Showing 135001 words to 138000 words out of 168255 words
ko daya. Ban da zafin zuciya da azabtar da kwakwalwa ba abin da suke sanya mata. Agogon hannunta na bakar fata samfurinpolo ta duba sai ta ga saura mintuna talatin a shiga paper.
Wani irin kuzari ya shige ta da taimakon Allah ta soma fahimtar bugaggen rubutun takardar da wanda ta yi jotting da hannunta. Kafin karfe takwas ta cika ta samu abin da ta samu da yake shes born gifted. Sau uku in ta bi topic kawai komai yawansa ya zauna mata.
Sai takwas ta tattara ta fito daga dakin karatun. A kofar lecture hall ta hango Rabia Sada, daga nesa suka daga wa juna hannu, sannan kowacce ta shige.
Usman bai zo daukarta ba sai karfe goma sha biyu na rana. Daga airport suka zarto bayan sun ga tashin Abdulazeez. Abin mamaki ta gansu (full house) duk a cikin motar. Motar da Daddy ya fi ji da ita duk cikin motocinsa. Wata ash-colour (Hyundai 2018 model) mai cin mutum takwas. Mami ba ta kara tsinkewa da lamarin Hafsat Dakata ba sai yau. Daddy ne a gaba, sai Ismael direba. A kujerun baya Usman ne da Mammah. Tare da Rabia suka iso jikin motar ta gaida su Mammah, ta amsa da faraa haka Daddy ya sa mata albarka.
Ta ce, Mommah ita ce ta yi covering dina duk abubuwan da suka wuce ni lokacin da na dawo daga Jimeta.
Madallah-madallah Mami Sada, Allah ya saka da khairan.
Daga nan suka yi sallama, sun ce ta zo su sauke ta, ta ce mijinta yana hanya, Mammah ta ce a ina suke zaune? Ta ce a Kubwa.
Insha Allah watarana Hafsat za ta zo gidanki, Allah ya yi albarka.
Sosai Maami ta ji dadi, a yadda ta gansu high class haka ba ta zaci za su yi wannan saukin kan ba. Daga ganin Baban nasu ba karamin mutum ba ne. Ta fadi a zuciyarta.
Suna tafe a hanya Daddy ke tambayarta ya jarrabawa? In ce ko ta rubutata da kyau? Murmushi ta yi, wannan jarrabawa ai sai taimakon Allah, in ta samo C she deserves a medal! Mammah ke gaya mata Haleem na zuwa gobe. A ranta ta ce, Wani na zuwa wani na tafiya, wanda Allah ya baiwa yaya da yawa nagartattu ya gama masa komai a rayuwa. Ko ba komai ta ji dadin albishir din zuwan Haleem din. Ta tabbata zai debe mata kewa, abokin kokawa, abokin wasan tseren keke, abokin kowacce dabdalar kuruciya.
Washegari Haleem Dakata ya iso, har da ita aka je filin jirgin saman Abuja dauko shi. Ya kara tsayi sosai, sai dai yaan nan da lange-langen jikinsa. A da tana ganin Usman ya fi kowa kama da Abdulazeez, ashe akwai wanda ya dame shi ya shanye cikin yayan gidan. Wannan har tsayuwarsa har tafiyarsa, har murmushinsa Abdulazeez Dakata ne. Yana saukowa daga jirgi ya cimmasu, babu Daddy tare da su yana office, su Ismael ya hau rungumewa, ya rungume Mammah har da kwanciya a kafadunta, ita ce ta ji kunya ta ture shi.
Ya ce, Mammah ki bar ni in ji duminki, wa ya yi dadewa irin tawa ba tare da ke ba?
Ta ce masa, Ka girma. You are no more a child now. You are Arch. HaleemDakata.
Lumshe ido ya yi, sannan ya iso ga Hafsat, Addar Mammah, an kara tsufa, kin haihu?
Harararsa ta yi, ta ce.Da na san abin da za ka yi min kenan da ban zo tarenka ba.
Yi hakuri, kada ku kai ni kotu, whereis he?
