Showing 120001 words to 123000 words out of 168255 words
yau ba haka ta ke. Ita kuma Mammah dalilin rashin walwalarta shi ne kada Abdulazeez ya ga fuskarta ya dame ta da wannan nataccen ban hakurin nashi. Har aka gama cin abincin daga shi har Hafsat babu wanda ya ci wani abin kirki.
.SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI
07030137870
*Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama*
A yammacin ranar Azumi ta dawo. Kusan Abdulazeez ya fi kowa farin cikin dawowar Baba Azumi, mai sonsa da jin kansa. Ya tabbata za ta taimaka masa sosai wajen shawo kan Mammansa.
Tun dawowarta ta fahimci yadda ta tafi ta barsu haka ta dawo ta tadda su, ba wani ci gaba daga bangaren uwargijiyarta. Ita ta ci gaba da kula da komai na Abdulazeez, tsaftar dakinsa da toilet dinsa da cikinsa. Ba tun yau ba ta san ba komai yake ci ba. Su sun yi rayuwa cikin turawa don haka suna amfani da ire-iren abincinsu sosai-sosai musamman kayan gwangwani. Abdulazeez kuwa na son Nigerian Food musamman na Yarbawa su Amala, sakwara, miyar ganye;su Ugu alayyahu, egusi, water leaf, da kifi da ganda saboda zamansa a kudu (Ibadan da Lagos gidansu Muazatu), su ta himmatu wurin yi masa nasa daban, wani lokacin su Hafsat rai na biyawa ta ce kuma ba mai ci har Maman nasu. Mammah kan kyabe baki ta ce,
Ina ruwan oduduwa dangin Yarbawa. Shi ya sa duk halinsu na naci kun diba. Ban da haka na ce a bar min gidana, a bar min ya ta, a je a auro yar Yarbawa kun ki, har asalin uwarta na jiyo ba yar Jigawa ba ce yar Ogun ce. Uban ne dan Jigawa.
Baba Azumi kan rausayar da kai ta ce, Kin san wani ba ya auren matar wani, jiya mun ga aurenta a obashin (ovasion magazine) Ismaeela ya kawo mana. Mammah ba ta kara bi ta kansu ba.
Su Hafsat sun fara C.A don haka a dan tsukin ba ta da sukuni, test-test da assignment kawai suke yi. Yau litinin, Mammah za ta je ganin likita kuma ya yi daidai da lokacin shigar Hafsat test. Ba yadda ta iya ta ce Salisu ya kai ta, in ya ajiye ta sai ya dawo ya same ta a Diff Hospital. Ita ya fara ajiyewa a asibitin, sannan ya karya kan motar suka nufi NILE shi da Hafsat.
Danja ce ta tsaida su a wani shatale-tale. Barrister Abdulazeez Dakata a nashi motar, cikin shirin office yake (fully robed). Ya yi tsakin bata masa lokacin da danja tayi don ya makara, ya dan juya gefen damansa sai ya hango Salisu da motar Mammah, a kujerar baya Hafsat ce ta warware handout tana ta karatu. Magana ya yi masa ba ta san suna yi ba, sai ji ta yi Salisu ya gangara ya faka a gefen titi. Ta dago don ta tambaye shi me ya tsaya yi zai makarar da ita, sai ji ta yi an bude kofar side din da ta ke. Mutum na karshe da ba ta zaci gani ba, suna yin kwana uku a gidan ba su hadu da juna ba sabida yanayin aikinsa da lokacin dawowarsa very late gefen maghriba. Lokacin ita ta shiga sallah, sai wajen cin abincin dare kawai suke haduwa, ita kuma ta tsame kanta. Don ko ta zauna ba iya ci ta ke ba saboda idanun Abdulazeez da na Mammah, kowanne na kokarin ganin cewa idonsa ya hana abin da ba ya so. Mammah ba ta son wadannan idanun na Abdulazeez su yi tasiri wajen karya lagonta, tunda ta bi kowacce kafa ta communication ta toshe. Shi kuma nasa idon so suke su fahimtar da ita how miserable and helpless they aresaboda rashin ta cikin rayuwarsa yanzu. Don haka ko da ta daina zaman cin abincin Mammah ba ta ce don me ba, ta ma fi son hakan. Amma tana tabbatarwa Azumi ta kai mata nata daki kuma ta ci. Da safe kuma Azumi a basket ta ke sanya masa karin kumallo ya tafi da shi office ba ya son abin da zai makarar da shi, mutum ne mai tsantseni a kan aikinsa da muhimmancin lokaci.
