Showing 105001 words to 108000 words out of 168255 words

Chapter 36 - Auren Kwangila Book 4 Hausa Novel Complete

Takori   

12 Dec 2024

318

har ta kai da haka? Shekara daya da watanni rututu ba kwana daya ba. Mikewa ta yi a azama ta bar dakin ta yi dakin Dr. Hamza.
Kallon news yake lokacin da ta shiga, sallama ma a cikinta ta yi ta. Gefensa ta zauna ta dafe kanta tana jujjuyawa. Remote ya sanya ya rage sautin talabijin din ya fuskance ta. Daddy ni wawuyar ina ce yaron nan ya yi wasa da hankalina har haka? Ko hakkin aure bai taba bata ba. Allah shi ne shaida ban hada wannan aure don in zalunci wani a cikinsu ba. But for the betterment of all of them. Ya wahalar da ni a banza! Ya bata min lokaci da aljihu da zuciyata duk a banza! Ba zan yi masa baki ba, amma ka zama shaida ko ya dawo daga baya ya ce in maida masa Hafsatu ko bayan raina aka maida ban yafe ba! Yau da yawun bakina ka aura wa Abdulazeez duk macen da yake so.
Tun dawowarta daga asibiti ba su zauna sun yi maganar ba, ko ta taso da ita katse ta yake ya ce sai ta samu lafiya. Murmushi ya yi irin nasu na manya, maabota wayewar kai da tsinkaye ya kira sunanta a tausashe.
Maryama, ni fa na dade da sanin Abdulazeez bai bar neman auren yarinyar nan ba ko bayan aurensa da Hafsatu.
Cikin madaukakin mamaki ta saki baki tana kallonsa. Nan ya gaya mata tattakin da mahaifin Muazatu ya yi har ofishinsa ya ce Muazatu ta gama Law-school in sun shirya su fito a yi aure. Amsar da ya ba shi cewa yanzun akwai wani uzuri a gaban yaron in ya gama da shi zai yi magana. Ya ce da ita.
Ta inda za ki gane ba da zuciya daya ya yi auren nan ba shi ne, saurin amincewarsa. Bayan a fili ya nuna kuma ya fada ba ya sonta, ga wadda yake so. In kin ci gaba da bincikarsu za ki gano bakinsu daya, akwai abin da suka shirya a boye ko daga wasikarsa da yadda ta dage wajen kare shi, da son na aura masa Muazatun. They have their own target, so ina so ki kwantar da hankalinki, ki bar sanya wa kanki ciwo a banza. Tarkonki ya riga ya yi kamu cikin shekara dayan da sukayi taren. Ki gode wa Allah ki kara binsu da addua, kuma ki fita daga sabgarsu.
Kare shi da ta ke yi alamomi ne na kauna da soyayya, ko shi kin ji ya zo ya doshe ni da zancen tsohuwar budurwarsa? Ni kuma zan ba shi mamaki, sai na aura masa ita!!!

******
Washegari da magriba da ya taso aiki gidan ya zarto. Kallo daya Mammah ta yi masa sai da gabanta ya fadi. Allah kadai ya san rabonsa da kwakkwaran abinci, a kwayar idanunsa ta ke gane yunwar cikinsa. Ya yi baki ya rame da ma jikin ba wani jiki ba. Dogon hancin ya kara zama pointed a tsakiyar fuskarsa. Lumsassun idanun sun kara fadawa ciki sun zurma ciki sosai sai suka kara zama oily sabida shekin da suke fitarwa, sun canza launi daga farare zuwa grey-greyhaka. Yana shigowa falon inda Mamman ta ke zaune ya nufo, a gefen kafafunta ya zauna ya gaishe ta.
Abu daya ya sa ta amsawa ganin Ismael da Usman sun bi ta da appealinglook, sun marairaice idanu suna dubanta kamar su suka yi laifin. Hafsat na can kusa da T.V da zurmemen hijabinta da carbi a hannunta, idar da sallarsu ta magriba kenan. Ya samu kujerar darare gefen Usman ya zauna ganin yadda Mammah ke cika tana batsewa.
