Showing 93001 words to 96000 words out of 168255 words
kare ba ne Yayansu? Akwai tafiya fa a gabanmu rana tana yi.
Ga ni nan Daddy. Kawai ya ce a sanyaye. Ya tabbata Hafsat ba za ta fito ba kenan. Da za ta fito da tsawon mintuna talatin din da ya share a zaune sun isa su fito da ita, daga dai cikin gida zuwa dakin Mallam. Wannan ma shaida ce mai tabbatar masa da cewa Hafsat ta karbi sakonsa;(And she acts accordingly).
Cikin sagewar gwiwa da debe tsammani ya fito daga gidan Malam Hashim Babbah Jimeta, ya ja motar da iyayensa da kakanninsa ke ciki, suka soma fita daga shiyyar Demsawo. Tafiya sannu-sannu har suka hau titi dodar suka bar garin Jimeta. Ji yake tamkar ya bar wani bari na gangar jikinsa cikin Jimeta, barin da bai san yadda zai yi ya dawo da shi jikinsa ba. Anya bai tafka kuskure ba? Ta yaya ya tabbatar rabuwa da Hafsat shi ne babban tsanin da zai samo masa Muazatu daga wajen mahaifiyarsa? Anya hakan ba shi ne kuskure ba maimakon ya zamo MAFITA a gare shi? Da wadannan tunanukan masu nauyi Abdulazeez yake tuki yana wuce dazuzzuka da bishiyoyi, garuruwa da kauyuka yana mai jin tamkar karshen rayuwarsa ya zo! Da wacce kalma zai kare kansa ranar da Mammah ta karbi sakin da ya yi wa Hafsat don ya samu Muazatu???
*******
Sai da ta ji tashin motocinsu sannan ta koma cikin gida. Dada ta tambaye ta sun tafi? Ta ce sun kama hanya. Kwananta uku ba inda ba a kai ta ba gidajen yan uwa da dangi. Ranar da ta cika sati gidan Yayanta Modibbo ta wuni a Use-Demsawo tare da matarshi Kaltum. Washegari kuma gidan mahaifinta wanda ke cikin gidajen malamai na jamiar Yola. Matarshi Aunty Kubra maaikaciyar gwamnati ce a hukumar haraji ta jiha, mace ce da ta san ciwon kanta, ta ke kuma rungume da su Imamu da zuciya daya.
Cikin sati daya da Hafsat ta yi a gidan mahaifinta Dr. Bashar tare da shi da yan uwanta na ciki daya Imamu da Abdurrahman tunda Modibbo da suke kira Hamma Modibbo yana nasa gidan, Modibbomaaikacin (Immigration Office) ne. Sabo mai tsanani ya shiga tsakaninsu musamman Imamu, wanda ke karatunsa a (American University Yola) a kan tsimi da tanadi. Shikuma Abdurrahman yana aiki da gidan wayar Etisalat. Rayuwar gidan abar koyi ce domin kowanne na da abun yi, sun fahimci juna kuma ilmi ya ratsa kowa. Tsakanin Imamu da Abdurrahman da Dr. Bashar din kansa har rige-rige ake wajen farantawa Hafsat da suke kira (GAAJI) wato auta da harshen fulatanci. Wannan ya taimaka kwarai wajen mantar da ita Abdulazeez da duniyarsa.
A karshen satin Daddy ya shirya musu tafiya zuwa NUMAN ainahin asalinsa don su kai Hafsat ta ga sauran yan uwansa tunda iyaye babu sun kare.
A motar Dacta Bashar kirar Sienna suka yi tafiyar har Hamma Modibbo da maidakinsa Kaltum. Ita da Kaltum na kujerar can baya, Abdurrahman, Modibbo da Imamu na kujerar gabansu, Daddy ke tukin motar, Aunty Kubra na gefensa. Tafiya ce mai dadi da sanya nishadi a gare su, suna tafe suna hira har suka isa garin Numan.
Yan uwan haihuwar Dacta Bashar su uku ne ke raye, Baffa Saadu, Malam Zakari da Surajo duk tare suke da iyalinsu a can Numan kowanne na da kwakkwarar sanaarsa. Su Malam Zakari sun ga yar dan uwansu sun kuma ji duk abin da ya faru da Habiba. Addua kan Habiba ta sha ta kamar yadda Hajiya Maryam ta sha tofin albarka da fatan alkhairi.