“I dont know!”. Ta sha kunu sosai ta zumburo masa baki. Dariya ya yi, ya ce, Mammah ina mijinta?
“In the U.S. Ta fada a gajarce, sannan suka rankaya suka nufi mota. Sai hira yake saki kamar rariya.
Anyi girke-girke na musamman don tarbar Haleem. A raayin Hajiya maryam ba ta da son yan aiki barkatai su cika mata gida. Tun tana amarya yar aiki daya ta ke dauka a cikin gida, sai maza na waje don kula da harabar gida da aike,guest house da sauransu. Sai ko maigadi, hatta wanki da guga dry-cleaning suke kaiwa duk don kada ta cika gida da hadimai. Tana da kwazo, juriya da himmar hidimtawa iyalinta. Da wuya a yi mata girkin mijinta da yayanta sai bisa lalurori irin wanda dan adamya gada, kamar rashin lafiya ko tafiya.
A tasowar Hafsat-Suhaanah sai suka hada hannu musamman da suka dawo Nigeria inda Hafsat din bata zuwa makaranta. Ayyukan Baba Azumi sun fi karfi ga wanke-wanke da share-share, goge-goge da wankin bayan gida. Sai sauran hidimar kicin. A yanzu Azumi shekaru sun tura karfinta ya ragu sosai, tana so ta samu lokaci ta gaya mata ta samo mata wata cikin iyalinta mai kuruciya ba don ta sallame ta ba, sai don yanzu abubuwa da yawa nauyin shekaru ba ya barinta ta yi mata su yadda ya kamata. So throughout ranar saboda zuwan Haleem ta zama busy ba ta samu lokacin zama ita kadai ba balle tunani ya aure ta, kuma ba ta da paper, inda duk ta gifta don kawowa Haleem abin da yake bukata sai ya tsokane ta, kiranta yake Senior Aunt. Shi yanzu ya daina kokawa da ita. Shes lookingolder and older saboda aure. Mammah kadai ke tare mata, ta ce su din ma watanni uku ta ba su su fiddo matan aure, ban da shi tunda bai gama ba. Ismael sai ya shafo kai ya ce,
Mammah mu ai mun dade da wuce wurin. Na gaya miki kullum zance nake zuwa a Apo gidan su Wasila. Ke kawai muke jira ki ce kule mu ce casss.
Usman sai ya yi tsaki, ya ce, Kai wallahi ban ga me ka gani a Wasilar nan ba, yarinya baka kirin mai kirar samudawa? Ni Mammah ai irin auren Yaya Azeez za ki min, ki je Kano cikin yaran nan ki dubo min kawai.
Mammah ta dinga shi masa albarka. Ismael ba ta hana shi ba, amma har ranta ba ta son auren bariki, balle irin wadda Ismael ya kallafawa rai, ba ta zaton za a samu yadda ake so daga gare su a gidan aure saboda budadden ido da gata da yayi musu yawa. Sannan su zo su janye dan daga jikin uwarsa da yan uwansa. Ta sha wahala a kan soyayyar Abdulazeez da Muazatu, ba ta fatan a sake maimaitawa.
Da daddare bayan sun yi dinner, Haleem ya ce da Suhaana yana son kunun gyada, Mammah ta ce Azumi ta yi masa ya ce shi sam na Suhaanah yake so ba na tsohuwa ba, ko ita Mammah da kanta ta yi masa. Ta ce ita ta gaji da tsirfarsa tunda ya zo bai barsu sun huta ba.
Hafsat ta ce, Mommah, bari in yi masa mana? Bakonka Annabinka.
Ta mike ta shiga kitchen.
Tana cikin aikinta ta jiyo ihun Haleem cikin murna yana fada wa Mammah Yaya Azeez na kira, a sailin wayar Mamman ce a hannunsa yana daukar lambobin yan uwa da abokan arziki da ba ya da su don ya kirasu ya gaishesu, kawai yaga kiran lambobin U.S. Hafsat na jin yadda rigima ta kaure a kan wanda zai fara magana da shi. Daga karshe dole sai a handsfree aka saka kiran suka taru har Mammah. Kafin ya ba wa daya amsa daya ya jefo tasa tambayar. Duk dai a kan yadda ya sauka ne da yadda ya tadda wajen, how much suka yi kewarsa da sauransu.
Runtse idanunta ta yi tana jin wani irin fili fetal a zuciyarta. It was like babu komai a birnin zuciyar sabida kewa. Kamar an yashe komai da ke cikinta. Birnin zuciyar is just empty! Wanda ya yi gininnika a cikinta ya yi kaura tare da komai da ke cikinta. The feeling is emotional mai ratsa zuciya da ruhi. Ba ta kara gane me ta ke yi a cikin kitchen din ba ko me ya kawo ta. Ta ga dai shigowar Mammah da sauri ta nufi gass da azama ta kashe wuta na tashi daga cikin karamar tukunya. Ta dauke tukunyar da karamin towel ta jefa ta a sink ta kunna mata famfo. Ta dubi Hafsat da ta yi tsuru-tsuru ta ce, Addah are you alright?”
Daga mata kai ta yi, To tunanin me ki ke yi haka na ji shirunki ya yi yawa? Daga dama kunun gyada, I then decided to check on you, sai ganin wuta na yi na tashi daga tukunya, in ce ko lafiya ki ke?
Kai ta daga mata cikin sanyin jiki ta gaza cewa komai. To ta ce me? Your son is drivingme crazy? Ba ni da tunanin komai sai nasa, ya maida ni emotional ya gudu ya bar ni? Da ta tabbatar ba za ta yi magana ba sai ta ce, Ki je daki zan yi masa. At least ta gode Allah Hafsat din ba ta kone ba.
SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI
07030137870
*Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama*
Ba ta da bakin musu ita ma ta fi son ta gusa daga gaban nata, don ta santa kamar mai gani har hanji ta ke a kan dukkan alamuransu. Ba ta sani ba in dai Mammah ce an riga an yi walkiya ta ganta.
Karfe goma na dare ta gama komai na shirin kwanciya, tana so ta tashi karfe ukku daidai na dare don mika kukanta ga Sarki Allah, ba ta da wani buri yanzu a rayuwa bayan shi, bayan neman sauki cikin alamarinsa, bayan neman soyayyarsa da kuma samun tasa soyayyar. Ta sani ba abin da ya fi karfin Rabbi, Shi mai kawo sauki ne cikin kowannen alamari muddin ka amince zai ba ka dukkan abin da ka roka yanzu ko anjima, ko ya jinkirta maka zuwa lokacin da yake ganin ya fi dacewa da kai. Tana neman sauki cikin soyayyar da ta yiscattering(yin dai-dai) da ruhinta, ta yi mata katutu a zuci, ta ke addabarta a kirji, ta ke dawainiya da duk fitar numfashinta.Ta ke neman maida ita wata tababbiya-tababbiya-mai-hankali-mai-hankali. Abdulazeez didnt deserve all these, zuciyar da ta damu da kai ta kuma san kana yi ita ta cancanci a yi wa irin wannan mahaukacin son don za ta karbi response in return.
Wanda zai sanyaya ta tasan ba aikin kawai ta ke yi ba, amma banda ta Yaya Azeez din da ba shi da damuwa a kan komai nata. Ba a kanta kawai ba, it seems like komai na duniya bai fiya damunsa ba ban da lauyancinsa, da tunanin hanyar da zai bi ya kara gogewa da kwarewa a cikinsa, ta hanyar karbar cases na marassa galihu masu tsauri da ko a manyan lauyoyin gwamnati ba kowa ke yarda ya karba ba, musamman idan suka lura client din babu mamora.
Tunanin da ta ke yi kenan ta ji an murdo kofarta an shigo. Daga kan filo ta dago ta dubi mai shigowar, Mammah ce.
Waya ce a hannunta, tana shigowa ta iso har inda ta ke. Wayar ta mika mata, Ungo wayarki, Daddy ya dawo miki da ita. A sha soyayya lafiya.
