Showing 126001 words to 129000 words out of 168255 words
Atiku. Daga nan Abuja, Kano za su wuce gidan marigayi Malam Abdullahi Dakata. Daddy ya san da zuwansu don yana office Malam ya kira shi ya gaya masa tahowarsu, ya kuma kira Mammah a take ya gaya mata. Nan da nan ta sa maaikatan gidan maza na waje su bude sashen baki su gyara duk da kusan koyaushe a gyare yake. Ita da Baba Azumi kuma suka shiga kitchen. Hafsat tana makaranta sai gefen maghriba ta dawo. Tun daga gate ta fahimci gidansu a cike yake, motocin buses(Yola Express) har ukku, tana kuma iya shaida motar Babanta Sienna da motocinsu Uncle Sagir data Modibbo. Tun Usman bai gama daidaita parking ba ta fice saura kadan ta fadi. Shi ya biyo ta da jakar hannunta cikin gidan.
Tana shiga falon farko ta yi arba da DAADA da gudu ta runtuma ta rungume tsohuwar, daga nan ta shiga bin matan daya bayan daya tana runguma bakin nan har kunne. A gaban Dr. Bashar ta dakata sai yashe baki ta ke. Cikin dan fillancin da ta koya wajen Dada ta ce da shi, Abba mi nani beldun larugo ma, noi lawol? (Abba na ji dadin ganinka, ya ya hanya?)
“Minma minani beldun larugo ma Ghaaji, on don jambe jaumu sare ma be saro ma(ni ma na ji dadin ganinki auta, ina fatan kina lafiya ke da mijinki da iyayenki)?
Mindon jam do hairu Abba (lafiya muke cikin alheri Abba).
Imamu ta kalla ta ce, Na yi mafarkinka Hamma Imamu, ashe ba da jimawa ba za ka zo.
Murmushi ya yi, ya ce, Gaji abeddi vodugo (kin kara kyau). Barrister ya iya kiwo.
Kunya ta ji ganin Mammah ta kalle ta.
Ta ce masa Ya Futy? Are you done with your project?
Ya ce, Na gama, ina jiran su kira ni defence. Barrister ya gaya min you are studying Geography, yana so ki zama malamar makaranta sabida sanyin halinki, teachingsai mai hakuri. I told him that is how our mother was, she is very cool. Kin san kusan koyaushe muna waya da shi. Shekaranjiya ya ce zai zo Jimeta in the nexttwo weeks sallama, zai tafi karo karatu.
Maganganunsa sun jefa ta a kogin mamaki, sun yi nitso da ita a kara son Abdulazeez, sai dai magana ta karshe ta kidima ta, karo karatu? Yaushe aka yi wannan maganar?
Kasancewar falon ya gauraye da hirarraki tsakanin bakin da jamaar gidan kasancewar har Daddy ya dawo ya zauna cikinsu ba mai jin hirarta da Yayanta Imamu, Yayan da ya fi sauran (Modibbo da Abdurrahman) shiga zuciyarta saboda kulawarsa gare ta da personality dinsa na son karatu irin nata. Imamu rikakken dan boko ne, wanda son zurfafa ilimin bokon ne ya hana shi aure da neman aiki har yanzu, tun bayan kammala digirinshi na farko. Ba tare da ya lura da yanayin kidima da labarinshi ya jefa ta ba ya shiga ba ta labarin kyakkyawar alakar da ke akwai tsakanin mahaifinsu da Abdulazeez a yanzu. Da kuma su kansu ba tare da saninta ba. Ya kare zancensa da tambayarta ko tare za su tafi? In tare za su tafi ya ya nata karatun?
Ajiyar zuciya mai nauyi Hafsat ta sauke ta dubi Yayanta Imamu, gaskiya ta gaya masa ita ba ta san da maganar ba. Rokonta ya yitunda ba ta sani din ba, kada ta ce ta ji ta a bakinsa. Da ya san ba ta sani ba da bai fada ba. Dariya ta yi, ta ce, Wallahi babu komai.
