Showing 51001 words to 54000 words out of 168255 words
ba. Ba sai ya biya bill ba, yana cikin billdin gidansu.
A takaice ya yi masa godiya ya juya zai fita, sai kuma ya kalli Harira a fizge, Ina jiranku a mota.
Da sauri ta mike tana yafa mayafi, sosai ta ke jin shakkarsa ba ta san me ya sa ba. Yana da tsare gida sosai kuma da alama ba ya son wargi. Hafsat da kanta ta mike ta yafa mayafin doguwar rigarta ta sauko daga gadon ta zura takalminta suka bi shi a baya.
Tunda ya shigo idanunta suka sauka a kansa sau daya, ta ga yadda ya yi murtuk da fuskar nan ba ta kara marmarin kallon inda yake ba, kuma da ma ita ba gwana ba ce a kan kallon nasa ba, ba tun yau ba. Abu ne da ta horu da shi tun tana karama; ta ganshi ta sunkuyar da kai.
Da ma ya tula shirginsa a kan kujerar gaban motar don haka baya suka shiga dukkansu, kuma ko kujerar (empty) ce babu fuskar zamanta kusa da shi. Ko da wasa ita ma ba za ta fara ba.
Ko da suka iso gida ya kwashi shirginsa ya kule a dakinsa, ba su kara ganinsa ba. Zama suka yi zugum-zugum a falo daga ita har Harira, kowacce ta yi tagumi cikinta na kugi. Zuwa yanzu Harira ta fahimci wannan auren da matsala, ba auren SO ba ne. Don ta lura ita ma amaryar ba ya gabanta. Amma dai ko ya ya ne a shekarunsa ya kamata a ce ya san cewa, akwai hakkin ciyarwa a kansa.
Ta dubi hafsat sai ta ji tausayinta ya kamata. A ganinta wannan salihar yarinyar mai kyau da kamala ta wuce auren RASHIN SO! To ba ta san wace irin kaddara ke tare da ita ba. Mikewa ta yi ta nufi kicin don ta ga ko za su samu abin da za su ci.
A daidai wannan lokacin Abdulazeez ya fito. Ya yi wanka ya sauya kayan jikinsa zuwa kananan kaya. Rike yake da mukullin motarsa da wayarsa ya wuce Hafsat a falon ba tare da ya ce mata uffan ba. Ba ta tsammanin ma ya kalle ta ya fice. Wata irin ajiyar zuciya ta saki ta sauke tagumin da ta yi ta mike ta nufi dakinta, ta ajiye mayafinta ta fada toilet ta sakar wa kanta showerna ruwa mai dumi. Ruwan na sauka a jikinta a hankali, sai ta ke ji kamar yana wanke mata zuciya, yana tafiya da yar damuwar da ta samu kanta a ciki tun shigowarta gidan. Rashin kulawar Abdulazeez gare ta bai dame ta ba ko kadan, tunda ta fi kowa sanin wane irin aure ke tsakaninsu. Horon yunwa da ta soma cin karo da shi a cikin auren shi ya so ya taba zuciyarta, musamman da yake ga mutum a tsakaninsu ko don ita ai ya rufa asirin rashin son nasa gare ta.
Tana zaune a gaban madubi tana shafa ta ji ana dan kwankwasa mata kofa. Rigar wanka ce a jikinta ta tawul ta kame gashin kanta a tsakiya da katon (hair-bound).
Shigo. Kawai ta ce, don ta san Harira ce.
Murda kofar ya yi ya shiga, ya tsaya daga jikin kofa hannayensa duka biyu rike da fararen ledoji guda biyu. Ta cikin madubi ta ga wanda ya shigo din, sai ta kasa juyowa ta yi kasa da kwayar idanunta. Ajiye ledojin ya yi ya juya ya fita tare da rufo mata kofar. Sun kusa gwabza karo da Harira wadda ta taho rike da plate shake da jallop din taliya, ta ja gefe da sauri ta ba shi hanya ya wuce. A ransa yana fadin, Abincin ma sai an dafa mata, gata mugun abu. To da babu wannan matar ni zan dafa kenan? Ko kuwa ana nufin kullum in je restaurant in sayo abinci sau uku a rana? Mtsew!
SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI
07030137870
*Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama*
Yau yana (office) da laasar ya samu wayar Mammah, ta ce da ya dawo ya dauko Harira da kayanta ya kawo mata ita za ta koma Sokoto. Mijinta yayi waya ta koma. Muryarsa ta nuna damuwa a sailin da yake cewa. Mammah da kin bashi hakuri zuwa gaba kadan, na ga alama suna jin dadin zama da junansu, kin ga ni in na fita tun safe sai karfe shida nake komawa gidan, tana debe mata kewa.
Mammah a dan hasale ta ce, Sanda na kawo ta kai ka ba ni shawara? Ko kuwa mace da aurenta sai ta dawo gidanku da zama?
Ya yi murmushi, Aah, ba ni ba ne, kuma ai dama ba nufina ta dawo kwatakwata ba kamar two months haka, lokacin ta saba.
To yanzu ma ban nemi shawararka ba, ka dauko ta ka kawo min ita na ce, in ka ga dama ka kwana ba ka koma gidan ba, ai zaman aure ne mu ma da haka muka saba a namu gidajen.
Za a yi yadda ki ka ce Mammah.
Ta kashe wayarta, ya ajiye tashi a gefe cikin zuciyarsa yana jinjina rigima kala-kala irin ta mahaifiyarsu.
A nata bangaren Hajiya Maryam Hamza Dakata murmushi ta yi tana rike da wayar a hannunta, ta dubi Daddy da ke gefenta ta gaya masa yadda suka yi da Abdulazeez. Ya ajiye takardun dalibansa da yake (marking) ya dube ta sosai.
To ke me ya sa za ki raba su da mai aikin?Na san ba wata waya da mijinta yayi don naji Azumin na gaya miki ya tafi fatauci ne Shagamu
Ta gyara zamanta tana fuskantarsa ta ce, Daddy, daga baya ne na fahimci na yi kuskure da na tura ta. Ba aure irin na Adda da Abdulazeez ake sanyawa third-party ba, in hakan ta kasance ba za su yi irin shakuwar da nake so su yi ba. Miji na tausaya wa matarsa in ya ga hidimar gida da ta abincinsa ta yi mata yawa, har ya yi marmarin dauke mata wasu hidindimun idan ya san cewa ya barta a gida tun safe har yamma ita kadai, zai fi damuwa da komawa gida cikin lokaci ya ga halin da ta ke ciki, ko ya dinga kiranta a waya sabanin in ya san akwai wani tare da ita.
Jinjina kai Daddy ya yi, ya ci gaba marking dinsa yana mamakin Maryam, ya ce, To sai yaushe kuma za ki barmu mu je mu gansu, nace in bazaki ba ni zani kin hana, ko ki kira ta a waya ki ji lafiyarta? Allah kadai ya san yadda ta ke cikin damuwa da wannan takunkumin naki.
A nan kuma dariya ta yi, ta kafe shi da kyawawan idanunta, Manta da su Daddy. Sai ranar da Abdulazeez a kan karan-karansa ya ga ya dace ya saya wa Suhaana waya. Mu kuwa sai ta shekara zamuje.
*****
Zaune ta ke a kan sallayarta bayan idar da sallar isha tana jan cazbaharta cikin istigfari, ta jiyo sallamar Harira daga bakin kofa. Juyawa ta yi suka hada ido, ta ganta ta sha lullubi dauke da katuwar (Ghana must go) dinta. Da sauri ta karashe lazimin ta shafa adduar cikin kulawa ta ce,
Aunty Harira ya ya dai? Tana mata kallon mamaki.
