Showing 111001 words to 114000 words out of 168255 words
ba don amincewa da kalaman Daddy ba sai don ta samu damar yin tunanin matakin da za ta dauka a kansugobe.
Washegarin ranar Uncle Abdulkarim ya tafi Lagos neman auren Muazatu Rufai wa AbdulazeezDakata. Hafsat kuwa tun fitar sadaga dakinta ta kashe wayarsa da ya bata. Ba don ba ta son yin magana da shi ba, sai don tana ganin yin hakan zai zamo tamkar hainci da cin amanaga Daddy.
******
Labarin da tsohon minista Abdulkarim Dakata ya zo wa da dan sa tsohon Ambassador Hamza Atikuda mai dakinsa bai musu dadi ba, ya karya duk wani budgetdinsu na gallazawa Abdulazeez da suka yi niyyar yi da auren masoyiyarsa da a yanzu suka gama fahimtar baya muradi. Attorney General Habib Rufai, ya ce Abdulazeez ya yi hakuri ya gaji da rashin tabbas dinsa da rashin tsayayyar magana daga shi har iyayensa, ya bada auren yarsa ga Barrister Muntada Akilu Lawal sun gama komai, jira suke a sallame ta daga asibiti a daura aure.
Duk da haka Daddy bai yi niyyar gaya masa ba, ya kudire a ransa sai ya gwada shi again a kan Muazatu don tabbatar da zancenta ya mutu a zuciyarsa ko kuwa tana kasa tana dabo ne???
Da safe Hafsat ta shiga gaida Mammah a dakinta kamar yadda ta saba bayan fitar Daddy office. Ciki-ciki ta amsa mata, ko darajar kallo bata samu ba. Hafsat ba ta lura ba, don dama cikin kwanakin Mamman nasu ba fiye walwala ta yi ba. Ta juya zuwa closet din Mammah din tana gyara mata, kayan wankinta da aka kawo daga wanki da guga ta ke shirya kowanne a bangarensa. Maryam Dakata yar kwalisa ce ta karshe. Bangaren Vlisco daban, na laces, na atamfofi, na material, na shadda kowanne da inda Hafsah ke masa matsugunni, ba za ka lalace da kallo ba sai ka je shoe rackdinta, ga bags ahangerdesign daban - daban. Ba ta san cewa daga bayanta Mammah binta ta ke da kallo ba. Hatta tafiyarta sai da ta yi observing (duba ta filla-filla) ba ta ga komai ya sauya ba, kai! Mammah kenan!Wata ajiyar zuciya ta saki wadda ta shiga kunnen Hafsah, ta kuwa juyo ta dube ta tayi maza ta daure fuska. Tana gamawa ta fito daga closet din za ta koma daki ta kafa sanaar tata (tunanin Abdulazeez) Mammah ta kira sunanta.
Dawowa ta yi ta zauna a kasan kafafunta, don ta lura magana ce a bakin Mammah. A nitse Maryam Dakata ta dubeta ta soma magana.
Sabida miji ya sake ki kin daina karatu ko? Za ki yi asarar komai ba auren ba future? Saboda shi ne autan maza wanda aka ce daga kanshi maza sun kare an daina haihuwarsu?
Nutsar da kanta kasa ta yi sosai tana jin faduwar gaba. Mammah ta ci gaba. To bude kunnuwanki da kyau ki jini. Sakin aure ba kanki farau ba, ba shi ne karshen rayuwar diya mace ba! It just means wannan mijin ba ya yi da ita, watanta wadda ta fi ta wani abuyake so. Me ya kamata ita wannan mace ta yi in ita mai hankali ce?
Tuni idanuwanta suka kawo ruwa, a bisa dalilin da ba ta tantance shi ba.
Da ke nake magaan Addah, idan macen da miji ya ce ba ya yi da ita, watanta yake so mai zurfin ilmi, ta matsa ta ba shi wuri ya kawo wadda tayi daidai da raayin sa, in ita mai hankali ce da sanin ciwon kaime ya kamata ta yi?
