Showing 159001 words to 162000 words out of 168255 words

Chapter 54 - Auren Kwangila Book 4 Hausa Novel Complete

Takori   

12 Dec 2024

329

******
Hafsat ta sauka lafiya a Abuja. Kwananta biyu ta huta gajiya, sannan ta koma makaranta. Ta tarar Haleem ya koma makaranta, Ismael da Usman na shirin tafiya hidimar kasa. Baba Azumi jikin girma ya motsa ba ta da lafiya, yarta Harira ta zo daga Sokoto wadda ta zauna da ita a gidanta tana amarya tana taya Mammah kula da ita, Mammah ta yi sabuwar mai aiki Jummai daga Minna ta ke. Ita da Harira suke zaune da Mammah kafin Harira ta koma Sokoto, saboda ta baro mijinta da yaranta. Jummai na da kirki sosai da faram-faram nan da nan suka saba. Ta ji dadin ganin Harira matuqa, Mammah ta gaya mata kullum sai ta yi zancenta. Nan da nan suka taru suka debe mata kewar Abdulazeez kasancewar daga Harira har Jummai masu son barkwanci ne na a buga a jarida.
Mammah kula ta ke da Hafsat da mugun cin abincinta yadda ya kamata da duk abin da mace mai juna biyu ke bukata. Salisu ke kai ta makaranta ya dauko ta, da daddare in za ta kwanta sai ta girke mata (food flask) a gefen gadonta saboda tashinta cikin dare cin abinci. Bayan wannan ba ta fuskanatar wata matsala, ko kwana biyu ba ta yi ba daga Jummai har Harira sun gane matsalar Hafsat din duk da Mammah bata fada musu ba. Sai suka kara zage damtse wajen taya ta kulawa da surukuwarta ko kofi ba sa bari ta wanke.
Baba Azumi na jin jiki sosai, ciwon kafa da ciwon baya daga karshe sai kwantar da ita aka yi a asibiti gabadaya. Kullum da daddare suna midnight call dinsu don lokacin ne kadai Abdulazeez yake free, komai ta yi a rana sai ta sanar da shi, shi ma duk abin da yake ciki sai ta ji. Harira ce ta ke kwana da mahaifiyarta Azumi, Mammah da Jummai na jigilar abinci, Hafsat ma kullum ta taso makaranta can ta ke fara biyawa sai dare suke komawa gida tare da Mammah. Asibitin yana da kyau sosai wanda iyalan gidan ke zuwa ne (Diff hospital) Hafsat ma anan take ganin likita, tana samun kulawa sosai. Kullum sai Hafsat ta gaya wa Abdulazeez damuwarta a kan ciwon uwar goyonta, ko tafiya ba ta iya yikuma Mammah ba ta bari ta kwana. Hakuri yake bata, ya ce. Ke ma patient ce. Insha Allah za ta tashi, girma ne.
Washegari Mammah ta tura Salisu da babbar mota har Sokoto ya debo yayan Azumi gabadaya su zo su duba ta, suka kuwa taho kwansu da kwarkwatarsu da yayansu sai da Salisu ya biya kudin motar haya bus guda daya suka taho tare, saboda motar ta gagara kwashe su. Baba Azumi sai budar ido ta yi ta ga yayanta maza da matan zagaye da gadonta kamar a mafarki. Sai da ta yi kuka don dadi, ta yi ta yi wa hajiya Maryam adduar alkhairi.
A tsakiyarsu ta hango Hafsat rungume da daya daga cikin jikokinta ta saje a cikinsu sai hira suke yi. Hawaye ya kara zubo mata ta ce a kirawo mata ita, hannunta ta kama tana ta yi mata addua tana fadin Allah ya sauke ki lafiya, Allah ya ba ki dan albarka irinki. Allah ya zaunar da ku lafiya ke da mijinki. Allah ya cika miki burikanki na duniya da lahira. Tabbas ke yar halak ce wadda ta san halacci, kin so ni kamar ni na haife ki, mijinki ya kaunace ni kamar ni na haife shi. Allah ya hada kawunnanku ku rayu tare, rayuwa mai tsayi da albarka.
