Showing 84001 words to 87000 words out of 168255 words
yanzu ba ma tare da ita. Ita ce Yaya Habiba mahaifiyar Modibbo da aka daura wa aure yau. Mun rabu da ita shekaru goma sha tara kenan, har gobe zukatanmu cikin taraddadi suke da tarin alhini. A duk halin da muke ciki farin cikinmu ragagge ne a dalilin rashinta, da rashin sanin wane hali ta ke ciki tunda kuwa ba mutuwa ta yi ba, bacewa ta yi sama ko kasa muka rasa ta.
Sai bayan shekaru masu yawa da muka tsananta addua komai ya bayyana gare mu na sanadin barinta gida, labarin mai tsaho ne Abdulazeez. Sannan ba mai dadin ji ba. Kuma mai taba zuciya.
Mun yi duk wani nema na duniya har gobe babu Yaya Habiba babu labarinta. Musabbabin fara ciwon hawan jinin Dada kenan, wanda ta ke fama da shi har gobe. Malam kuwa a duk istikharar da zai yi a kan Habiba ya ce ba ya ganin komai sai duhu, Allah ya rufe masa komai, mun kasa sanin komai a kanta. Tun muna cikin tashin hankali har a hankali muka soma sabawa da rashin Yaya Habiba.
A yanzu sai dai mu tuno ta mu yi mata addua, amma mun saba da rashinta, shekaru goma sha tara ba kwana tara ba ne. A yau babban danta Ridhwan (Modibbo) ya yi aure, kaninsa Abdurrahman na ajin karshe a jamia, sai autanta Imaamu yana aji uku a FUTY, to ka ji.
Ajiyar zuciya mai nauyi Abdulazeez ya sauke, a lokacin da Sagir ya saka aya na takaitaccen labarin da yake ba shi. Ya tambayeshi ina mijnta? Sagir ya ce Yana nan a raye. Da ka kula da wani farin mutum mai hula ruwan kasa da farar shadda a wurin daurin auren nan yanata gaisawa da jamaa shine mahaifin su Modibbo. Malami ne a tsangayar harshen turanci a FUTY. Duk wanda ya kwana ya tashi a Federal University of Technology Yola, ya san da zaman Farfesa Bashar Maijamaa sabida rubuce-rubucensa a kan koyar da harshen turanci a jamiar FUTY.
Abdulazeez na son sake tambayarsa ko me suka gano sanadin barin Habiban gida bayan watanni da batan nata?Sai shesshekar kukan Dada suka ji, wadda tun sanda Sagir ya fara bada labarin ta soma kuka.
Duk cikin yayana ta fi kowannensu taimaka mini, kafin a yi mata aure ban san shiga madafi don yin girki ba, data tafi gidan miji ma bata fasa dafowa ta kawomin ba, ta fi dukkansu kyautayi a gare ni. Zuciyarta mai kyau ce, mai kaunar UWA, mai nufin alkhairi ga kowa. Samun mace mai kyautayi da jin kan UWA kamarta a wannan zamanin abu ne mai wuya.
Ta so mijinta da zuciya daya, ta zauna da shi tsakani da Allah tun ba shi da komai. Rana daya Hajara ta raba su, ta shiga tsakaninta da yayanta. Ta bar su sun girma babu dumin Uwa. Ta raba ni da nagartacciyar diyata! Ba zan taba yafewa Hajara ba har duniya ta nade.......
Ta ci gaba da kuka sosai mai taba zuciyar duk mai imani.
Ki ba ni watanni hudu Dada, as alawyer(a matsayina na lauya) na yi alkawarin binciko miki labarin yarki Habiba, domin kamar na santa, kamar na taba ganinta a wani wuri.
Abdulazeez ya samu kansa da fada ba tareda ya shirya kalaman akan harshensa ba, sun fito ne kai tsaye ba tareda karbar umarni daga zuciyarsa ba sakamakon tausayin wannan UWA mai tsananin begen diyarta.
Daga Sagir har Dada zabura suka yi suka mike tsaye. Hannu dafe da kirji, baki a bude.
Da gaske Abdulazeez?