Bayan dawowarsu daga Numan da kwana daya Dada ta aiko Nuru ya zo ya dawo mata da Hafsat ta yi shirin komawa gidan mijinta, Mammah ta yi mata waya cewa hutun su Hafsat ya kare za su koma makaranta ranar litinin kwana uku masu zuwa.
Tun barin su Mammah Jimeta Hafsat ba ta kara kunna wayarta ba. A ganinta wayar ba ta da sauran amfani a gare ta. Ba ta da sauran alaka da wanda ya mallaka mata wayar amfanin me zata yi mata? Mammah kuwa da Baba Azumi in ta samu nutsuwa za ta dinga kiransu ko ta wayar Dada ne tana gaishe su.
Da ta dawo Demsawo ta tadda sakon Mammah daga bakin Dada, rasa me za ta ce ta yi. Ta fito fili ta ce da Dada ba ita ba Abuja, mijinta ya sake ta ko me? Kwata-kwata ba ta son tuna cewa an sake ta kalmar tana yi mata maqaqi a zuciya. Wa za ta gaya wa tsakanin Malam, Mammah da Daada ba tare da hankalinsa ya tashi ba? Ko dai shiru za ta yi ta koma Abujan ta ci gaba da zama gidan Mammah ta cigaba da zuwa makaranta tunda ba za ta iya barin karatunta ba? To amma Yayan Haleem ya sake ki, kuma ki koma ki ci gaba da zama gidan mahaifinsa? Alhalin ba rasa muhallin zama ki ka yi ba? Wata zuciyar ta ce.
Haba Hafsatu? Kada ki zam-makaho warke ka karya sandarka! Har abada ba ki da gidan da ya fi na su Abdulazeez din in har duniya da halacci da amana. Koma gaban Mammah ki ci gaba da karatunki in har za ta barki, ki kuma cika alkawarinki na taimaka wa Abdulazeez ya cimma burinsa...... Wani hanin ga Allah baiwa ne!.
Da wannan shawarar Hafsat ta soma shiri kamar yadda Dada ke ta yi mata itama don komawa Abuja. Sai dai irin hakukuwa da sauyoyin da Dada ke damawa kala-kala tana ba ta, ta ce ta shanye a kan idanunta kasa gane kansu ta yi. Da ta tambaye ta ko magungunan me ta ke bata? Cewa ta yi na gyaran aure ne. Bakinta ta ja ta yi shiru ta ci gaba da shirya yan kayan da ta zo da su wadanda duk sun ji jiki saboda maimaita su da ta yi ta yi tana wankewa kasancewar ba ta debo kaya da yawa ba.
Ana i-gobe Hafsat za ta koma Abuja, Mammah ta kira ta a wayar Dada, ko gaisawa ba su yi ba ta soma yi mata fadan rashin amfani da wayarta da ta ke yi. Hakuri ta yi ta ba ta, ta gaya mata sun yi tafiya zuwa Numan kuma tun zuwanta ba ta zama. Ziyarce-ziyarcen dangi ake raka ta nesa da kusa. Mammah ta karbi uzurinta, ta kuma gaya mata goben jirgi za ta hawo ta dawo. Abdulazeez ba ya kasar, ya je America graduation convocation na Ismael daga jamiar Harvard, daga can za su wuce na Usman a Brussels sai nan da sati biyu za su dawo shi da Ismael da Usman din. Don haka nan Asokoro za ta taho in ya dawo sai su koma gidan nasu.
Wata ajiyar zuciya Hafsat ta yi cikin sanyin murya irin nata ta ce, Toh Mommah, sai Allah ya kawo ni lafiya. A gaida Baba Azumi da Daddy.
Za su ji, ki gaida Dada da Malam da duk mutanen gidan.
Da wannan suka yi sallama.