Duk dakin amsawa suke yi da, Ameen-ameen. Ban da Hafsat da haka kawai jikinta ya yi sanyi da wannan doguwar addua da Baba Azumi ke kwarara mata a yau a bainar jamaa. Zamewa ta yi ta koma can karshen dakin ta zauna kanta yana sarawa, don ko ya ya ta yi doguwar tsayuwa sai ta ji hajijiya da ciwon kai. Hirar ta koma tsakanin Azumi da yayanta da jikokinta har Mammah ta iso kawo abincin dare. Ta kuma ce da su su yi sallama ta tafi da su gida su huta gajiyar hanya, su ci abinci.
A guest house dinsu aka sauke su duka, Jummai da Harira na ta shigar musu da abinci na alfarma. Suka kwana cikin jinjina mutunci irin na Maryam Dakata. Uwarsu kam ta zauna da mutanen kirki babu irin alherin da ba ta samu a jikinsu ba, su ma kansu sun huta da su ba wanda bai ci arzikinsu ba. Da safe bayan sun karya kumallo kowa ya yi wanka aka yi shirin komawa asibiti. Sai aka bugo wa Hajiya Maryam waya, Azumi rai ya yi halinsa da asubahin ranar.
Iyakar kidimewa Maryam ta rude, Innalillahi wainna ilaihi rajiun. Kawai ta ke ambata, wayar ta sulale ta fadi daga hannunta. Ta zame ta zauna a gefen gadonta tana ci gaba da salati da dayanta Allah. Ina za ta nemo karfin gwiwar kallon idanun yayan Azumi da jikokinta ta gaya musu gushewarta a doron kasa? Ga Hafsat mai yaron ciki... kawai sai ta fashe da kuka.
A haka Jummai ta same ta, jinta shiru-shiru kowa ya shirya ita ake jira a tafi asibiti. Hafsat ba ta nan tana makaranta. Jummai ta samu Mammah tana gursheken kuka. Tuni jikinta ya ba ta, Mammah ta ce ta hada wayar da ta tarwatse ta miqo mata. Kuka ta ke hawaye sun hade da majina. Jummai ta yi yadda ta ce, ta kira Daddy shi a lokacin ya isa office. Ta gaya amsa, shi da yake namiji ne cewa ya yi, ga shi nan zuwa. Asibitin ya nufa ya karbo gawar don yau Harira ma ba ta kwana wajenta ba, ta ga yan uwa kuma jikin nata ya fi na kowacce rana samun sauqi. Sai ta biyo su. Da nufin a dawo tare gabadaya da safe.
Suna tsaitsaye a harabar gidan duk sun sha wanka sun ci kwalliya, masu goyo sun goya yayansu sai gani suka yi get ya bude, motar asibiti zungureriya ta shigo. Kofofinta suka bude, malaman asibiti biyu suka sauko da gawar a kan gado. Babban danta Yushau shi ne mai karfin halin karasawa ya bude fuskarta da aka lullube. Ai kuwa ya fasa kuka wanda ya tabbatar wa sauran yan uwansa da zatonsu. Daidai lokacin da motar Daddy ta biyo baya, sannan ta su Ismael.
Gida ya rikice ta koina hatta Ismael da Usman kuka suke yi. Yushau ya matsa kusa da Daddy ya yi kuka ya koshi, Daddy na bashi baki, ya roke shi suna so su tafi da Azumi gida Sokoto su yi janaizarta a can. Daddy bai musa ba, nan ya shirya motoci har da shi da yayansa suka dauki hanyar Sokoto, Mammah ta ce za ta biyo bayansu daga baya saboda Hafsat ba kowa a gidan.
A kan hanyarsu ta dawowa gida ta ga Salisu ya dauki hanyar gida maimakon ta asibiti, ta ce, Salisu mu fara zuwa asibiti in ga Baba tukun.
Bai juyo ba ya ce, An sallame ta. Kamar yadda Mama ta tsara masa.
