Showing 72001 words to 75000 words out of 168255 words

Chapter 25 - Auren Kwangila Book 4 Hausa Novel Complete

Takori   

12 Dec 2024

295

kanta kawai ta yi da mikewa ta hau ninke sallayar. Ita ma za ta fi son hakan, kadaicin kawai ta ke so. Ta yi jinyar sabon alamarin nan da ke faruwa da zuciyarta.
Harararsa Mammah ta yi, amma fuskarta annuri ta ke fitarwa.
To Alhaji, ai ka bari ku ci abinci ko? Were having a get-to-gether dinner today in honour of Hafsats eighteenth birthday. Za a yi hotuna da vedio a aje don tarihi.
Za mu dawo. Ya fada tare da kama hannun Hafsat ya mika da ita tsaye, ita kuma ta kwace cikin jin kunya.
“Shes not in the mood Mammah, za mu dawo in an kwana biyu.
Daure fuska Hajiya Maryam ta yi, ganin yadda yasaHafsat ke jin kunya kamar ta shige cikin kasa da abinda yakeyi din a gabanta.
Na fi ka sanin shes not in the mood din ai, a haka nake so a yi hotunan da vedion. Na so in yi mata ne tun jiya ranar da ta cika shekara sha takwas Allah bai yi ba. Ko hawaye ta ke a haka za a yi, ka je ka sauko da Daddy.
Murmushi ya yi ya saki hannun Hafsat ya juya ya fita, sosai Mammah ta ba shi dariya, wai ya je ya sauko da Daddy sai ka ce wani dan karamin yaro? Kawai tana neman hanyar da zata kore shi ya bar musu dakin ne.
Tare suka ci abinci gabadaya a makeken family dining din gidan, uwar da uban da yayan su biyar, Abdulazeez kusa da Hafsat, Ismaeel ne ya dauko digital camera dinsa ya dinga daukar hotuna da vedio. Duk abin da wannan family suka san zai faranta wa Hafsat yau shi suke mata har Daddy. Ko ita butulu ce dole ta manta komai ta saki jikinta ta koma cikin walwala.
Hotuna sun yi kyau sosai, Ismaeel ya ce zai wanko ya kawo musu gida. Mammah ta gama hada mata komai suka rako su har bakin mota suka shiga suka nufo gida.
Ba wanda ya yi magana a tsakaninsu har suka shigo gida. Kowa ya nemi dakinsa, wanka ta yi don ta ji dadin jikinta tayi brush yadda ta saba duk dare sannan ta fito ta sanya kayan barci. Ta shafa turaren (Rihanna Rogue) sama-sama ta bi lafiyar gado.
Ya jawo (files) din da ya dawo dasu daga officebayan ya fito daga wanka, ya daura wasu tausasan pajamasruwan makuba na(Neiman Marcus)ya yi amfani da turarukan da yake amfani da su da daddare (beforemidnight, da midnight oud)wai zai yi aiki don kore wa kansa tensiondin da yake ciki, amma abin mamaki ba ya fahimtar komai a cikin takardun, dole ya mayar ya rufe saboda Hafsat kawai yake gani tana gilmawa a cikinsu, da yanayin da ta ke ciki a yau.
Tana bukatar mai kaunarta a kusa da ita, kada kadaicin rayuwar ya yi mata yawa. To amma ya yi wa kansa alkawarin ba shi ba sake shiga turakarta tun lokacin da ya tsallake rijiya da baya, me zai iya yi na nuna mata yana tare da ita cikin kowanne hali da ta samu kanta a ciki?
“Be with her today, the whole night. (Ka kasance tare da ita yau, a tsayin daren bakidayansa).
Kaso tamanin na zuciyarsa ya amince da hakan, kaso ashirin yana kalubalanta. Ba don komai ba sai don gudun abin da hakan zai haifar, sai dai yana da tabbacin ya yarda da kansa ba zai iya cutar da Hafsat ba, rayuwarta bakidaya amana ce yanzu a hannunsa. Faruwar wani abu da ya danganci auratayya a tsakaninsu ko ya ya yake don kankanta zalunci ne da cutarwa a gare ta.