Tunda Hafsat ta ji muryanshi a falon da scent dinsa ba ta kara wani kwakkwaran motsi ba, ba ta juyo ba balle ta kalle shi. Ta ji yadda muryarshi ta kara sirancewa. Zuciyarta ta soma wani irin harbawa tana fama da kai-kawonta cikin kirjinta. Daddy ya shigo falon rike da brief-case dinsa ya mike ya karba kowa ya yi masa sannu da zuwa, ya wuce part dinsa kai tsaye. Abdulazeez na biye da shi. Mammah ta nufi kitchen wajen Baba Azumi ta ce ta hada wa wancan mutumin abinci, amma ba in ji ta ba. Murmushi Azumi ta yi, ta ce.
Ya ci albarkacin ya taba auren yarki ma ai wani abu ne Mammah.
Hararar Azumin ta yi, ta yi wucewarta daki. Azumi ta yi murmushi tana girmama hali na dattaku da karimci irin na uwargijiyarta, nata ba nata ba ne, na wani shi ne nata. Irinsu kuwa yayansu ba sa tozarta a rayuwa. Ta san Abdulazeez ya yi laifi da ya cancanci kowanne irin hukunci daga gare ta, amma ba ta jin dadin yadda ta yi watsi da shi gabadaya da duk wani alamarinshi. Ta tabbata ko bai fada ba yana can yana tunanin yadda zai yi ya gyara kuskurensa.
Ta roke ta ta bashi dama ko da ita ce ta karshe. Ba wanda yake sama da aikata kuskure a wannan duniyar tamu? Wasu lokutan daga kurakuranmu muke gane yadda za mu tari rayuwa a gaba. Amma Mammah ta fito fili tace da ita kada ta kara yi mata maganar Abdulazeez. Wannan ya zamo na farko kuma na karshe. Don haka yau ba karamin dadi ta ji ba ganin ta ce a bashi abinci.Duk da tace ba in ji ta ba. Duk fushin uwa bata iya jure yunwar cikin dan ta. Azumi ta fada a fili cikin madafin (kitcen) a lokacin da takezubawa Abdulazeez abinci mai rai da motsi.
Daddy ya dube shi cikin nutsuwa, fuskarsa fayau babu alamun wata damuwa ko bacin raiya ce. Mun gama magana da Kawu Abdulkarim zai je nema maka auren a Lagos din, gobe in Allah ya kaimu zai tafi ta jirgi, kuma insha Allah abin ba zai dauki lokaci ba, ko don ka samu nutsuwa. Daga ganinka ko abinci ba ka samu. Mun yarda da kaddara kuma mun karbe ta da hannu bibbiyu. Ka yi hakuri mun takura rayuwarka da auren da ba ka so, we never know rashin son ka da Hafsat mai zafi ne har haka. Allah ya sanya albarka a auren da zaka yi. Ita kuma Hafsan Allah ya musanya mata da mafi alkhairi.
Ga mamakin Daddy hawaye ya kama yi. Hawaye sosai kamar an bude famfo. Wani abu da bazai iya tuna lokaci na karshe da ya gani daga idanun Abdulazeez ba, har a lokacin yarintarsa. Dr. Hamza ya yi biris da shi kamar bai san yana yi ba ya shiga tattara wasu takardu a kan center-table yana zuba su cikin files.
Muryar Abdulazeez cikin rauni ya tsinkaya a tsakar kansa.
Daddy, ni na ce ka nema min aure?
Ba tare da ya juyo ya dube shi ba ya amsa. Hafsat ta nemi ayi mata wannan alfarmar, roko mai dimbin yawa.A yanzu kam ba abinda zata roka mu kasa yi mata don mun gurgunta mata rayuwa. Mun kuma fahimci har gobe kana son yarinyar nan yar Attorney-General Habibu Rufai dalilin rabuwarku kenan. Ko ba don haka ba sai in barka kai kadai a gida bayan ka saki matarka? Yadda Abuja ta lalace din nan zan zuba maka ido ka zauna kai kadai bayan ka dandana auren ka san dadinsa da rashin dadinsa?