Suka hada baki wajen fadar hakan. Gyada kansa yayi cikin tabbatar musu da sahihancin furucin sa.
Tun ranar da na fara ganinka zuciyata ta gaya min kana da alaka da Habiban da na sani. Rokona daya mu bar zancen nan a matsayin sirri a tsakaninmu zuwa dawowata. Na yi muku alkawarin da kafata zan dawo da cikakken bayani a kan Habiba, da shaidu kwarara.
Da ya zo nan, ya kuma tuna Habiban ba ta duniya sai ya ji kwalla ta cika masa idanu.
Kabar ni in gaya wa Malam na samu wanda ya taba ce min ya ga Habiba bayan shekaru sha tara kafin mu tadda kushewa ko na ji dadi a zuciyata.
Dada ta fada tana kukan farin ciki.
Za ki iya gaya wa Malam, amma daga shi babu kari har in dawo. Bana so ku kasance cikin zullumi har tsayin wannan lokacin ne shi ya sa.
Zullumi ko kwanciyar hankali? A kalla dai mun san tana nan ba mutuwa ta yi ba.......
Sai ya kauda ido, ya share ambaliyar hawayen da suka cika masa ido da yatsun hannunsa.
Karfe biyar daidai na yamma jirginsu ya taso daga Adamawa zuwa FCT Abuja.
*****
Hafsat ta ji dadin tsarabar kindirmo, man shanu, masa da kuli da Abdulazeez ya kawo mata daga Jimeta. Sosai ta ci ta koshi ta sanya ragowar a firji za ta dinga dumama musu a microwave har ta kare, nonon ma da man shanun duk a (fridge) ta adana su.
Washegarin ranar ya kai ta ta baiwa Mammah hakurin fushin da ta ke yi da ita, ta ce ita ba fushi ta yi ba, tana so ne ta yi hankali da kawayen zamani, Nigeria ba Brussels ba ce ta kama kanta, ta rungume mijinta ta fita sabgar kowacce tarkacen kawa in ba haka ba za su kai ta su baro.
Hafsat dai hakuri ta ke bayarwa a kan laifin da ba nata ba.
Ita da Abdulazeez yanzu wani irin kyakkyawan zama ne a tsakaninsu. Kowanne gani yake ba mai kirki a duniya irin dan uwansa. Ya wadata ta da duk wani abu da dan Adam ke bukata na abinci da suttura da na amfani. Bai kara (attempting) neman komai daga gare ta ba, ganin iyayenta da kakanninta da irin gidan da ta fito da ya yi, ya kara mata kima da martaba a idanunsa. Ya yarda Hafsat ba gangar da zai ci amfaninta ya yar da kwaurenta ba ce. Gara ya maida ita ga iyayenta da yan uwanta cikin mutuncinta, ta samu miji na gari mai nagartattun halaye irin nata ta aura. In yaso ya zame mata bango abin jingina a duk sanda ta bukaci hakan. Don haka soyayyarsa da Muazatu ta kara karfi a wannan dan tsukin wadda saura kadan ta kammala (Law-school) dinta.
Jarrabawar su Hafsat ta fito, ta kwaso pointsmasu yawa har (300). Ba da jimawa baya samar mata gurbi a NILE jamiar nan mai zaman kanta dake birnin tarayyah, Abuja.
Duk wani shige da fice da dalibi zai yi don zama cikakken dan makaranta Hafsat tare da Abdulazeez suka yi shi. Ta zama cikakkiyar dalibar Nile University a tsangayar ilimi da koyarwa (education) inda za ta gwanance a fannin koyar da ilimin halicce haliccen duniya Geography (Education/Geography).
Ba sa kwana a daki daya, Abdulazeez ya haramtawa kansa wannan. Kullum kuma shi yake kai ta makaranta da kansa sannan ya wuce office. Don haka basa bata lokaci da safe suna fita da wuri, in ta riga shi tashi ya tura direban office dinsu ya maida ta gida, in sun tashi lokaci daya shi zai biya ya dauke ta su tafi gida. Wannan ma ya taka wata rawa ta musamman wajen sanya shakuwa mai tsananin karfi a tsakaninsu.
