Showing 15001 words to 18000 words out of 168255 words

Chapter 6 - Auren Kwangila Book 4 Hausa Novel Complete

Takori   

12 Dec 2024

291

ta bakinta. Kowannensu fuskarsa na nuna “Mammah ki yarda da hakan”.
Hajiya Maryam ta sa habar zaninta ta goge fuska da majina, “Daddy ba ta da lafiya ne, tana da pneumonia, tana bukatar ruwan nono da dumin jikin uwa, in ban shayar da ita ba bani da kulawar da zan ba ta fiye da hakan”.
Mikewa ya yi yana dakile fuska. Ya kakkabe rigarsa ya nufi matattakalar da za ta sada shi da dakinsa. Yana tafe yana fadin, “Shawara ta rage ga mai shiga rijiya, na ba ku daga yau zuwa gobe ku yi shawara, har madara zan dauki nauyin saye sadaqah fisabilillahi. Amma in ba haka ba gobe zan sa a buga mata fasfo ku kai ta inda ku ka dauko uwarta”. Ya yi wucewarsa ya shige daki ya rufo kofa.
Usman ya matso sosai jikin mammanshi, idonsa a kan babyn da ta zuba fararen yatsunta cikin baki tana tsotso alamun yunwa.
“Mammah ki yarda don Allah mana? Tunda mun samu ya bar mana?”
Isma’el ya ce, “Mammah don Allah ki yarda ta sha madaran, rayuwa da ciwo duka na Allah ne, idan mai tsawon rai ce sai ki ga Allah ya raya mana ita. Take heart Mammah...”. Ya fada tare da kai hannu santar kirjinta yana shafawa alamun ta yi hakuri ta bi abin da Babansu ke so.
Hajiya Maryam ta tsura wa ‘ya’yan nata ido, yara masu hankali da tunani tun a qananan shekaru irin nasu. Har sun fi ta tawakkali da hangen nesa. Da gaske Allah shi ne mai rayawa ba nonon uwa ba. Ta rungumo su gefe da gefenta, jaririyar na bisa cinyarta, ta sumbaci kowannensu a goshinsa,
“Na amince. Gobe zan gaya wa Daddy. Yanzu zan fara ba ta madara kun ji ana kiran sallah, maza kowa ya je ya yi alwala yanzu Daddy zai sauko ku wuce masallaci”.
Duk suka mike cike da murna har da tsalle suka nufi toilet don dauro alwalar. Ita kuma ta dauki ledar shopping dinta da babyn ta nufi dakinta.
A take ta tafasa ruwan zafi ta hada madarar ta soma ba ta. Wata irin kauna tana mamaye zuciyarta na ‘yar da ba ta san daga ina uwarta ta ke ba balle ubanta. Sai dai kaso 90% na zuciyarta ya amince yarinyar nan ba shegiya ba ce, da ubanta. Habiba ba ta yi kama da mutanen banza ba, sannan ba yarinya ba ce balle a ce shege ta yi ta gudu. Ta fi amincewa da cewa wani nau’i ne na kaddarar rayuwa ya rabo ta da gidan mijinta da iyaye da ‘yan uwanta.
Ba ta yi gigin zuwa turakar Daddy a yau ba kwata-kwata, shi ma bai neme ta ba. Duk abubuwan da ta saba yi masa kafin su kwanta da kansa ya yi, zuciyarsa fal haushin Maryam, tunda daga samun ‘ya har ta fara watsar da shi, da ma a ce ita ta haifa da sauki ba zai damu ba. Ya yi tsaki yana shan ‘gahwah’ (coffee) ya fi sau shurin masaki. A haka ya kwana cikin bacin rai, ita kuma tana can tana ceton rayuwar ‘yar marainiyar Allah. Ta kashe A.C ta kunna (room heater), ta ciro kayan sanyi masu kyau cikin sayayyar da ta yi ta sunke ta a ciki, da pampers. Ta cika mata ciki da madarar da Dr. Unaisa ta yi umarni. Nan da nan ta hau baccinta cikin kwanciyar hankali. A lokacin ne ta tuno da Daddy, ta yi ajiyar zuciya ta yi shirin bacci ta manna jaririyar a jikinta, ta rufe su ruf cikin lallausar bargo, suka yi bacci abinsu.
