Showing 156001 words to 159000 words out of 168255 words

Chapter 53 - Auren Kwangila Book 4 Hausa Novel Complete

Takori   

12 Dec 2024

316

ni. Da na zo na sayi kaya masu yawa wasu ko taba su ban yi ba har yau. Ba tare da ta kalle shi ba ta ce. Ba fa kai nake sayawa ba Malam . Haleem nake daukarwa!.
Dariya ya yi da ya tuno wani zuwa da ya yi Jeddah Haleem din ya faki idon Mammah da Baba Azumi ya danne ta yana kirbarta tana ta zabga ihu, shi ya daga shi daga ruwan cikinta. Ta sha wahala iri-iri a hannun Haleem, amma duk gidan har gobe ba wanda ta ke so kamar shi.
“Shine kuma kike gwadawa da ni? Ai na fishi tsaho? Kuma shi mai kiba ne. Ki hada da Usman ko banza ya sha jigilar kai ki makaranta ya dauko ki, a lokacin da aka sanya ni a makarantar Mammah,kuma dai yana son ki kullum mukayi waya sai ya tambayi lafiyarki.
Dariya ta yi jin abinda yace wai (makarantar Mammah) ta ce, He is the first in the list, na saya mashi a Texas, shi da Hamma Imamu.
Ya ce, Abba fa?
Kai ma ka san ba ya saka kananan kaya.
Ki saya masa wani abun to, ga agoguna ga takalma?
Waya ta fiddo ta kira Imamu ta tambaye shi lambar kafar Abbansu, sannan ta dauka mishi takalma kafa uku da tsadadden agogon POLO. Ya ce hatta Malam da Daada sai an yi musu tsaraba. Dariya ta yi ta ce, ita ba ta ga abin da ya dace da su a nan ba, ya bari in ta koma gida za ta saya masu.
Ya ce, Wallahi ko ki ma Ismael tsaraba ko na gaya masa kin ware shi, kin maida shi saniyar ware. Ta zumburo baki, tace ba abinda zan saya da sunansa, ina kaiwa zai gayamin bakar maganar da sai tayi shekara tana damuna.Ka manta sanda yace nikazama ce, don kawai ya rako Mammah ban yi wankan safe ba, zai aura maka yar gayu. Murmushi Abdulazeez yayi yana tuno ranar shima, abubuwa da yawa sun faru a ranar very bitter and sweeteralso,ya kada ya raya ta ki, sai ya fiddo waya ya kira Ismael.
Ishma, Hafsat ta yi wa kowa tsaraba ban da kai saboda laifuffukanka masu yawa ne.
Ismael yayi dariya ya ce ya ba ta wayar. Da farko tace bazata karba ba sai ta ga rashin kirkinta, shi Abdulazeez Ishma ne nasa yafi shiri dashi a kan sauran duk da shine sakonsa. Karba tayi tana hura hanci, ita ga wadda zaa bawa hakuri. Ismael yayi gyaran murya sannan yace,
“Addahmeye na daukar zafi da ni haka? Da zaki yiwa kowa tsaraba banda ni?Ni fa ko da na ce zan aura wa Yaya yar gayu, in kin mutu nake nufi!.
“......Insha Allahu Wasila ce za ta fara mutuwa kafin ni.....
Abdulazeez ya fizge wayar jin ana zancen mutuwa ga Hafsat ta fara hawaye a tsakiyar shago. Ba ta hango komai sai ranar da za ta mutu ta bar Abdulazeez kamar yadda Ishma yayi mata fata, ya manta da ita ya auri watanta. Ta karbe duk wannan soyayyar da yake gwada mata wadda daga ita sai Allah sai shi suka san yadda take. Hannunta ya kama suka bar shagon bayan ya biya su kudin kayan da suka dauka. Sannan ya kira Ismael suna cikin taxi don komawa gidaya soma sauke masa fada da bacin rai mai tsanani, ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba. “Daga yi maka abin arziki Ishma, wai ni babba inaso in gyara muamalar ku dana lura bata da dadi duk da na san kai ne ba ka da gaskiya? Ashe girma na bai isa yayi amfani ba Ismael?” Ya karasa cikin kwantar da sauti.