******
Sosai Hafsat ke jin dadin abin da ta ke karanta. Darasin (Geography) da ma na cikin darussan da ta ke so tun a sakandire. Shi ma Abdulazeez ganin ta samu A1 a darasin ya sanya shi zabar mata shi, sannan halayenta za su yi kyau da na malamin makaranta saboda tana da hakuri, sanyin rai da juriya.
Hafsat na jin dadin karatunta a NILE fiye da tsammani, ta yi kawa wata mutuniyar Zamfara mai suna Mami, aiki ne ya kawo mijinta Abubakar Sadik Abuja, Mami za ta girme mata da wajen shekaru hudu don shekarunta ashirin da biyu. Komai na Hafsat da yanayin shigarta na kamala da tsantseni na burge Mami wadda ainahin sunanta Rabia Sada. Mijin Mami maaikacin Etisalat ne, duk ajinsu babu wanda Rabia ta ga ya kamata ta yi abota da shi sai Hafsat Dakata, ko don ta amfana da ita saboda cikin dan lokaci hazakarta ta (good foundation) din da ta samu ta fito fili, kowa ya fahimci talented ce. Daga assignment har test ita ce zakaran gwajin dafi. Ita dai Hafsat ba ta zura jiki a kawancensu da Mami sosai, saboda yadda Mammah ta tsoratar da ita a kan kawayen Abuja, amma yadda Mamin ke nace mata ya sa dole ta ke kula ta, amma a abin da ya shafi harkar karatu kadai. Ba ta taba yarda wata magana bayan ta karatu ta hada su ba.
Har ga shi watanni sun gangara suna shirin fara jarrabawar (first semister) wanda ya zo daidai da kammala (Law-school) din Muazatu wadda ta shafe watanni goma a jihar Yola.
*****
Yau a kan idon Mami da mijinta Abubakar Abdulazeez ya dauki Hafsat, da ta bude motar ta shiga ta zauna, sunkuyawa ya yita saman kanta yana gyara mata sarkar wuyanta da ta harde cikin gashin kanta ta baya,gashin yake zarewa daga cikin sarkar a hankalihannayensa zagaye da ita. Yayin da kanta ke kusa da kafadunsa. Sosai Mami ta saki baki da hanci da ido daga nesa ta ke kallonsu da mamaki, don ba ta taba sanin Hafsat na da aure ba ganinta yarinya karama danya shataf. Couple din sun zauna mata a zuciya sun kasa bacewa, sai zancensu ta ke yi wa mijinta a hanya. Ba ta taba ganin matar da ta dace da miji irin Hafsat Dakata ba, har kishi ya sike Sadik ya ce.
Wallahi zai ajiye ta a gefen titi, ina ruwanta da kallon mijin kawarta har ta ke yaba shi a gabansa sabida jahilci? Sosai Mami ta kama kanta don ta san halinsa sarai zai iya ajiye ta a titin a kan kishinsa, amma ta sa a ranta za ta tirke Hafsat sai ta ba ta labarin rayuwarta da inda ta hadu da wannan handsome da ta dade ba ta ga namiji mai tarin abubuwan da ya mallaka ba.Duk da itama ta san ba abune mai sauki samun hakan daga Hafsat din ba yadda take ji da class dinnan da zata tsaya tana wani bata labarin rayuwarta ko na mijinta. Amma ance a rashin tayi akan bar arha. Zata gwada saarta.
A washegari da ta turke Hafsat da tambaya, nan da nan tayi fuska, ta ce ita ba mijinta ba ne, Yayanta ne.
Amma irin Yaya a dangi ko familyfriends din nan ko? Saboda ita dai ta ga abin da ta gani wanda ya sanya ta shakka a kan zancen Hafsat. Murmushi Hafsat ta yi har kuncin nan ya lotsa ciki sosai. Murmushin da Mami ta kara dorawa a sikeli.
Ke me ye damuwarki Mami a kan hakan? Daga ganin mutum ba ki san ko wane ne ba sai ki ce mijina ne? To babu ko daya.