A wannan gabar,wannan matakin, ta riga ta gama fahimtar abin da Mammanta ke ankarar da ita. Sai dai zuciyarta da soyayya ta riga ta gama illatawa ta lullube ruf,har babu masaka tsinke jin zafin kalaman Mammah ta ke a kan Dan ta, wanda ita ta tsugunna ta haifi abintaballe tace bata kaunarsa, amma cikin kalamanta kaf babu uzuri ko sanayyaa gareshi ko daya, indirectly she want her to do away with him kawai don yayi kuskuren da babu wanda yake sama da aikata shi a matsayin mu na yan adam,don haka ta kama mamakinta a can karkashin zuciyarta; tambayar kanta take ita din (Maryam Dakata) shin wace irin uwa ce? Ashe gaskiyar Abdulazeez da ya ce ba shi da kowa yanzu a gidan nan daga ita Hafsat sai Allah! Sun dauka da zafi har fiye da ita da aka yi wa sakin. Shin Mammah na tunanin akwai wata halitta da za ta aje a doron duniya daga jinin jikinta da za ta yi mata laifin da za ta kasa yafewa?
Ran Hajiya Maryam in yayi dubu to ya kai kololuwar baci da reaction din Hafsat, mai nuna babu jin zafin Abdulazeez a ranta, bata ji zafin komai da Abdulazeez yayi gareta ba. Kada dai tana can wajen miji tana shan AC ta yi sakacin da dare daya kacal Abdulazeez ya juye mata kwanya? Da salon yaudararsa dacontracts din da ya kware akai? Tsawa ta daka mata, Answer me I said...!. (Nace ki bani amsa).
Hafsat ta soma kuka, cikin rishin kukan ta ce, She has to forget him and move forward... (sai ta manta da shi ta fuskanci gaba),
Ta gyada kai cikin gamsuwa da abin da ta furta da bakinta, sannan ta nunata da dan yatsa(abinda bata taba yi ba).
Kin fadi amsa daidai da abin da ya kamace ki. Forget him... move forward...thinkbig for your future!Ki je ki karkade takardunki gobe ki koma makaranta. Ni da kaina zan dinga kai ki ina dauko ki ba direba ba.
Hafsat ta gyada kai. Umartarta ta yi da ta tashi ta ba ta wuri, mai nuna har yanzu ranta a bace yake. Sum-sum-sum ta mike kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki, har ta kai bakin kofa ta tsinto muryar Mammah a tsakiyar kanta. Ina wayar da ya baki? Bani ita nan!
Saura kadan Hafsat ta saki fitsari a wando don kaduwa da mamaki hadi da tsoro. Amma ba ta ce komai ba, a sanyaye ta murda kofar ta fita, ba ta yi mintuna biyu ba ta dawo da galleliyar wayar Abdulazeez ta russuna ta mika mata. Mammah ta jinjina kai sannan ta karba ta yi jifa da wayar can karshen gadonta.
Ko da Hafsat ta koma daki toilet ta shige ta kulle kanta, guilty conscienceya bi ya dabaibaye ta, ta shiga tunanin da wane ido zata kara kallon idanun Mammah, ga kuma son mijin da tausayinsawanda shi yafi komai yawa a daidai wannan lokacin. Da ta san Mammah za ta kwace wayar da jiya ba ta kashe ta ba, da ta barta sun yi sallama da juna, da ta gaya masa how much she love and missed him, da ta gaya masa ta yafe masa baki da baki. Da ta yi masa goodnight kiss din da ya nema ta ki yi masa ta kore shi dole.Yanzu kam ta san da wuya su kara kadaicewa nan kusa tunda Mammah ta gano me ya faru jiya. Kuka ta dinga yi wanda ba ya mata wahala. Ita yanzu wane karatu za ta iya? Ta dade da tsanar karatun. Babu komai a zuciya da kwakwalwarta sai Abdulazeez Hamzah Atiku!!!