Tun asuba kukan baby ya tashe ta, ta tashi zaune ta dauke ta ta yi toilet da ita. Wanka ta yi mata da ruwa mai dumi sosai, ta nado ta cikin shawul. Shafe ta ta yi da man zaitun ta canza mata (diaper), ta shirya ta cikin (overall) farare tas! Da hula mai kauri. Sannan ta hado madararta ta shiga ba ta. Ta kura mata ido ba ta ko kiftawa. Habiba ta ke tunawa da karamcinta, da yanzu ta fara jiyo sukurniyarta tana shara da goge-goge kafin ta fada kicin ta hada mata kayan girki kafin ta sauko. Hawaye suka ciko a idonta, me ya sa Habiba ta yaudare ta? Me ya sa ta boye mata asalinta da cikin da ta ke dauke da shi? Rayuwar yarinyar a gaba ta ke kokawa idan Allah ya raya ta ta fahimci ita din ba uwarta ce mahaifiya ba, ba a san kowa nata ba, ba a san daga inda ta fito ba. Ta ajiye ajiyar zuciya mai nauyi, ta share hawayen idanunta. A hankali ta sanya babyn cikin gadon da ta hada yanzu, sai bacci ta ke sadidan cikin koshin lafiya.
Wanka ta yi, ta ci gayunta kamar yadda ta saba, kai ba za ka ce ta yi shekaru talatin da biyarba. Ta san sirrin gyara na diya mace kala-kala. Ta lakanci ado da kwalisa tun tana budurwa, haka yanzu da shekaru suka fara turawa ba abin da ya canza Maryam Dakata. Farar mace mai farar aniya, uwar gidan Professor kuma Ambassador Hamza Atiku Sakata.
Kicin ta fada ta soma hada wa iyalinta abin kari. Sosai ta yi latti, domin har gari ya waye. Sanin Daddyn a sama-sama yake da ita ta ce bari ta yi masa abincin da ya fi so, don ta dan faranta ransa. Kunun gyada ta hada ya ji madara yadda ya kamata. Ta hau suyar sinasir din da ta kwaba tun daren jiya. A gurguje ta ke yin komai, miyar ta ji ganyen alayyahu sosai da tsokar kaji. Sun dahu sun yi lugub. Yaran kuma (quaker oat) ta dama musu, ta soya musu ‘pancake’ ta shirya wa kowanne a sundukin abincinsa. Da hanzari ta shirya wa Daddy tebur jin baby ta fara kuka. Su Isma’el suka fito daga dakinsu cikin shirin makaranta kowanne goye da dirkekiyar (school bag) dinsa.
“Mammah sabahul khair”. Duk suka fadi a tare bayan sun shigo kichin din cikin russunawa.
Kansu ta shafa daya bayan daya tana murmushi, “Sabahul khair, ‘yan albarka, kun tashi lafiya?”.
Isma’el ya ce, “Karasa aikinki Mammah, I will help you with the baby”.
Ta yi murmushi ta daga masa kanta.
“Madararta na nan a kan (side drawer) ba ta ina zuwa”.
Da hanzarinshi ya juya zuwa dakin nata.
Tun a kan Halim Isma’el ya iya raino, shi ke taimaka mata da rainon Halim har ya yi wayau. Yanzun ma baby ya ciro daga gadonta ya aza a kafadunshi yana rirriga ta har ta yi shiru. Ya zauna gefen gadon Mammah ya ba ta ruwan zam-zam ta sha sosai, sannan ya sanya mata madarar a baki. A ranshi yana cewa, duk da dai an ce ba a gane kamannin jariri, amma wannan da ganinta Habibah ce sak!
Mammah turakar Daddy ta nufa da saurinta, suka ci karo a matattakalar bene ya yo shirin office tsaf, rike da (briefcase) dinsa. Ta karba suka sauko tare, sai faman dauke mata kai yake yi. Ta yi murmushi a ranta ta ce, “Insha Allahu watarana sai ka yi alfahari da ‘yar da ba ka son rikewa din”.
