Showing 117001 words to 120000 words out of 168255 words

Chapter 40 - Auren Kwangila Book 4 Hausa Novel Complete

Takori   

12 Dec 2024

311

Eh, yaudara mana? They blackmailed her! She didnt deserve such a betrayal! Dagakowannensu. Kuka sosai ta soma yi, ta mike ta isa ga closet dinta tana canza kaya, ko dankwali ba ta tsaya dauka ba ta nufi dakin Hajiya Maryam.
Da rabe-rabe a jikin bango ta shiga dakin, guilty conscience na abinda ya faru na dibanta duk da ta san ba laifin ta bane amma ita Mammah ai bata san haka ba, fuskarta fal hawaye ta shiga dakin. A gefen gadonta ta same ta tana waya, kallo daya Mammah ta yi mata ta dauke kanta, ta ci gaba da maganar da ta ke yi. Ta lallaba ta isa ga gefen kafarta ta zauna tana ta share hawaye.
Ta fi minti goma sha biyar tana magana a waya inda ta fahimci da Auta Haleem ne, tana shirya masa zuwa hutu daga Sweden karshen watan nan. Da ta kammala tana ji suka yi sallama, ta ce Love you too Haleem.
Ta ajiye wayar tana shirin mikewa don ta bar mata dakin Hafsat tayi maza ta rike kafarta tana kuka. Don Allah Mammah ki yi hakuri ki saurare ni, ba ni na kira shi ba, bansan sanda ya shigo ba, kawai ganinsa na yi a kaina na zo zan fita ya rufe kofar. Mammah in kin yi fushi da ni ina zan sanya rayuwata in samu irin sanyin da nake samu a tare da ke?
Janye kafafunta ta yi, amma ta koma ta zauna, ta ce. Za ki samu a wurin mijinki,wanda ba kya son bacin ransa, mijin da ya yanke igiyar aurenki ya watsar, ya ce wata mai aji yake so ba ke ba. Yar masu kudi mai zurfin ilimi. You are unbelievable Hafsat! Sau nawa za mu yi wannan maganar? For the first time na fara shakkarki, don kin canza daga Addah ta da na sani, tunda har zaa iya hada baki da ke a yi wasa da hankalina. Naji komai na abin da kuka kulla kada don ban yi miki zancen ba ki dauka ban ji ba.
Karshen tashin hankali Hafsat ta shige shi, kukan ma ta neme shi ta rasa. Ba ta taba zaton alamarin zai yi girma haka a zuciyar Mammah ba, da ko kusa ba ta sanya kanta a ciki ba. Ba ta san sakin wani abu ne special ba, a lokacin tana ganin all a woman wants is knowledge(abinda diya mace ke bukata shine kawai ilmi), kuma Mammah ta hana ta, ta ce AURE shine gaba. Tana so ta ga yan uwanta na jini,tanaso ta ga wanda ya diga jini ya haifeta, Mammah ba ta taba damuwa da hakan ba. Bata so ma ayi mata zancen. Ba ta so ta takura mata da ta nemo mata danginta za ta ga kamar ta raina kulawar da suke bata ne.
Abdulazeez ya zo kamar daga sama ya ce zai yi mata duk wadannan abubuwan cikin sirri, kuma cikin dan lokaci kalilan. All he need in return shi ne ta amince za su rabu bayan shekara daya! Dokinta ga hakan,enthusiasm dinta ga son zuzzurfan ilmi, rashin sanin me auren kansa ya kunsa, da rashin sanin cewa SAKI shi ne babban koma baya ga rayuwar diya mace, da rashin sanin cewa babu mai iko da zuciyarsa sai Ubangijin da ya halitta masa ita, su suka taru suka kai ta ga amincewa ga bukatar Abdulazeez Hamza Atiku,ba wasa da hankalin Hajiya Maryam ba, ko nufin yaudara a gare ta.