Harira ta rausayar da kai, Hansatu Allah ya sada mu da alkhairi, zan koma gidan Mammanku ta turo a dauke ni.
Gaban Hafsat ne ya bada wani irin damm! Zuciyarta wadda da ma a karye ta ke kullum ta sake karyewa. Rasa me za ta ce ta yi, Harira na ta yi mata adduar fatan alheri, da zaman lafiya ita da mijinta ba ta iya ta amsa ba, sai jin (horn) din Abdulazeez suka yi, wanda ya sa Harira sungumar jakarta ta wuce. Wani kuzari ya shige ta da ta tuna watakila rabuwarsu kenan har abada ya kamata ta yi mata alheri ko ya ya ne, domin hakika ta ji dadin zama da Harira, mace mai saukin kai da sanin yakamata, mara shisshigi da saido.
Ta dade da fahimtar zaman da ta ke yi da mijinta ba zama ne na soyayya ba, amma ko da wasa ba ta taba tambayarta wani abu a kai ba. Kokari ta ke ta sanya ta a hanyar yadda za ta kyautatawa Abdulazeez ko ba zai kula ta ba. Kullum sai ta tsaya ta ga sun shirya masa abinci sau uku a rana, mai rai da lafiya. In zai fita sai ta ce, ta raka shi da (basket) din karin kumallonsa, haka in ya dawo za ta ce ta fita ta kwaso kwanukan daga bayan motarsa, ta yi masa sannu da zuwa ko ranta ba ya so. Girki kawai ta sani, sai wanka da tsaftar jikinta, amma gyaran gida Harira ce. In ta ce ba za ta yi kewarta ba, ko ba ta ji dadin zama da ita ba, to tabbas ta yi karya ta kwana da yunwa.
Idanunta babu dalili ma kawo kwalla suke yi, balle yau ta yi dalili. Da hanzari ta mike ta bude (wardrove) dinta. Manyan turamen atamfofin (Vlisco) ta kwaso har guda biyar da sinkin sabulai guda goma ta watsa a katuwar leda ta bi ta da su da sauri.
Har ya tada motar ya yi reverse ya hango fitowarta da gudu-gudu ta madubi. Ya dan dakata har ta cimmasu. Bude kofar motar ta yi ta azawa Harira a cinya, sai ga hawayen sun zubo.
Harira kanta daurewa ta ke yi, amma idanunta sun kada sun yi jazir. Ta daure ta kama hannun Hafsat ta ce, To me ye na kuka Hansatu na? Ai ana tare, Baba Azumi ta riga ta hada mu. Na yi miki alkawarin in ki ka haihu ni zan zo in yi miki jego, ke dai ki yi kokari kafin shekara mai zuwa ki haiho min santalelen ango ko kawa mai kirki kamarki, kin ji?
Kokarin jan motarsa ya soma don sun soma ba shi haushi. Maganganun Harira sun yi masa wani iri, sai ya ji kamar da shi ta ke. Hafsat ta ja baya ta rufe mata kofar ya fizgi motar da gudu. La-shakka da cikin kasa ne da ya bule ta da kura, sai aka yi saa kananan fararen duwatsu ne shimfide da harabar gidan bakidayanta.
Ciki ta koma ta fada gadonta tana kuka riris, kuka mai dalilai da yawa. Mammah ta daina sonta ne? Ismaeel, Usman da Halim ma? Baba Azumi ma? Tunda Mammah ta yi mata aure kuma shi kenan ta rabu da ita? Auren da ta tabbatar ba dadinsa ta ke ji ba. Yar Harirar da ta bata tana debe mata kewa ta dauke abarta duk don a takura ta a nuna mata yanzu ba mai sonta? Ya ya za ta yi rayuwa a gidan nan daga ita sai Abdulazeez din da shara ta fita daraja a idonsa?
Ya Allah ka kawo min sauki ni Hafsatu, idan kuma mutuwa za ta fi min sauki ka gaggauta daukar raina in huta da zaman gidan nan.