Su Isma’el ya kwala wa kira yana kokarin ficewa daga falon ba tare da ya dubi (dining) din ba. Ba ta yi fushi ba, ta ce, “Daddy break fast fa?”
“I’m ok”. Ya fada yana duba agogo.
Ta ji ba dadi yadda mata ke ji in sun takarkare sun zabga wa maigida girki ya ki ci.
Usman da Halim suka wuce tare da shi, Isma’el ya fito dauke da baby ya mika wa Mammah, sannan ya dau jakarsa da kwandon abincinsa ya bi bayansu da gudu. Ta yi ajiyar zuciya ta goya baby jikinta a sanyaye. Da gaske Hamzanta ya canza daga halin da ta sanshi da shi. Ta san shi mutum ne mai tausayi da taimakon na kasa da shi, ba ta san me wannan yarinyar ta tare masa cikin gidan nan ba, da alama za ta fuskanci barazana mai yawa a rayuwar aurenta a kan rikon yarinyar daga mijinta, abin kaunarta. Ta kuma shirya karbar kowanne kalubale in har zai bari su rayu tare. Ba za ta kai ta Nigeria ba, inda ko sun je babu inda za ta kai ta a karba in ba gidan marayu ba.
Ta shirya yin jihadin rikon ‘yar Habibah ko da Daddy zai kara aure ya kora ta Nigeria a dalilin haka. Ta watsar da tunanin ta shiga harkokinta. Islamiyyar ma ta daina zuwa sai ‘yarta ta isa bari a makarantar rainon yara (creche). Amma dole ta nemi ‘yar aiki don ayyukan gidan sun fi karfinta. Karshen ta dai Takarin da bata so.
A nan unguwarsu Albasaatin ta yi kawaye biyu ‘yan Nigeria matan ma’aikatan Embassy, daya matar mataimakin Daddy ce Safiyya sun fi su dadewa a Saudiyyah sosai, bayan ta gama girkin rana ta kira Anty Safiyya ta ce ta cigita mata mai aiki don Allah Takari, ta ce ta bari sai Juma’ah za ta shiga Misfalah in ta je Harami za ta taho mata da ita. Ta yi godiya suka aje wayan.
A daren ranar, Hajiya Maryam ta yi shiri kamar yadda ta saba ta nufi turakar maigidanta, aiki yake yi a tsakiyar gadonsa cikin na’ura mai kwakwalwa. Ciki-ciki ya amsa sallamarta ba tare da ya dago daga abin da yake yi ba. Kokarin sauke baby ta ke daga bayanta don ta koma ta dauko gadonta. Da hanzari ya dago ido ya dube su. Ya zare farin gilashin kara karfin gani da ke idanunsa, cikin kaushin murya yake magana.
“Ban gane ba? Kina nufin tare zan kwana da yarinyar nan? Ta ya ya ki ke tunanin zan iya jure kukan jaririn da ba nawa ba? Excuse me please,Maryam! It’s enough wallahi, abin da ki ke min a kan yarinyar nan ya ishe ni. You are forcing me to be a father of your adopted daughter while i’m not. To bari ki ji in gaya miki, wannan ya zamo na farko kuma na karshe. Daga yau sai yau, kada ki kara kawo min ita dakin barcina. Ke kanki na hakura da ke in har za ki hada hidima ta da tata, ko za ki hada mana makwanci. Idan duk alfarmar da na yi mata ba ki gode min ba zan ba ki mamaki wallahi, don aure zan kara ki ji dadin kula da ‘yarki......”
Tana kuka sosai ta juya da ‘yarta a kafada jikinta har rawa yake, domin Daddy fada yake sosai. Cikin babban sauti wanda ba ta taba sanin yana da shi ba. Tana fita ya banke kofarsa yana sakin tsaki. Haka suka kwana kamar jiya zukata babu dadi.