Maryam din data rayu shekaru goma sha takwas da doriyaagainst all odds don tserar da rayuwarta tun tana cikin kwalba (incubator).Ta zabi Da mai sunan Da a cikin yayan ta ta aura mata,ba tareda laakari da nata matsayin ba, duk don ta samar da kyakkyawar rayuwa a gareta a shekarun girma bayan wadanda ta samar a shekarun kuruciya.
Hafsat ta ga ba ta da mafita a yau ban da warware wa Mammah komai, wannan Mammah din da ba ta da kamarta, yadda komai ya faru da dalilin amincewarta.

“It happened on 31st september a studyroom da ki ka ce in je mu ganafor the first time...........
Tiryan-tiryan ta gaya mata komai, har irin zaman da suka yi a gidansu a Sun-City. Amma da ta zo inda suka soma having physical contact sai ta ke kaucewa. Ta kare da cewa.
Ban taba sanin yana da kirki ba sai da na zauna da shi, abubuwa da yawa da na girma ina gani a tare da shi, sai na tadda su akasi ga tunanina. Ko a cikin mutane shi na daban ne. Yana da qualities da za a so shi a kansu ba tare da amincewar zuciya ba; he is genius, he is unique.
Ya tabbatar da kasancewarsa mai gaskiya da rikon amana a kan Muazatu. Ya tabbatar shi mai muhimmanta alkawari ne akaina da Muazatu. Duk alkawuran da ya daukar min ya cika min. Sai na ga bari ni ma in taimake shi ya kai ga samun wannan burin nasa guda daya. He used to say;he has only one weakness... shi ne soyayyar Muazatu. Mommah in na ce sai ya ci gaba da zama da ni bayan duk wannan halarcin da ya yi min, shi kada ya auri wadda yake soya samu farin ciki na zamo cikin masu son kansu da yawa. Bayan Annabi SAW yace imanin mu baya cika har sai mun so wa yan uwanmu abinda muke so wa kanmu.
Nima ba da son raina ne aka yi sakin ba,but a iyaka tunaninsa a lokacin (its the only solution), kuma na ji ciwo sosai a zuciyata yadda bazan iya kwatantawa ba Mammah. Ki tambayi Dada I became unconsciousna lokaci mai tsawo lokacin da na tsinci takardarsa cikin jakata. A lokacin ne na gane yanzu ba karatun nake bukata bawhile it is too late, akwai wani abu wanda ya fi shi muhimmanci ga diya mace wanda ni na rasa a halin yanzu..... (Sai bayan ta fadi hakan kuma ta ji kunya sosai, watairin kunyar Mammah da bata taba ji ba tsayin rayuwar ta, ta ga kamar ta ce ne da Mamansa tana sonsa indirectly) bayan ba haka take nufin fada ba.
Mammah ba ta nuna a kage ta ke da son jin karshen bayanin nata ba. Amma jin ta yi shiru ta kasa ci gaba sai ta fahimci kalmomin bakinta sun kare. Kallonta ta ke tana jin tausayinta da jin son ta sosai yana karuwa a ranta. Hafsat din kanta na kasa. Maryam Dakata ta kira sunanta cike da kulawa.
A hankali ta dago amma ta kasa kallon kwayar idanunta, sai yanzu ne ta ankara da irin kalaman da ta ke bulbularwa ba tare da tunanin wa ta ke gaya wa su ba. Ta gama fallasa asirin zuciyarta ba da saninta ba. Ta gaya wa UWA tana cikin soyayyar Danta a fakaice, wannan abin kunya da me ya yi kama??? Kanta ta kara sunkuyarwa tana jin tamkar ta ce da kasar ta tsage ta shige. Mammah ta fahimci halin da ta ke ciki, murmushi ta yi ta ce.
Ni na nutsu na saurare ki, amma ni kin ki saurara ta. Tambaya biyu kawai nake son in yi miki, in ki ka amsa min su genuinely na daina shiga tsakaninki da mijinki kuma a yau dinnan zan tattaraki in maida ke dakinki don na lura kun fi kusa, kun wuce da tunanina.......