Aiki yake a office Barrister Surayyah ta shigo, ransa ya yi mummunan baci, ta zo ne kawai ta kara masa damuwa kan wacce yake ciki. Da surutanta na banza na rashin kamun kai. Ya tattare girar sama da ta kasa ya maida fuskar kamar hadarin gabas. Wani irin kwarjini ya yi mata, hakan yasa ta hau inda-inda na abin da ya kawo ta, wai photocopy za ta yi a ofishinsa nasu injin ya samu matsala. Nuni kawai ya yi mata da machine din ya mike ya soma tattare takardunsa da systemdinsa ya cire wayarsa daga caji ya bar mata ofishin. Ya bawa masinjansa umarnin in ta fito ya rufe masa ofishin.
Ba tun yau ba hakan ta sha faruwa, Barrister Surayyah Saidu ya kwana da sanin sonsa ta ke yi a matsayinta na matar aure kuma. Rashin samun fuska ya hana ta fitowa gaba da gaba ta gaya masa. Tafe yake a kan hanyar Asokoro yana tunanin abin yana Allah wadai da wannan rikitaccen zamani da Allah ya kawo mu. Saboda takurar Surayya da ire-irenta cikin Abuja ya soma tunanin komawa karo karatunsa (L.LM) ya fara gajiya da Federal High Court. Bai samu wannan matsalar a Ibadan ba zamanin karatunsa. Bari dai ya gama da kalubalen da ke fuskantarsa yanzu. He wanted to move forward...
Har ya iso gidansu tunani yake yi, tunanin abin da ya sa Hafsat kin yarda ta yi amfani da wayar da ya bata jiya. Wane irin lallashi ko ban baki ko ban hakuri kuma zai yi mata bayan wanda ya kwashe awanni biyar cur yana yi mata jiya ta fahimce shi? Ita ce kadai hope dinsa a gidan nan.
Kusan tare suka shigo gidan shi da Daddy da ke kwance a bayan mota hyundai Salisu ya dawo da shi daga ofis. Shi ya karba ma Daddyn tarkacen hannunshi, ya bude sliding doorta shiga falon farko, Ismael ya fara hanga yana kallon tashar Sunnah T.V, babu Mammah da Hafsat suna kitchen suna aikin abincin dare. Ismael ya yi musu sannu da zuwa suka wuce shi zuwa sassan Daddy.
Har gaban Daddy ya isa ya mika mishi kayan, sannan ya samu waje ya zauna ya tankwashe kafafunsa yadda ya saba in yana gabansu cikin tsantsan ladabi. Daddy ya ajiye hularsa ya ce, Yanzu da ma zan kira ka, kakanka ya dawo daga Lagos.
Wani irin bugawa kirjinsa ya yi ya sunkuyar da kansa kasa. Daidai lokacin da Mammah ta shigo dauke da Jug da cups da bowldata shako da dambun naman kaza ta jero a kan karamin tray zuwa gaban Daddyn.
Dambun naman ya soma ci wanda ya zame masa alada, Abdulazeez ya gaida Mammah ta kauda kai kafin ta amsa kamar ba ta so, zuciyarsa ta yi masa ba dadi jikinsa ya kara yin laasar. Daddy ya yi kamar bai ga halin da yake ciki ba ya dora bayani.
Sun ba ka aure. Sati mai zuwa kakan naka ya tsayar za su koma a daura aure. Na bada sadaki dubu dari biyu amma kawun yaki karba ya dawo min da su ya biya daga aljihunsa. Sai ka je ka fara shirin daurin aure da abokanka da gyaran gida ko fenti ne ka sake, ke kuma Maryama ku shirya ku wuce Kano a can zaa yi komai.
Da sauri ta ce. Ai ba sai na je ba, auren dan fari? Inna Hafsatu da su Zuwaira zasu yi duk abin da ya kamata, ga iyayensa su Furairah duk sun isa gabatar da komai. In an kawo amarya na je in ga dakin yar masu kudi da mulki. Allah ya sanya alkhairi.