Zuciyar Hafsat ce ta yi wani tsalle ta fita daga kirjinta tayi shawagi sannan ta dawo. Kafin ta gama farfadowa Hajiya Maryam ta yi ficewarta. Wayarta ta kalla da dumbin shauki. Wani farin ciki ya rufe ta. Ba ta yi zaton da charge a ciki ba amma tana kunnawa ta ga Mammah ta shake mata ita da lantarki. Da sauri ta duba kudi, naira dubu goma cas! Sweet Mommah. Ta fada a fili. Abbanta ta soma kira.
“Ghaaji, yau ke ce a waya?
Wani dadi mara misaltuwa ya ratsa zuciyarta, wato soyayyar ma kala-kala ce, kuma ta iyaye daban ta ke. Ina ma! Ina ma!! Ina ma ta rayu da wannan Habiban? Ina ma Habiban tana tare da Abba? A hakan ma ta gode Allah da tarin niimomin da ya yi mata. Na bar mata wadannan dimbin masoya zagaye da ita. His blessings upon her are countless, endless, limitless.
Alhamdu lillah!.
Abin da ta furta kenan a fili, kuma Abban ya ji. Shi ma wani abu ya taba zuciyarsa, kusan tunani daya suke yi (Habiba) a dai-dai wannan lokacin. Daga bisani kowanne ya ware suka shiga hira. Suna yin sallama ta kira Daada, daga ita sai Malam Babba, Imamu, Abdurrahman da Yaya Modibbo. Ta yi musu ya suka je gida, ta ji lafiyar kowannensu. Sannan ta kira Kawunta Sagir shima ta gaisheshi. Cikinsu babu wanda bai nuna yabawarsa da karimci irin na iyayenta kuma surukanta ba. A zuciyarta ta ce. “Sun wuce da tunaninku, ba ku ga komai ba daga zuriar Malam Abdullahi Dakata.
Sai a lokacin ta bar wayar ta huta. Ta kashe fitila, so ta ke ta yi bacci, don kada ta kasa tashi qiyamul-layl da adduaoin ta kamar yadda ta kudurta. Ba ta jima ba bacci barawo ya sace ta.
Uku daidai na sulusin dare alarm din wayar da ta saita ya tada ta. Alwalah ta shiga ta dauro ta fuskanci alkibla. A yau adduoI da dama ta yi, ta yi wa uwarta da ke kabari, ta yi wa Mammah ta fatan gamawa da duniya lafiya, ta yi wa Daddy na yalwatar arziki da lafiya, ta yi wa kanta adduoI masu yawa. Ta yi wa Daada da Malam na nisan kwana da lafiya madauwamiya. Sai dai me? Instead(maimakon) ta yi adduar da ta tashi don ta yi, wato rokon Allah ya rage mata son Abdulazeez, ya sa masa soyayyarta shima, sai ta samu kanta da yi masa addua. In tace addua to tana nufin addua a kan komai; a ciki ta roki Allah Ya kare shi a duk inda ya shiga, Ya shige masa gaba a kan duk abin da ya sa gaba. Ya cika masa burikansa na alkhairi, Ya ba shi dukkan alkhairin rayuwa Ya bashi nisan kwana...... Sannan Ya kare mata shi daga ZINA da sauran ayyukan sabo masu kamanceceniya da ita.
Hannunta a sama ba ta kai ga shafawa ba ta ji wayarta na kira da tune din takbeer da ta saita kiran wayarta da shi. A nutse ta kammala adduarta ta shafa ba tareda damuwa da kiran ba, zuwa lokacin wayar ta katse har sau biyu ta sake ci gaba da ruri. Sai da ta koma gado ta kwanta, sannan ta jawo ta. Lambobi ne rututu da suka fara da (+917) da ba ta shaida code din ko ina ne ba. Da farko ta yanke shawarar kin dagawa, amma ganin ba a da niyyar fasa kiran sai ta daure ta yi sliding answer button’ din.
Assalamu alaikum.