An yi hira ta zumunci iri-iri, an ci abinci an sha ababen sha daban-daban. Sai wajen karfe tara Abdulazeez ya dawo ya tadda su duk da dai ya san da zuwan nasu, suna hanya Dr. Bashar ya gaya masa da suka iso ma Daddy ya kira shi ya sanar da shi ya ce yana office yana cike-ciken takardu kasancewar tafiyar tasu saura sati daya. Sai yanzu ya gama ya dawo. Hannu Dr. Bashar ya bude masa tun shigowarsa yana fadin,
Come here my son.
Kunya ya ji sosai, ya so ya fara isa gurin Malam Babbah, amma Dr. Bashar ya makale shi. Ismael dariya abin ya ba shi ganin reaction dinsa kamar mace a gaban suruki, wai Yaya Azeez ne da jin kunyar wani. Har karfe goma na dare suna falon, sannan kowa ya fara neman makwanci, mazan a hoteldin (Berkshire, Asokoro) Daddy ya yi musu masauki, matan suna guest rooms wasu suna cikin gidan. Hafsat ta ceDada bakuwarta ce gado daya za su kwana. Mammah kuma Aunty Kubra da Kaltum matar Modibbo ta kai nata dakin. A dakin Baba Azumi ma akwai su matan Yaya Tijjani, matan sauran yayyen marigayiya Habiba su biyar, sauran kuma suna guest rooms din gidan. Malam Babbah an ba shi daki daya a dakin bakin saboda ya ce ba zai iya kwanan hotel ba.
Da manyan jifa-jifan Daddy Ismael, Usman da Salisu suka yi ta jigilarsu zuwa hotel. Abdulazeez yana dakin Malam Babba, sabuwar hira suka bude, Malam Babba na son jin labarin rayuwar yarsa Habeebah a Jeddah da kuruciyar Hafsat.In ya tambayi Abdulazeez dayan wannan, murmushi yake yi ya ceMalam Habeeba ispious (mai ibada ce) as far as I know. Ba abin da ta ke so irin jumaah ta zagayo mu shiga cikin Haraam, mu yi umrah (dawaf, safah da marwah) ta yi ta sallah a maqama Ibrahim. Na dade da lura da hakan a tare da ita, sannan tana son karatun alkurani. Akwai islamiyyah da Daddy ya sanya ni ta Larabawa a can Jeddeh idan na je musu hutu, idan na dawo sai ta ce in karanta mata inda aka kara min. As for Hafsat ba zan iya karar da komai a kan kuruciyarta ba.
Saboda sun yi dukkan kuruciyarsu a wata kasar TuraiBelgium yayin da ni nake nan Nigeria. Dan sanin da na yi mata sanda suke Saudiyyah ne. An haife ta bakwaini, ta dade a cikin incubator;wata kwalba ce da ake saka jariran da aka haifa ba su isa lokacin haihuwa ba. Ban taba yi mata kallon rayayya ba; dalili na shine an haife ta bakwaini, kuma uwa bata mike ba, sannan ga pneumonia. Amma buwayar Allah da ta wuce misali. Tunda ta taso shakka ta ta ke, ban san dalili ba.
Ya dan yi shiru cikin jin kunyar abin da zai fada a gaba.
Kodayake laifina ne Malam, ban ja ta a jiki yadda ya kamata ba, na so Habeeba kamar Yayata, amma abin mamaki Hafsat ba ta shiga raina ba, shagwabarta ta yi yawa. It doesnt sound good ko Malam?
Malam Hashim na jin turanci, saboda ya sha gwagwarmaya a rayuwarsa, kuma ya yi alaka da masu ilimin boko. Furtawa a kan harshensa ne ba ya yi, don haka tsaf ya ji abin da Abdulazeez ya ce. Murmushi ya yi, ya ce,
Ga shi kuma an ce a so kare har jelarsa..
Dariya ya yi cikin jin nauyi. Tsorona ta ke ji sosai kamar dodo
Saboda ba ka sakar mata fuska. Inji Malam.
Ya tura hannunsa cikin tarin sumar kansa, wani murmushi ya subuce masa.
Sai kuma Mammah ta zo ta hada aure ba?
Saboda ta yi maganinka.