Mommah ba haka ba ne, ni wallahi..... Ta fada kamar za ta yi kuka, amma ta kasa karasawa. Mammah ta riga ta gama fahimtar tana son Abdulazeez yanzu, ina za ta kai wannan kunyar?
Addah yau suruka na zame miki? To idan na koma suruka ina za ki nemo uwa? Ke ki ka zauna da ni a lokacin da shi yake nesanta kansa da ni. Ke na sani a matsayin ya ba shi ba. Ban zaci aurenki da shi zai sa ki canza min matsayi ba. Tashi ki je in kin shirya magana da ni a matsayin UWA kya dawo, amma yau suruka ki ke kallona.
Murmushi ta yi har sai da kumatunta suka lotsa ciki sosai. An-ti Ummeeee.... Wato Ke uwata ce.(Yau aka tuno larabcin Jeddah).
Kallonta Hajiya Maryam ta yi a tsanake, ta tabbatar ta samu nutsuwa sosai sannan ta ce. Naji duk bayaninki kuma na fahimce ki. Tambayoyi biyun da zaki amsa min properly sune;How sure are you (ta ya ya ki ka tabbatar) yanzu yana sonki so na haqiqa? How sure are you ya daina son ita waccan din ko ya fasa aurenta acan gaba, idan kika koma gidansa?
Shiru ta yi don ita kanta ba ta sani ba. Abin da ta sanin shi ne zamanta da shi a yadda suke a gidansu ko babu soyayyar ya fiye mata wannan zaman gashin kumar da ake musu a yanzu. She cant get into his mind(bazata iya shiga zuciyarsa ba balle ta gano wadannan amsoshin). Zuciya abin sirri ce. Sai dai abu guda da ta ke da tabbaci shi ne, ba zai taba yi mata karya ba. Karya is out of his vocab bank (vocabulary bank).
Sannan kuma ita zuciyar ai tana canzawa Mammah, kamar yadda komai na duniya ke iya canzawa. Nima ai da ba son nashi nake ba. Lokaci daya na tsinci kaina dumu-dumu a duniyar da in ba shi ba zan iya rayuwa ba. Sannan yana da damarkarin mata biyu ma bayan ni da Muazatu. Mammah ta duba wannan mana ta yi masa uzuri. Sai dai ko giyar wake ta sha ta san itama ba za ta iya yi wa Mammah wannan bayanin ba. Zai bayyana gare ta cewa ta makance a son mijinta, wanda a zahiri hakan ne. Ta yadda bata ji bata kuma hango komai sai na yadda zata koma rayuwa da shi.Saidai fa bazata taba zabar sa akan Mammah ba koda son ne zai yi ajalinta. Gara ta zuba ido ta bar wa Allah alamarinsa, ta bar Mammah ta yi hukuncin da ta ke ganin shi ne daidai. Duk son da ta ke masa ta san bai yi na wanda ita da ta haife shi take masa ba. Idan so cuta ne, to hakuri da biyayyar iyaye maganin komai ne.
Kina iya tashi ki je ki yi wanka mu yi shirin dora lunch. Ranar da ki ka samu amsa ga tambayoyina ki zo ki goya mijinki ku koma gidanku. Kuma ki tabbatar kin nemi wani abu kin ci. Silly girl kawai.
Sum-sum-sum ta fice kanta a kasa. Mammah ba ta bi ta kanta ba, ta fito falon. Abdulazeez ne da Usman, Ismael ya fita. Hira suke amma tana shigowa falon suka yi shiru. Fuska dinke ta wuce su zuwa part din Daddy. Ta same shi yana ta aiki cikin projects din dalibansa na PhD, kasancewar yau ba zai shiga jamia ba.