Ismael dariya yake yiko a kwalarsa ya ce, Ai ba za mu taba shiryawa ba sai ranar da ta daina shagwaba da kazanta a gidan miji.
A karshe gajiya ya yi ya rabu da shi, saboda ya fara sa masa ciwon kai. Haka Allah ya yi shi(very annoying). Hafsat kuma ba ta daina kuka ba har suka je gida, kayan ma duk shi ya kai mata daki. A kujerar falo ta zube tana ta sharar ido. Sunkuyawa ya yi a gabanta bayan ya fito daga dakinta ya juyo mata bayansa....
She wonder what he is going to dohaka sunkuye a gabanta duk da hawayen da ta ke yi. Haubayan nan Hafsat in goya ki, yi maza ki riga yayan Abdulazeez hawa, in mutuwar da ya ke ambato ta zo ta ganki a bayana za ta ji kunyar dauke ki ke kadaita barni. Sai ta hada mu mu biyun ta dauka.
Da gudu ta haye bayan nasa ta kwanta, ta sarkafo hannayenta a wuyansa ta rungume shi tsantsan,kukan ya rikide ya koma dariya. Sosai ya bata dariya.
Ba mutuwa nake gudu ba Yaya Azeez, yadda za ka manta da ni ne idan na mutun kayi aurenka.
Shi ne na ce mu makale juna kawai mu zama kamar alkaki, yadda za ta ji kunyar dauke ki ta bar ni. Har a lahira ina rokon Allah ya zaba min HAFSAT-SUHAANAH matsayin matata a gidan aljanna, na yi miki alkawarin ko Hurul-eeni ba zan roka ba!.
Sosai ta manne a bayan nasa tana wani irin blushing da bata jin ta taba yin irinsa a rayuwarta, wanda ke fitowa tun daga karkashin zuciyarta. Hakika kalamansa sun ratsa har tsakiyar ruhinta sun haifar da farin ciki da annashuwa marar misali. Tuni ta mance da shirmen Ishma ta rungume mijinta. Rokon Allah ta ke cikin zuciyarta ya biye bakin Abdulazeez Dakata. Ya sa in mutuwa ta zo ta dauke su tare, in ya so su bar ma Mammah yayansu ta goya. Cikin wannan nishadin suka shige bedroomdinsu ba sa ganin kowa da komai a gabansu da bayansu sai junansu








SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI
07030137870

*Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama*
Tun Hajiya Maryam na kidayar kwanakin dawowar Hafsat tana jiran Abdulazeez ya kira ta ya ce rana kaza za ta taso, har lissafin ya subuce mata. Hafsat dai tunda ta saka kafa kasar America Abdulazeez ya raba ta da wayarta. A cewarsa gabadaya lokacin nasa ne, sai ya yi covering shekarar da ya yi asara har da doriyar watanni biyar a banza,cikin yan satittikan da suka zamo nasa. Sati uku suka cika, aka shiga na hudu, shi ma ya kare aka shiga na biyar Abdulazeez bai da niyyar maido mata Hafsat ta koma makaranta. Ta yi fadan har ta gaji kullum da uzurin da zai bayar.
Uzuri na karshe da ya ba ta shi ne, Hafsat ba ta jin dadi yana tsoron sako ta a jirgi ita kadai, a bari zuwa wata mai kamawa sai ya yi kokari ya kawo ta da kansa, ko kwana biyu ne ya yi ya koma. Dan jim! Mammah ta yi kafin ta ce, Me ya same ta?
Cikin damuwa ya ce, Ni ma ban sani ba, ba dama ta dora girki dai sai ta yi amai, wai ba ta son kamshin abinci. Idan na siyo ma bata ci ba tare da ya dawo ba. Snacks kadai da Pepsi ke zama a cikinta...