Yana da yakinin zai rike amanar Hafsat kamar yadda zai rike Haleem, ko da shi zai cutu, albarkacin mahaifiyarsa da halayen kwarai na yarinyar, wadanda suka ba ta matsayi na musamman a zuciyarsa.
Wayarsa ya mika hannu ya dauko, sai kuma ga kiran Muazatu ya shigo. Ga mamakinsa sai bai ji dadin kiran da ta yi masa a wannan lokacin ba. Ko bai fada ba muryarsa ta nuna hakan a sanda ya amsa wayar.
Muazatu ya aka yi?
Ta yi dan jim, don ba haka ya saba amsa mata waya ba, muryarsa a dusashe. Ba abin da ba ta kissima a zuciyarta ba da cewa shi ke faruwa, wato tare yake da matar da yake cewa ba ya so. Ta yi magana a kai cibi ya zama kari. Makoshinta da lebban bakinta suka bushe rayas, ta kasa ce masa komai saboda wani bakin ciki da wutar kishi da ya zo ya tokare ta, sai ji ya yi ta kashe wayarta.
Ya duba sosai ya tabbatar kashewa ta yi, sai yake tambayar kansa laifin da ya yi mata? Iyaka hangensa bai gani ba don haka ya rabu da ita, ya kira Hafsat.
Kwance ta ke kawai tsakiyar niimtaccen gadonta, barci ya ki zuwa, ta rufe rabin jikinta da duvet da wayarta a hannunta tana duba hotunan da Ismael ya turo mata da suka dauka dazu, ta tsayar a kan wanda ya dauke su ita da Abdulazeez ya rankwafo ta bayanta kamar tare aka halicce su. Duk sun yi murmushi. Zooming hoton ta sake yi tana hango abubuwa da dama. In dai ba yaudararta zuciyarta ke yi ba, to kuwa tana gaya mata sun dace da juna. Ya fi ta tsayi, ya fi ta fadi (physique chest) gare shi. Komai na halittarsa abin mace ta tsaya ta kare wa kallo ne. Ko shi ya sa Muazatu ta kasa hakura da shi ta bar mata duk da ya aure ta? Ta ke jira ayo waje da ita domin ita ta shigo? Ko ita mene ne aibunta da Abdulazeez ya kasa sonta?
Tambayoyin da zuciyarta ke mata da abubuwan da ta ke darsa mata a yau sun fara ba ta tsoro saboda ba ta ga dalilinsu ba. Tunda bai boye ba ya fada mata ita ba matar aurensa ba ce, matar wucin gadi ce, ta samu kanta da tambayar zuciyarta; mene ne bambancin matar aure da matar wucin-gadi? Ina ma tana da karfin zuciyar da za ta iya yi masa wannan tambayar??
Daidai wannan lokacin kiransa ya shigo cikin wayar da sunan da ta yi saving dinsa da sai a yanzu ta ke kalubalantar kanta kan dalilin ajiye lambarsa da wannan sunan Hussy wato Husband, amma ta kasa gogewa. Ai shi ma ya fada; Aure kowanne iri ne yana da martaba da mutuncinsa. Aurenku ma aure ne tunda ana tare ba a rabu ba, thus,hesindeed your husband wanda kowa ya shaida, ku kadai kuka san kun bashi waadi. Amma wadanda suka daura shi da kyakkyawar niyya suka daura da sadaki da waliyyyai da shaidu kamar kowanne auren sunnah. Amma ga mamakinta ta kasa amsa wayar tasa, a kan dalilin da ba za ta ce mene ne shi ba. Ta yi har ta katse, ya sake kira a karo na biyu.
Hafsat ta ce cikin ranta, Ko sau dari za ka kira ba zan amsa ba Yaya Azeez, me ya kai matar wucin-gadi zuwa turakar maigida a daidai wannan lokacin? Gara in rage shige maka, in tsaya a matsayina kafin zuciya ta ta kumbura a kanka da alamuranka masu ban mamaki. Na kasa gane inda ka sa gaba, na kasa gane inda ni kaina nake heading a kan alamarinmu. Yau kadaicin kawai nake bukata. I want to be alone!.