Tsam ta mike ta bar musu falon. Zuciyarta na wani irin zafi. Kafin ta kai kicin ta share hawaye sau uku. Saboda ita bata san minister Abdulkarim yazo da bayanin baza su bawa Abdulazeez Muazatu ba, sun mata miji. Bata san duk bayanin Daddy ne ya shirya abinsa ba. Tanashiga ta tadda Hafsat ta takarkare tana ta suyar dankali, tun jiya ta lura saboda fadan da ta yi mata ta daina walwala kwata-kwata, yau ta kai ta shoppinga Sahad na komawa makaranta da laasar har suka zo gida uffan ba ta ce mata ba. Ita ma sai ta basar da ita. A ranta mamaki ta ke yi tana fadin ta yaro kyau ta ke......Yau ni Hafsat kewa fushi sabida da namiji. Amma mu zuba ni da ku. Yadda na hada wannan auren cikin mutunci kuka hada baki kuka tozarta ni ya kare har abada! Zan ga karshen soyayyah.
Ta ce. Yi a hankali kada ki kone hannu.
Ta ce a hankali ba tareda ta juyo ba. Ai na gama, kwashewa nake sai in je in yi sallah. Ta ce, To jira ni in kwashe abincin duka, mu je sallar tare.
Hafsat ta ce, Toh.
Ta jingina da kitchen cabinet tana jiranta bayan ta gama nata.
Sai ga Abdulazeez har cikin kitchen din. Suna hada ido gaban Hafsat ya yi mummunan faduwa. Wata irin rama ta gano a jikinsa da fuskarsa, idanunsa sun kada yadda suke yi in yana tsananin jin yunwa ya dawo daga ofis. Ta yi hanzarin sunkuyar da kanta, tana karbar sakon bugun zuciyarta. Mammah ta juyo ta dube shi ta ci gaba da kwashe abincinta a warmers, a cikin ranta mamaki ta ke yau Abdulazeez ne a kitchen? Ba ta yi zaton ko hanyar kitchen din ya sani ba komai saidai yace a dauko masa kafin ya bar gidan. Ita ma zuciyarta ta tabu da ganin yadda ya sauya, ta ce. Ko lafiya?
Hafsat ya dan kalla ya russunar da idanunsa. Ajiya na bata zan karba. Kai tsaye Mammah ta ce, Wayarka?
Ya yi shiru.
Ta ce. To in ita ce tana hannun Usman na bashi tun safe ya baka.
A sanyaye ya juya ya fita daga corridor din kitchen din ya dakata yana kallon Hafsat daga nesa wadda ke fuskantar kofar shiga kitchen din. Ta dago suka hada ido, kallonta yake kallon Me ya sa ki ka yi min haka? Ita kuma ta rausayar da kai, kallonI have no idea. Ta ke yi masa.
Sai ji ta yi Mammah ta buga mata ludayin miya a tsakar kanta tana fadin. Za ki wuce mu je ko sai na tsokale miki idanun munafurcin? Shashasha. Wawuya kawai! Wadda ba ta san ciwon kanta ba.
Da sauri Abdulazeez ya bar wajen, yana jin sababin da ake matan har kokon ransa.
Maitama ya nufa kai tsaye gidan tsohon Minister Abdulkarim Dakata, he has to cancel it all. Daddy na shirin kashe shi da ransa! Shi bai ce musu yana bukatar Muazatu yanzu ba. Ya dage sai ya aura masa harda biya masa sadaki na makudan kudi. Ko auren Hafsat da kansa aka ce ya biya, amma wannan da yake na mugunta ne an ce fenti kawai ake bukata yayi. He have a lot to tackle a gabansa ba karin aure ba. Shi ina zai kai mata biyu? Idan har igiyoyin aure uku ne daya ya ce ya saki, kuma ya ce ya mayar tun abun bai je koina ba.
Ya same su complete happy familykamar yadda suke koyaushe. Tare da samarin yayansu; Shaaban da Farhan saannin Ismael da Usman ne. Ramadan ne saansa. Nan ya yi sallahr Isha, sai ya zauna a kan sajjadar ya yi shiru ya rasa abin da zai fara roka ma kansa. Wargajewar zancen aurensa da Muazatu ko dawowar Hafsat gidansa? Daga karshe sai ya daga hannu ya ce.
Na bar maKa alamarina Ya Ubangiji, Ka zaba min abin da ya fi alkhairi, Ka sassauto da zuciyar Mammanah, Ka sanyaya mata, Ka sa ta afuwanta min. Abin da yake ta fada cikin adduar sa ta yau kenan.