Tana shigowa ta soma korafi ko gaisawa ba ta bari sun yi ba. Ya kasa fahimtar daya kwakkwara cikin complains din nata. Abu daya ya fahimta; Abdulazeezya bar mata gida! Ya zo ne kawai don ya takura wa Hafsat ya zuge ta ta ki yi mata biyayya. Kansa ya mayar kan abin da yake yi ya ci gaba, amma ya kasa fahimtar komai saboda ta dame shi da korafin ta. Dakatawa ya yi ya cire medicated lensesdinsa, ya dau waya ya kira Abdulazeez ba tareda sanin yana cikin gidan ba, ko mintuna uku bai yi ba ya shigo, wannan karon ya sauya kayan jikinsa da alama wanka yayi a lokacin da itada Hafsat suke heart-to-heart talk dinsu. Shirt ce fara sol long-sleeved mai rubutun Nordstorm da ruwan tokar trouserajikinsa. Ya yi kyau sosai kuruciyarsa ta fito fili. Yana ganin yanayin Mammah ya san kararsa ta kawo. Daddy tun kafin ya zauna ya ce dashi. Me ka yi mata?
Sunkuyar da kansa ya yi ya ce Daddy a sanina babu komai. Na dai kwaso kayana ne kawai na dawo nan, saboda matsalolin da nake fuskanta na zama ni kadai da na abinci da tsabtar gidan kansa. Sanda nake dawowa daga office na gaji, abinci kawai nake bukata kuma babu. Sai dai in kara bata lokaci in yi expressda kaina shi ma kuma wani lokacin gajiya ba ta barina sai dai insha coke in kwanta. In na ce sai na tsaya na biya na saya sallar magriba za ta wuce ni. Ka san kuma mutum da ya saba komai a yi masa, sannan the house is somehow dirtyalways. Ya fada cikin muryar da dole a ji tausayinsa amma banda Hajiya Maryam.
Dr. Hamza ya ce. Ki barshi ya zauna mana? A kanki yake zaune? Ga mari ga tsinka jaka?
Cikin mamakin abin da ya fada ta ce, Haka ma za ka ce? Wace jakar na tsinka masa?
To in dai gidana ne na ce ya zauna, ki gode Allah da ya ba ki shiryayyun yaya a wannan zamanin, wasu da yawa irin damar da ya samu suke nema su tambade. Kai kuma na ba ka wata daya ka kawo min matar aure.Attorney ya bada auren yarsa har katin gayyata ya kawo min duk da ban samu na je ba, tunda ita Hafsat din uwarta tace bata yarda ta koma ba ka barta tabi abinda uwarta ke so. Idan watan nan ya wuce ba ka kawo min mata ba zan je Kano in nemo maka duk wadda na ga dama saboda kai din na dade da gane cewa namamajo ne akan mata, in banda haka ta yaya ga wata an halatta maka a cikin gida da igiyoyin aure na halali,amma hankalinka da soyayyar ka bakidaya suna ga wata a waje, don haka gara in cika maka gida dasu ko ka nutsu dana gidan aure. Ban amince zamanka ya zama zaman shiga sabgar Hafsat a gidannan ba ko ka dinga shigar mata daki, kowa yayi zaman kansa. Is that ok with you two?
Mammah kamar ta goya Daddy yadda ya wanke mata shi tas! Ta ji dadin wannan hukunci har fiye da zaton ta, itata fara fita ranta ya yi wasai daga takaicin da ya cusa mata yau. Dama abin da ya fi ci mata tuwo a kwarya kenan; shiga dakin Hafsat da yake yi. Ban da haka ya yi ta zama a gidan mana ita ina ruwanta?
Bayan fitarta Abdulazeez ji ya yi kamar an sauke masa wani gingimemen dutse daga kansa maimakon wankin babban bargon da akai masa ya bata masa rai. Attorney ya ba da auren yarsa! Whichmeansbai karya alkawari ba! An je nema masa auren kamar yadda ya alkawarta, dissappointment din daga iyayenta ne. Babu kaffara a kansa, babu tunanin ya ci amanar wata halitta da ta ba shi dukkan yarda da aminci.
Karasawa ya yi gefen kafafun mahaifin nasa, wanda ya maida gilashin idonsa ya ci gaba da abin da yake yi alamar ya gama magana da su.