Ta mike hannu ta yi (light up) daga makunnin da ke jikin gadonta. Fitilu masu sassaucin haske suka maye gurbin masu hasken. Hoton nasu ta ci gaba da kallo tana ta ci gaba da zooming dinsa kamar ta zuko Abdulazeez din daga cikinsa ta mayar jikinta su zama abu guda saboda wani irin intense feelingdake bakuntarta, zuwa lokacin ya gaji da kiran ta ya kyale ta.
Tana cikin wannan halin ta ji an zura mukulli a jikin kofarta ana budewa. Sosai ta razana, sai dai kuma ta san ba mai yin hakan sai mamallakin gidan. Don haka tsoron nata ya ragu, ta bai wa kofar attention dinta tare da boye wayarta da sauri cikin quilt har ya bude ya shigo. Rufe ido ta yi ita a dole ga wadda ta yi nisa a barci. Ta yi zaton zai koma ne daga bakin kofa kamar yadda ya saba, amma sharia sabanin hankali.
Kai tsaye gadon ya nufo, ya hawo shi bakidaya ya bude duvet din ya shige ciki ya kwanta a gefenta. Ji ya yi kafarsa ta shuri abu ya sa hannu ya dauko, wayar Hafsat ce, wadda ta suma a kwance sabida kaduwa da mamaki, Abdulazeez a kan gadon barcinta?
Ba ta son ta yi motsin da zai fahimci idonta biyu, tunda dai bai rabe ta ba, ya yi amfani da daya filon ne ya kwanta kusa da ita, don haka ta ci gaba da tamke idonta. Sai dai zuciyarta harbawa ta ke yi kamar ta faso allon kirjinta ta fito saboda gigicewa. Ba ta sani ba wayarta na hannunsa, kuma tana nan a yadda ta boye ta. Kyakkyawar fuskarsa ce a hoton ta cika screen din da alama zooming ake ta yi. Da ya matse shi sai ya ga ashe ma ita da shi ne wanda Ismael ya dauke su dazu, amma ba kanta ta ke kallo ba, shi kawai ta ke kallo. Sosai mamaki da alajabi suka taru suka lullube shi, ya kuma tabbatar idonta biyu ba barci ta ke yi ba, abin da ta ke yi kenan kafin ya shigo. Ba ya so ya yarda da abin da zuciyarsa ke gaya masa, don haka shi ma ya boye wayar a kasan filo a zuwan bai gani ba yana karyata zargin da zuciyarsa ke nanatawa. Mene ne a cikin kallon hoto? Babu komai. Kawai tana gani ne ba da wata manufa ba. Shes very young... hakan ba zai kasance da ita ba at this tender age... in ji wani bangare na zuciyarsa. Sai kuma wani irin tausayi da bai san dalilinsa ba ya tsirga masa. Duk yadda yake gudun yin zalunci a cikin tafiyar nan anya zai tsira daga aikatashin?
Hafsat ba mutum ba ce? Ko kuwa babu zuciya a cikin kirjinta? Ko kuwa halittar ta daban ce da ta sauran yaya mata? In babu so babu shaawa? Idan ya katange kansa daga soyayyar kowacce diya mace bayan Muazatu zai iya katange Hafsat daga hakan a kansa a matsayinsa na mijin aurenta da ba ta da wani makusanci da ya wuce shi a yanzu? Su kwana gida daya su wayi gari tare su wuni gida daya? Abin da ya faru dazu tsakaninta da saurayi ya fado masa. Wani irin yanayi ya shiga mai wuyar fassarawa fiye da tsammaninsa.
Dakin ya dauki shiru ga zafi ya dameshi kasancewar Hafsat bata amfani da AC, ta saba da rayuwar ta a haka don tsira da lafiyarta. Ba ka jin komai sai bugun zuciyoyinsu, saukar numfashin kowannensu ya sauyaya koma akai-akai yake sauka. Hafsat ta rasa a duniyar da ta tsinci kanta a yau kasantuwar Abdulazeez tare da ita, a gado daya, cikin mayafi daya. Wata irin nutsuwa ta ji na sauka a zuciya da ruhinta. Zuciyarta ta shiga wani irin kai-kawo tsakanin kirjinta da kwakwalwarta. Anya kuwa kadaici ta ke so kamar yadda ta yi tsammani a farko ko kadaicewa da Abdulazeez? Idan haka mata ke samun nutsuwa in suna tare da mazansu na halal a gado daya, ashe kuwa babu wadda zata so a sake ta, ashe kuwa babu wadda za ta so wata mace ta rabi mijinta. Ina kuma a ce da baby kwance a tsakani yana kicking (in between) a tsakaninsu?