Hajiya Maryam kokari ta yi sosai ta danne alhinin da ta ke ciki, amma ba ta yarda sun yi tsayuwar minti biyar tare ba. Ta tambaye ta Salisu ya ce an sallame ta, kuma na zo gida ban gansu ba daga ita har bakin. Ba tare da ta dube ta ba, ta ce, Sun wuce gida Sokoto da ita, sun ce a can za su karasa jinyarta tunda ta samu sauki. Ni ma gobe zan bi su in kara tabbatar da samun saukin nata.
Ta ce, Mu tafi tare Mommah, na san ba za ki wuce kwana daya ba.
Kai ta girgiza, Kwana uku zan yi, ki zauna saboda makaranta, ko in kai ki gidan Hajiya Halima ko gidan Kawunku?
Ta girgiza kai don ba ta son harkar gidan Anty Zuwaira ba tun yau ba. Zan yi zamana ni kadai, ni da ba wuni nake a gidan ba?
Mammah ta ce, ba zan iya barinki ke kadai ba zan dauko Saadiyya yar hajiya Halima ta taya ki zama.
Ba tare da damuwa ba ta amince.
A daren direban Hajiya Halima ya kawo Saadiyya, budurwa ce ita ma a Nile ta ke karatu. Da suka gane yan makaranta daya ne, sai suka saki jiki da juna suke ta hirarsu. Mammah ta jaddadawa Saadiyyah yadda za ta kula da abincin Hafsat ita abin har kunya yake ba ta, yadda Mammah ke treating dinta ko a gaban waye kamar wata karamar yarinya.
Ta ce, Kai Mommah ita kadai za ta dinga girkin? Tunda mu biyu ne mu yi tare mana.
Ta ce, Ban yarda ba, kin ji na gaya miki. Saadiyyah ko ferar dankali kada ki bata.
Tana dariya ta ce, Toh Mammah.
Hafsat akwai shagwaba, Mammarta ta daure mata kugun yinta.
Da safe Salisu ya kama hanyar airport da Mammah, bayan sun sauke su Hafsat a makaranta, suka wuce zuwa Sokoto.







SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI
07030137870

*Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama*
Bayan sadakar ukun Azumi mutanen gidan suka dawo gabadaya duk jikkunansu a sanyaye cike da kewar tsohuwa Azumi. Abdulazeez ya san da rasuwar, shi ma kuma ya fi kowa jin dadin hukuncin da Mammah ta dauka na rashin sanar da Hafsat. Adduar da ba ta yi mata ba ya hada yake yi musu su biyu. Har Azumi ta yi arbain da rasuwa Hafsat ba ta sani ba. Ranar sadakar arbain Daddy ya aika wa iyalinta kudi masu yawa a sayi duk abin da ya kamata a yi sadaka, da ma kuma sun tafi da komai nata da ke gidan. Rayuwa kenan, Azumi kamar ba a yi ta ba a gidan tsohon Ambassador Hamza Atiku. Allah ka sa mu cika da kyau da imani, mu gama lafiya da kowa, amin.
******
Hafsat ta ci gaba da rainon cikinta karkashin kulawar uwa/suruka ta gari Hajiya Maryam Hamza Atiku. A gefe tana ci gaba da karatunta cike da kwazo. Semester ta kare suka yi jarrabawa amma hutun na sati biyu kacal. Wannan karon ko Yola ba ta je ba balle ace America, Mammah ta ce ita da hawa jirgi sai ta haihu kuma. Ga hutun daman ba yawa, shi ma a nasa bangaren da ya gama semester din farko ya so ya zo gida, amma yana da dissertation da zai rubuta a cikin hutun, dole ya hakura tunda kullum suna tare a waya da daddare. Sai da cikin Hafsat ya cika watanni bakwai Mammah ta gaya mata gaskiyar rasuwar Babarta Azumi. Hafsat ta sha kuka kamar ranta zai fita, kamar a lokacin aka yi mutuwar, hatta Abdulazeez ta yi fushi da shi kan shi ma bai gaya mata ba, Mammah ma an yi fushi da ita na kwana biyu tana ta lallashi tana bada hakuri. Abdulazeez ya ce.
