Showing 60001 words to 63000 words out of 168255 words

Chapter 21 - Auren Kwangila Book 4 Hausa Novel Complete

Takori   

12 Dec 2024

303

Bai kware da hausa ba, bafullatani ne don haka rabin hirarsa da Turanci yake yi wa Abdulazeez. Ya ce shi dan asalin Adamawa ne, ya yi dukkan karatunshi a FUTY, ya yi (Law School) a Lagos. Ya dade da fara aiki, kasancewar gwamnatin tarayya yake wa aiki sau biyu ana canza masa wajen aiki. Ya zauna a Kaduna, ya zauna a Jigawa yanzu kuma aka dawo da shi nan. Yana da mata yar uwarsa da yara biyu.
Daidai lokacin da suka shigo Kubwa yana nuna masa hanya har kofar gidan da ya kama a Kubwa. Abdulazeez ya sauke shi, ya yi nufin juyawa amma Sagir ya dage sai ya shigo sun gaisa da matarsa Rabia, ya ce da shi ya yi dare, amma Sagir ya nace saboda ya ji dadin taimakon da ya yi masa sosai.
Suna shiga falon zuciyar Abdulazeez ta yi wani irin harbawa, wata yarinya ya gani mai yawan sumar kai fara sol, an kame mata gashin a tsakiyar kanta da ribbon. Ba za ta wuce shekaru biyar ba, idan har ba warkewa ya yi daga makanta ba wannan Suhaana ce tana karama, lokacin da suke Jeddah yana ganinta in ya je hutu.
Da gudu ta sheko ta rungume mahaifinta, shi kuma ya daga ta sama suna ta magana cikin fulatanci da ba ya ji. Sai ga Mamanta ta billo daga kicin dauke da yaro a hannunta, fara kyakkaywa amma babu wayewar matan zamani sosai a tare da ita, ta gaishe su, mijin na mata bayanin Abdulazeez da taimakon da ya yi masa cikin fulatanci. Kara rusunawa ta yi tana kara gaishe shi, ta ce cikin yar hausarta mara amo.
Don Allah ka zauna ku ci abincin dare a nan.
Murmushi ya yi, ya ce, Na baro Madam ita kadai.
Babu damuwa, ka ba ni waya in yi mata magana.
Dariya ya yi, Ba za ta fahimci hausarki ba.
Ta dan turbune fuska, Duk gidanmu na fi su iya hausa saboda ni na zauna a cikin Hausawa a Kaduna da Jigawa.
Sagir ya gaya mini.
Jan hannunsa Sagir ya yi ya ba shi ruwan alwala ya nuna masa bayin da ke cikin falon, yana gaya masa Rabia bata gajiya da magana, ya shiga ya yi alwala, alajabin zuciyarsa na kara ninkuwa. Tabbas in ya rantse ba zai yi kaffara ba yana tare da jinin Hafsat. Idan a da yana kokwanton kamanninta da Sagir kamanni ne kawai ganin wannan yarinyar ya kara tabbatar masa da zarginsa, sannan Adamawa ai Yola kenan. Kuma a cikin Yola JIMETA take. Last week da yayi browsing garin a kokarin sa na soma binciken ya gano Jimetan a cikin Yola ne, itace (Yola North).Idan har bai manta ba shi ne garin da mahaifiyar Suhaana ta gaya masa nan ne garinsu. Allah mai karfin iko! Buwayi gagara misali.
Shi da Sagir suka yi sallar magriba, ya ja shi dining suka ci abinci, tuwon shinkafa ne miyar taushe, ta ji tantakwashi da man shanu. Yaushe rabon da ya ci tuwon shinkafa! Sosai ya ji dadin abincin ya yi musu godiya. Naira dubu biyar ya ba wa yarsu, ya ce ta sha (choculate). Uwar ta yi godiya suka rako shi har bakin motarsa ya ja ya tafi suna daga masa hannu.
Yana tafe a kan titi yana tunani, sanyin A.Cn motarshi na ratsa kasusuwa da bargonsa. Allah ya dube shi ya kusa yanke masa wahala insha Allahu. Zai cika wa Hafsat alkawurrurukan da ya daukar mata a kan lokaci, zai ci gaba da manne wa Sagir tare da bincikarsa har ya tabbatar da zarginsa, amma ba zai hada su da Hafsat ba in har ya zamanto da gaske sune yan uwanta, sai waadin aurensu ya cika.
Don haka ko da ya shigo ta dade da yin bacci. Bai damu da ya neme ta ba ya wuce dakinsa don ya san yau ba ta da damuwa tunda ta yi magana da Mammanta, hankalinta ya kwanta.







SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI
07030137870

*Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama*

Barrister Abdulazeez Dakata ya koma da bayansa ya jingina a jikin kujerar da yake zaune. Kewar Muazatu ta sauko masa, yau kwana uku ba su yi magana ba, ya san kuma bai isa ya kira ta a wannan lokacin ba (as a law-school student). Fassara reactions din Suhaana yake so ya yi, wadanda ta yi yau a gabansa ya gane inda ta sa gaba, ya kasa. Idan haushinsa ta ke ji me ya yi mata? Da ma can ya yi mata alkawarin samun kulawa irin ta maaurata ne da yanzu ya saba alkawari ya bata mata rai? Ya yi zaton ya fada mata kowa zai yi zaman kansa ne ba tare da shiga rayuwar dan uwansa ba?
In ta manta ne zai iya sake zaunar da ita ya sake yi mata rehearsal na rayuwar da za su yi har zuwa waadin auren. Idan bukata gare ta na wani abu, ko kayan abinci ta bude baki ta ce babu kaza mana, shi yake hana ayi zalinci balle shi a kan-karan-kansa ya zalunci na kasa da shi. Ya ci gaba da lalubawa cikin kwakwalwarsa yana nemo ta inda ya kuskure mata. Wata zuciyar ta ce, Kicin... waya... audugar mata...!!!
Kansa ya sara, wadannan ma bukatu ne masu muhimmanci a wajen mace tunda ya san ba zai iya bukatar da ta fi kowacce din ba. Mikewa ya yi ya nufi kicin yana dube-dube, abubuwa da yawa irin su dankali, albasa, doya, kayan miya duk babu. Ya bude freezer da sauri ya mayar ya rufe. Babu komai! Ya bude firji nan ma babu komai na kayan girki, irinsu (Veggies), babu lemuka, babu ruwan sha komai na kayan masarufin gida babu a kicin din. Ya so ya fahimci hakan tun da jimawa abubuwan da ke kansa suka mantar dashi. To don me ba za ta bude baki ta gaya masa ba? Ko bata da baki ne?
Zuciya mai gaskiya da adalci a tsakiyar kirjinsa ta ce da shi.
A ina ta ganka? In ka dawo ba ka nemanta, in za ka fita ba ka gaya mata. Kowanne irin aure akwai bincikar lafiyar iyali a cikinsa, banda naka.
Kikkifta ido ya shiga yi, irin na guilty conscience, ya fito daga kicin din. Ya sa a ransa zai dinga bincikar lafiyarta ko da bayan kwana dai-daya ne.
Dakinsa ya shige ya yi wanka, ya yi sallar laasar ya sanya kananan kaya marassa nauyi ya dauki makullin motarsa ya fice.
Kasuwa da supermarkets ya shiga, duk abin da ya kamata maigida ya ajiye a gidansa ya sayo, wanda zai jima bai kare ba. Hatta pad katon guda ya saya. Waya ce dai har yanzu zuciyarsa ta ki amince masa da ya sai mata a kan dalilai masu dama. Ya juyo kan motarsa ya nufo gida, booth dinsa da kujerar bayansa shake taf da kaya.
Danfulani ya sa ya kwaso kayan ya shiga da su kicin ya tsaya yana nuna masa inda zai adana kowanne.