Washegari bayan yara sun tafi makaranta, shi kuma ya tafi office, kamar jiya yau ma bai kula abincin da ta bata lokaci ta shirya masa ba. Tun asuba ta tashi ta soya masa waina (masa) don ta san yana matukar sonta, haka ya tsallake ya bar mata kayanta kamar jiya ya sa ‘ya’yansa a gaba suka tafi. Su kansu yaran ba sa cikin walwala ganin halin da iyayensu ke ciki na rashin walwalar suma, yanayi ne da ba su taba ganinsu a ciki ba tun tashinsu. Daddy da Mammah suna matukar kaunar junansu, sun fahimci juna, ra’ayinsu daya kusan a kan komai na rayuwa, sai yau a kan ‘yar Habiba, kowanne gani yake shi ne a kan gaskiya.
Shi Dr. Hamza ba muguwar zuciya ce da shi ba, ba rashin tausayi gare shi ba, ba kin taimako gare shi ba, a’ah, ra’ayi ne na rikau irin na Malam Bature, duk wani taimako da zai wa mutum ko jininsa ne ya fi yarda ya yi masa shi daga nesa komin girmansa, amma ban da ya dauko shi ya kawo cikin family dinsa. Ita kuma Hajiya Maryam tana matukar son Habibah, son ne ya shafi abin da ta haifa, sannan tana tunanin in ba ta rike yarinyar nan ba ina za ta kai ta? Ba ta san komai da ya dangaci Habibah ba ba ta san daga inda ta fito ba, sannan in ta kai ta gidan marayu tana tausayin rayuwar da za ta taso a ciki. Za ta taso ne a shegance, a shegantata bayan ita ta yarda yarinyar nan ba shegiya ba ce da ubanta, akwai abin da ya rabo Habiba da mahaifinta. Me ya sa Daddy ba zai yi mata alfarma ba?
Hantsi na dagawa ta samu wayar Anti Safiyyah ta daga suka gaisa da tambayar lafiyar yara. Anti Safiyya ta ce, “Mai aikin babba ki ke so ko yarinya, ko budurwa?”
“Babba dai, wadda ta san ciwon kanta. Ban da wadda ba ta kai shekaru hamsin ba”.
Safiyyah ta ce, “To alhamdu lillahi an samu. Sunanta Azumi, ‘yar Sakoto ce, zan kawo ta ranar juma’a insha Allahu. Za a dinga biyanta Riyal dari biyu duk wata, duk irin hidimar da ki ke so ta yi miki za ta yi miki, ku dai tattauna a tsakaninku”.
“Na gode Safiyyah sosai. Na gode Allah ya kara zumunci”. In ji Mammah. Da haka suka ajiye wayar.
A cikin wannan hali na zaman doya da manja, zuciya ba dadi, Hajiya Maryam ta ci gaba da zama da mijinta a dalilin ‘yar mai aikinta. Ana i’gobe za su cika kwana bakwai da baro asibiti tunanin ragon suna (haqiqa) ya dame ta. A yadda Daddy ke kumbure-kumburen nan za ta doshe shi da zancen yanka ragon suna? Ta yi tunanin ta bai wa Salah ya sayo da kudinta kamar yadda ta yi amfani da kudinta wajen siya mata suttura, madara kam ya saya katan-katan kamar yadda ya furta, sai dai wani (positive) tunani ya shige ta. Bai kamata tun yanzu ta soma yin gaban kanta a kan yarinyar ba, dole ta ba shi hakkin da yake cewa tana ‘forcing’ dinshi na zaman uban yarinyar yana so ko ba ya so, in ta sayi rago ta yanka mata ya tabbata ita ce uwarta, ita ce ubanta kenan,
“You must be the father you don’t want to be Daddy!”. Ta fada a fili.
A daren ranar ta cancada kwalliya, turare kala-kala ta feshe jikinta da shi, a gobe ta ke sa ran za a kawo mata sabuwar mai aikin. Ba za ta iya barin Baby ita kadai ba, don haka ta kira Usman da Isma’eel da Halim ta jere su a gadonta ta ce su kwana a nan.
“Isma’el ba ka da nauyin barci, ka kula da baby in ta motsa. Ga madararta, ga ruwan zam-zam dinta ka duba pampers akai-akai”.
“Dont worry Mammah, je ki lallasar mana Daddy ya daina fushi da ke. Mammah tausayinki nake ji, ya ce wai wata sabuwar mata zai kawo mana ke kin daina sonsa sabida jaririya”.