Mami ta ajiye biron hannunta tana murmushi ta ke kallon Hafsat. Ni na ga abin da ya sa na tambaya ko kin ki gaya min Hafsat, a sanda ya bude miki murfin mota ki ka shiga ki ka zauna, ya sunkuya yana gyara miki sarkar wuyanki. Akwai wani babban alamari cikin kwayar idanunsa a kanki. In kin sani kina boye min ne ban ga laifinki ba, don na dade da sanin kawance na da ke bai dadaki da kasa ba. In kuma ba ki sani ba, ina mai sanar da ke wannan. Idan kuma da gaske Yayanki ne kamar yadda kika dage im telling you wannan Yayancin will turn to something very special nan ba da dadewa ba.
Bin labban Mami Sada ta yi da kallo, a lokacin da ta ke furta kalamanta. A ranta tana mamakin me ta gani da ya sa ta fadar hakan?Ko jiya Abdulazeez kwana ya yi da wadda yake so a kan waya, tsakaninta da shi ya kai ta makaranta ya dauko ta, ta dafa masa abinci ya ci. Ba ta da sauran buri a kan Abdulazeez yanzu, ta dade da yi wa zuciyarta fada, kuma zuciyar ta dade da shiga taitayinta. Ba ta sanya mata komai sai tunanintahowar ranar karewar KWANGILA wadda ta tabbata tana tafe nan bada jimawa ba. Bai gaya mata ba, amma tana lissafe da watanni, kuma ta ji yana fadin zai tafi Lagos (call to Bar Ceremony) din masoyiyarsa, ba ita ya gayawa ba, abokinsa Abdallah ta ji yana gayawa a waya.
Ga mamakin Mami gani ta yi idanun Hafsat sun cicciko da wata zazzafar kwallah. Ta kuma dade da barin jihar da suke ciki, ta lula wata jihar daban ta tunani mai zurfi. Wannan ya tabbatar mata akwai wani alamari mai girma tsakanin Hafsat da handsome din da ta kira Yayanta kamar yadda ta ke ikirari. Amma tunda Hafsat mutum ce da ba ta son a yi mata shisshigi cikin (personal life) dinta zai fi kyau ta kyale ta.
Ni dai shawarata ita ce, duk runtsi kada ki bari ya kubuce miki, nasan mijinki ne ba saurayi ba, irin wadannan daban ne Hafsat, alamu sun nuna yana daga cikin mazan da matan waje ba za su kyale wa matansu na gida kadai ba. In wannan ce matsalarki Hafsat ki cire kunya da kawaici ki damke mijinki da hannu bibbiyu, in ba haka ba za ki sha mamaki cikin garinnan.
Sosai Hafsat ta yi mamakin yadda Mami ta gane Abdulazeez mijinta ne. Maganganunta kuma kamar ta san me take ciki a rayuwarta da shi din. Bata ce komai ba sai binta da kallo.
A wannan ranar direban office dinsu ya sa ya maida ita gida sabida ayyuka da suka yi masa yawa. Don haka a hanyarsu ta dawowa ta kifa kanta jikin murfin motar ta yi kukanta mai isarta ta koshi. Kukan tausayin kanta... kukan rashin sanin mene ne aibunta da Abdulazeez ya kasa sonta har duniya ta fara gane tana da matsala makamanciyar wannan a tare da shi?
Aibubbuka da yawa Hafsat. Babban cikinsu rasin asali, don haka ki ci gaba da yi masa uzuri kamar yadda ki ka faro, watarana sai labari. In ji zuciyarta.
******
Sai da ya bari Hafsat ta kammala jarrabawar karshen zango da ta ke zanawa sannan ya je gida a wata ranar lahadi tunda ba ranar aiki ba ce, ya tabbatar Daddy yana gida a lokacin Ismael ya koma America, Haleem da Usman ne kawai ya rage ba su koma inda suka fito ba. Ya samu Mammah da Azumi uwar goyon Suhaana wadda a yanzu za a iya ce mata kaka a gare su, ya ce ya zo ne da muhimmiyar magana, yana bukatar su zauna a falo dukkanninsu.
Mammah ta je ta fito da Daddy ya same su a falon har Haleem.