Ba ta san sanda ta yi motsi ba don ta gaji da kwanciya a kan barinta na dama. Tana so ta sauya barin kwanciya ba ta so ya san idonta biyu, kuma ba ta sani ba ko babu space mai yawa a tsakaninsu ta goge shi? Ta takura sosai, ga wannan abin da ke tsakiyar kirjinta yana yawo shi ma ya takura mata.... Abubuwa kawai yake gaya mata kala-kala wadanda suka faru, da wadanda za su faru ranar da ta rabu da Abdulazeez ya auri Muazatu...... shin wai ita wace irin shashasha ce da ta yarda ta zauna ya gindaya mata abin da ya ga dama ta hau kai ta zauna don kawai tana so ta yi karatu ta ga danginta? Me ta rasa na dangi? Da me Daddy ya rage ta na mahaifi? Me ta rasa a uwa? Su Ismaeel arent enough? IsntBaba Azumi a great Grandma?Iyalin Abdullahi Dakata bakidaya ba su ishe ta rayuwa ba? KARATU! Zuciyarta ta ambato. Ko da ace Abdulazeez bai kai ta makaranta ba, ba ta da ilimin da zai isheta ta rayu da shi har karshen rayuwarta? Nasa ba zai ishe su ba? Gabadaya kwangilar na nufin za ta samu wadannan abubuwan, amma shi za ta rasa shi!!!
Hafsat-Suhaana ji ta yi zuciyarta ta yi wani matsanancin duhu kamar hadadden hadari mai tafe da guguwa da cida mai gigitarwa. Mai barazanar tafiya da mutum dungurugum in ya zauna a cikin wannan guguwa. To haka ta samu kanta kwatankwacin a cikin guguwa wadda in ta ci gaba da yin wannan zazzafan tunanin guguwar nan da ke tarnaki a zuciyarta za ta tafi da ruhinta ta mutu, Abdulazeez ya huta da wannan kayan nadama da ya jefa ta a ciki.
Zan amince in rasa komai, in dai zan tsira da shi...!!!
Conclusion na zuciyarta kenan.
Amma ai kin riga kin yi alkawari, sannan yadda ki ka amince da hakan shi ma abin da ya yarda da shi kenan a kan Muazatu, har kuwa fushin iyayensa.
Zuciyarta ta yi wani bakikirin, ga wani irin tukuki na fita daga cikinta. In ba ta yi kuskure ba za ta iya cewa, har tururi ta ke yi... ba ta ankara ba ta ji hawaye masu dumi suna sauka suna jika filon da ta ke kwance a kai.
Motsi ta sake yi kadan har ga Allah ta gaji da wannan azabtacciyar kwanciya wadda ko motsi ba ta isa ta yi ba. A na me? Ita da gadonta da dakinta? Tsaki ta saki, tsuuu!
Abdulazeez, wanda zuwa wannan lokacin shi ma a nasa bangaren kwakwalwarsa neman tarwatsewa ta ke yi da tuno abin da ya faru dazu, ya janye duvet din daga jikinsu bakidayaya yi gefe da shi. Ya tashi ya zauna. Cikin shakakkiyar murya ya ce.
Ni ki ke yi wa tsaki Hafsat?
So ta ke ta ce, wanda ya tsargu da shinake ta tuna abin da hakan zai janyo. Ta fahimci abu na karshe da ya ki jini kenan(a kawo masa raini), amma fisabilillahi ya takura mata, ya hana ta barci, ya muzguna wa zuciya da kwanyarta. Ya zo dakinta har gadonta ya hana ta sukuni. Tashi ta yi zaune ta dafe kanta da hannuwanta bibbiyu. Shi ma mikewa ya yi ya zauna ya jingina da filonsa. Da kallonsa ta ke da ta ga yadda yake kallonta da kyawawan idanunsa.
