Showing 54001 words to 57000 words out of 168255 words

Chapter 19 - Auren Kwangila Book 4 Hausa Novel Complete

Takori   

12 Dec 2024

301

kai daga kallonta ya mayar bisa (computer).
Tunanin me ka ke ta yi haka Barrister ina ta magana ba ka jina?
Ina jinki.
To amma ka yi shiru?
Ki yi hakuri ba zan iya duba miki files din nan ba, amma zan bai wa Abdallah. Ni ma in zan samu mai rage min nawa ayyukan zan so.
Surayyah ta dan bata rai, Ka ce dai kana tunanin budurwarka, amma ba ka da ayyuka da yawa, tunda jiya ku ka gama shariar da ka ke yi.
Murmushi ya yi har dimple dinsa ya lotsa gashin saman idonsa ya kwanta sosai a kan lumsassun idanunsa. Ba tare da ya dube ta ba, hannunsa a kan (system) dinsa ya ce, Budurwa kuma? Ai an dade da wuce wurin Surayyah. Im married. Sai bayan ya fada zuciyarsa ta jefo masa tambaya.
Are you really married?
Ya girgiza kai da sauri, a fili ya ce.
No, not really.
Ita dai Barrister Surayyah ta saki ido da baki da kunne duka tana kallonsa tana saurarensa, shaidaniyar zuciyarta na kara kawata mata shi ta kowacce fuska, shikadai ke burgeta duk fadin kotun, akan sa mantawa take ita matar aure ce, ba ta ma fahimci me yake fada ba. Ya kashe system din ya dube ta.
Ki wuce gaba a motarki zan bi ki a baya, sai dai bana gudu a titi ni kada ki bace mini. Ni ma zan sayi Jamb form.
To mu yi amfani da mota ta mana?
Haram, in shiga motar matar mutane.
Ni zan shiga taka.
Allah ya kiyashe ni daukar mace a gaban mota ba Muazatu ba.
Sosai abin da ya fada din ya yi mata ciwo, ta ce. Ai sai ka tafi kai kadai, ni ban iya tafiya a hankali ba.
Ta juya, ya bi bayanta yana fadin, Ga shi kuma bana niyyar yin abu in fasa.
Ta zumburo baki suka fice tare, kowa ya shiga tasa motar a haka suka tafi. Da gayya Surayyah ke sharara gudu shi kuma bai yi kasa a gwiwa ba wajen binta, har suka isa. Suka nemi wuri suka yi parking ita ta shige gaba suka sayi forms din, babbar yarta ta sayawa, shi kuma ya saya da sunan Hafsat Hamza Atiku Dakata.
A hanyarsu ta dawowa ya yi mata signal ya dauke kan motarsa ya nufi gida, bai koma (office) ba duk da lokacin tashinsa bai yi ba. Yana so ya cike mata da sauri tunda ya ji cewa babu isasshen lokaci.
Yaushe rabon duniya da ayyaraye!
Suhaana ta ce a ranta, lokacin da ta tsinkayi muryar mijinta Abdulazeez na yi mata sallama a kofar kicin, ta bada baya tana soya miya a kan gass wadda za ta sanya a firji ta yi mata kwana biyu tana amfani da ita, don kayan abincin da ke cike da firji da freezer da nama da kifi duk sun kamo hanyar karewa, girke-girken da ta saba dole ta hakura ta koma cin fara da miya. Su kansu kayan miyar daga wadannan da ta ke soyawa babu wasu, cancana abinta za ta yi tunda ba ta san ina za ta nemo wasu ba. Kayan abinci kam suna nan a shake a buhunhuna da katon-katon ta san har gaba da shekara ba za su kare ba.
Yau kwananta hudu ba ta sanya Abdulazeez a idonta ba, ta kan dai jiyo bare-barensa a kicin in ya dawo kafin magriba, lokacin kam ita ta kammala abin da ta ke yi ta shige daki don ta lura yana jin dadin yin aiki a falon in tana nan kuma sai ya kuke a daki, shi ya sa ta haramta wa kanta zaman falon don ya sake a gidansa.
Amma abin mamaki yau ga shi a gidan karfe hudu na yamma, wai yana yi mata sallama. Amsawa ta yi ciki-ciki ba tare da ta juyo ba. Sosai ta ke jin kiyayyarsa a ranta don ta lura bayan rashin so ba shi da imani ko kankani, ba shi da kirki, ba shi da adalci.