Cikin dusashshiyar murya da kuka ya karar da karsashinta ya ce. Daddy ni fa tun washegarin da na yi sakin na maida aurena, ban ganta ba ne balle in gaya mata, sannan ba ta rike waya balle in kira ta.
Wani sakaran kallo Dr. Hamza ya yi masa. Da ma auren yarjejeniya aure ne?
Wani busasshen miyau ya hadiye mai azabar daci, Daddy ka fahimce ni don Allah, its a mistake, ka gaya wa Mammah na tuba na bi Allah na bi ku. I want my wife back.
Daddy ya ce, Aaha! Ni me ye nawa a ciki? Can muku kai da uwarka, ni dan daura aure ne in biya sadaki, kuma na damkawa waliyinka Abdulkarim ya kai Legas. Na sauke duty na as a fathera karo na biyu ban barka ba aure ba. Na yi maka abin da ranka ke so, in ba ka gode min ba akalla kada ka sa ni ciwon kai. Na dauka makaman yakinmu muka zubar muka yi maka abin da ka ke so don a zauna lafiya? Me ya sa dan Adam baa iya masa? Ko kana nufin ka ce ka fasa auren Muazatun bayan ka yi mata alkawarin za ka saki matarka ka aure ta?
Kai tsaye ya ce Daddy na fasa, wallahi Hafsat na ke so. Ku yi min alfarma Daddy one last chance!.
Zama sosai Dr. Hamza ya yi, ya ce, Kuma? To ba ka isa ba. Ba za ka maida ni karamin mutum ba. Ka sa a ranka ka auri yar Attorney ka gama, kai da wadda ba ka so kuma kun yi sallama ta har abada.
Ya shige bedroom dinsa ya barshi anan.
Ya dade a zaune ya rasa ta inda zai fara tunanin rayuwa da wata mace cikin gidansa ba wannan mamallakiyar gidan ba, wadda aka gina gidan da sunanta ta tsara abunta yadda ta ke so, uwarta ta shirya mata shi daidai da burin ta, ta ke kwana ta ke wuni tana tsaftace shi da kamsasa shi, ta zauna da shi cikin kyautatawa da karimci. Ta sayo wa kanta kauna da soyayya ba tare da kowa ya koyar da ita ba. Ya shiga tunano abubuwan da yake hangowa a Muazatu; ba wani abu ba ne banda zaton she will be very good in bed. A zamansa da Hafsat da dan physical releationship din da ya shiga tsakaninsu ya gane ba abu mafi dadi da ban shaawa ga Da namijin da ya san ciwon kansa, irin ya mallaki mace innocentwadda bata san komai a wannan fannin ba, mai asalin YAKANAH (sunan wani littafin Takori)maabociyar alkunya ga mijin aurenta, take kuma tsananin kaunarsa a karkashin zuciyarta ba tareda ta fito da hakan a sarari ba saida ya fahimta cikn reactions dinta, emotions dinta da kwayar idanunta. Inyaso shi da kansa ya koyar da ita yadda yake so ta zama ba wadda ta shigo da iyawarta tun daga waje ba.... he cursed his previous perception (Ya tsinewa tunaninsa na baya).
Haka ya mike cikin matsanancin sanyin jiki da na gwiwa. Ganin cewa Tsohon Ambasadan ba zai kuma sauraron komai daga gareshi ba, ya shiga ratsa falullukan gidansu yana wucewa. Bai tadda kowa a falon farko ba inda nan alummar gidan suka fi zama. Yana kallon abincin da Azumi ta ajiye masa amma ba ya jin ko ruwa zai iya kurba a gidan nan. Har zai fice ya ji kamar an fizgo shi an dawo da shi baya. Zai ga Hafsat a yau kuma a gidannanno matter whatya jaddada mata ya maidata dakin ta tana so ko bata so tunda don haka taki kunna wayarta, ya kuma ji daga bakinta; shin ta amince da hukuncin Daddy da Mammah? Ya auri Muazatu akan dole a raba su har abada???
Kai tsaye dakinta ya nufa ko gabansa ba ya gani sosai. Wata mahaukaciyar soyayya ke dawainiya da shi. Wannan kuma alkawarin Allah ne, duk namijin da ya saki matarsa babu kwakkwaran dalili sai Ubangiji ya hukunta shi da soyayyarta.