Uncle Abdulkarim ya aiko Farhan ya kira shi jin shirunsa ya yi yawa, ga shi ya ce wajensa ya zo. Sai da Farhan ya jira shi ya kammala adduoinsa, sannan ya gaya masa Daddy na jiransa.
Kallo daya ya yi masa ya dubi Aunty Zuwaira ya ce. Je ki hado mindinner.
Ko ba ta daraja dangin mijinta ban da iyalin Dr. Hamza Atiku.Dinner mai rai da motsi ta hado har da zazzafan black tea. Sanya shi ya yi a gaba ya ce ya cinye abincin nan a gabansa in yana so ya saurare shi. Haka ya zauna ya yi ta turawa kamar yana cin dusa. Ya bude masa gwangwanin coke yasan yana sonta sosai tun yana yaro ya bashi ya shanye, ya zuba masa ruwa ya sha. Abdulazeez ya samu ya soma regaining consciousnessdinsa. Idanun karamin Kakan na kansa ya san dai ba zai wuce damuwar auren nan da aka hana shi a Lagos ba.
Sanda uban ya kira shi da maganar auren ya yi mamaki, ya ce duka-duka yaushe aka yi aurensa, how could he cope with two wives a shekarunsa? Daddy ya ce rabu da Abdulazeez, ka je ka nemo masa auren nan shi ne kawai maganinsa, ba ka sanin muhimmancin abunka sai ranar da ya kubuce maka. Ya saki mai sunan Addah, bayan ya nemo mata iyayenta. Musabbabin sakin ne har yau ba mu sani ba, ta ki fada, ya ki fada.
A lokacin ne Minister Abdulkarim ya tuno yadda suka yi da Abdulazeez a kan auren Hafsat. Idan a da ya ce rashin asali ne, to ba ga shi ya bi shawarar da ya bashi a baya ya nemo mata asalin ba? Dole akwai abin da suke boyewa dukkansu,wanda ya tabbatar ya zu ba rashin asali bane, ya kuma sa a ransa yau sai ya ji shi. Sai da ya tabbatar ya samu nutsuwa ya ce da shi.
“Whats wrong my grandson? (Me ya faru jika na)
Sunkuyar da kai ya yi, ya kara tankwashe kafafunsa cikin matsanancin ladabi, cikin damuwa ya ce Uncle ba da yawuna Daddy yake nema min aure ba. In factwannan tsohuwar magana ce tsakanina da yarinyar na kuma dade rabona da ita. Alkawarin da na yi mata na cika shi, daya alkawarin zan yi masa rafkanuwa (wato na aurenta). Koda kuwa na azumi dari (100) ne Uncle. Alamarin ba daga ni ba ne daga Allah ne,alamari ne irin na zuciya da mutum baida iko a kanta. Ka taimake ni ka bashi hakuri ya mayar min da matata, ban san wani hakikanin so ba sai a kanta. Kuskure ne na yi,ina neman afuwa da yafiyarsu, don Allah Uncle ka taimaka mini.
Cikin idanu Abdulkarim Dakata ke kallon jikan nasa, yana karanto zahirin abin da ke zuciyarshi ne zallah yake amayarwa. Ya amince gaskiyar zuciyarsa kawai yake gaya masa kuma Dr. Hamza bai gaya masa gaskiyar yadda ta kaya zuwansa Lagos wajen Attorney General ba. A matsayinsa na babba, tuni ya gano dalilin Dr. Hamza.
Ya ce. A kan me ka saki matarka?
Abdulazeez bai zaci wannan tambayar ba, don haka sosai ta ruda shi, ya hau kame-kame, abin da Abdulkarim Dakata ya tsinta cikin kame-kamen nasa kawai shi ne;
......Wallahi ba don bana sonta ba ne!!!
Ya tausasa murya ya ce.
Abdulazeez, sai na san matsalarka gabadaya zan iya dosar mahaifinka. Ka tuna ba ni na haifar masa kai ba balle in tursasa shi kan duk hukuncin da ya yiwa rayuwarka.Feel free to discuss your problem with your junior grandpa. Im at a door to