Wasu tawagar hawaye suka shimfido a kan kundukukinta, ba ta yi wani hobbasa na hana su zuba ko share su ba. Zubar tasu ne kawai zai sa ta ji sanyi a zuciyarta. Ko da ya ce za su yi AUREN KWANGILA, auren cin gashin kai ba ta zaci har da rashin sanin halin da junansu ke ciki ba, yanzu in mutuwa ta yi haka gawarta za ta rube ta lalace a daki sai ta fara doyi zai sani. In ciwo ta ke sai ya ci ya cinye ta zai sa ni.
Tun tana tunanin Mammah da mutanen gidansu, har ta hakura ta daina, ta yarda Mammah ta aurar da ita ga azzalumin danta ne don ta gaji da ita, ya kashe ta da bakin cikinsa duk su huta. Hawayen suka fara gudu suna sauka a kan kirjinta, hakoranta na karkarwa suna haduwa da junansu saboda kuka mai cin rai, amma ta sa hannu ta toshe bakinta ba ta son amon kukan nata ya fito fili.
Abdulazeez ransa ya so ya baci da yadda ta yi watsin Allah-tsine da shi a bakin kofa, ta kuma amsa sallamarsa kamar ba ta so. Sannan ta ki juyowa. Kwafa ya yi ya zuro jikinsa ya idasa shigowa cikin kicin din yana kallon abin da ta ke yi. A matsayinsa na wanda rabonsa da abinci tun daren jiya, sosai miyansa ya tsinke da wannan hadaddiyar miyar wadda ta ji naman saniya zuku-zuku sai tashin kamshin spices da mushroom curryta ke yi. Ya hadiye miyau mukut! Ya bi ta da harara duk kuwa da ance aikin banza harara cikin duhu don kuwa bayanta kawai yake iya gani.
Sallama fa nake yi amma ki ka yi banza da ni?
Haushi ya ba ta sosai, kamar ta juyo ta dalla masa mari amma ina! Ko tsakiyar idanunsa ba za ta iya kalla ba balle mummunar magana ta hada su har akai ga abin da zuciyarta ke kissima mata.
Na amsa ai. Ta sake amsawa ciki-cikin. Cikin hadiye kukanta gabadaya. Kwafa ya sake yi ya juya ya fice yana fadin, In kin ga dama ki zo ki yi min bayani in cike form dinki ne na jamb.
Ai ba ta san lokacin da ta saki ludayin miyar a kasa ba ta biyo bayansa. Jin karar faduwar ludayin ne ya sa Abdulazeez ya juyo sai ganinta ya yi har ta kusa cimmasa, fuskarta jage-jage da hawaye. Wani abu mai kama da tausayi ya so ya tsirga masa, yana mamakin son karatu irin nata, wato fushi ta ke da shi sosai a kan laifin da bai sani ba, amma jin zancen jamb ta manta komai ta biyo shi har ta manta ta bar wuta a kunne.
Dakatawa ya yi, ta zo ta shige shi ta yi falo ya dawo ya kashe gass cooker din da kansa, ya rufe mata miyar sannan ya bar kicin din.
A falon ya same ta a tsaye, zama ya yi cikin (3 seater) ya jawo briefcase dinsa ya fito da scratch card din da receipt ya daga lumsassun idanunsa ya dube ta, Kawo takardunki, sai ki zauna mu cike.
Zan iya cikewa da kaina.
Kina da system ne?
Akwai tawa ta gida, amma babu internet connection.
Ga mamakinta sai ya tura mata jakar laptop dinsa.
Dauki wannan ki yi da ita, ki hanzarta ki gama zuwa gobe sun kusa rufewa.
Dauka ta yi ta matsa gabansa ta karbi scratch din da sauran takardun ta tsugunna a gabansa ta yi shiru. Tunanin me ya tsayar da ita yake yi, sai ji ya yi can a tsakar kansa tana fadin, Na gode sosai.
Ya bude idanunsa sosai a kanta daga lumshewar da suke yi da kansu, You dont need to thank me. Its part of our contract, kin manta ne?
Girgiza kai ta yi, a sanyaye ta ce, Ban manta ba, duk da haka na gode.
Sai ya kasa ba ta amsa ya bi ta da ido har ta mike ta shige daki dauke da system din cikin nutsuwa.







SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI
07030137870

*Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama*

A yadda ransa yake a jagule din nan, ya san Muazatu ce kawai za ta iya tafiyar da damuwarsa, ga shi ya mata laifi, ya bata mata rai tun jiya yake ignoring call dinta. Tun kafin ya karasa dakinsa ya kira ta. Ya manna wayar a kunnensa ya murda kofar dakinsa, ya shige ya mayar ya rufe, har da murza key.
Kamar a mafarki Muazatu Rufai wadda ta fita hayyacinta cikin kwana biyu ta yi firgai-firgai saboda tashin hankalin da ta samu kanta a ciki, ta ga sunan Habeeb-qalby da ta sanya wa Abdulazeez Dakata na yawo a screen din wayarta. Sai ta dauka gizo ne idanunta ke mata kamar yadda suke mata tun jiya, don haka har kiran ya kare bata taba wayar ba, sai ma wasu azababbun hawaye masu dan banzan yaji da ta ji sun kwaranyo mata. A karo na biyu wayar ta ci gaba da ba da ruri da Habeeb-qalby, ta kai hannunta ta damke gashin kanta tana ta cije labbanta na kasa da hakoranta tana rokon Allah in mafarki ta ke ta farka.
A nasa bangaren Abdulazeez jikinsa ne ya yi sanyi, ya tabbatar bai kyauta wa masoyiyarsa ba, kamar wani wanda ya yi auren soyayya da zai janye jiki daga gare ta don kawai an kawo masa amrya? To me ye gaminsa da amaryar da ya janye wa Muazatu dominta? Wata zuciyar ta ce da shi, Ba don amarya ba ne, kalamin bakinta ne. Ba ta iya magana ba. Ba ya so kowa ya shiga (personal life) dinshi hatta iyayensa haka Allah ya halicce shi, don haka yake kara kyamatar wannan auren, don a ganinsa Mammah ta shiga rayuwarsa da yawa ta rushe masa future ta hanyar aura masa yarinyar da ba ta yi daidai da tsarin rayuwarsa ba. Zai kuma bi duk hanyar da zai bi ya gyara rayuwarsa yadda ya riga ya tsara tun lokacin da ya mallaki hankalin kansa. Ya yi fushi da Muazatu amma ya huce, ya kuma kara tabbatarwa kansa ba zai iya rayuwa ba tare da ita ba, dole ya lallashe ta.
Ki yi hakuri Muazatu.
Abin da ya rubutakenan ya tura mata.
Muazatu ta karanta abin da Abdulazeez ya turo mata. Lumshe idanunta ta yi, wata rahma ta sauka a zuciyarta. Kalaman (are short, yet they mean alot to her) girmansu ya yi na ruwan kogi ya wanke zuciyarta. Duk da haka ba ta mayar da amsa ba, ba ta kuma kira shi ba sai da ya kara ragaita. Ya turo mata sako na biyu.
Muazatu please, Im sorry.