Fitowarta daga wanka kenan, ta zauna gaban mirrow tana shafa lotion na (cocoa butter) a jikinta, daure da faffadan towel har gwiwarta. Da ta gama kuma kayan barci za ta sanya ta kwanta. Ji ta yi an murdo kofar a hankali an shigo. Ta yi zaton ganin daya daga cikin mutum biyu; Mammah ko Baba Azumi, tunda su ne kadai masu shigowa dakinnata.Amma su kam suna sallama ai har su jira a basu izni. Saidai me? Dagowar nan da zata yida wa zata yi arba? Abdulazeez ne; Her Ex- Abdulazeez, Eh... ta kira shi Ex don kalmar da ta dace da su yanzu kenan. Takaitaccen kallo daya ta yi masa ta dauke kanta. A cikin takaitaccen kallon data yi masan wasu rikitattun alamura da dama ta gano a tare da shi irin wadanda bata taba gani ba cikin kwayan idanunsa. Amma wannan ba shi ne a gabanta ba, yanayin da ya shigo ya same ta ne sanin cewa yanzun ba muharraminta ba ne, kuma tsakaninta da wardrove da nisa, idan kuma ta mike tamkar ta yi hakan da gayya ne har gara ma ta ci gaba da zamanta a yadda take kuma a inda take. Sunkuyar da kanta ta yi tana tuno yadda Yaya Azeez ya iya rufe ido ya rubuta mata saki, duk irin zaman amincin da suka yi.Ai ko da yarjejeniya akwai wani abu da bahaushe ke mutuntawa in relationship da ya kira da suna sabo turken wawa kuma dai ma ai haram baya haramta halaal, kawai saboda wata banzar budurwarsa. Ta tuno bakin cikin Muazatu da ta dinga kwankwada daga gare shi launi-launi kamar wadda bata da tsokar zuciya a cikin kirjinta.Ko ita mayya ce ta hakura da Abdulazeez Dakata! Za ta cika wa Daddy duk alkawurrukan da ta daukar masa, Allah ya hada kowa da rabonsa na alheri.......!!!
Ji ta yi kawai kuka ya zo mata,kukan da bata shurya yinsa ba bata kuma so zuwansa ba, domin zai nuna rauninta wanda a yanzu take jin bata da shi indai akan Abdulazeez ne, kokari take ta maida hawayen kada ta barsu su zubo har yayi zaton tana da damuwa akansa. Abdulazeez jingine kawai yake a jikin kofa ya zuba mata shanyayyun idanunsa da suka kara kankancewa. Wani dunkulallen abu da ya tsaya masa a makogaro tun rabuwarsuyaki wucewa ya ji yana narkewa yana (dissolving gradually). Hafsat ba ta ankara da yaushe Abdulazeez ya tako har ya iso gabanta ba. Abin da ta fahimta kawai shi neta ji sanda ya mikar da ita tsaye a lokacin da bata zata ba, sai kuma ta tsinci kanta gabadayanannade cikin jikinsa ya zagayeta da dukkan hannayensa yayi mata kyakkyawan masauki a physique chestdinsa. Wani bigire da ba za ta iya mance duniyar da yake jefa ta ba duk da hakan ya faru ne sau bai fi ta kirga ba. The familiar scent of ‘Creed Aventus, his heart beats and hers...suka taru suka maida itadevastated suka soma yakar duk wani alwashi da ta ci a kansa cikin dan kankanin lokaci. Ba ta gama farfadowa daga wannan duniyar ba ta ji Abdulazeez ya soma sumbatar duk inda bakinsa ke iya kaiwa daga dogon wuyanta zuwa fuskarta,a karshe bakinta ya zama final destinationdinsa sai da ta nemi numfashinta da hayyacinta na wucin-gadi ta rasa. Can tsakar kanta kalaman nan nasa suka soma amsa-kuwwa..... Na sake ki ba don bana sonki ba...... rauni na guda daya ne; ina son MUAZATU!
