Showing 69001 words to 72000 words out of 168255 words

Chapter 24 - Auren Kwangila Book 4 Hausa Novel Complete

Takori   

12 Dec 2024

314

ganta idonta luhu-luhu ya tabbatar masa ko isasshen barci ba ta yi ba. Tausayi ta ba shi sosai, kowanne dan Adam da abin da yake so, shi Muazatu yake so, Hafsat kuma karatu ta ke so. Yana rokon Allah ya cika mata burinta, shi kuma Ya ba shi ikon zama tsanin cikar wannan burin.
Da suka isa ya nuna mata inda za ta fito ta zauna ta jira shi idan sun gama. Sai da ta shiga ajin zana takardar ya ga shigar invigilators sannan ya bar makarantar zuwa gidansu.
A can ya karya kumallo ya tadda Mammah da Baba Azumi na shirye-shiryen tarbar Ismaeel, Usman da Haleem. Sun kasa zaune sun kasa tsaye. Ya tambayi Mammah karfe nawa za su sauka?
Ta ce, Nan da awanni biyu.
Ya kudure a ransa zai ba da mamaki ba tare da ya yi shawara da Mammah ba.
Kafin azahar ya koma, ta gama papers dinta tsaf ta fito. Inda ya nuna mata ta jira shi ta nufa kai tsaye, ta samu wani benci ta zauna. Tana nan zaune tana kallon shige da ficen mutane wasu a kafa, wasu a motoci. Kamar daga sama ta ji muryar namiji yana yi mata sallama.
Da sauri ta juyo, kallo daya ta yi masa ta gane fuskarsa, a kusa da ita ya zana papers dinsa, zai girme mata sosai don zai yi shekaru ashirin da uku. Dauke kanta ta yi ta amsa sallamarsa. Karshen bencin da ta ke zaune ya zauna,
Kin riga kowa submitting wannan ya nuna kin shirya wa jarrabawar nan sosai.
In magana fa ta karatu ce Hafsat ba ta shariya.
OBJ questionsdin ne sai an yi wani shiri?
Murmushi ya yi, ya ce, A wajenmu yan Nigeria sai an yi, don ke da ganinki Afro-Arabian ce.
A nan kuma shiru ta yi masa.
Wace Uni za ki?
Ban sani ba wallahi, ba ni na cike ba.
Haka ya yi ta janta da hira, wani ta amsa wani ta share shi don ba ta ga dalili ba, kuma ba ta iya wulakanta mutane ba.
Tun daga nesa ya hango Hafsat a inda ya ce ta zauna, amma abin mamaki tare ta ke da wani a benci daya. Hafsat murmushi ta ke yi wani irin murmushi da ya ba shi mamaki, kuma saurayin yana magana, wani irin kyau ta yi masa da handbagdinta a kan cinya. Amma tsaya... wane ne wannan saurayin na kusa da ita? Me ye alakarsu da har ta ke sakar masa wannan murmushin a matsayinta na matar aure? Ba ya tsammanin ko su Ismaeel tana yi wa wannan murmushin (A idonsa fa). Girarsa ta tattare ta hade wuri guda, cike da mamakin yadda yake tsaye a gefensu zaune cikin mota, amma ba ta ma ganshi ba. Wayarsa ya dauka ya kira numbarta don ga dukkan alamu ba su da niyyar rabuwa ko zai kwashe awanni yana jira. Yana kallon sanda ta bude jakarta ta dauko wayar ta kara a kunnenta. Muryarta mara amo mai tsananin taushi ta fito tar-tar ta speaker don wayar a jone ta ke da aux na motar. Bai amsa sallamarta ba ya yi shiru kawai yana jinta.
Yaya ka iso? Ban ganka ba. Kana ina?
Sai kuma ta fara juye-juye alamun tana nemansa.
Tana ganin motar ta ce da matashin wani abu, sai gani ya yi ta tashi, shi ma ya biyo ta sun nufo motar tare, amma ba ta sake cewa komai ba. Daga inda yake ya fahimci saurayin ne yake ta magana ta yi shiru, inda ya fahimci ta gane shi ne ya zo, kuma shirun da ya yi mata yana da maana. Har suka karaso idanunsa a kanta bai dauke ba, ta bude kofar tare da sallama ta shiga ta zauna.