Bai karasa ba ya ji Mammah ta kashe wayar, sai da gabansa ya fadi, cike da tsoron ko wata mummunar cutar ce da bai sani ba ya fadi symptoms dinta? Ya juya ya dubi Hafsat din wadda ke kwance a dandaryar marbles kamar wadda tayi wata uku tana jinya, damuwarsa ta kara nunkuwa. Ya ce, Don Allah Hafsat ki yarda mu je asibiti, na yi miki alkawarin ba zan yarda su yi miki allurar ba, kuma ki tashi daga tayal din nan sanyinsa zai cutar da ke.
Kukan da ta kwana tana yi ta ci gaba, da kyar in ba mutuwar da Ismael ya yi mata fata ce ta iso ba, ba tare da ta ga Danta da Abdulazeez ba. Yau kwananta biyar cikin wannan halin ta ki yarda su je asibiti, honeymoon ya guntile ya koma jinya. Ta yi-ta yi ya sa ta a jirgi ta tafi ya ki, shi a wahale ita a wahale, yana cutuwa ta fannin karatunsa sosai, ita kuma ba abin da ta ke tsoro a duniya irin a huda jikinta da allura, ta san yadda ta ke vomiting din nan abu na farko da asibiti za su yi mata shi ne, saka drip. Ya taso daga inda yake rubutu cikin system dinsa ya dago ta daga tiles din ya hada da jikinsa. Sai kawai ta fasa kuka tana fiffizgewa, ita dai ya kyaleta ta fi jin dadin can. Zama ya yi a kasa ya rungume ta kamar shi ma zai yi kukan. To ni ki kwanta a kaina duk yadda ki ke so, kiyi birgima kiyi ta kukan yadda yayi miki, amma ba zan iya kallonki kwance a kasa ba sanyin nan na huda jikin ki.
Zamewa ta yi ta koma inda ya dauko ta ta yi kwanciyarta ta juya masa baya. Abdulazeez ya rafka tagumi ya soma tunanin ko dai ya yi musu yadda suke so ne ita da Mammah ya maida ita gida? Duk da cewa zamanta tare da shi as a patient nauyi ta zame masa, musamman yadda karatunshi ya dau zafi a wannan dan tsakanin, ya fiye masa rashinta cikin gidan sau dubun dubata duk da yanzu babu abin da ta ke tsinana masa sai aikin kwashe amai da gogewa da ya hau kansa. Wanka ma shi yake mata, abinci sai dai ya sayo ita kuma ya sayo mata snacksda pepsi amma wallahi hes enjoying this new life fiye da farkon zamansa a gidan shi kadai.
Sai dare ya samu wayar Mammah, da sauri ya amsa a lokacin yana kan hanyar komawa gida ya fita sayo harpic na wankin toilet dinsu. Muryoyinsu su biyu ya ji ita da Daddy, da alama a handsfree suke magana, Daddy ya ce, Kana jina ko Abdulazeez?
Ya ce, Ina jinka Daddy.
Mammah ta ce, Kai kadai ne?
Ya ce, Eh, a titi ma nake.
Daddy ya ce, Ka je ka kira hospital din su zo su tafi da ita da kansu, kada ma ka tsaya a wajen ta ganka. Idan ta samu karfin jikinta ka sako ta jirgi ba abin da zai faru insha Allah.
Cikin damuwa ya ce, To Daddy.
A tare suka hada baki, Yauwa Abdulazeez Allah ya yi muku albarka.
Ji ya yi damuwarsa ta tafi gabadaya, ya amsa da karsashi, Ameen-ameen Daddy, ameen Mammah.
Hafsat na kwance ya shigo ya ce, Tashi ki shirya za mu yi baki yanzu.
Bata fuska ta yi zai katse mata kwanciyar jin dadinta ta kan marbles wanda ya fi komai dadi a gare ta yanzu. Da ya ga tana bata masa lokaci ya shiga ya dauko mata doguwar abaya da mayafinta kawai ya ciccibo ta ya hau saka mata, sai cin fushi ta ke tana mita.
Wadanne irin baki ne tun ina da lafiyata ba su zo ba sai yanzu da na koma gawa ta ki rami?