Washegari Dr. Bashar da kansa da Imamu suka kai Hafsat da kayanta filin jirgin saman Yola, jirgin Azman ta bi zuwa Abuja. Babanta ne ya biya kudin tikitin duk da Mammah ta aiko mata da kudi ta account dinta, ita a wajenta har gobe nauyin Hafsat yana wuyansu ba abin da ya canza.
*SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI
07030137870
*Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama*
*****
Ta sauka a Abuja da misalin karfe shidda na yamma, a reception suka hadu da Salisu direban gidansu ya zo daukanta. Ya karbi kayanta ya sanya a boot ya bude mata murfin motar ta shiga ta zauna ya rufe suka nufo Asokoro.
Suna shigowa tangamemen getdin gidan ta hango Mammah a kofar shiga babban falo tana jiran isowar su. Ta kara kyau, kullum kamar ana kara mata kuruciya, za ka rantse ba ta haifi Haleem ba balle uwa-uba Abdulazeez. Wasu zafafan hawaye na tausayin Hajiya Maryam da ita kanta suka cicciko idanunta. Ta san tana son aurenta da dukkan zuciya da ruhinta, amma ta yi amanna Mammah ta fi ta son wannan auren da dorewarsa. To ya za su yi? Tunda wanda ke da iko da igiyoyin auren ya tsittsinka su? Ba ya sonta! Ba ya bukatar hada rayuwa da ita, dole ita da Mammah su dau dangana su hakurkurtar da zukantansu. Allah ya sa hakan ya zama alkhairi ga rayuwar kowannensu. Ta sa gefen mayafinta a fakaice ta share hawayenta.
Mammah na tsaye aka fito da kayanta na boot ta kasa jiranta ta karaso inda ta ke ta tako ta iso jikin motar ta bude mata kofa. Salisu ya roke ta ta bar masa kayan zai shiga da su. Ta kama hannun Hafsat abinda ta lura da shi jikin Hafsat a matukar sanyaye yake tamkar wadda aka yiwa duka. Idanunta sun kode da alamun ta jima bata sanya musu kwalli ba. Kai in ba ta yi kuskure ba, za ta iya cewa Hafsat ta rame. Ta dai bar komai a cikinta Hafsat din ta samu ta huta.
Dakinta na yammatanci aka shigar da komai nata, a can ta yi wanka ta yi sallah kuma har can Baba Azumi ta kai mata abincinta ba su ce ta zo ta ci a dining ba kamar yadda yake a aladar gidan duk don ta samu nutsuwa.
Ta nemi wata doguwar riga mara nauyi cikin kayanta ta sanya, ta zauna da zummar ta ci abincin, amma duk yadda ta kai da kokarin ganin ta ci din abin ya faskara. Zuciyarta ta yi nisa wajen tunanin yadda za ta nunawa Mammah takardar sakinta! Haka ta saka abincin a gabanta tana kallo kwata-kwata hankalinta ba ya jikinta. Sau biyu Mammah na shigowa jin shirun nata ya yi yawa tana ganinta cikin wannan halin. Azumi ma shigowarta biyu, har suka fita ba ta san sun shigo ba balle fitarsu.
Mammah dakinta ta koma ta yi shiru, daga bisani ta yi kiran Baba Azumi, ta shigo ta zauna gefen uwargijiyarta a kan center carpet, Mammah na gefen gadonta.
Ba ki fahimci Adda na cikin damuwa ba?
Azumi ta gyara zama ta ce, Ni kuwa na fahimci hakan. Har magana na yi mata sau uku ba ta san ina yi ba.
To a ganinki me ke damunta? Ko a da Hafsat da ta san ba ta da kowa sai mu ba ta sanya kanta cikin damuwa ba sai yanzu?
Ba kya tunanin tafiyar mijin ce? Inji Baba Azumi.
Ba ta magana da shi a waya. Ya gaya min rabon da ya yi magana da ita tun a Jimeta. Ta kashe wayarta kwata-kwata tsayin kwanakin nan data yi acan. Da na yi mata fadan kashe wayar cewa ta yi ba ta samun zama, kuma ta je kauye. Shin a wannan zamanin duk inda ka je za ka kasa yin muamala da waya? Balle ka kasa magana da mijin aurenka tsayin sati biyu?
Duk sai suka yi shiru. Daga bisani Azumi ta ce
Ina tunanin matsala ce suka samu a tsakaninsu.