Barrister da sanyin safiyar nan, ya aka yi?
Murmushi ya yi ya sadda kansa kasa. Har gobe Dr. Hamza bai bar jan yayansa a jiki ba duk da dukkanninsu a yanzu babu wanda bai isa a yi masa aure ba banda Haleem, shi ma da a kauye ne ba irin rayuwarsu ba, da tuni ya jima da yin auren.
Sai da kowa ya nutsu ya ba shi hankalinsa, sannan ya fara ba su labari tiryan-tiryan tun hirar da yayi da Habiba aranar da alamarin zai faru, da bincike da ya soma a boye akan garin Jimeta, haduwarsa da Barrister Sagir Hashim Jimeta. Yadda ya rika nace masa duk da kasancewarshi ba mai son harka da jamaa ba, sai dalilin kamanninshi da Suhaana. Yadda suka zama abokai na jiki a watannin da suka gabata da yadda har yake zuwa gidansa cin abincin dare duk don ya shiga jikinsa, ya tabbatar da abin da yake son tabbatarwa.
Gayyatarshi daurin auren dan Yayarshi da Sagir yayi, da abin da ya faru zuwansu Jimeta ya kwashe duk ya gaya musu. Mammah da Baba Azumi sai kabbara suke yi zukatansu fal farin ciki. Dr. Hamza Atiku sunkuyar da kai ya yi yana tuna tarin wautar da ya yi a baya, yana kara istigfari cikin zuciyarsa.
Ka yi maganar da Addah?
Mammah ta tambaya.
Girgiza kai ya yi, Ban taba yi mata zancen ba har bayan da na tabbatar, saboda bana son abin da zai dagula karatunta.
Masha Allahu. In ji Mammah.
Tafiya Jimeta ta same mu, tunda ai ta kare jarrabawar ko?
Ta gama jiya.
Bari in yi wa mutanen Kano waya su shirya don gabadayanmu za a yi wannan tafiya.
Kan ka ce me ye wannan Mammah ta hau bugawa su Adda Hafsatu waya, su Luba, Mariya, Furera da Murja, har Aunty Zuwaira da ke nan Abuja ba ta bari ba. Matar Uncle Idris da matar Ibrahima da sauransu. Cewa su yi shiri za su tafi Yola an gano iyayen Addarta. Tsofaffin hotunansu da suka sha yi da Habiba a Jeddah ta hau bincikowa, Abdulazeez ma yana da wasu daga ciki, ya sanya a aljihu ya tafi da su har Jimeta da zummar in bukatar hakan ta taso ya fiddo su, to kuma da ya canza shawarar rashin tada maganar a lokacin daurin auren ya dawo da abinsa ya boye inda Hafsat ba za ta gani ba.
Shiri sosai wannan family ke yi na tafiya Jimeta (Yola North), wanda za su yi kwanaki uku masu zuwa. Mammah ta kasa bari har zuwa karshen mako don haka ta sanya tafiyar ranar Laraba, masu aiki su dauki uzuri.
Washegari a ofis dinsu ya tadda Sagir yana rubutu cikin wasu files. Gaisawa suka yi kamar yadda suka saba, tun kafin ya yi magana Sagir ya riga shi, ya gaya masa Dada ta ce a yi masa tuni kan maganar nan ko tana da rabon ganin yarta a sauran numfashinta. Ta fara kasa jurewa jiran.
Sadda kai Abdulazeez ya yi yana jin wani iri a zuciyarsa. Daga bisani ya ce da Sagir, abin da ya kawo shi kenan. Iyayensa sun yi shirin tafiya Jimeta a kan maganar Habiba ranar Larabar nan ya sanar da su Dada.
Iyayenka???
Sagir ya tambaya cikin mamaki.
Daga masa kai Abdulazeez ya yi da siririn murmushi a fatar bakinsa, ya ce,
Dogon labari ne Sagir, amma a gidanmu Yayarka ta zauna. Sauran bayani sai mun isa can.
Daskarewa Sagir ya yi a zaune, yana tazbihi yana kadaita Allah.
SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI
07030137870
*Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama*