Showing 108001 words to 111000 words out of 168255 words

Chapter 37 - Auren Kwangila Book 4 Hausa Novel Complete

Takori   

12 Dec 2024

310

da kuwa da kalmarI love you ne, ba ta so ya fara yanzu don kawai yana son ya farantawa iyayensa, ko don ya tsira da sauran mutuncinsa da kekwayaridanunta wanda har gobe ninkuwa yake yi akan dalilin da bata sani ba duk da ya furta saki a gareta. Ido ya zuba mata yayin da ta kawar da kai gefe taki yarda ta kalli sashen da yake, wani irin sassanyan kyau ne da ita natural wanda bai taba tsayawa ya tantance shi ba, ko kuma giyar son da ke dibansa a yanzu ce take nuna masa hakan? Ba zai iya ganewa ba. Shi dai ya san ta masa kyau a idanunsa irin yadda bai taba gani ba.
Wata nannauyar ajiyar zuciya ya saki wadda ba ta sa Hafsat ta kalle shi ba. Gefen hagunta ta ke kallo, yayin da yake zaune a damanta. Wani irin kwarjini ta yi masa a yau, ya ji yana shakkar furta abin da yake son furtawa. Zuciyar mazantakarsa ta karfafe shi da cewa, Matar ka ce fa! Mace ba ta taba yi wa mijinta kwarjini sai in ya tabbatar shi din mai tarin laifi ne a gare ta. Yes.He admit shi mai laifi ne da yafiyarta kawai yake nema a yanzu. He is dying to haveeven a single word from her amma ga dukkan alamu ba zai samu daga Hafsat din ba. She is no longer the Hafsat he know mai son kyautata masa da neman kulawarsa ta kowacce fuska. Har in bata samu hakan ba ta shiga wani hali. Wannan kallo daya zaka yi mata ka fahimci so kawai ta ke ya tashi a wurinnan ya rabu da ita, ya kyale ta ya fita daga rayuwarta, zamansa tare da ita a yau ya takura ta (ba kamar wancan zamanin ba da babu abinda take so irin ta ganshi a kusa da itaby her side koda ba hira suke yi ba).Ko bata furta hakan ba an ce labarin zuciya a tambayi fuska. Idanuwan ta sun fada, yanayin ta bakidaya ya nuna. Wani abu da shi kuma bai shirya wa a yanzun ba, daga nan har gaban abada (wato fita daga sabgar tata).
Gyara zamansa ya yi ya kamo habarta da hannunsa na dama, a kokarinsa na son su dubi junafor the first time don yana tantamar anya Hafsat din da ya sani ce wannan? Amma maimakon hakan Hafsat sai ta rufe idanunta gabadaya, the long eye-lashes suka bi idon suka kwanta duk da a jike suke da hawaye. Rufe idon da ya birkita shi sai jin saukar harshensa ta yi saman fuskarta yana dauke hawayen da ke zuba, alamarin da ya rikita Hafsat ya soma kwace duk wasu makaman yakinta, amma a hakan kokari ta ke ta nuna bijirewarta, hankalinta in ya yi dubu ya tashi da ta tuna babu aure ko na kwangilar a tsakaninsu, ta kuma bude dukkan idanunta ta dube shi.
Sai da ta gwammace ba ta bude idon ba don gaba daya kwayar idon Abdulazeez tsoro ta bata, bata taba ganin sa cikin wannan halin ba(lasciviousness) zallah a cikinsu irin wadda bata taba gani daga gare shi ba. Baya ta yi da karfi ya riko ta.Kada ki bari ta kai mu da haka Hafsah...., kada ki bari in sa miki karfi. Na ce na maida ke, ba tun yau ba Hafsah... kina nan a matsayin matata da amincewar kowa ko babu, and I need my wife NOW!”








”SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI
07030137870

*Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama*

Sarai ta fahimci manufar Abdulazeez cikin kwayan idanunsa kadai koda bai janye duk wani hijabi dake tsakaninsu a yau ya furta da bakinsa ba.Hafsat ta fahimci kukatactic dinta, ko karfinta bai isa ya raba ta da Abdulazeez a yau ba, ko daga irin rikon da yayi mata, ta soma tunano abin da zai iya faruwa in ta barshi ya rinjaye ta.The worst thingkusancinsu ga iyayensu, ga ta ga Mammah, sannan auren ma duk da yace ya mayar ita bata yarda da sahihanci da ingancinsa ba, ta fi yadda da gurbatacce ne tun waazin data ji a rediyo shekaranjiya akan yin yarjejeniya a cikin aure.Sai ta soma roko muryarta na shaking ba tare dasanin hakan kara triggeringdin shi yake yi ba. Ta kankame jikinta wuri guda ganin kamar baisan ma tana yi ba lamarin kara girmama yake yi, kafin da azama ta mike tsaye, muryarta na karkarwa hadi da jikinta gabadaya ta soma maganar da ba ta yi niyya ba tana hawaye.
Yaya Azeez me ya sa haka don Allah? Im no longer your wife. Kuma a gidanmu? Na hada ka da Allah ka tafi, ka yi hakuri na yi maka alkawarin zan saurare ka da duk abin da ka zo da shi, amma ba yau ba........
Daga inda ta barshi zaune a kasa ba sauran kuzari ko na cikin cokali a tare da shi ya daga jikakkun idanunsa ya dube ta, tayi azamar sunkuyar da kanta.
Then let me hug you properly Hafsah..... Ba zan yi wani abun bayan hakan baI promised.I just want to be closer to you again, in tabbatar Im not that far from you.....
Ba yadda ta iya, tana ji kumatana gani ya mike, da wani irin rawar jiki ya rungume tan.Wata irin tight runguma tamkar zai tsaga zuciyarsa ya sanyata ciki don tsoron kada wani abu wai shi rabuwa ya sakegittawa a tsakanin su. Wanda ya tabbatar target din iyayensa kenan bazasu taba sauraron sa ba. Babu wani uzri da zai kawo da zai yi tasiri a zukatansu. Hafsat din dama ita ce hope dinsa gata itama yau ta bashi mamaki, alamu sun nuna ko a da tana son sa kamar yadda ya dade da fahimta to yanzu ta daina son sa.Kanta na tsakiyar kirjinsa duk suka yi shiru, basa komai sai sauraron bugun zuciyar junansu. Kowanne tunanin da yake daban ne amma akan dan uwansa ne. Ita dai Hafsat a nata bangaren, Muazatu ce a kahon zuciyarta, ta tsaya mata a makogaro ta ki wucewa da wani irin kishi mai tsanani wanda ya sababba mata tsanar Abdulazeezdin bakidayadon sanin irin zurfin son da ya ke mata. How could she live with a husband like him zuciyarsa na ga watanta? Abinda ta jura a baya ko kusa bazata iya jurar rabin-rabin sa yanzu ba saboda ta fara sanin ciwon kanta, don haka maganar su mayar da wannan gallababben auren a gareta ma bata taso ba ta je ta cigaba da kwankwadar bakin cikin Muazatu.Sai dai a yadda ya zo yau ya soma sanya shakku a zuciyarta;could all these be fake? Ana karya da emotionna zuciya da gangar jiki kuwa? Bai taba zama irin yau a gare ta ba. Jikinsa kansa wani irin rawa yake da ya samu ya rungumetan yadda ya bukata. To ina ya kai Muazatun? Fatanta dai a yanzu ya tafi, kada wani ya ji motsinsu a gidan nan ina za ta sanya kanta? Ina alkawarin da ta yi wa Daddy?
Zamewa ta yi daga jikinsa ta isa ga wardrove ta fiddo doguwar riga da sauri ta sanya, saboda rikicewa a baibai ta sanya rigar. Ta dade da manta cewatawul ne kawai a jikinta. Koda suke auren ai bai taba kare mata kallo haka ba sai yau da batasan sunan auren nasu ba? Gashin kanta tarwatse a kafadunta duk ya hargitse, duk yana tsayeinda ta barshi yana kallonta daga ya koma bisa gadonta ya kishingide.Yadda ta ke yin komai a gaggauce ga hawaye na bulbula duk sai ta bashi tausayi.
“Please go Yaya Azeez... help me and go.
Ya kalli cikin idanunta ya lumshe mata lumsassun idanuwansa. I will go Hafsah, but on one condition; switch on your phone.
Ta sa bayan hannunta ta share idonta, a kagare ta ce. Tana hannun Daddy!.
Hannu ya zura cikin aljihun sassalkarmakubar shaddagetzner da ke jikinsa wadda zuwa yanzu duk tayi squeezing ya fiddo babbar wayarsa ya mika mata. Use mine, I will call you tonight. (Yi amfani da tawa, zan kiraki cikin dare).
Karasowa ta yi tsakiyar dakin inda yake zaune a kan rug ta mika hannu don ta karba ba wai don ta amince wa zuciyarta za ta yi abin da ya ce din ba, aah sai don ta samu ya tafi. Amma sai ya hada hannun nata da wayar ya janyo ta ta fado bisa cinyoyinsa. Hannayensa ya sa ya zagaye ta ya kwantar da kai bisa kafadarta, da muryar da a yanzu shi kansa ya ke tantamar kasantuwarta mallakinsa ya sake maimaita tambayar da yayi mata tun farkon shigowarsa dakin bata bashi amsa ba.
Hafsah are we still friends?
Rufe idanunta ta yi, cikin kokawa da numfashi hadi datsokar naman da ke cikin kirjinta (zuciya), wadda ke yi mata wani irin kai-kawo da sabon son Abdulazeez data binne da ransa ya taso bakidaya ya soma yabanya. Girgiza kai ta yi kai tsaye cikin rawar murya ta ce.
No, we are not.
Ko da na ce Im sorry Hafsah?
Mikewa ta yi da niyyar gudu ya sake fizgo ta, ya kankame ta cikin jikinsa.
Dubi yadda na zama Hafsah saboda rashinki, ko abinci ba na ci, bana iya aiki a ofis, bana iya shiga court, ba na barci Hafsah, ban san na aikata kuskure mafi muni ga rayuwa ta ba sai na ranar da na dawo daga Jimeta babu ke a gidan Hafsah! Sometimes our mistakes serves as an instrument of improving our imperfections and shortcomings. Daddy da Mammah sun shirya azabtar da ni a kan kuskurena Hafsah, amma in muka hada kai muka nuna musu muna son juna dole su kyalemu mu koma aurenmu. In sun ki Hafsat zan basu mamaki; sai dai nima in dawo nan mu zauna tare, amma komai mai sauki ne in kina bayana. Na rantse miki ba irin rayuwar da mukayi zamu maimaita ba ki daina tunanin komai ki dauke shi bygone. Ki tausayawa Abdulazeez dinki, ba shi da kowa yanzu a gidan nan daga Allah sai ke....!!!.
Duk wasu kalamai na namiji mai hikima Abdulazeez ya yi amfani da su yau a kunnen Hafsat don ya wanke laifinsa, tare da jaddada mata babu wata mace a zuciyarsa sai ita. Mace mai rauni da saurin karaya, hadi da kasancewar zuciyar ta riga tanarke tayi raga-raga a soyayya na lokaci mai tsawo ba tareda ta samu martani ba. Yau har abinda mafarkinta bai taba bata ba Abdulazeez ya gaya mata. Tuni ta mance da wata Muazatu, kashedin Daddy da duk batancin da Abdulazeez ya yi mata.Ta nemi duka makaman yakinta ta rasa duk kuwa da yadda tayi musu kyakkyawan riko a baya.Wadannan kalaman na Abdulazeez na yan mintoci sun wanke duk wasu kasurgumanlaifukan sa da ta dade tana kallonsa dasu. A karshe ya ce mata aurensu yana nan ba abinda ya same shi tunda dama saki daya yayi,kuma tun tana Jimeta ya maida ta. Ta kashe waya saboda shi da tuni ya gaya mata. Amma zai kara bincike a wurin malamai shima. Wadannan sauran igiyoyin biyu kuma zai kiyaye su yadda zai kiyaye ransatill eternity!
Tana so ta tambaye shi zancen Muazatu ba ta so ta bata wannan mooddin da suke ciki. Wanda tsayin a shekara guda da watanninda suka yi gida daya basu taba kasancewa a cikin kwatankwacin irinsa ba. Kuma bata so ta bude baki tayi magana yaji kalaman bakinta kada ya ga hucewarta da yawa.Don haka ba ta dai ce komai ba, amma labarin zuciya a tambayi fuska. A fuskarta ya ga sassauci,kuma a kwayar idanunta yaga soyayyardake zuciyarta da yayi zaton tayi expirena regaininggradually (farfadowa a hankali). Tashi ta yi daga jikinsa ta koma gefen gado ta zauna. Mikewa ya yi ya kawo mata wayar har inda ta koma tazauna din. Ta karba ta ajiye a gefe ba tare da ta dube shi ba, ta ce. Please go, its almost past twelve Yaya Azeez.
Za ka iya karanto damuwar da zamansa har wannan lokacin a dakin ya jefa ta a sautin muryarta kuma zaka iya gani akan kyakkyawar fuskarta karara. Kanta ya zo ya tsaya ya zuba hannayensa duka cikin aljihun kaftaninsa ya ce. I will. Amma me zan samu daga amaryata Hafsah da zai sa in yi barci mai dadi a yau?
Tsuke baki ta yi, sannan ta yi kicin-kicin da fuska, ta soma kunkuninta. Bakomai take cewa cikin kunkunin nata ba banda (nidai don Allah ka tafi)ya kasa jin me take cewa. Lebunanta biyu ya kama na sama dana kasa da yatsunsa biyu da babban yatsan sa ibham da dan ali sabbab ya matse da karfi. Hannu ta kai ta doke hannunsa. Da mamaki yace. Hafsah!!!
Ta ce a kumbure. Naam.
Ni ki ke bugewa? Bata yi niyyar magana ba amma ta san halin sa saraiabu kadan zai ce ta masa rashin kunya koda shine bashi da gaskiya. Idonta ya cicciko da kwallah tace.
To ba kai ne ba? Gashi ka kumbura min lebe.I just want you to go.
Kugunsa ya kama da dukkan hannayensa daga tsaye yana dubanta da wata irin siga.
Idan na ki fa?
I will not use your phone.Ta amsa da sauri.
“Ok, lemme go now!.
Ya ci gaba da tsayuwar kuma, yana kallon ta kamar ya hadiye ta.
Dafe kanta ta yi, sabida tsayuwar tasa a kanta na making dinta unease. Kanta har ya fara sarawa.
Hafsah! Ya sake kiranta, wannan karon sigar kiran da tasirinsa tun daga kwakwalwarta har yatsun kafarta.
Dagowa ta yi a hankali ta dube shi da rinannun idanunta.Sai dai kuma bata jima ba da dagowar da sauri ta maida kanta kasa. Bai taba yi mata wannan deep and lingering look din ba. Kamar yadda ya ce din ne, he just need his wife ta ga hakan a kwayar idanunsa. Hafsat ta yarda in ba ta lallaba Yaya Azeez ya tafi ba yau zai kwanan mata a daki, ya hada ta da abin kunyar da ba ta da inda za ta kai nauyinsa.
Yaya Azeez don Allah ka tafi, call me as soon ka isa gida, we will talk about it. Ta fada cikin sanyin murya, wadda ke nuna babu fushinsa a zuciyarta.
Tsugunnawa ya yi ya dafa gwiwoyinta da hannayensa biyu. Tunani nake Hafsah ko na je gidan wahala zan sha. Damuwa bazata barni inyi barci ba. Yau so nake na zama mijin Hafsah na haqiqah, ta yadda zan bar ma Mammah tabon da ba za ta iya raba mu ba. ButIm not sure and Im afraid ko auren ya maidu ko bai maidu ba, wannan shine damuwata Hafsah. Yanzu za ta iya raba mu easily (asaukake)tunda ban tabbatar da aurena ba, babu iddata akanki.
Magana yake da muryar da bai taba yi wa wata diya mace magana da irinta ba. Ita kanta Hafsan da ake yi wa maganar kunya ta jefa ta kuma ba sosai take jin ta ba.
Abdulazeez ya kai hannu ya dago habarta, runtse idanunta ta yi saboda har gobe wannan respect din da ta ke ganin Abdulazeez da shi na babban Yayansu yana nan ba abinda ya canza, aka zo aka kara nauyin aure akan wancan. Yau kuma ga shi ya sanya ta a gaba yana gaya mata maganganun da suka fi karfin hankalinta. Kwantar da kanshi ya yi a cinyoyinta abin da ya kara ninka kunyar tata.Please Hafsah tell Mammah you love your husband ko da ba kya sona. I will make sure I made it realistic, I will teach you how to, balle ma na san kina sona tuntuni ko Hafsah? Ba za ki hukunta Yayanki a kan kuskurensa ba, bazaki duba baya ba gaba kawai zaki kalla ko? Kin min uzuri mai yawa a cikin zamanmu, ina rokon ki kara min da wannan ko da shi ne zai zama na karshe. Ki kula da wayar, ki barta a jikinki, a vibration.
Ta ce. Toh!. Dasauri, don dai ta samu ya tafi.
Ya mike a kasalance, ya zura hannayensa cikin aljihun wandonsa. Ya soma takawa zai fice, sai kuma ya juyo.
Ba zan samu komai ba Hafsah? Not even a single good night kiss???
Rufe fuskarta ta yi da dukkan tafukanta. Me kuma yayi saura? Abdulazeez ya amayar da komai dake cikinsa wata da watanni da bata taba zaton ma irinmaganganun zasu iya fitowa daga bakinsa ba. Cikin rawar murya tace.
Yaya Azeez ka je don Allah... I want to be alone!.
Jikinsa ba lakka, cikin wani irin yanayi ya bar gidan.
*********

A sassan Daddy suna hirar tsakar dareshi da Mammah, sun yi barci sun farka suna hirar alamuran yayansu, masu sakin da masu karatuabroad, suka ji alamun fitar mota daga gidansu. Ba karamin kaduwa sukai ba. Da gudu suka isa ga taga suka daga labule. (GMC Terrain) din Abdulazeez suka gani tana fita a hankali, bayan ya fita maigadi ya maida gate din ya rufe.
Azeez a gidan nan at this time? Mammah ta fada cikin mamaki tana kallon agogo. Karfe biyu daidai na dare.
Dariya Daddy ya yi ciki-ciki ya koma gadonsa ya kwanta ya harde kafafunsa, amma bai yi magana ba. Sababi ta kama yi ita kadai kamar ta ci babu, kamar da uban nashi ta ke tunda dai shi ai baya nan bai san tana yi ba. Zancen da tafi nanatawa;zai zo gobe ya tadda ni. Me Abdulazeez ke yi mata cikin gida a wannan tsakar daren? Har ta yi ta gama Daddy bai ce uffan ba. Dankwalinta ta dauka tana shirin barin dakin zuwa na Hafsahita ta bata amsar tambayarta tunda Daddy ya mata banza. A fusace Ambassador Hamza ya fizgo ta. Saura kadan ta sha kasa, Allah ya taimake ta ta fada gefen jikinsa.
A kausashe ya ce Maryama!Sau nawa zan gaya miki ki fita harkar yaran nan? Wallahi za ki sha kunya in ba ki kama girmanki ba. Tsakanin mace da miji sai Allah, ki zuba musu ido.
Ta hakura da fita wajen Hafsat ne kawai ba don ta yarda da abin da ya fada ba, a wurin ta babu komai tsakanin Abdulazeez da Hafsat sai kiyayyah! Kiyayyar sa gareta a fili take in har Daddy zaiyi adalci, wata yaudarar dai yake son sake shirya mata ko wata kwangilar irin wadda ya kware akai.Ta hakura ne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login