****
Kusan kwanan da ta yi tana kuka shi ya sa washegari ta makara, don bayan ta idar da sallar asubah a nan kan sallayar barci ya sake yin awon gaba da ita. Ba ita ta farka ba sai bakwai da rabi, kuma lokacin ne Abdulazeez ya ke tafiya aiki. Salati ta yi ta mike da ta dubi agogo ta fada toilet ta rage mararta ta wanko bakinta ta fio falo don wucewa kicin ta gani ko akwai abin da za ta iya ba shi na gaggawa duk da ta san da kyar ne in bai fice ba.
Amma ga mamakinta yana tsaye jikin dining yana daura agogo, ya shirya tsaf cikin suit bakake da farin tie a wuyansa kamar kullum yana kurbar tea din da ya hada cikin cup a gurguje.
Karfe tara daidai zai shiga kotu a kan case din wasu yara da kanin mahaifinsu ya cinye musu gado, tun daren jiya ya gama (compiling) duk wasu hujjoji da ya tara, amma ya manta da wani (recording) da ya yi saving dinsa a kan desktopdinsa ta ofis dole ya yi sauri ya je ya yi burning dinsa zuwa discyadda in ta kama zaa iya playing dinsa a kotun saboda haka kusan a gurguje ya kammala shirinsa yau ya fito. Ya samu ya hada shayin don ba ya jin yau yana bukatar abinci daga safe har dare, sai ya ga abin da ya turewa buzu nadi a kan wannan case din kamar yadda ya saba, musamman case na marayu ba ya daukarsa da sauki.
Jiya saboda wannan aikin bai samu ya kwanta da wuri ba don haka a dan makare ya tashi ya shirya ya fito falon. Sanyin A.C da ya ratsa shi a falon ya ba shi mamaki, don ya lura duk lokacin da ta fito da asuba sai ta kashe ta, amma yanzu ya tabbatar yadda ya barta jiya da daddare ya shiga daki ya kwanta haka ta kwana tana aiki. Talbijin a kunne, wutar falo a kunne, wadanda kullum sai ta kashe su ta ke kwanciya. Ya kafa wa kofar dakinta ido kamar hakan ne zai tabbatar masa tun shigarta daki jiya tana kukan tafiyar Harira ba ta kara fitowa ba.
Sai ya matsa ya kashe A.Cn da sauran kayan wutar gabadaya ya tsaya nan jikin dining ya hada teadin da yake sha wanda ya dafa da butar ruwan zafi (kettle) yana sha daga tsayen da yake yana daura agogo.
A daidai lokacin Hafsat-Suhaana ta murdo kofar dakinta ta fito. Sanye ta ke cikin riga da wando na barci masu kauri, kanta cikin hular wanka (shower-cap), bai juyo ya dube ta ba da yake ya bata baya, tunda har ta fito to lafiya ta ke kenan. Ya karasa shanye shayinsa ya ajiye kofin a kan (table) ya dora (wig) dinsa a kansa ya suri rigar lauyoyinsa da (briefcase) ya fice zuwa harabar gidan. Ya bude motarsa ya shiga, ya ajiye kayan hannunsa a kujerar gefensa ya yi wa motarsa key Danfulani ya bude masa get ya murza kan motarsa ya nufi (office).
Barin Harira gidan maimakon ya kawo shakuwa kamar yadda Hajiya Maryam ta yi zato, sai ya kara lalata zaman gidan. Hafsat sai ta yi kwana biyu ba ta sanya Abdulazeez a idanunta ba. Da safe ya daina bi ta kan abincinta, da ma Harira ke cewa ta dauka ta bishi ta sanya mishi a mota, shi kuma ba ya musantawa in ta kawo ko in ta ce masa Ga breakfast yanzu kuwa da babu Harira ba ta da wannan kwarin gwiwar, shi ma ba ya nuna yana bukata, in ya fito zai hada tea ko coffee ya sha ya fice, ita kuma ta kama kanta sosai, ba ta yi masa shisshigi ta tsaya a matsayin da ya ajiye ta na mai yi masa gadin gida. Ya daina turo direbansa daukar abincin rana tun tafiyar Harira ko me ye dalili ba za ta iya cewa ba.