Dariya ya yi, ya ce. Na yi protest fa kala-kala Malam, ni da kai aminai ne, can we make a very tight secret?
Jinjina kai tsoho Hashim Babbah Jimeta ya yi, ya ce, Fadi da Hausa ko fullata.
Ya zama serious ganin yadda dattijon ma ya dauki seriousnessya dora a kamilalliyar fuskar dattijantakarsa, mai cike da farin gemanya. Na ce za mu iya yin sirri ba tare da kowa ya ji ba? Sai don ka roka min Mammah alfarma da afuwarta?
A shirya nake da yin hakan Abdulazeez.
Malam kowa yana kuskure ko?
Gyada kai Malam ya yi, Har Annabawa da sahabbai. Ban da Khatimul Anbiyae wa Imamul Mursaleena.
Wata nutsuwa Abdulazeez ya ji ta saukar masa, kaunar dattijon ta kara ratsa shi. Ya ji zai iya gaya masa komai tsakaninsa da Hafsat ko da ba zai yi masa uzuri ba. Komai ya farke masa tun daga ranar da Mammah ta bijiro masa da maganar bukatarta na ya auri Hafsat har gabar da suke kai a yanzu. Ya kare zancensa da cewa,
Shi ne kuskure mafi girma da na san na taba yi a rayuwata da girmana Malam. Ban san ya ya SO na hakika yake ba sai a kan Hafsat! Ban san cewa soyayyar aure daban ta ke da soyayyar matan waje ba sai da Mammah ta aura min Hafsat! Ban san wani abu mafi azabtarwa a rayuwata ba sai da ta kwace min Hafsat. Ban san ladabtarwa mafi wahala ba sai raba ni da Hafsah da Mammah ta yi a halin yanzu. Ta hana ni Hafsat tun bayan maida aurenmu da su Baffa suka yi, ko ganinta ba ta bari in yi Malam duk da ta san auren ya maidu. Malam babu wani nauin ban hakuri da ban baki da ban yi mata ba ta ki saurarena. Na hada ta da Adda Hafsatu (mahaifiyarta) ko ta ga girmanta ta mayar min Hafsat, amma Adda ta ce ta yi mata daidai, ba za ta ko sanya baki ba. Malam sun kasa yi min uzuri su karbi kuskurena kamar yadda na tabbatar ni mai laifi ne, kuma na karbi laifina. Ka taimaka ka roka min ita don na ga tana ganin girmanka, ko ba za ta ba ni Hafsat in tafi da ita ba, ta dinga amsa gaisuwata yadda ya kamata, ta daina fushi da ni, kuma ta yafe min laifin da na yi mata.
Kasancewarsa mutum mai tarin ilimin addini da sani a fannonin zamantakewar yau da kullum, ya fahimci duk labarin da Abdulazeez ya ba shi, da abin da yake so ya fahimta indirectly (yana matukar son Hafsat daga baya bayan da ya zauna da ita na tsawon shekara daya da wasu watanni). Mammanshi kuma ta ki yarda da shi a karo na biyu, bata yarda da sauyin zuciyar tasa bata ki maida masa Hafsat don ta sayo mata mutunci da martaba a idanunsa. Wannan wace irin mutum ce maabociyar kawaici da karah? Mai maida nata ba nata ba ne, na waninta shi ne nata? Mai rufe ido ta hukunta dan cikinta da mafi azabtarwar hukunci a gare shi akan yar wani? Ai ko Abdulazeez ba ya son Hafsat kuma ya ce yana son karo mata uku bayan ita in har yana raye ya samu ya gama.
Hannunsa ya kama ya rike cikin nasa yana dubanshi cike da kauna. Yayin da shi ya sunkuyar da kansa guilty concience na sakin Hafsat na lullube shi. Malam Babba ya ce.
Ina Muazatu yanzu? Bayan ita akwai wata wadda ka ke so?
Jin zancen ya yi kamar daga sama kasancewar ba shi ya tsammaci ji ba. Girgiza kai ya yi da sauri, Babu wannan zancen fa Malam. Na ba ka cikakken labarin ne don ka fahimci komai ba don a tado wannan zancen ba mara fasali. Wani alamari ne da ya riga ya shude, babu ko birbishinsa a zuciyata yanzu. Soyayya ce ta shekarun kuruciya kuma ta dade da gushewa.