Me ye dalilinki na kin daukan waya ta?
Yadda ya yi maganar cikin kwantaccen sauti sosai ya kara lugwigwita zuciyarta. Da farko shiru ta yi sai da ya kara nanatawa. Fuskarta ta kifa cikin tafukanta ta ba shi amsa cikin raunin murya.
Barci nake yi.
Wayarta ya zaro daga inda ya tura ta ya boye a bayan filonsa ya rike a hannunsa ba tareda saninta ba.
Barci ko kallon mijinki?
Muryar da ya yi amfani da ita wajen fadin hakan ba ya tsammanin ya taba magana da irinta a tsayin rayuwarsa. Duk da muryar ta karasa kassara ta,hakan bai hana ta yin jarumtakar kare kanta ba. A bayanta yake a kishingide, tana gabansa da kadan azaune ta mike kafafunta a kan gadon. Baya ganin fuskarta sai bayanta da kwantaccen gashin kanta wanda ke ta sheki da kyalli cikin dim-light din. Girgiza kanta ta yi cikin musanta zancensa.
Ni ba ni da miji. Hasalima ban san da kasancewar kowa cikin dakin nan ba bayan ni Hafsat.
Murmushi ya yi, karfin gwiwarta ya kayatar da shi, ko da kuwa kalamanta sun masa ciwo. Wayar ya dora mata a kan cinyarta, Wannan da ki ke kallo fa?
Sosai ta razana, don ba ta taba tsammanin wayar nan tana hannunsa ba. Dauke wayar ta yi ta rike a hannunta, ta ba shi amsa.
Mijin wucin-gadi ne.
Sai ga hawaye suna safka dai-daya a kan kundukukinta. Zuciyarta na yi mata wani irin ciwo da tsanar Abdulazeez da duk abin da ya shafe shi. Da bai shiga rayuwarta ba, da yanzu duk haka ba ta faru ba. Da ba a aura mata shi ba, da yanzu tana gidansu tare da Mammanta, da yan uwanta cikin sukunin zuciya. Gabadaya ya shiga zuciyarta ya kekketata, ta rasa abu guda daya da kwakwalwa da zuciyarta ke nufi da wannan walagigin da ta ke yi da ruhinta a kan Abdulazeez Dakata, wanda bai san kowa ba sai kansa. Kowa ya mutu da hurtings in dai shi zai tsira da wata banza Muazatu har mahaifiyarsa kuwa.
Hafsah!
Abdulazeez ya kira ta muryarshi na rawa. Shi ya fadi kalmar wucin-gadi yanzu da ta ba shi irinta ji ya yi kamar ta huda masa hanji. Ya rasa abin da ke masa dadi. Hannunta ya jawo da karfi ta fado jikinsa karo na farko a rayuwar aurensu. Kuka ta saki mara amo bare sauti, wannan kuka yana fitar da zafin da ke zuciyarta ne kawai, amma ba shi da sauti sai shessheka.
Rungume ta ya yi a tsakiyar kirjinsa da wata irin runguma mai tsananin karfi, kamar zai tsaga tsakiyar kirjinsa ya sanya ta har ta soma tunanin kashin bayanta zai karye.
Kokarin kwace kanta ta ke yi, amma ko gezau ta kasa ture wannan giant wanda ya riga ya gama kekketa zuciyarta, yake shirin dumping dinta nan ba da dadewa ba. Ina ruwansa da ita? Ina ruwansa da rayuwarta?Meye dalilin sa na zuwa dakinta yanzu? Yadda ta yi alkawari za ta cika da izinin Allah, ta san ba ta da matsayin samar wa zuciyarta abin da ta ke so a yanzu, wato ci gaba da rayuwa da shi har karshen rayuwarsu, fitina ce kawai da giggiwa irin na zuciya.
Idan Abdulazeez mai son kai ne (selfish) hakika ya kwatanta adalci a cikin (selfishness) dinsa. Ya kamata ita ma ta kwatanta,ba a biye wa zuciya sai ta kai mutum ta baro. Ya ci gaba da rayuwa da ita alhalin babu soyayyarta ko digo a zuciyarsa? Ta ruguza masa farin ciki don amfanin kanta? Ko wannan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login