******
Sanda Hafsat ta dauki computer din Abdulazeez ta shiga daki tsakiyar gadonta ta ajiye ta, tana cike da doki ta nemo takardun karatunta cikin lockers din da ta adana wasu muhimman takardunta da littattafai na makarantarsu ta (St. John Berchamans College). Lokacin da Mammahta hadasu cikin kayanta don ta san watarana za ta bukace su.
A dokance ta ke komai, amma me? Tana kunna system din fuskar wata kyakkyawar mace ne a home-screen din tana kwance a kan hannayenta tana sakin wani irin tattausan murmushi. An ce ko ba SO aure daban yake, Allah (Subhanahu wataala) shi kadai ya san iyakacin karfin izzarSa a cikinsa. Ji ta yi ranta ya wani irin jagule, zuciyarta ta matse, idanunta sun rufe da kansu. Ko bai gaya mata ba wannan ce Muazatu kenan. Wadda Abdulazeez ya yarda ya saba wa iyayensa a kanta, ya jefa Mammah cikin dawwamammen bakin ciki da bacin rai a kanta. Ta ji ta tsani Muazatu, wata irin tsana da ba ta taba yi wa dan-Adam dan uwanta ba. Bacin ran da ya sanya ta kasa yin abin da ta ke dokance da yi, zuciyarta ta yi duhu matsananci. Kawai sai ta kashe komai ta ture gefe ta koma ta kwanta, ta lumshe idanunta.
Sai da suka gama kimtsa komai ya sallami Danfulani, ya zuba ruwa a karamar tukunya ya dora a gass ya kunna. Nan da nan ya yi zafi, ya dauko ledar cous-cous cikin katon dinsa ya farke ya juye rabi. Ya kashe gass din. Ya kwashe gabadaya a (food-warmer) ya diba a plate. Miyar da ransa ya biya da ita tun dazu ya diba ya zuba a kai ya sanya mata sauran a firji yadda ya ganta, ya ja gefe kan karamin dining din cikin kitchen din ya ci ya koshi.
Ya kora da ruwa mai sanyi ya fito ya yi dakinsa.
Karo ya ci da katon din (sanitary pad) da macleans din (beverly hills formula) da ya saya mata a falo har da shampoo din (pert-plus) a cikin katuwar leda don haka ya dawo da baya ya dauka ya fasa shiga nasa dakin ya nufi nata. Daga kwanciyar da ta yi barci ya dauke ta, ga ciwon kai. Ya yi sallama har sau uku bai ji ta amsa ba, ya yi niyyar ajiyewa a nan bakin kofa ya tafi sai ya tuna da systemdinsa, kuma zai yi amfani da ita yanzun.
Babu tunanin komai a ransa ya murda kofar dakin ya shiga don a tsammaninsa ma ko tana toilet ne. Barci ta ke yi, ta saki jikinta sosai tana bacci bilhaqqi. Gashin kanta ya wargaje a kan filo bakikirin da shi mai sulbi da sheki, amma tsayinsa bai wuce dokin wuyanta ba. Abin da bai taba gani a matan da ya taba sani ba sai na kanti, musamman Muazatu kullum cikin adon gashin kanti ta ke shi ya sa ya fahimci ba ta da gashin ne, kuma ba ta son a gane. Ga wata irin tattausar fata mai hasken da babu surki da mayukan kanti (natural), bakinta jazur dan mitsitsi gwanin ban shaawa. Gashin idonta mai tsayi ya bi fatar idon ya kwanta a kan matsakaitan idanunta.
Doguwar riga ce a jikinta mara hannu irin ta robar nan ta bi fatar jikinta ta kwanta a koina, kalarta (orange). Kirjinta bai cika sosai ba, amma cikar kugunta ya nuna Allah ya ajiye mace nan da wani dan lokaci. Bai san tsayin mintunan da ya kwashe a tsaye yana kare mata kallo ba har sai da ta motsa ta juya, ta ji kamar inuwar mutum a kanta. Da sauri ta bude idanunta da suka sauya kala saboda bacci ta sauke su a kan Abdulazeez Dakata, wanda ya yi hanzarin sunkuyawa zai dauki system dinsa. Nata hannun ta kai ta dafe system din. Wani gefen yake kallo bai yarda ya juyo ba balle ta ga kwayan idanunsa.