Sannan ya sake kira.
Wannan karon ta amsa kiran, amma maimakon ta ce komai, kuka ta sanya masa. Kyale ta ya yi ta yi har ta gaji. Ta share hawayenta sannan ta ce,
Na huce.
Murmushi ya yi, ya gyara kwanciyarsa cikin niimtaccen gadonsa, ya ja quilt ya rufe rabin jikinsa, ya canza rikon wayar daga dama zuwa hagu.
So soon haka?
Murmushi ta yi kamar yana ganinta.
Tunda ka san ka yi min laifin, ka kuma amsa ka yi, ci gaba da fushin nawa na mene ne?
Au, ni ba ki san kin yi min laifi ba? Ki dubi tsabar idona ki ce wai.....
In ana sulhu ba a tone-tone. Ta katse shi.
Ki yarda to ba ni kadai na yi laifi ba, dukkanmu mun yi wa juna. Muazatu bana son raini, ko da aure tsakaninmu bai kamata ki ce min kada in kusanci matata ba. Ina ruwanki? This is my personal world, mind your own business. Im sorry once again for not picking your calls. In na ce ban yi kewarki ba na yi babbar karya. I love you Muazatu, you are the goal I want to achieve now, believe me or not.
Wata doguwar ajiyar zuciya Muazatu ta sauke, duk da kalamansa na farko sun yi radadi a zuciyarta, to na karshen sun wanke radadin. Haka yake, haka Allah ya halicce shi, ba ya boye gaskiyar abin da ke zuciyarsa don ya faranta maka, ba ya karya don a so shi, in za ka so shi ka so shi a yadda ka same shi. Ta dade da fahimtar hakan.
Im sorry too...
...and I love you more...
Dariya ta saki har da wata irin shesshekar shauki. Suka ci gaba da hirarsu yadda suka saba, amma ta yau ta fi ta kullum gardi.
Bayan fitarsa da rufo kofarsa Hafsat tasowa ta yi ta dauki ledojin da ya aje ya fice ta bude. Sunkin gasassun kaji ne suyar (YAHUZA) da juice da fresh milk da daurin (shawarma) har guda biyar. Harira ta yi sallama ta yi mata izinin shigowa. Ta aje mata abincin da ta dafo (express). Cikin sanyin muryarta ta ce da ita,
Ga shi kuma ya sayo da baki dafa ba.
Ba komai, gobe sai in dumama in ci.
Ta mika mata leda daya ta karba, ta yi godiya ta dau abincin da ta kawo ta fita tana fadin,
Allah ya tashe mu lafiya, in kin ci ki sha magungunan naki.
Hafsat ta ce, Insha Allah. Ta fita ta rufo mata kofar.
Zama ta yi a tsakar dakinta ta ci kazar nan ta koshi, ta sha magani sannan ta yi sallolin nafila kamar yadda ta saba. Ta sanya kayan barci masu laushi, ta yi addua ta kashe wuta mai haske, ta bar dim-lightta kwanta.
Asuba ta gari Hafsat-Suhaana.