Ajiyar zuciya ta yi sakamakon tunanin da ya tafi da ita kawai saboda arba da Abdulazeez a inda bata zata ba. Fuskarsa babu wasa ya ce.
Fito, ni zan karasa da ke.
Cikin damuwa ta ce, Ni ba zan fito ba, Mammah.....
Wallahi kin ji na rantse ko ki fito ko in dauke ki na fiddo ki, a kan me wani gardi zai fita da matata ni me ye amfanina? Kawaicin da nake yi ne ba ki san ina yi ba sai na fito da true colour dina?
Daga amon muryarsa ta fahimci a matukar fusace yake, Mammah ta gwammace Salisu ya kai Hafsat makaranta a kansa, Salisu ne trusted dinta, shi kuma dan taadda mai cutar mata da ya. Jikinta har bari yake ta cizgo jakarta ta fito daga motar, ba tun yau ba ta san duk abin da ya fada zai iya aikatawa.
Shi ya bude mata kofar gaba ta zauna ya rufe. Ya zagaya ya shiga bangarensa. Da matsanancin gudu ya fizgi motar. Ban da faduwa ba abin da gabanta ke yi, tunanin Mammah kawai ta ke yi. Me Salisu zai je ya gaya mata? Ta shiga ukunta! A wannan dan tsukin burinta kawai ta ci gaba da yi wa Mammah biyayya a kan duk abin da ta ke so. Ta fahimci duk abin da Mammah ta ke so ta fahimta. Ta kamma kanta, ta bi abin a sannu. Kada tayi garaje, kada tayi gaggawa wajen komawa cikin rayuwarsa. Namiji ba abin yarda ba ne. Sannan ba dan goyo bane. Balle mai wayo da wayewar kai irin Abdulazeez Dakata, the smartest person she have ever know. Ba ya fadin sirrikansa sai dai reactions dinsa su nuna. Kamar yadda Mammah ta kafe a kai ne, how sure she is yanzun yana sonta? How sure she is ya daina son Muazatu? Duk da ko yana sonta ko ba ya sonta yanzun doesnt mattertunda ta yi aure ta barshi.
Amma Mammah a kan gaskiyarta ta ke, shekara daya da watanni da suka kwashe tare karkashin inuwar aure me ya hana ya so ta? Sai bayan ya yanke ta daga cikin rayuwarshi ta dawo gaban wadda take sonta da kauna ta har abada? Wata zuciyar mai tsananin so da kare Abdulazeez ta ce. Ke ma me ya hana ki so shi da farko, sai bayan kin zauna da shi? Wanda ke nufin dukkaninku abu daya ku ke bautawa;You didnt get to know each other well sai bayan zaman.You are not close to each other sai bayan zaman. Soyayya kuma bata faruwa sai da kusanci. Soyayyar bata huda kowannenku ba sai a cikin zaman. Give him a chance Hafsat, reason with him. Zuciyarta ta ji tana yin wani irin laushi wanda ya sa ko da ta ga ya bar hanyar Nile ba ta damu sosai ba.
Sai dai ta sa a ranta cikin kowanne hali shell not betray her mother! Shellstand by her not by him (ba za ta ci amanar Mammansu ba, za ta tsaya a bayanta baa bayanshi ba). Ginin da ya nufa da su ya tabbatar mata ofishinsa ya kawo ta, (Federal High Court of Nigeria).