Zan dauki laptop din ne.
Ban yi ba. Ta fada da murya irin ta wanda ya tashi daga barci.
Tuni ya manta da komai, ya juyo ya dube ta da mamaki.
Ba ki yi ba? Amma na gaya miki ki hanzarta ko? Za su rufe kuma ni ma ina amfani da shi.
Tura baki ta yi gaba ta kyabe shi abin dariya.
Na kunna zan yi, hoton yammata ya hana ni ganin icons din.
Ta sakar masa abarsa ta shiga tattare takardunta da suka watse a kan gadon.
Kasa dauka ya yi, mamaki kamar zai kashe shi. Shi yarinyar nan ta ke kyabewa baki? Ya girgiza kai ya dauki abarsa, bai ga laifin kowa ba sai kanshi, shi ya bada kafa har ta soma raina shi. Sanda ba ta ganinsa ta isa ta cuno masa baki ne har ta ce ya zuba yammata a computer? Kwafa ya yi wadda ta zame masa alada in abu ya ba shi haushi. Yanzu haka hoton Muazatu ta gani shi ne za ta yi masa sharri wai yammata. Kamar irin ya zuba hotunan mata kala-kala din nan.
Har ya kai bakin kofa ya rasa abin da ya saukar da haushin da ta ba shi, sai ya dakata ya juyo ya mika mata hannun damansa na hagun na rike da laptop.
Ba ni takardun ni in yi miki.
Ba musu ta tattara ta mika masa, idanunta na kallon taga. Dawowa ya yi ya amsa, ya fice yana murmushi.
Aladar maza ne jin dadi in matansu na gida sun nuna suna kishinsu ko me? Ita din yarinya ce karama da ya tabbata ba ta san mene ne so ba, amma ta samu zuciyarta da kishinsa.
Bai san me ya sa hakan ya darsa abin da ya ji a zuciyarsa ba. Bayan ya gama cike mata takardun cike da mamakin hazakarta a dukkan makarantun da ta yi a Jeddah da Brussels ya yi submitting sai ya dauko tangamemen hoton Muazatu da ke dakinsa ya dawo da shi falo ya kafa. Kana shigowa falon da shi za ka fara tozali.
Ba ita ta fito daga daki ba, sai da yunwar cikinta ta hana ta jin dadin kwanciyar da ta ke ta yi tunda ta yi sallar ishai. A hankali ta sauko daga gadon ta nufi kitchen. Nan ta tadda plate da cokalin da ya ci abinci da warmer a kan dining. Da sauri ta bude inda ta tadda farin cous-cous, a plate din da ya ci ta zuba, ba tareda ta tsaya wankewa ba saboda yunwa, ta bude firji ta zuba miya ko dumamawa ba ta tsaya yi ba ta zauna ta hau zubi.
Sai da ta yi kat! Ta yi gyatsa ta yi hamdala ta sha ruwa sosai, ta wanke kayan da suka bata, sannan ta bar kicin din.
Ba ta yi tozali da hoton Muazatu ba sai washegari. Sai da ta gwammace da ta sani ba ta yi magana a kai ba. Dauke kai ta yi daga kan hoton ta ci gaba da sabgoginta kamar yadda ta saba. Amma abin ya yi mata ciwo sosai, da ma an ce mutum shi yake bada dama a gane abin da ba ya so. Za kuwa ta ba shi mamaki, ko a fuska ba zai kuma gane ba ta son Muazatu ba.
A daki ta tadda wata katuwar leda da ta lura tun jiya ya ajiye ta, zama ta yi a gefen gado ta jawo ta ta bude. Kunya ce sosai ta kama ta ganin abin da ya sayo mata, sai dai ta ji dadin macleans din sosai, kuma wanda ta ke so ko a Brussels tunda suka dawo ba ta same shi ba (beverlyhills formula). Da kuma Harpic da parazones na wanke toilet sannan air wicks har kala uku. Ta ji dadi sosai a ranta, wannan ya nuna yana daga cikin mutane masu gano laifukansu da kansu su gyara, ba zalunci da rashin adalci ba ne da ta yi inkari da su. Musamman da ta shiga kitchen ta bude firij da freezer sosai ta yi istigfari na kuskuren fahimtar da ta yi masa a farko.