Zai iya rantsuwa ko shopping mall yarinyar nan za ta shiga sai ta yi sallama, daya daga cikin kyawawan dabiunta da ke burge shi kenan. Amma yadda ta jefa shi cikin matsanancin bacin rai yau bai jin ko kallon fuskarta zai iya yi balle amsa sallamarta. Ba ta dauke hannunta daga rufe kofar motar da ta yi ba ya yi mata giya ya fizge ta da wani irin gudu kamar zai tashi sama da su.
Sun hau titi sosai sun kama hanyar cikin gari, so ta ke ta ce ya rage gudun babu fuska, hasalima ba ta taba ganin fuskarsa haka kamar hadari ba, takurewa ta yi a kujerarta ta hade jikinta wuri guda ta yi shiru. Abin kirkin da ya yi niyyar yi mata yau yake so ya fasa, wata zuciyar na tausarsa. Ya karya kan motar ya hau titin da zai kai shi unguwarsu Asokoro.
Kamar daga sama Hafsat ta tsinkayi muryar Abdulazeez a cikin kanta, cikin yanayi mai boye halin da zuciyar mutum ke ciki.
Waye shi?
Ya tambaya a matukar gajarce. Ba tare da ya dauke kansa daga titi ba, kuma ba tare da ya dube ta ba.
Ta murza yatsun hannunta cikin junansu, sannan ta ce, Ni ma ban sanshi ba.
Muryarta ta nuna zullumin da ta ke ciki irin na guilty conscious. Bai sauya daga yanayin da yake ciki ba ya ci gaba da tambaya.
Ba ki sanshi ba ki ke hira da shi kina matar aure? Ba ki sanshi ba murmushinki ya zama mai arha a gare shi? For Allahs sake me ya hada ki da saurayi Suhaana? Wace irin hira zai miki har ya samu murmushinki haka?
Dagowa ta yi ta kalle shi. Har zuwa wannan lokacin idonsa na kan titi. Ya ci gaba da magana cikin bacin rai ammawannan karon kamar cikin lallashi.
Aure kowanne iri ne yana da martaba da mutuncinsa. Kuma kin sani wannan auren yana da limit kina da enough timeda in maza dari ki ke son kulawa a nan gaba za ki yi. So please kar ki kara bana so, I repeat it, bana so! Kada ki ba da kofar da za a fahimci irin zaman auren da muke yi.
Sai ta yi shiru tana kallon hanya cikin mamakinsa. Ta yi rantsuwa ta daina sanya alamarin Muazatu a ranta, amma da ta ce ashe babu dadi. Maganarsa ta karshe ta yi mata ciwo wai ta bari sai aurensu ya kare ta kula maza dari in tana so. Ita da a rayuwar da ta yi cikin turawa ma ba ta sanya kanta cikin shaanin maza ko ya ya yake saboda yadda Mammah ke kwabarta a kullum, sai yanzu da ta ke da sunan matar aure?
Aurensa da ta ke tare da shi yanzun kawai yake karewa, ba ruwanshi da duk irin rayuwar da za ta yi a gaba, koda kuwa ta karuwanci ce, to kula maza dari a yana nufin karuwanci.
Ji ta yi idanunta sun cicciko da kwallah. Amma ta yi kokarin maida ita. Ta koma ta jingina da kujera ta rufe idonta ba tare da ta ce da shi komai ba. Ba ta bude idonta ba lokaci mai tsawo, sai da ta ji ya ja birki ya kashe motar. Sai dai da ta bude idon maimakon ta ganta kofar gidanta, sai ganinta ta yi a kofar gidan iyayensu (gidansu).
Duk wani bacin rai nemansa ta yi ta rasa. Da sauri ta dube shi kamar ta rungume shi. Ya wani hade rai ya matse gira ya dauke kai daga kallonta. Murmushi ta yi ta soma kicin-kicin bude kofa amma ta kasa. A marairaice ta dube shi kamar za ta yi kuka.