We want to save lives, wasu na tafiya wasu na zuwa! Haka rayuwar ta gada, take heart sweetheart.

******
Ranar wata litinin Hafsat ta sankato katon danta a asibitin (DIFF) mai tsananin kama da ubansa. Lokacin watanni biyu suka rage wa Abdulazeez ya gama L.LM dinsa. Fadin farin cikin da wannan family suka samu kansu a ciki ba daga su ba, ba daga mutanen Yola ba, ba zai misaltu ba. Zo ki hango jika a hannun tsohon Ambassador Dr. Hamza Atiku Dakata yana ta tofe shi da addua ya hana Maryam dauka wai in ta ga ya fi shi kyau sakinshi za ta yi. Gefe ta koma tana bai wa Hafsat tea a baki tana fadin.
Ka yi ka gama Daddy, ga sabon jini ba abin da zan yi da tsoho mai furfura.
Duk da Hafsat cikin hajijiyar haihuwa ta ke sai da ta yi wa maganarsu dariya a fili. Daddy ya haskawa Baby camera da galleliyar wayarshi ya dana masa hoto ya tura wa ubansa. Wannan ya faru tun a asibiti kafin su dawo gida. Kwanansu hudu suka tattaro bakidaya suka yo Kano inda Mammah ta ce a can za a yi taron suna.
Adda Hafsatu ta girka garwa a murhu ta soma wanke Hafsat da ganyen dalbejiya da runhu. Babyn ma ita ta ke masa wanka safe da yamma. A dakin Addar suke kwana ita da Mammah suna gado ita da jaririnta, Mammah na bisa carpet ta jefa filo bisa. Duk kukan darensa ba ya hana ta barcinta domin kuwa sun san yadda suke yi masa ya yi shiru. Azababben jego Addah ke mata har kuka ta ke yi in ana wankan nan na runhu da gashi da zaman ruwan zafi.
Ana i-gobe suna gidan ya kacame da shirye-shiryen abincin gobe, duk kannen Hajiya Maryam sun zo da yayansu gidan ba masaka tsinke, Aunty Mariya ta goye babyn ta rufe shi ta fita da shi dakin da suke. Hafsat ta fito daga wankan yamma ta shirya cikin atamfa (Vlisco) ruwan goro da ratsin blue ta daura dankwalin sama-sama ta kwanta tana hutawa. Tunanin Abdulazeez ta ke yi, rabonta da shi tun ana i-gobe za ta haihu, zafin nakuda ya sa ba ta tuna da wayarta ba sai bayan ta haihu. Da aka sallamo su ta neme ta a dakinta ta rasa har suka taho Kano ba ta tambayi Mammah ba saboda kunya, ta san da ta ji tana cigiyar waya ta san wanda ta ke so ta kira shi ya sa ta biyo gida (fillanci) ta yi shiru kawai.
Tana kwance tana wannan tunanin ta ji iskar da ta ke shaka tana sauyawa da wani atmosphere mai dadi da kwantar da zuciya;the familiar scent of creed aventus, idan mafarki ta ke yi tana rokon Allah kada ya tada ita daga wannan daddadan mafarki. Tattausan hannunsa ta ji cikin nata ya matsa shi sosai yatsunsa sarkafe da nata. A hankali ta ke bude idonta don tsoro ta ke ji kada ta bude idon gabadaya ta ga ba haka ba, gradually idanuwan suka washe a dakin hasken kwan fitila ya haska mata shi sosai. The last person da ba ta yi tsammanin gani nan kusa ba. Taimaka mata ya yi ta mike daga kwanciyar, abinka da danyen jiki koina ya yi taushi tubus ya yi wani irin fresh kamar da ka taba ta jini zai yi tsartuwa, ta zama kamar sai ka wanke hannu kafin ka taba. Gefenta ya dawo ya zauna kafafunsa na zube a kasa ya ciccibo ta gabadayanta ya aza bisa cinyoyinsa. Kallonta yake cikin ido da wani irin yanayi cikin kwayar idonsa. Kunya ta kamata sai kokarin guduwa ta ke yi, sai ji ta yi ya fara kissing dinta gabagadi ta inda duk ya samu a matukar dokance. Aunty Mariya da ta shigo kawo yaro ta yi kyakkyawan gani ai ba shiri ta juya sai ta ci uban tuntube da robar wankan baby da ba a dauke ba saura kadan ta fadi, ta dafe babyn da ke bayanta da iyakacin karfinta. Da sauri Hafsat ta dire kasa, shi kuma ya hau yi mata.