Malam ya ce, Tana ina yanzu?
Da sauri ya ce, Ta yi aure Malam, ko ba ta yi aure ba bari in maka a fili tunda hakan ka ke so, bana son ta yanzu, ban kuma san me ya kai ni ga son nata ba a wancan lokacin saboda bata dace dani ba ta kowanne bangare. Na lissafa lamarina da ita cikin kaddarori masu zuwa su wuce a rayuwar dan Adam.
Malam ya fahimce shi sosai, amma don ya kara kore shakku ya kuma tabbatar Hajiya Maryam ba ta shiga hakkin Abdulazeez saboda Hafsat ba, sai ya ce,
An taba son mace a daina Abdulazeez?
Da sauri ya ce, Wasu kaddarorin na shigowa rayuwarmu ba don su tabbata ba, ana haduwa da su a kan hanya a kuma rabu kafin a iso gida. (Dreams are conceived, but not all dreams are born alive. Some are aborted. Others are stillborn. -Zainab Alkali).Wannan ne zahirin tsakanina da Muazatu.
Malam ya gamsu da bayaninsa, sannan ya yi murmushi ya dube shi, bari in in kara yi maka nawa bayanin akan masalar aurenku. Duk da BaffaAtiku yayi nasa. Tunda ka yi kome na gaggawa kafin kammala iddah kuma saki guda daya ne aurenka da Hafsatu yana nan ba abin da ya same shi. Niyyar farkodama sharia ba ta yarda da ita ba tunda an gina ta ne a kan muta, komen da ka yi wa sakin da kyakkyawar niyya da tsaftar zuciya shi ne ya gyara auren.
Abdulazeez ya san Baffa ya fadi hakan, amma da Malam ya kara maimaitawa sai ya ji hankalinsa ya kara kwanciya. Murmushi yake ta yi, sai da Malam ya yi masa dariya. Fada ya koma yi masa kan abin da ya yi (yarjejeniya a cikin aure), ya ce aure ba abin wasa ba ne, ibadah ce wadda ake neman dacewar Ubangiji a cikinta. Cikin kowacce ibada sai an sa taqwa wajen biyayya ga mahalicci. Ba abu ne da ake yinshi kara-zube don biyan bukatar rai ba; abu ne da ke gine kan tsari da dokoki na shariah ba a hada shi da son cimma wata manufa. Ya gargade shi da yin istigfari da tuba nasuuhan. Wato tuba da zummar ba za a sake maimaita wannan kuskuren ba. A karshe ya ce.
Ka sani Hafsat yar Hajiya Maryama ce babu wani mai iko da ita sama da ita. Har kuwa Dr. Bashar, don haka lallashi da ban-baki da kamun kafa za mu yi shi har sai ta hakura. Za a iya yi mata dole, amma abin da zai biyo bayan yin dolen shi ne abin gudu, wato tsaurara mata fushi a zuciyarta. A shirye nake da in tsugunna a gabanta gobe in yo mana bikon Hafsat ka ji ko? Je ka ka yi baccinka har da minshari. Amma ni ma ina rokon alfarmar ka zo Jimeta in karo maka kyawawan fulani guda biyu, Hafsatu ta yi maka kadan.
Dariya ya yi, ya ce, Malam! Bari mu fara kama dahir tukunna,ma yi wannan zancen daga baya, watakila nan da shekaru ashirin!
******
WASHEGARI
Assalamu alaikum. Mammah ta fada daga bakin kofar dakin da aka sauki Malam Babba. Gyaran murya ya yi, ya ce, Ameen walaikumussalam, shigo daga ciki Hajiya Maryama.