Da ya dawo karfe shida wanka yake yi ya shiga kicin ya kama girkinsa ya yi ta bare-barensa duk ya baba mata kicin ya tara mata kayan wanke-wanke. Tunda ta lura ya daina cin abincinta ta daina dafawa da shi, iya cikinta ta ke dafawa don duk ranar da ta ajiye masa na dare, a ganinta lokacin yana gida. To yadda ta ajiye shi haka za ta dawo ta samu abinta, ta dauka ta sa a firji washegari da safe ta yi steaming dinsa ta cinye don uwarta ba ta koya mata almubazzaranci da abinci ba, ko ta dumama ta mika wa maigadinsu.
Yana ganin abincinta wanda ya san don shi ta ajiye, amma tunda ta daina ce masa ga abinci zai tsallake shi ya yi abinsa. Girki ba bakonsa ba ne, don kuwa shi ya raini kansa ba wani ne ya raine shi ba.
Da ya gama ya zai zauna a dining din kicin din ya ci abinsa don ba ta wasa da tsaftar madafin nasu. Yana gamawa zai shige daki ya hau aiki, in kuma ba ta a falon to zai yi zamansa ne a nan ya baje takardunsa da systems dinsa ya yi aikinsa. Shi kadai ya san yaushe yake shiga daki ya kwanta.
Hafsat ba ta kara shiga shirginsa, wanka ta ke yi ta dauro alwala ta gurfana a side din da ta ware ta yi shimfida cikin dakin ya zama muhallin ibadarta, ta gurfana gaban mahaliccinta tana kai masa bukatunta.
****
Haka kwanakin ke mirgina musu har tsayin watanni ukku, rayuwar tasu ba wani abu mai dadi da za a dorar, connection dinsa da Muazatu ya yi rauni saboda ta samu tafiya (Law School) a jihar Adamawa (Yola) dole ta maida kai ta ajiye soyayyar a gefe, shi ma cikin lokacin nan fama yake da cases iri-iri masu zafi saboda a hankali fasaharsa da kwarewarsa a kan aikinsa ke fitowa sarari. Ya shiga sahun lauyoyi yan gaban-goshin gwamnati wadanda ake damkawa duk wani case na marassa galihu, (private individuals) sun fara son janye Abduazeez Dakata, amma ya tsaya a raayinsa na kasancewa lauyan gwamnatin tarayya mai rajin kare hakkin yan kasa. Wanda babban burinsa a gaba shi ne, barin Bar zuwa Bench. Wato daga lauya zuwa mai shariah (justice).
Yau yana zaune a office wata abokiyar aikinsa Barrister Surayyah Tanko ta isko shi rike da wasu files a hannunta. Tana zuwa ta dire masa su. Aiki yake yi, amma ya dago ya dube ta, Taimaka ka duba min su Barrister Abdulazeez ka gani ko akwai abin da ya kamata mu kara ni da Adebayo. Zan je (Jamb Office) na dawo yanzu, zan sayo wa Suhaima jamb form, saura kwana uku a rufe. In aka rufe kuma sai wata shekarar.
Idonsa ya dan kafa mata, matar aure ce amma tana son shiga shaaninsa da yawa bai san dalili ba. Sai kuma ya ji kamar ta yi masa tuni game da wani nauyi da ke kansa.
Hafsat!. Sunan ya fado masa a rai (with a low tune).
Surayyah ta gyara tsayuwa ganin sai kallonta yake yi, amma in ka dubi tsakiyar idonsa za ka lura ba ita yake kallo ba, tunani yake yi. Ta kada masa yatsunta a fuska, ya dauke