Dariya ya yi, ya ce, Ashe kin iya Hausa kike cewa baki iya ba?
Ta zumburo baki ya kama lebunan da yatsunsa biyu, Ki yi a hankali da ni kada na karasa gawar, kin ga ina tausaya miki kwana biyu, to ki lallaba ni in ci gaba da daga miki kafa har ki warware in koma angwancina.
Rufe idonta ta yi da tafukanta, Yaya Azeez ka dinga jin kunyata mana, ni fa kanwarka ce.
Hannayen da ta rufe idon da su ya dauke, ya dube ta cikin ido ya dage girarshi sama ya ce, Really?
Neman wajen boyo ta koma a jikinsa, shi kuma ya ki yarda da hakan, wai lallai ta dube shi cikin ido ta maimaita ita kanwarshi ce ba matarshi ba. Suna wannan diramar suka ji kararrawa. Mayafin ya dauko ya nannada mata a ka ya taimaka mata ta mike, Mu je mu bude musu, ga su nan sun iso.
Har takalami ya dauko mata. Cikin mamaki ta ce, To ka je ka bude musu mana? Na sani ko da maza?
Hannunta ya ja zuwa bakin kofar yana fadin, Aah mata ne.
Mata! Ta fada in exclamation! Tuni ya gano inda ta nufa, kawai ya yi dariya ya bude kofar. Hafsat ta yi arba da kyawawan matan turawa guda biyu, amma dai da fararen kayan maaikatan jinya a jikinsu. Wani murmushi suka kashe ta da shi, kowacce ta kama hannunta daya suka yi gaba da ita zuwa farar ambulance din da suka zo a cikinta. Ta waiwaya hagu da dama babu Abdulazeez babu alamarsa, ya gudu ta inda ba ta sani ba. Ta so yi musu gardamar kin shiga motar, ta ga za su gwada mata karfi duk da dai lallashinta suke yi, amma fa ba ta ga za su yarda da abin da ta ke so ba. Sai tsintar kanta ta yi a wani kyakkyawan asibiti.
Abin da ta ke gudun shi aka fara yi mata, tana kuka tana komai. Ta sha allurai kala-kala, kulawa dai zallah kamar tana gaban Mammanta. Zuwa washegari dai kam da kanta ta nemi abinci white rice and stew, haka suka kawo mata. Lallabata suke kamar kwai in ta tambayi mijinta su ce sai ta daina kukan allura za su barshi ya zo. Kwananta uku ta samu karfin jikinta sosai, haraswar ta tsaya, sai mugun cin abinci kamar tashin hankali. Magungunan da za su kara mata karfi da lafiya suka bata suna kara jadda mata ta dinga sha kullum kuma ta dinga kula da kanta. A daren ranar suka sallame ta, ba ta ga Abdulazeez ba sai lokacin. Bai ce komai ba ya kamo hannunta yana sakar mata wani irin murmushi, suka shiga taxi ta kai su gida.
Suna shigowa falo ya wani irin juyo ya sure ta bai dire ta a koina ba sai dakin barcinsu. Ba don kar ya saukar mata da hajijiya ba juyi yake so ya yi ta yi da ita. Idanu ya zuba mata kamar zai cinye ta. Kafin ya mirginota ta dawo samansa, ya ce, Kin san wani abu?
Hafsat wadda duk ta bi ta tsorace da abubuwan da yake yi masu kama da na sabon kamu, ta ce, Aa, ban sani ba.
Har na soma hango ki kina breastfeeding Hafsat. Oh me! Ya rungume ta.
Hafsat wadda ta ji zancen a baibai ba ta fahimce shi sosai ba. Rokonsa ta ke ya gaya mata abin da yake nufi da hakan amma ya ki, hanyar faranta ran junansu yake bi kala-kala, lungu da sako kusufa-kusufa. Ranar yau ta kasance cikin jerin ranakun farin cikinsa a rayuwa, ba zai taba mantawa da ita ba. Its a SECOND day in historybayan ranar dawowar ta cikin rayuwarsa. Abin da ya ce mata kawai kenan. A karshe da suka koma cikin consciousness ya damka mata passport dinta da tikitinta. Muryarsa abin tausayi ya ce.