Wallahi in ki ka fito da hawaye juyawa za mu yi. Mu shiga a tare, in mun je falo ki zauna kusa da ni, kada ki yi hannu da Haleem balle Ismaeel. In na kula ki, ki ba ni attention, kin san Mammah proffessional ce wajen karanto psychological movesdin kowa cikin yayanta, don haka ki nutsu.
Ita dai burinta ya bude mata kofa ta ganta a falon gidansu, don haka da gaggawa ta amsa. Sai da ya gama yangarsa da noke-noke da neme-neme cikin motar na babu gaira babu dalili, zuciyarta kamar ta fito ta bakinta don takaici, sannan ya bude kofofin motar.
A tare suka fito tana so ta shiga da sauri, amma dole ta jira shi ya zagayo suka jera, What a perfect match? Abin da Ismaeel ya fada kenan wanda suka fara tozali da shi a cikin falon yana cin abinci a dandaryar kasa.
Haleem, Usman, Mammah, Daddy, Ramadan da Shaaban da Farhan yayan Uncle Abdulkareem wadanda su ma gidansu a nan Abuja ne unguwar Maitama, suna hade a makeken family diningdin gidan suna cin nasu abincin. Tare da su aka je aka dauko su Ismaeel daga filin jirgi.
Hafsat kasa jure wannan tafiyar da Abdulazeez ke so su yi ta yi, ana shigowa falon taku daya-biyu ta sheka da gudu ta rungume uwarta, uwar da babu kamarta a duniyarta, wadda ta fi dutsen sapphire daraja a gare ta. Hajiya Maryam Hamza Atiku.
Lallai ma, wato duk cikar mu nan Mammah kadai ki ka yi kewa? Inji Auta Haleem.
Kyale ta Brother, ni sau daya ta taba kirana a waya, ni in na kira ta a ce na aje voicemail. Cewar Usman wanda ba su cika shiri ba, shi halinsa ma daban ne da na kowa a gidan, bai cika shiga shirgin mutane ba hatta iyayensa sai dai su neme shi, irin mutanen nan ne masu kamewa, shi dai bar shi ya fuskanci karatunsa ya fiddo (CGPA) mai daraja.
Wai ni yarinyar nan ta ke kira bachelor saboda ta riga ni aure kamar ba a hannuna ta soma ta-ta-ta ba. Cewar Ismaeel.
Haka kowannensu ke jifanta da korafinsa, ita dai ta yi shiru ta dora kanta a kafadar Mammah sai murmushi ta ke yi. Tana binsu da idanun kauna daya bayan daya. Mammah wadda farin cikinta ya kasa boyuwa ta ce,
Kai ku kyale min yarinya ina dalili? Daga jarabawa ta dawo ko hutawa ba ta yi ba.
Ta ja mata kujerar kusa da ita ta zauna, ta tsugunna ta gaida Daddy wanda ke magana da Abdulazeez tun shigowarsu. Sosai ya amsa yana kara jin yarinyar har cikin ransa da matsayi iri-iri na ya, na suruka, na rabin jiki ga Abdulazeez dan da bai da kamarsa. Hatta sauran yayan sun san haka, sai dai su yi hakuri, duk wani Da ya biyo bayan Abdulazeez a wajen tsohon Ambassada Hamza Atiku.
Sai ga Baba Azumi ta billo daga corridor din kicin tana dauke da katon din ruwan sha mai sanyi na FARO. Da Hafsat ta fara tozali fuskarta ta washe, bakinta ya fadada, ta rasa dalilin wannan gashin kuma na Hajiya Maryam, wai ba za su je wajen Hafsat ba sai ta shekara a gidan miji, ga shi ai su sun kasa jurewa sun zabi mai fishshe su. Tunda sun zo ai ba za ta kore su ba.
Oyoyo da yar Baba, oyoyo da yar Mammah, lale da amarya mai abin mamaki.
Turbunewa Hafsat ta yi tana cuno baki, Da na zo da kaina Baba Azumi? Wai ke ma har da ke, ba kya nemana... kin manta da ni...
Ina kaka za ta manta da jikanyarta? Wane mutum!!!
Gabadaya aka yi dariya, sabida irin yadda ta jinjina girman alamarin. Hafsat ta karasa gare ta ta rungume ta.
I missed you so much Baba...