Murmushi ta yi, ta ce, “Isma’el Allah ne ya halatta masa auren mata har hudu in yana da iko. Ba saboda jaririyarmu ba ne. Kuma ba saboda ita yake fushin da yake yi ba, ni ce na yi masa laifi”. Ta fadi hakan ne don kada su fassara mahaifin nasu a matsayin mutum mara tausayi da adalci. Wanda tuni hakan ya fara darsuwa a zuciyar Isma’el tunda ya fi Usman da Halim wayo. Amma yanzun ya yarda da abin da Mammah ta ce, sai dai ko kusa ba ya son Daddy da wata macen bayan mahaifiyarsu. Akwai abokinsa a makaranta a Abuja da yake ba shi labarin cewa Mamansa ta rasu wajen haihuwarsa a hannun (step-mother) dinsa yake, kullum sai ta dake shi ta sa babansa ya dake shi, kuma ba ta bashi abinci sai mai aikinsu ce ta ke ba shi. Wannan labari da Salim ya ba shi ya tsaya masa a zuci, ba ya so ya ji an ce za a kara aure.
Da haka Mammah ta wuce ta barshi yana tunani, yana kallon Baby da ke barcinta cikin kwanciyar hankali a cikin kyakkyawan gadonta da ke gefensu. Usman da Halim tuni sun yi barci.
Mammah ta yi sallama a kasaitaccen (bedroom) na Ambassador Hamza Dakata, tuni ya kashe fitila ya rufe kwamfuta yana azkar din barci, dole ya amsa sallamar don bai zaci ganinta a lokacin ba. Kwana shida kenan rabon da su hada makwanci, in ya ce ba ya kewar Maryam ya san ya yi babbar karya ya kwana da yunwa. Mace daya tamkar da dubu wadda ta mamaye filin mata goma a zuciya da ruhinsa, ta haifa masa sanyin idaniya ABDUL’AZEEZ HAMZAH ATIKU, in ya ce zai hada matsayinta da na wata mace da sunan aure ya san ya fada ne kawai don ya ji dadin bakinsa ko ya huce haushi amma Maryam ta wuce nan a zuciyarsa.
Jin ta ya yi ta kwanta a gadon bayansa ta sanya tausasan hannuwanta ta rungume shi, hawayenta na sauka saf-saf a kan kafadunsa. Runtse ido ya yi wani sanyi na ratsa zuciyarsa. Ta ja bargon da yake kokarin rufawa ta ajiye a gefe.
“Ka yi hakuri Daddy don Allah ka yi hakuri, na yarda laifina ne, na kasa hakura da tsarinka in yi maka biyayya. Na yi ne don neman lada a wurin Ubangiji ba don in bata maka rai ba Daddy”. Ta fadi cikin shesshekar kuka mai motsa zuciya balle zuciyar masoyi. Kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya dago ta ya juyo suka fuskanci juna.
“Why Maryam? Me ya sa ki ka zabi farin cikin wasu bare da ba ki hada alakar komai da su ba a kan nawa? Na dade ina mamaki, ina tambayar kaina anya Maryam dina ce? Ta bar ni kwana shidda ba tare da ta san halin da nake ciki ba? Ya ya nake rayuwa? Me nake ci nake rayuwar? Anya Maryam ke ce???”
Hawaye ta ke sharewa sosai,
“Tunda ka gaza fahimtata Daddy, ka kasa mara min baya mu ceci rai, mu yi jihadin rikon maraya tare, mu yi domin neman lada a wurin Ubangiji na amince ka fadi duk yadda ka ke so a yi da jaririyar nan na maka alkawarin zan bi, in har za mu koma rayuwarmu ta baya ka kuma fasa auren da ka ke cewa yara za ka yi. Ba zan iya hada ka da kowacce mace ba Daddy ‘depression’ zai kama ni”.
Bai san sanda dariya ta kwace masa ba, ya yi sosai sannan ya gintse fuska, “Ina nan fa ina jiyo laccar da ki ke wa Isma’el yaushe ki ka juya ta a baibai?
Kin ce Allah ya ba ni iko, yanzu kuma kin ce ‘depression’ zai kama ki, dole in yi aure Maryam

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login