Na amsa wa Daddy da Mammah za ki koma gobe. Hafsat na ba ki amanar kanki da kanki da ta abin da ke cikinki. Ban yarda ki jigata shi saboda bokon nan naki ba. Ni ko third class ki ka fiddo in dai BABY na zai zo cikin koshin lafiya Allah ya sanya albarka. Aclass of degree ba shi ne matsayin ilmi ko kokarin dalibi ba. It determines the condition da dalibin yake ciki a yayin karatun, duk da kokarin ma yana taka muhimmiyar rawa. Iwill come soon... and I will miss you soon. Ya kwantar da kai a kafadunta. Yayi shiru.
Hafsat is speechless. Cikin tarin zantukansa masu kama da wasiyyar bankwana sentencedaya ta tsaya mata a rai, Amanar kanki da ta abin da ke cikinki. Which means ......an gaya wa Yaya Azeez she is pregnant a asibiti, dalilin farin cikinsa haka kenan. To shi cikin haka ake samunsa cikin dan lokaci kalilan? Kamar kiftawar ido? Kamar a majigi? Shekara daya da doriya ba a same shi ba sai yanzu? Zancen zucinta ya subuce ya fito fili.
Dariya sosai ta baiwa Abdulazeez ya dago kansa daga kafadunta ya dube ta cikin ido da idanunsa da ke sanyaya mata zuciya.
Saboda wancan lokacin its a crime in Nigeria. Yanzu kuwa baa Nigeria muke ba,it is allowed here in the U.S.
Ita ma sai abin ya ba ta dariya, ta tuno lokacin da ta zauna tana zancen da shi babu ko kunya. Kai ta rafka wauta a baya, kada Allah ya maimaita. A daren ya hada mata kayanta da tsarabar da ta dade tana jida. Har Baba Azumi ta samu dogayen riguna biyu masu kyau na masu jini a jika. A daren gabadayansa cikinsu ba wanda ya runtsa..., The farewell is very very emotional (bankwanan ma taba zuciya ne). Soyayyar cikinsa is an extraordinary (babu kamarta a tarihin rayuwarsu). Alkawururruka suke daukarwa juna kamar ba za su kara haduwa ba sai a Darussalam. Duk da bakin Hafsat ya mutu, tun daga jin labarin ta kusan zama UWA, uwar ma ta jikokin Hamzah Atiku da Maryam Dakata; mutane mafiya darajar girma da kima a gare ta fiye da kowa a duniya in ka cire wadanda suka yi silar zuwanta duniya. Shin ko adadi nawa za ta so wannan Dan? Mai cin tudun soyayya uku a zuciyarta???
Na farko na kasancewarsa Dan da ya fito daga mahaifarta, na biyu na kasancewarsa daga jinin jikin ABDULAZEEZ Hamzah Atiku; wani kwayan mutum guda daya da ta ke so da dukkan ruhi da zuciyarta da soyayyah marar misali. Na uku kasancewarshi jikan Mammah. Jikan ma na farko da bata taba dauka ba sai a kansa.

Sai da aka sanar cewa za a rufe jirgin sannan Abdulazeez ya raba Hafsat da jikinsa. Suna daga tsaye ya kowa ya shige ya barta. Ita ce karshen shiga ta zauna a (first class seat) dinta yadda tazo daga barin dama ta barshi tsaye ya zuba hannayenshi cikin aljihun bakin wandonNordstrom da ke jikinsa da farar T/shirt Tommy Hilfiger. Har ta bace wa ganinsa murmushi ne a kan fatar bakinsa, image din wannan yanayin da wannan ranar ya zauna mata a zuciya. Lokacin da jirgi ya karci kasa ya lula sama cikin hazo sai ta sa hannayenta biyu ta dafe cikinta. Wata amana da ta karba da hannu bibbiyu ta ke rokon Allah ya taya ta rikonta. Ta zame musu sanyin idaniya dukkaninsu, kuma nauin farin ciki ga iyayensu.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login