Mammah ta runtse ido kadan ba ta ce komai ba, amma ta yarda da abin da ta ce din.
Ki zuba musu ido Maman Haleem, kada ki tambaya, kada ki bi baasi. Tsakanin mace da miji sai Allah. Sanda za su shirya kansu ba za ki sani ba.
Zuciyar Hajiya Maryam babu dadi, ta ce, Haka ne. Amma can a karkashin zuciyarta tana jin ba dadi, sanin cewa auren Abdulazeez da Suhaana ba normal auren so ba ne. Sai dai ya taho da nasara fiye da yadda ta tsammatar masa. Tana tsoron duk wata matsala da ka iya tasowa a cikinsa.
“Ya Rabbi Sallim!
Ta furta a fili bayan fitar Azumi daga dakinta.
******
Kwanan Hafsat biyu kenan da dawowa daga Jimeta. Mammah na lure da ita, ba abin da ya canza cikin yanayin da ta dawo da shi, sannan ko sau daya ba ta ga ta jona wayarta a caji ba balle ta kunna. Washegarin ranar suka koma makaranta. Hafsat ta sani, amma ko alama ba ta yi wa Mammah zancen ba. Ji ta yi karatun kansa ya fita a ranta, duk wani buri da ta ci masa ya zagwanye. Ashe karatu ba shi ne farin cikin rayuwa ba? Ashe akwai abin da yamace ta fi bukata a rayuwarta fiye da karatun boko? Ashe ba abin da ya fi muni ga rayuwar diya mace fiye da sakin da ada ta ke ganin ba komai ba ne? Ashe tsakanin zuciyarta da Abdulazeez soyayyah ce kuma kauna ce mai tsananin da zuciyarta ta kasa karbar rabuwa da shi da sauki???
Duka a bandaki (toilet) ta ke wannan tunanin, ta shiga da zummar wanka, amma sai ta bige da zama a kan (soak-away) ta shiga shesshekar kuka, kukan da a baya ba ta yi ba tun ganin takardar sakinta. Koyaushe cikin mutane ta ke a Jimeta ko gaban kakanninta, suna yi mata hirarrakin uwarta da ke debe mata kaso 80% na tunanin Abdulazeez da karewar KWANGILARsu. Yanzu ne komai ya rufto mata take jin kanta cikin wata irin kewa mara misaltuwa. Tamkar ta rasa komai na jin dadin duniya, tamkar ta rasa komai data taba mallaka a rayuwarta.Zamanta cikin gidansu da kasancewarta kusa da wadda ta fi kowa kusanci da shi a duniya ya maido komai sabo kuma danye a zuciyarta, ya maido mata komai baya na rayuwarda ta yi da shi ta shekara da watanni.Yadda shekarar ta kasance dalla-dalla a kan tafin hannunta....... Daga rayuwar DUHU zuwa rayuwa mai HASKE kafin ta karkare ta koma DUHU dudum a halin yanzu kenan da wannan rayuwar taduhu da haske ta kare bakidaya. Sai dai duk ta inda zuciyarta ta karkata don baiwa Abdulazeez laifi Hafsat ta ki karba, zuciyar mai so da kaunar Abdulazeez kare shi ta ke yi. A bisa dalili da dama da hujjojinta kwarara!
Muhimmi cikin hujjojinta shine;Abdulazeez bai taba yaudararta da cewa za su dore da rayuwar aurensu ba! Bai taba yaudararta da kalmar SO ba. Zuciyarta ce ta zarme zuwa ga son abinda yafi karfinta.... ta zamo out of her controlta jefa ta cikin matsananciyar soyayya da kaunar Abdulazeez din data ke da tabbacin baya son ta. Ba ta yarda da hakan ba sai yau da suka rabu, auren kwangilar ya kare! A yau ta yarda cewa ta dauki lokaci mai tsawo cikin soyayyar Abdulazeez Dakata ba tare da saninta ba. Wani kwantaccen so mai bin jiki da jijiya. Ba ta fahimci hakan ba sai a kurarren lokaci, lokacin da ya zamo haramiyarta...!!!