Kokarin kwatar kai ta soma yi, ganin alamarin na neman shallake karfi da iyawarta sai ta sa kuka.Kukan da ta san, shi kadai ke kwatarta daga hannun Abdulazeez a duk lokacin da irin haka ta faru.Tamkar wanda aka yi wa allurar kashe kuzari sai ya dakata amma ba tare da ya raba ta da jikinsa ba, hot kisses din da yake blusteringaggressively ya daina. Ya maida kanta kan kafadunsa.Ga mamakinta samun kanta tayi da kwanciya sosai a kafadun nasa..kamar dama canjiran wannan damar take yi.Kasancewar ya kere ta a tsawo sai da ya rankwafa, hakan sai ya zamanto tamkar ya boye ta ne gabadaya cikin jikinsa. Cikin kunnenta da muryarsa mai tsananin taushi da yawan kashe mata jiki yace da ita.
“Are we still friends?
Shiru Hafsat ta yi kamar ruwa ya cinye ta, ruwan hawayenta sai ya kara yawa da jin kalamansa yana sauka a gadon bayansa. Janye jikinta ta yi a hankali ta durkushe a kan kafafunta, shi ma sai ya bi ta ya tsugunna a gabanta irin tsugunnon neman afuwa. Fuskarta ta sanya a tsakanin cinyoyinta ta ki dagowa ta kalle shi. Sake tausasa muryarshi ya yi ya rankwafa saitin kunnenta.
“Hafsat and Abdulazeez are meant to be together forever! Auren kwangilar, ya kare ne don ya gyara auren,ya tsaftace shi daga kuskuren da aka tafka wajen gina shi, ki sa wannan a ranki. So please ki kyale zuciyarki ta huta ta samu abinda ta ke so, ki daina takura mata a banza. I know it will hurt, but you donno how much it deeply hurtthe culprit.(Nasan laifin nawa da ciwo, amma baki san yadda yake azabtar da mai laifin ba). Yadda tawa zuciyar ta kasa zama lafiya kema taki ba za ta taba zama ba sai ta dawo ga mamallakinta. Zan barki ki kwanta Hafsat, sai da safe. Amma ki yi min alfarma ki kunna wayarki, I just want to be saying good night. Zan samu Hafsah???
Nan ma shiru, kamar da dutse yake magana, kuma ta ki dagowa. A wurin Hafsat in ma da gaske Abdulazeez yake maganganun da yake yi ya zo a matukar makare (very late) lokacin da zuciyarta ta riga ta kangare da karbar rayuwa a duk yadda tazo mata. Ta riga ta koya mata hakura dashi da duk dadi duk wuya daga lokacin da ya gaya matain written (a rubuce) ya zabi Muazatu akan ta. Cikin damuwa ya ce.
Hafsat in ba ki dago kin amsa ni ba, ki tabbata zan kwana a dakinki. I will make sure na yi abin da Mammanki za ta maida min ke a gobe. Zan yi abin da na shekara ban taba yia nawa gidan bayau a gidanta. Wallahi Hafsat da gaske nake, za mu yi first night dinmu yau a dakin nan idan ba ki dago kin min magana ba.
Daga intonation din muryarshi ta fahimci babu wasa cikin alamarinsa, wani irin tsoro ya shige ta da tashin hankali. Ta cira kai daga tsakankanin cinyoyinta ta dago, amma ba ta dube shi ba, fuskar nan murtuk kamar hadarin gabas idanunta sun yi jazir sabida kukan da ta ci. Cikin ranta ta riga ta ci alwashin yaki da zuciyarta in dai a kan Abdulazeez ne, bata jin yanada sauran kalaman da zai kassara ta dasu. Bashi da ragowar kowanneremnant(small remaining) birbishin soyayyaa tareda ita da zai sake tasiri akanta.
Wai shin ba ta basu fili ba shi da Muazatun tasa, ta bar musu gidansu kamar yadda ya bukata, ta fita daga cikin rayuwarsa da yace bata da gurbi? Me ya kawo shi inda ta ke yanzu?
Abdulazeez bai yi kama da mayaudara ba, bashi da attributes dinsu ko daya, bai taba yaudararta ba ko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login