Ta fada a nitse. Jin mai kiran ba shi da niyyar yin magana. Cike take da mamakin wanene zai kirata da sulusin dare irin haka? Sai da ya ja fasali har tana tunanin kashe wayarta don ta fara tsorata da yi wa kanta fadan me ya kai ta amsawa ma, kira cikin talatainin dare da international number. Sai ji ta yi murya a ciki, kamar wanda aka yiwa dole yayi magana, ya ce.
Ba dole ba ne na amsa sallamarki a fili ba ai, tunda na amsa cikin raina.
Wani numfashi mai tsayi ta zuqa ta furzar daga huhunta. Mutum na karshe da ba ta kawo zai kara bi ta kanta ba, she feels like smilingamma ta hana kanta, ita ce mace ba shi ba, ita ya kamata ta yi jan ajin da yake yi mata. Amma anya za ta iya?
In ma ba ki iya ba ki koya, Abdulazeez sai an bi hankali. Ja zarenki a sannuAddar Mommanta!Bi shi a yadda yazo.
Zuciya mafi hankali da nutsuwa ta shawartar. Don haka sai ta yi shiru, ba ta ga dalilin da za a kira ta ba, kuma ya yi mata kasaita da iko ba.
Kiran wayata ma sai kin ga dama za ki dauka ko? Tunda ke bazaki kira ni ba bayan an gayamin an baki waya. Wannan duk a cikin rashin tausayinki ne da kika kware akai, ko a cikin fannonin rashin so irin naki?
Murmushi ta yiwa kanta mai ciwo, ita Abdulazeez yake yi wa korafin rashin so! To ita wanne za ta yi masa? Ya yi tafiya bai gaya mata ba, bai neme ta ba sai da ta neme shi. Ta je ya yi mata wulakanci, sannan yanzu yana fadin ba ta sonshi, ba ta tausayinshi. Shiru ta kara yi masa wanda ya fi komai fusata shi. Da zai iya da ya kyale ta, amma ina! Ba zai iya nutsuwa ba sai ya ji muryarta ko da kuwa abin da za ta fada mishi din ba mai dadi ba ne.
Ya tabbatar Hafsat bazata ce masa komai ba, kuma bata da niyyar hakan, sannan ya tabbata tana jin sa. Don yana iya jin saukar numfashinta wanda ke fita akai-akai.
“Shi ke nan Hafsah, zan barki ki yi rayuwarki the way you want it (yadda ki ke sonta), amma ki ke sanya wa a ranki akwai wani mutum far away (a nesa) da ya damu da ke da yawa, yake fatan jin ko da kalma guda daga gare ki a yau to keep him companyhar wayewar gari amma ya kasa samu. Wannan mutumin ba wani bane face mijinki Abdulazeez Dakata.Stayblessed.
Ya yi maganar ne da wata murya data nuna rauninsa a yau, ba tareda ya san raunin ya bayyana kansa ba cikin intonation din sa, mai tasirin kashe jiki da gabban kowaccediya mace, balle ga macen aure ga mijin da ta ke matukar so. Macen ma mai rauni irin Hafsat-Suhaanah. Mijin kuma ba kowa bane Abdulazeez din ne data hana idonta bacci saboda shi, saboda ta roki Allah ta samu kwatankwacin wannan soyayyar da wannan kulawar daga gareshi. Kafin ta yi wani yunkuri, ya kashe. Shefeels like calling him back..amma wata zuciyar ta hana. Barshi shima ya ji in rashin kulawar da dadi. Zuciyarta ta ciko ta yi tantsan da farin cikin jin kalamansa, daga wannan emptinessdin da ta ke ji a baya, wani irin nishadi ya lullube ta. Da haka ta samu barci mai nauyi da dadi ya yi awon gaba da ita. Wanda ta dade ba ta yi irinsa ba.
Washegari paper har biyu ta zana (Regional Geography and Rural Geography). Tana fitowa daga dakin jarabawar ta kunna wayarta, sakon sms ne ya fara shigowa. Yau Haleem ne ya zo tafiya da ita. Tana tafe zuwa motar