Fuskarta ta sanya cikin tafukanta ta dinga kuka wanda ke fitowa tun daga karkashin zuciyarta.
Shigowar Hajiya Maryam na uku kenan dakin tana komawa ta fita da sauri, saboda zuciyarta da ta kasa jure sauraron irin kukan da Hafsat din ke yi. Ta koma dakinta jikinta har rawa yake yi. Babu wanda zai tada hankalin Hafsat, ya jefa ta cikin wannan halin in ba mijinta Abdulazeez ba, tunda wa ta ke da shi bayan iyayenta da su in ba shi ba? Babu wanda zai bata mata rai a Jimeta! Zuciyarta na son daukar waya ta kira shi, wata zuciyar na hana ta.So ta ke ta ce da shi da ka bata min ran marainiyar Allah Addah yar amana ta, gara ni ka bata nawa ran. Ta tuna shawarar da Baba Azumi ta bata; Kada ta shiga, kada tatambaya, kada ta bi baasi. Baba Azumi ba yar aiki ce kawai agareta ba yanzu, uwa ce a gareta, kuma wanda ya riga ka kwana dole ya riga ka tashi. Bataso ta yarda da kaso mafi rinjaye na zuciyarta da ke cewa, Abdulazeez ba ya son Hafsat har yanzu....... damuwar Hafsat kenan.
Shigowar Daddy dakin nata yana tambayar wasu mukullansa ya sa ta farfadowa daga zazzafan tunanin da ta fada, wanda zuwa yanzu ya fara tafarfasa zuciyarta. Dagowa ta yi a hankali ta dube shi idanunta jazir. Da sauri Dr. Hamza ya karasa shigowa dakin, Lafiya Maryama? Me ya faru? Mutuwa aka yi? Ya kama dukkan hannayenta biyu ya rike cikin nasa. Ganin yadda hankalinsa ya tashi da ganin yanayinta ya sa ta nemo wa kanta murmushi wanda bai wuce iya fatar bakinta ba.
Bai kamata ta ce masa komai ba, tunda itama ba ta san me ke faruwa din ba. Ga shi Baba Azumi ta ce ta ba su lokaci, watakila da ya dawo sun koma gidansu komai zai wuce, ko harshe da hakori ai ana sabawa. Ita da ta yi auren soyayya da Prof. Hamza wane irin bacin rai ne bai jefa ta a ciki ba, kuma ta jure sun zauna a haka har aka zo gejin da bacin ran nata shi ne abu na karshe da yake guje mawa?
Hafsat ce ba ta jin dadi. Ta fada a hankali yadda zai kwantar da hankalinsa.
Ya ce, Ai sai ku je asibiti a duba ta, ba ki zauna kina tagumi da jan ido ba.
Ya dauki mukullayensa a kan lokar gadonta, ya juya. Har ya kai bakin kofa ya kama marikin kofar sai ya juyo da murmushi a kan fuskarsa.
Ko amarya zan samu ne kwanan nan aka gaya min indirectly?
Duk yanayin da ta ke ciki sai da ta yi murmushi, a zuciyarta ta ce, Ina ma hakan ne!
Sai dai a matsayinta na mace, kuma babba ba ta ga wani alamu na juna biyu a tare da Hafsan ba. Jin ba ta ce komai ba ya lura kuma ba ta son magana sai ya fita, zuciyarsa na gaya masa kamar ta sakaya masa wani abu, amma ko ma mene ne in ta yi wari da bakinta za ta fada mishi.
Haka suka zauna a gidan su uku tsayin sati biyun, ba sa ummm ba sa umm-umm. Baba Azumi ce kadai ke yi musu hira. Ita ma idan tayi-tayi ta rasa mai tayata sai ta yi shiru. Ana i-gobe Abdulazeez da su Ismael za su dawo Hajiya Maryam ta ce wa Hafsat ta shirya ta koma gidanta, su tafi da Baba Azumi don ta taya ta su yi tiding gidan ta kwana, za ta turo Salisu ya dauke ta in Abdulazeez ya sauka a Abuja.
Hajiya Maryam na ganin yadda Hafsat ta kidime ta rikice, ta gigice, a karshe ma kasa zaman wurin ta yi