Sannu Aunty Mariya, dan waye a bayanki?
Wata uwar harara ta zuba masa, ta ce, Danka ne! Ina ma na fadi mun fadi ni da shi in ga ta karshen soyayya a cikin mutane?
Da ya yi wata zabura sai ga shi a gabanta, What? Jaririn kwana shiddan ki ke goyawa? Idan kafarsa ta lankwashe fa? Sauko shi, maza sauko shi.
Ya soma kokarin kwanto goyon daga jikinta da kansa. Kunya ta lullube Hafsat shaf! Ya manta da wa yake magana, kanwar mahaifiyarsa ce ba yar mace da dan namiji suke ba balle ya ce abokiyar wasansa ce. Shi yake abin kunyan, amma ita ke jin kunyar a jikinta. Mariya ta kwance masa dansa tana harararsa bai ko san tana yi ba ya tafi duniyar kallon kyautar da Allah ya yi masa kamar ya yi khaki ya tofar. Aunty Mariya ta fice tana ta fadace-fadace wai Abdulazeez ya yi mata rashin kunya saboda ta goya dansa.
Zo ki gani Hafsat yana tsotson bakinsa yana murmushi, may be he is saying welcome to me.
Tuntsirewa ta yi da dariya.
Ai tun jiya yake tambayarka.
Da gaske? Shi ne ba ki min waya kin gaya min ba?
Abin sai ya koma bai wa Hafsat tausayi, saboda shi tsakaninsa da Allah ya yarda. Fathers love. Ta fada a hankali har ya shiga kunnuwansa.
Which is like no other. Ya ba ta amsa, sannan ya sanya hannun hagunsa ya janyo ta barin hagunsa ya hada su ita da jaririn ya rungume ya lumshe idanunsa.
Allah ya yi muku albarka, Allah ya taya ni kulawa da ku. Idan bana nan Allah ya kula min da ku. Allah ya sa mahaddacin Alqurani ne, sanyin idaniya ga iyayensa da kakanninsa, abin alfahari ga alummah....
Hafsat na ta amsawa da Ameen-ameen. Cikin jin kunya.
Karkata kunnensa ya yi zuwa bakinsa yana masa kalmar shahada, ya yi masa khutbah da sunan da ba ta sani ba. Ya ciro dabinon da ya yo guzuri na (ajwa) daga aljihunsa ya tauna ya sanya masa a baki, yaro ya kama lashe baki, cike da annashuwa ya ce, Hafsat zo ki gani, ya san zaki.
Ta waiwaya ta sake waiwayawa bakin kofa da window. Yaya Azeez, don Allah ka bari kada a jiyo mu, za a ce kana rashin kunya, ko ba ka ji me Aunty Mariya ta fita tana fada dazun ba?
Wata banzar harara ya yi mata, ya ce, To hell with the kunyar, in samu Dan kaina na farko ba zan gode wa Allah ba? Ba zan yi farin ciki ba? Saboda kada ace banida kunya?
Sassauta murya ta yi cikin lallashi, Ba haka nake nufi ba, nufina ka boye kada ka bari a ji sai in kuna ku biyu kai da shi. Nan kuwa gidan iyaye ne kowa na iya ji.
Babban yatsansa ya sa na tsakiya da na farko ya dalle mata baki, ta dafe bakinta don azaba nan da nan ya kumbura. Idanunta sai da suka yi ja.
Ya ce, Gobe ki kara gaya mini traditional folkloresirin wadannan goya shi zan yi in fita tsakar gida kunyar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login