Baba Azumi na jin turanci sama-sama ta ji abin da Hafsat ta ce.
Kin yi fari, kin yi kiba, Babban Yaya ya iya kiwo. Mu ma mun yi kewarki yar Mammah, kullum ma muna yi (kewar). Ta fada tana bubbuga bayanta.
Da kyar Baba Azumi ta samu Adda ta sake ta. Hafsat na ji Mammah na tambayar Abdulazeez ko ciwon Hafsat ya taba tashi? Dago kai ya yi ya dubi mahaifiyarsa cikin mamaki, dama tana da wani ciwo ne?
Mantawa ka yi tun haihuwarta tana da pneumonia? Habiba na shan ruwan sanyi sosai da yin taammali dashi
Tsit falon ya yi, kowannensu na tuno Habiban da rayuwarta ta dan gajeren lokaci tare da su, wadda ba za su taba mantawa ba. Hafsat ji ta yi kamar an yi mata shocking a lokutta da dama mantawa ta ke tana da wata uwar bayan Mammah, tunda ita dai ba ta santa ba ko a hoto. Ga shi Mammah ba ta so a yi zancen. Yau tunda ita ta tado shi ba wani ya sa ta ba, sai ta gaya mata cikakken asalinta.
Shesshekar kukanta kawai aka ji ya ratsa shirun da aka yi, Don Allah don Annabi Mommah ki gaya min wace ce ni a cikinku? Na san ba ki yi min haihuwa ta jini ba da ba ki hada aurena da Yaya Abdulazeez ba. Na dade da sanin wannan, ina da wata uwar daban bayan ke. To amma uba fa? Ko shege ne ta yi ta kawo muku...
Sunkuyar da kai suka yi bakidayansu, saboda su ma ba su da wannan amsar. Abdulazeez ne ya katse shirun da shesshekar kukanta ya ce, Suhaana, Hafsat Suhaana. Har sau biyu.
Ta amsa cikin rishin kuka, Dago ki dube ni. Dagowar ta yi ta dube shi, in lissafin da ta ke yi daidai ne shekarunta goma sha takwas jiya, su gaya mata ko ma wane iri ne asalinta za ta iya dauka. Don hakawith eager( da zakuwa) ta ke kallon mijin nata, tsakiyar iyaye da yan uwansa idanunta cike da hawaye.
Ba shegenki ta yi ba, ni ta gaya min kina da uba kamar kowa da yan uwa na ciki daya har ukku, kuma ba ta yi kama da mutuniyar banza ba. Mace ce mai cikar mutunci, mai kirkin gaske. Da yardar Allah sai na nemo mahaifinki da yan uwanki Hafsat na sadar da ke gare su. Ki ba ni wata uku, I promised.
Daga kai ta yi cikin amincewa, Wipe-off the tears... (goge hawayen). Ya fada cikin kankanuwar murya.
Kunya ya ba ta sosai, tasa gyalen abayarta ta rufe fuskar bakidaya. Dariya kowa yake mata, zuciyar Hajiya Maryam kamar koramar madara da zuma don dadi na kulawar da Abdulazeez ya nuna akan Hafsat a gaban kowa. Ita dai haka ta ke so, Abdulazeez ya so Suhaana da zuciya daya, in ya yi hakan ya gama mata komai, kuma albarkarta gare shi ba za ta taba yankewa ba.
A yau Hafsat-Suhaana ta san ko wace ce ita a cikin iyalin gidannan, daga bakin uwarta/surukarta Maryam Dakata. Labarin da ya tsaya mata a zuciya ya kasa wucewa;yar mai aikinta ce ita! Babu wata alakar jini ko ta yaya! Her mum is her servant, her maid. Ba ta san daga inda ta ke ba, amma ta raine ta, raino irin na fisabilillahi, wanda dan cikinka kawai za ka iya yi mawa, duk hakan bai isa ba Abdulazeez ta zaba mata a matsayin miji. Dan gatan da bai rasa komai ba, mai asali da ilimi. Mutane irinta nawa ne a cikin alumma??