Ya yi parking a parking lot ya cire wayoyinsa daga cajin da ya sanya su a motar. Ya dauko suit-case da jakar system dinsa, wig dinshi a hannu ya fita daga motar. Tsayawa ya yi yana jiran ta fito ya rufe motar. Hafsat ta ki ko da motsi. Kyale ta ya yi ya je office din ya ajiye kayan hannunshi ya dawo, da ya shigo cikin motar juya masa keya ta yi tana duban taga. Murmushi ya yi ya ce,
Me ki ke nufi da ni ne yarinyar nan?
Ba tare da ta juyo ba ta turo baki, Laifin me na yi da za ka kawo ni kotu? Test zan yi amma already ka sa ta subuce mini. Za ka iya jin damuwar hakan sosai a amon muryarta, domin ta shirya wa gwajin sosai ta kwana tana karatu.
Hannunta ya fizgo ta yi juyowar da ba shiri, a fusace ya ce. To hell with your test, duniya kawai ki ka sa a ranki ba kya tunanin lahirarki. Da kin san yawan zunubin da Mammah ke sanya ki kina kwasa da kin tausaya wa kanki Hafsat. Tana tare da mijinta kullum tana gyara aljannarta, ta nesanta ki da naki kina ta kusanta kanki da wuta. Shin ni ba mutum ba ne, ba ni da feeling? Shekaruna talatin da uku har yau ban san ya ya aure yake ba. Hafsat ko ba kya sona dole ne ni ma ki yi min biyayya yadda ki ke mata. Ko kuwa shi kenan saboda na yi laifi ni rayuwata ta kare?
Kuka ta soma yi a hankali, ta rasa inda za ta tsoma zuciyarta, shi da Mamansa sun sa ta a kwana, kowanne gani yake shi ya kamata ta yi wa biyayya, a wannan lokacin ba ta san me ya kamata ta yi ko ta ce masa ba banda;
Me ka ke so in yi maka yaya Azeez? Hannunta da ke cikin nasa ya janyo a hakali ya hade ratar da ke tsakaninsu. Ajiyar zuciya kawai suke yi dukkanninsu cikin motar. Wata irin nutsuwa da suka dade rabonsu da ita ke overwhelmingdinsu tun daga kwakwalwa har babban yatsar kafarsu. Tsawon mintuna ba wanda ya iya yin magana a cikinsu. Hafsat ce ta ankara mutane na gilmawa jefi-jefi suna aje motocinsu. A hankali ta zame jikinta daga nashi ta koma cikin kujerarta sosai ta zauna, ta lumshe idanunta, karfin scent dinsa da na air-freshner din motar suka hade da sanyin A.C suka bada wata atmospheremai dadi a cikin motar. Kansa ya kwantar a kan sitiyarin yana regaining hargitsewar bugun zuciyarshi. Sun jima a haka kafin cikin raunin murya ya ce.
Gidanmu nake so mu koma Hafsat direct daga wajen nan. Na roke ki kada ki ce min aah...
Kai ta shiga girgizawa da sauri showing resentment (cikin nuna rashin yarda) I cannot do this to Mommah (bazan iya yin haka ga Mammah ba).
Dagowa ya yi daga kan sitiyarin ya dube ta sosai cikin tsakiyar idanunta, duk da ta ki yarda su hada idanu ta san idonsa akanta yake. Then blame yourself kan duk abin da na zaba mana!.
Ya tada motar ya fita daga harabar kotun kasa, ya hau kan titin da zai kai shi titin Aguiyi Ironsi. Hafsat dai ikon Allah ta ke kallo, gabanta na tsananta faduwa don bata san me yake nufi ko ina zai kai su ba, sai dai zuciyarta na gaya mata... ko me Abdulazeez zai zaba musun nan ba alheri ba ne gare su.........!!!Mu karasa a littafi na hudu kuma na karshe. Kada ku damu, tare suke. Taku har abada Sumayyah Abdulkadir Takori
Buk 4
SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI
07030137870
*Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama*
A ganinta hakuri da biyayya shi ne abin da ya kamace su daga ita har shi. Duk abinda hakuri bai bayar ba rashinsa ma bazai taba bayarwa ba! Hafsat dai sai dago kanta ta yi daga tunaninta ta gansu a harabarRockviewHotelAbuja.