Shi kadai ya san yadda daren jiya ya kasance masa a tarihin rayuwarsa. Wani sabon alamari da ya bakunci gangar jikinsa don ba zai ce da zuciya ba. Ita zuciya so ne a cikinta, gangar jiki kuma ba ka iya katange shi daga abin da ya ga dama. A shekarunsa a duniya talatin kuma cikakken musulmi, mai tsantseni wanda bai taba yin zina ba, yake rokon Allah kullum ya tserar da shi daga aikatata, Ubangiji subhana ya amshi duainsa bai taba aikatawar ba har zuwa yau da aka dauko wata mace da bai so aka mallaka masa da igiyoyin aure.
A tunaninsa yadda ta shigo, haka za ta koma inda ta fito, saboda bai yi tanadin hada rayuwa da ita ba ta kowacce fuska. Sannan a perception dinsa ba ka shaawar mace sai kana sonta. Ya yarda ya amince har zuciyarsa ba ya son Suhaana, babu soyayyarta ko rabin cokali a zuciyarsa, amma ganin da ya yi mata jiya tana bacci ya tunatar da shi cewa shi ma namiji ne, yana bukatar mace for now. Ba sai ana son mace kadai ake shaawarta ba. A cire duk wata maganar gangar jikinsa, so ko rashinsa, (he need a wife). Gane hakan da ya yi bai hana (criticsms) iri-iri zuwa cikin kansa ba... Wannan alamari da gangar jikinsa ke bukata a yanzu baa farawa don a daina... what of idan ta yi ciki? Ya ya rabuwar za ta kasance mai sauki idan da Da a tsakani? Wane uzuri zai kawowa Mammah idan ya mayar mata yarinya da ciki?
Runtse idanunsa ya yi da karfi ya ci gaba da juyi a makeken gadonsa cikin wani hali na kaka-ni-kayi! Wata zuciyarsa ta kawo shawarar ya kai ta asibiti a yi mata (family planning), da gaggawa wata zuciyarta hana ta ce, hakan zalunci ne, babban zalunci!!! Ba ta taba haihuwa ba, idan ka lalata mata mahaifa sannan ka sake ta, Allah ba zai barka ba.
Cikin halin da ya kwana kenan, ya rasa inda zai sa kansa. Duk shawarar da ya kama in ya zurfafa tunani, sai ya ga ba mafita ba ce. Mafita guda biyu ce, ya sa mata ido ta koma a yadda ta zo. Ya auro Muazatu su shimfida rayuwa mai maana da soyayya mara yankewa. Ko kuma ya maida Hafsat cikakkiyar matarsa, amma babu rabuwa, kuma babu Muazatu... sosai yake girgiza kai inresentment..... zan iya jure komi in dai zan same ki Muazatu!!! Ya fada a fili cikin rashin sanin abin yi, da ciwon mara mai tsanani ya kwana.
Bai taba ganin dare mai tsayin na yau ba a kafatanin rayuwarsa. Idan haka sauran watannin da suka rage musu za su kare, ashe ba zai kai su da sauran numfashi ba.
Mataki biyu Abdulazeez ya dauka don kare auren kwangilarsa lafiya ba tare da ya kara fadawa halin da ya samu kansa jiya ba. Na farko ya daina shiga dakin Hafsat, in ganin lafiyar tata ya zama dole, zai dinga jiranta a falo. Mataki na biyu, zai sai mata waya ya dinga kiranta yana jin lafiyar tata don rage kusanci a tsakaninsu. Zai ci gaba da kin dawowa gida sai ta kure. Rashin Muazatu ma ya taimaka wajen samun sararinsa da har wata mace za ta yi kokarin kutsowa cikin rayuwarsa. Muazatu ba ta barinsa haka nan ba sa tare, sai in

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login