Don Allah Daddy ka taimaka min ta huce, ka taya ni ba ta hakuri, ta yi fushi da ni mai tsanani, na amsa na yi laifi ku dubi girman Allah ku yafe min. Daddy ko gaisuwa ta ba ta amsawa, na janyo mata cuta, Daddy in na mutu yanzu wuta zan tafi babu tantama...
Ta yi min alkhairi na saka mata da butulci. Ban san darajar abinda ta ba ni ba sai da lokaci ya kure mini, kuskuren ya riga ya afku. Ni babu wata mata da zan iya kawowa cikin sati hudu daga nan har gaban abada sai HAFSAH! Ko ba za ta mayar min da ita ba atleast ta furta yafiyarta gare ni in samu sauki a zuciyata....
Na ji. I will talk to her.Abin da tsohon Ambassador Hamzah Atiku ya ce da shi kawai ke nan a matukar gajarce.
Jiki ba kwari ya baro falon nasa ya koma main parlour. A can ya yi kyakkyawan gani, Hafsat ce ta yi wanka ta canza kayan jikinta da wasu riga da skirt yan kanti na calvin klien jajaye da ratsin baki. Ta gyare gashin kanta ta kalmashe shi cikin bound kalar kayan jikinta. Ko ba komai dai anbi umarninsa anyi masa kwalliya. Ta zubo soyayyen chips tubus dashi da saucedin hanta da koda a faranti tana ci da cokali mai yatsu, ga coffeemai zafi a karamin kofi a gefe. Wani abu ya hadiye da ya tokare a makoshinsa ya koma can kujerar karshe ya harde dogayen kafafunsa. Kallonta kawai yake kamar ya samu T.V, ai a cikin sharuddan da aka kafa masa din ba a ce kada ya kalle ta ba.Kuma kallon babu zunubi. Ta yi kamar ba ta san da shi a falon ba, ta ci gaba da cin abincinta a tsanake.

Usman ya ce, Shi mijin ba zaa ba shi ba?
Ta ce, Na karfi ne!.
Ya kama baki. Rashin kunya ne abin?
Ta yi masa shiru. Mikewa ya yi har inda ta ke ya dauke farantin ya kwace kofin ya kai masa. Karba ya yi da murmushi ya ce. Na gode Usman, you are the best. Ya dora a center-table ya soma cin abinsa.
Tashi ta yi cikin fushi ta yi kitchen wajen Mammah. Mommah kin ga Ya Usman ya kwace min abinci ya bashi?
Zuba wani. Kawai ta ce don ba ta son surutu.
Usman ya shigo kitchen din yana fadin, Mammah yarinyar nan ba ta da imani na lura. Ya Azeez tun safe ba abin da ya ci sai ruwan shayi, amma ta shako faranti ta zauna tana cin abinta a gabansa babu ko tayi.
Hajiya Maryam ta juyo ta watsa masa harara, ai ba ta san kan zancen ba. Ta nuna shi da yatsa ta ce Usman, ka kiyaye ni, kada ka shiga hancina don in na tashi fyato ka ba za ka ji dadi ba.
Allah ya ba ku hakuri. Ya ce yana hada hannuwa irin na indiyawa. Hafsat ta yi masa gwalo da ta ga Mammah ta juya. Ya yi mata alamar, za mu gamu ne ya bar kitchen din.
Da rana gabadayansu suka ci abincin rana har Daddy da Abdulazeez a kan tebir. Shi da ita sai satar kallon juna babu ko kwakkwaran motsi daga Hafsat. Daga Mammah har daddy babu mai walwala a fuska. Shi ya fara jin zafin matar tasa ne kan hukuncinta a kan Abdulazeez, ba karamin karya mishi zuciya ya yi ba dazun daurewa kawai ya yi. An ce so-so ne, amma son kai ya fi. Yana son dansa fa, na Hafsat karah ne. Ita kuwa Maryama na wani shi ne nata kullum nata ba nata ba ne, ba tun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login