Kallon tsoro ta fara yi masa, amma ya ki ko ya dubi inda ta ke. Tana nan zaune ya je ya dawo ya bude kofar side dinta, jakarta ya fara daukowa sannan ya ce,
Mu je daga ciki.
A raunane ta ce Yayan Haleem,Hotel? Hasken fararen idanunta kadai da yadda ta wargazasu a kansa, suka gusar da duk wani tension da yake ciki. Yadda ta yi maganar ya kwaikwaya. To ko mu ma yan abin nan dinne ne?
Tsoron zuciyarta ya ninka na farko ganin Abdulazeez na nade hannun suit dinsa da zummar daukanta a gaban mutanen da ke shige da fice. Sauri ta yi ta fito, kiris ya rage ta fashe da kuka ta wuce gaba ta barshi a baya. Sai da suka shiga reception ta dakata har ya cimmata don batasan ina zata nufa ba, hannunta ya rike suka wuce cikin lifter. Suna shiga lifterta kwace hannunta ta harare shi ta gefen ido. Jinjina kai yayi, ya ce.
Ki harareni yadda kike so. Za ki yi bayani ne Hafsah.
A ranta ta ce Allah na kowa ne, tuni ya riga ya zame min gata.
Katin kofar ya sa a jikin kofar kawai ta bude,ya bata hanya ta wuce tukunna ya mayar ya rufe sai faman cin magani take yi. Fuskar nan kamar kunun kanwa sabida kirnewa. In ma ya lura to ba abinda zai iya tasiri bane akansa a wannan lokacin. Tun daga bakin kofar Hafsat ta gane yau ta shigo wata koma da taimakon Allah ne kadai zai fitar da ita. Ta san dai ya yar da jakarta da ke hannunsa a muhallin da bata tantance ba. Ya kuma raba ta da mayafi da dankwalin kanta cikin wata irinnutsuwa. Idanunsa na fidda wani chemistry zuwa cikin nata mai bayyana intent and in depth sorrow din da ya kasance ciki na rashinta lokaci mai tsawo. Sauran alamuran da suka biyo baya sun fi karfin ta iya bayyana su; Is a kind of gentle romance wanda ba ta taba sanin akwai irinsa a duniya ba. Tashin hankalinta ragagge ne sanin cewa she is safe a yau kam. Kwananta biyu da karbar bakonta kuma a iya saninta na addini da na boko mace mai alada miji ba ya kusantarta.
A yadda ya santa da tsoron ta shiga hannunsa ya yi mamaki da yau ba ta tsorata sosai ba, karewa ma she contributed a lotdonganin ya samu nutsuwar da bai da ita,wanda hakan ya zo masa kamar a mafarki. Don haka duniyar da suka fada mai nisan zango ceda ta shallake tunanin su. Sai da komai ya kankama ya gane Hafsat shigo-shigo ba zurfi ta yi masa (abun mata ce a jikinta). Alamarin da ya jefa shi cikin wani hali wanda ita kanta sai da ta tausaya. Gefen gadon ya koma ya zauna ya dafe kansa da ke tsananin ciwo hade da ciwon mara mai tsanani da ya bakunce shi, kodayake ya dade yana damunsa a kwanakin nan tun dawowarsa gidansu da Hafsat din da yake yawan gani kodayaushe tana gilmawa ta gabansa. Itama Hafsat din shiru ta yi, tayi tsuruu a gefensa kamar wadda ta yiwa sarki karya. Tana farin ciki da kubutarta, amma hakika tausayin Abdulazeez ya mamaye farin cikin. Ya cancanci samun farin ciki komai kankantarsa a yau daga gare ta. Duk da tana da tabbacin ko lafiyarta kalau ba za ta amince ba.