Ta tura kofar ta shiga, Azumi ta biyo bayanta dauke da tray mai girma. Gaban Malam din ta isa ta ajiye wanda ya yi wanka ya shirya cikin farar shaddah, ya sha farin rawani da babbar riga, farin gemunsa ya kwanta sosai. Azumi ta gaishe shi a nan ne Hajiya maryam ta gabatar da ita wajensa matsayin uwa ta biyu ga Hafsa tun a Birnin Jeddah. Kujuba-kujubar rayuwa a kasashen ketare duk tare aka yi ta har yau da aka dawo gida. Ta gaya masa mutuniyar Sokoto ce, yayanta da jikoki duk suna can. Zaman Hafsat takeyi yau shekara sha takwas. Malam Hashim ya kara gaisawa da Azumi, ya yi mata adduar alkhairi. Mammah ta matsa gabansa, ta ce.
Wanne zan zuba wa Malam? Kunun Acca, na Alkama ko na gyada?
Murmushi ya yi, ya ce, Sannunku da hidima, muna rokon Ubangiji ya fi mu godewa. Zuba na Acca.
Ta tsiyaya masa a kofin tangaran, ta zuba masa kosai da aka yi shi luba-luba ya ji albasa da kwai, a gefe ta zuba dankalin hausa (sweet potatoe) da na Turawa. Sai farfesun bindin Saniya a kwanon tangaram. Suka mike don su ba shi wuri ya ci abinci. Ya ce, Hajiya Maryama in ba abin da ki ke yi ki zauna in gama akwai abin da nake so mu tattauna.
To babu komai Malam, bari in je in sallami su Dada sai in dawo kafin nan ka kammala.
Babu laifi. In ji shi.
SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI
07030137870
*Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama*
Sai dai kowa a gidan ya karya aka fidda kwanukan wanke-wanke kafin a dora abincin rana, sannan Mammah ta samu nutsuwa, ta dawo ta tadda Malam. Sai da suka sake sabuwar gaisuwa ya ce da ita, Akwai shanu da tumaki da marigayiya ta ke kiwo guda biyar a cikin garkena kafin barinta gida. An ci gaba da kiwatawa a bayanta. A yanzu haka sun bunkasa da albarka mai yawa, kafin in taho na sa an tattara su wuri guda an raba su ga magadantayadda Ubangiji ya yi umarni. Na Hafsatu ban san ya zan yi da su ba na ce in mun zo zan ji ta bakinki.
Ajiyar zuciya Mammah ta yi ta gyara zamanta, sannan ta ce, Ni ma a hannuna akwai kudin aikinta na tsayin lokacin da ta yi tare da mu, na so in ba ta a karshen kowanne wata ta ce in dinga tara mata, tun a wancan lokacin na zuba su a wani account a kasar Saudiyyah ban kara waiwayarsu ba, sai dai details din komai yana hannuna, zuwa yanzu Allah kadai ya san hauhawar da suka yi. Zan sa Babansu ya dawo da su account dinsa da yake har yanzu yana da ajiya da su, sai ya ba ni in ba ku a sake rabawa magadanta. Sannan ita Hafsat akwai wasu kudaden masu yawa a account dinta wanda Babansu ya bude musu ita da sauran yan uwanta a kasar Belgium, kowannensu na amfani da nashi ban da ita don haka ni yanzu Hafsat ta fi ni kudi, ta koma Hajiya Hafsatu. Ta karashe da dariya.
Shiru Malam Hashim ya yi yana magana da zuciyarsa, wace irin mutum ce Maryam Dakata? Anya akwai sauran mutane irinta a duniya? Yanzu har wani kudin aikin Habeebah ta ke ajje da shi bayan dawainiyar abin da ta haifa ta bar mata? Da kyar ya iya yin magana, amma hawaye cike da idanunsa.
Duk da wannan hakki ne na magada, amma na ari bakinsu dukkansu na ce mun yafe! Ya taso daga inda yake zaune a kan center carpet ya iso gabanta ya durkusa tana zaune a kan kujera.
Alfarma muke nema wadda daga ita babu saura cikin dimbin alfarmominki Hajiya Maryama. Cikin wannan kyautayi naki mai yawa, cikin wannan adalci naki abin kwatance, da wannan zuciya mai taimako irin taki wadda babu irinta, ki bar waiwaye da hango komai na baya da ya riga ya wuce, ko wanda zai faru a gaba, ki maida wa yaron nan matarsa! Mun