Yanzu ta gano dalilin da ya sa Abdulazeez ya kasa sonta! Allah sarki!! Ai ya yi kokari ma, kokarin da maza irinsa da yawa ba za su iya ba. A yau ta karbi uzurinsa da hannu bibbiyu, na son rabuwa da ita a gaba, za ta taimaka masa ya cika burin rayuwarsa ya yi auren da maza masu gata irinsa ke yi, wanda hankalinsa zai kwanta da shi. Ba don Mammah ce ta haife shi ba, da ta ce ta zalunce shi da ta hada shi aure da ita don kawai tana sonta. Wannan bai isa hujja ba a ganinta. Ta gyara mata rayuwa shi ta gurgunta tashi, ta hanyar aura masa yarinya irinta mara galihu mara asali mai kaskantaccen matsayin a gidansu. Amma faruwar wannan alamarin a yau da abin da Abdulazeez ya yi mata na karamci a gaban iyaye da yan uwansa sai ya kawo wani SABON ALAMARI mai girma a zuciyarta a kansa. Wani bakon feeling da ba ta san daga ina yake fitowa ba tsakanin zuciya, ruhi da gangar jikinta. Ya dasa wata katotuwar bishiya mai yawan ganyayyaki, sai yabanya (yado) suke a rassan jikinta. Babu wani bangare na wadannan halittu guda uku tsakanin zuciya, ruhi da gangar jiki da ba ya ambaton sunansa a wannan lokacin da murya mai tsananin amo da amsa kuwwa.......ABDULAZEEZ HAMZAH ATTIKOU... cikin sauti maabocin amo da karsashi. Jinsa ta ke yi a koina na sassan jikinta da wannan sabon alamari mai ban mamaki da ba ta taba tsintar kanta a ciki ba.
Kowa ya dubi Hafsat ya san ta zama cool a kan yadda ta zo a farko. Da faraa da faram-faram, da dokin kowa nata.
Sai babu wanda ya bai wa canzawarta hankalinsa. Hatta Mammah kuwa, sun alakanta hakan da sabon labarin rayuwarta da ta ji. Abdulazeez ne kawai ya lura da canzawarta mai harshen damo ce (mai maana biyu), kasancewarsa wanda yake kwana ya tashi gida daya da ita a halin yanzu, kuma a irin shakuwar da suka yi a wannan lokacin zai iya cewa ko Mammah ba za ta gaya masa wace ce Hafsat ba, sai dai ta gaya masa (little Hafsat) amma ba baligar ba.
Hafsat-Suhaana mai sanyin hali ce, ba ta da daukar duniya da fadi, mai kirki ce, mai girmama na gaba da ita. Mai gudun zuciya da karbar rayuwa a duk yadda ta zo mata ba tare da ta yi jayayya da ita ba. Yanayinta ba ya iya boye abin da ke zuciyarta. Wadannan sune manyan halayenta da ya fahimta a tsayin zamansa tareda ita.
Sosai ya fahimci hayaniyar gidan ta daina burge ta, tana bukatar privacy na yin nazarin sabon labarin da ta ji da kuma yadda zuciyarta za ta karbe shi, ta saba da shi, tana bukatar kadaicewa ta yi jinyar zuciyarta.
Mammah dai duk abin da ta san Hafsat na so shi ta ke kokarin yi mata yau. Ta kawo wannan ta kawo wancan. Duk don ta kawar mata da damuwar. Baba Azumi na can kitchen tana yi mata awara kwano guda da za ta sanya a firji ta dinga soyawa in ta ji marmari kasancewar tana sonta. Ishma ya yi mata tsaraba sosai na (English wears) da takalma da jaka leda guda. Ta idar da sallar magriba a dakin Mammah, ta ci gaba da zama shiru a kan sallayar ita ba lazimi ba ita ba addua ba; deep in thought.
Abdulazeez ya shigo dakin ya isa har inda ta ke zaune ya tsaya a kanta, Mammah na gefe tana shirya mata kayan girki da ta siya mata a Bacco. Bai ma lura Mammah tana gefe ba yake magana.
Hafsat, mu tafi gida.
Dagowa ta yi ta dube shi da kwayan idanunta da suka kankance. Wani irin kallo ta ke masa a yau withutmost respect da ita kanta ba ta san irinsa ba. Samun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login