A hankali ta iso inda yake zaune a gefen gadon kafafunsa a kasa, ta kwantar da kai a bayansa. Cikin sanyin murya ta ce,
Im sorry.
Bai ce mata komai ba, wayarsa da ke ta kuwwa a kan bedside din ya dauka. Ya yi sliding kiran ya amsa.
Tunda ka san ba halina ba ne in zo in kuma fitan, kasan ina da uzuri ne. Ya jefar da wayar ya janyota ta dawo jikinsa. Wani irin kallo yake binta da shi da sai da ta kasa jurewa ta rufe fuskarta da hannunta daya.
Dole ki rufe fuska tunda kin san kin yi nasara a kaina, Mammah ta san haka ki ka girma kuwa Hafsah? Ita kullum tana miki kallon babynta a Jeddah acikin incubator? Anyway I appreciate, and I must thank Hafsah for this great moment.
Wata irin kunya da ba ta taba ji ba a rayuwarta ita ta lullube ta a wannan lokacin. Mikewa ta yi tana kumburi irin na nade tabarmar kunya.
Please Yaya Azeez mu bar wajen nan, ba mutuncinmu ba ne.
Ni mutunci na ne. Ya fada bai da alamar tashi sai wani lafiyayyen kallo da yake ta binta da shi.
Abubuwanta ta soma tsincewa a dakin wadanda yayiwa fatalin Allah-tsine, ta daura kallabinta ta yafa mayafi ta juya masa baya. Dariya ce ta kama shi ganin zip din rigarta ta baya bakidayaa bude, ya ce. InnaHafsatu saura zip din.
Hannu ta kai ta shafo wajen. YaIlahi! Wata harara ta juyo ta zuba masa tamkar idanun sa fado.Tasowa ya yi cikin takun nutsuwaya iso gabanta, idonsa kan bakin data ke ta turowa gaba.
“Lemme help.....(bari in taimaka).
Ta zumburo baki tareda ja baya. Bana so, ka bari!. Ya daga hannuwa sama daga taimako? Da na sani na yi shiru Mammanki ta gyara miki da kanta. Ya fada yana ja da baya cikin hadiye dariya.
Kansa ta yi da wani sabon kuka da ya zo mata nan take kamar mai shirin rufeshi da duka, data tuno rashin kyautawar data yiwa Mammah. Ya kuwa yi mata wata irin kyakkyawar runguma ya hade bakunansuin no space measure.Hawayen ya shiga daukewa..., ko kadan bai barsu sun sauko kan kundukukinta ba.... Komai ya dawo sabo kamar baa yi shi ba. Hafsat ta tausayawa kanta a wannan rana don har azahar Abdulazeez bai barta ta huta ba,amarcinsa yake yiiri-iri kamar babu gobe. Sai da ya samu relief daga tsofaffin damuwoyin sa da suka dade yana fama da su a kan Hafsah sannan da magiya da roko har da hawayenta ta samu ya amince zai maida ita makaranta.
Test dai har biyu ta yi asararsu, amma Abdulazeez ya ce mata ladan da ta samu ya ishe ta shiga aljannah. In dai miji ke wa matarsa sanadin shiga aljannah, yau ya daga mata ta shiga cikin aminci Ud-khuluhaabissalaam!. Ya fada da larabcin da har yau bai manta ba. Wanda yasa Hafsat tuno birnin Jeddah with nostalgia.
Suna hanyar NILE ya na tuki, batareda ya juyo ya dube ta ba yace,
Karfe nawa za a dauke ki?
Ciki-ciki tace. Sai 5pm Mommah za ta zo.
A gaban department dinsu ya ajiye ta, kafin ta fita ya rike hannunta. Ta juyo ta dube shi idanunta narai-narai, sunyi wani irin maiko da kyalli, wani yanayi da yake matukar son gani cikin idanunta,a zuciyarta ta ce, “Oh ni! Me kuma ya saura?
“Take a look into my eyes Hafsah! Will you now believe it if