
Ya amsa a ladabce,kansa na kasa, kasancewar yasa a ransa bazai kara jayayya da iyayensa ba har karshen rayuwarsa! Amma kallo daya za ka yi masa ka fahimci bai so wannan tafiya ba. Tamkar wata obstacle ce ga isa ga Hafsat da gyara gundumemen kuskurensa da wuri. Zuciyarsa na lallashinsa da cewa, Hafsat-Suhaanahwill not expose his shortcomings, za ta yi masa uzuri kamar yadda ta saba, za ta rufa masa asiri kamar yadda ta saba, zata jira shi har ya dawo kafin ta dawo Abuja bazata dawo ita kadai ba komai dadewar da zai yi balle sati daya kacal, tunda ma ai shi zai je ya dauko ta wanda dole a jira ya dawo.
Abin da Abdulazeez Dakata ya manta shi ne duk yadda muka kai ga tsara wa kanmu alamura sai Allah ya nufa. Bai yiwuwa mu yi ta tafka kuskure yadda muke so mu ce zamu gyara komai a lokacin da muka ga dama. Allah yana ara mana dama mai dumbin yawa a rayuwa mu yi ta yin abin da muka ga dama, rana daya in Ya tashi kama mu ba Zai ba mu damarrepentingna minti daya ba. Wasu alamuran na zuwa cikin rayuwarmu don su zama iznah a gare mu.
SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI
07030137870
*Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama*
*****
A falo ya tadda Hafsat, ta yi daidai da takardu irin na zane manya-manyan nan tana zana World Atlas. Wani assignment ne na cikin hutu (holiday assignment) aka basu akan wani kwas map analysis. Zane ta ke yi na kwallon duniya world map ta maida hankalinta kacokam kan abinda ta ke yi. Idan ka kalle ta a zuciyar ka abinda zaka fara cewa shine; (A Geographer withdetermination and enthusiasm). Ko shigowar motarsa ba ta ji ba balle takun sawunsa. Tsayawa ya yi a bakin kofar shigowa falon ya jingina da kofar hannunshi na hagu na dogare da kofar dayan na cikin aljihun wandonsa. Langabar da kansa ya yi gefe yana kallonta. Watanni goma sha biyar kenan cif da aurensu, wanda ya yi daidai da SHEKARA DAYA da watanni uku.
Abubuwa da yawa sun faru cikin wadannan watanni goma sha biyar din wadanda ba za su taba shafewa daga kwakwalwarsa ba! Masu dadi da marassa dadi, na ban dariya dana ban haushi. A cikin wadannan watanni, Muazatu ta gama LLB tayi karatu a Law-school ta gama ta fito a matsayin cikakkiyar lauya daidai da burinsa na matar da zai aura.
Ya zauna da Hafsat-Suhaana cikin wadannan watanni zama wanda aka tsara yadda zai kasance tun farko, amma abin mamaki ya rikide ya jirkice zuwa ba yadda aka tsara shi ba. Ya zo da abubuwa masu yawa beyond his mere or casual assumption......
Awata rana irin ta yau daidai wannan lokacin yana rungume da Muazatu a ofis dinsa yana daukar mata alkawurran da baa so musulmi ya dauka saboda ba shi ke iko da rayuwarsa ba. Gabadaya rayuwarmu rubutacciya ce tun haihuwarmu a Allon Lauhul-Mahfuz. Manzon Rahma (S.A.W) ya ce, yana daga cikin alamomin munafuki in ya yi alkawari sai ya saba, in aka amince masa sai ya yi hainci, idan ya yi zance sai ya yi karya (Bukhari).
Ya yi wa Muazatu alkawari, in ya saba sunansa MUNAFIKI. Ya yi wa Muazatu zance tun daga karkashin zuciyarsa, in ya canza shi ya yi KARYA. Muazatu ta amince masa, in ya zabi Hafsat ya barta ya yi HAINCI. Ta rabu da kowanne Da namiji saboda shi. Shekaru ukku kenan cif tana dakon soyayyarsa mai wahala a zuci. Lokaci ya zo da zai aiwatar da kalaman bakinsa yana so ko ba ya so. To amma anya babu babban kuskure a cikin alamarin nan? Yaya rayuwar Hafsat za ta kasance in ya rabu da ita? Karatunta zai dore? Mammah za ta barta ta ci gaba da makaranta babu aure? Zuciyarsa wadda har yau ba ta baiwa Hafsat matsugunni guda daya a cikinta ba ta ce da shi.
Tun