******
Washegari da safe bayan ta yi sallar asubah ta yi wanka. Ta shirya tsaf cikin wata lallausar atamfar (holland) koriya shar, ta yi daurin kai sosai ya zauna mata a kai cif-cif gwanin ban shaawa. Dressing din da bai dameta ba amma Mammah tace dole ta dinga yin shi yanzu ta rage zama da dogayen rigunan nan nata, ta feshe jikinta da turaruka masu kamshi, wadanda Mammah ta cika mata gaban madubi da su. Ta zura kyawawan kafafunta cikin (flat shoe light green) samfurin polota fito falo.
Motsin Harira ta ji a inda ta fahimci kitchen ne, sai ta bi ta can. Daga bakin kofa ta tsaya tana dan murmushi,
Anty Harira ina kwana, mun tashi lafiya?
Harira ta saki dariya jin an kira ta da Aunty, ta juyo, Lafiya kalau Hansatu, ya karfin jikin?
Na warware, ba inda ke min ciwo.
Haka ake so, na kammala abincin kari ina zanik-kai muku?
Me ya sa ba ki jira ni na zo mun yi tare ba? Jiya ma haka ki ki yi girki ke kadai.
Murmushi Harira ta yi, a ranta ta ce, Mene ne amfanina?
A fili kuma ta ce, Kina fama da rashin lafiya zanis-sa ki aiki Hansatu?
To na warke. Yanzu tare za mu dinga yi, ki yi shara, wanke-wanke da sauran ayyuka, ki bar min girki.
Shi kenan Hansatu, tunda haka kinka bida. Zo ki gani, ashe gidan cike yake da kayan abinci, firinji cikke da nama da kihi har da markadadden kayan miya bokiti guda.
Hafsat ta idasa shiga kicin din suna dubawa tana sanya wa Mammah albarka cikin zuciyarta. Ita ta kwashe tangarayen da harira ta zuba soyayyen dankali da Agada (plaintain) da farfesun kayan ciki ta kai kan kyakkyawan dining table wanda aka yi wa muhalli a can wata kusurwa ta falon. Ta dawo ta dauki flask din shayi da tea cupsda kayan hadin shayin duka ta jera su a diningta samu wuri a daya daga jerin kujerun falon ta zauna.
T.V ta ke son kunnawa, ba ta san ya za ta jona ta ba, sai ga shi ya fito rike da gown dinshi a hannu (bakar rigar lauyoyi) da wiga kansa (hular lauyoyi) yana tsuke tie din wuyansa. Gabadaya falon ya gauraye da kamshinmasculineturarensa (Creed Aventus) har Hafsat ta ji turaren jikinta ba kamshi yake ba. Kafafunsa cikin (black covers) kirar Italy yana takun nan nasa gab-gab-gab shi ba sauri ba, shi ba tafiya a hankali ba. Idanu suka hada sosai, dukkansu sai suka dauke kai cikin koinkula. Ita ta fara dauke idonta ta mayar wani gefen, wata hudubar Mammah ta fado mata tun tana karama, Duk inda ki ka ga babba ki gaishe shi ko da da shekara ya girme miki. Sakamakon hakan sai ta samu kanta da zamowa daga cikin kujerar da ta ke zaune cikin nutsuwa bakinta ya ambato kalmar, Sabahul khair. Da accentdinta mai taushi.
Barrister Abdulazeez Dakata ya mirgina kai ya amsa a ginshire, Lafiya lau.
Ya ci gaba da tafiya a falon zai fice. Hafsat ta samu kanta da cewa, Ga abincin karin kumallo. Cikin harshenta na Brussels. Sai bayan ta fada ta shiga cikin nadama da juyayin wa ya aike ta? Bai ce ta shiga rayuwarsa ba a rayuwar auren da ya shirya musu. Amma ga mamakinta sai ya ba ta amsa da turanci, don shi ba wai ya kware a yaren nasu ba ne, amma yana ji.
Na makara, amma a sanya a basket a sa min a mota.
Cikin nutsuwa ta mike ta shiga madafin ta dauko (food-basket) sabo fil ta dauko kanan food flasksmasu kyau ta fito ta juye kowanne a flask daya. Ta dauki filas din ruwan zafi zata saka cikin basket din sai ya ce, Bar wannan, inada kettle ina shan (coffee) a office.
Kanta a kasa ta ce, Toh.Ya fice, ta bi bayansa tana dauke da kwandon.
A jikin kofar motar ta tsaya ya bude ya shiga, sannan ya mika hannu ya bude (lock) din kujerar baya ta sanya basket din. Sai ya ce mata,
Thank you.
Ya rufo kofar.
Juyawa ta yi ta koma, shi kuma ya murza kan motarsa kirar (GMC) ya yi reverse Danfulani ya bude masa kofa ya fice.
Kicin ta leka ta tadda Harira a dining din kicin din tana karyawa, ta gyare koina tsaf.
Sannu da aiki Anty Harira, ki dinga zuba wa maigadan gidan nan abinci don Allah.
Harira ta ce, Ba sai kin fada ba, na ba shi tun dazu.
Ta ce, Ok.
Falo ta koma wajen kayan wuta ta yi ta kokari har ta jona T.V ta zauna da remote a hannunta, har ta nemo wata tashar Larabawa suna girke-girken kasar Turkiya da yadda ake sarrafa su. Sosai abin ya dauki hankalinta. Sai ta ji shaawar gwada abin da suke koyarwa don haka ta shiga dakinta ta samo jotter da biro ta soma (jotting-down) daki-daki yadda za ta gane. Wani irin tsire suke nuna yadda ake yi na nikakken nama mai suna adana kebabi da recipe din, a zuciyarta tana fadin ta samu abin yi za ta gwada su ci ita

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login