Showing 81001 words to 84000 words out of 168255 words

Chapter 28 - Auren Kwangila Book 4 Hausa Novel Complete

Takori   

12 Dec 2024

669

lokaci sai gudu yake yi yana tunatar da shi manyan alamuran da ke gabansa. Tafe yake daga masallaci zuwa gida yana tuki a hankali yana tunani cikin neman mafita ga rayuwarsa. Yadda yake tafiyar da motar tsammani za ka yi tayoyinta sun lalace ne. A haka dai har Allah ya nufa ya zo gida.
Yadda ya bar gidan haka ya dawo ya same shi. Ya fahimci Hafsat ba ta fito ba. Dakin nata ya leka duk jikinsa a sanyaye yake, tana durkushe a kan sallaya ita ba sallah ba, ita ba barci ba. Ya dade rike da murfin kofar yana kallonta, abubuwan da suka far a dakin mintuna kalilan da suka gabata na dawo masa. Wani gajeren lokaci ne da ya kasa gushewa a cikin rai da zuciyarsa. Ajiyar zuciya mai nauyi ta subuce masa, wadda ta ankarar da Addah wanzuwarsa a dakin, duk da kafin hakan kamshin jikinsa ya ziyarci hancinta. Ba ta kawo shi ba ne, saboda yadda suka cakuda da juna a yau sosai ita kanta kamshin creed aventus ta koma yi bakidayanta. Kasa dagowa ta yi ta dube shi sabida nauyinsa da ta samu kanta a ciki tun faruwar alamarin. Kamar wannan shi ne karo na farko, sai da ya kira sunanta.
Dagowa ta yi ta zauna sosai ta dafe gado da hannunta na dama, amma ga mamakinta ta kasa kallonshi. Murmushi ya yi ya shigo har tsakiyar dakin ya tsaya, hannayensa duka biyu zube cikin aljihun bakin jeans din da ke jikinsa.
Yau da wuri zan kwanta, saboda gobe lahadi ina so zan yi sammako, za mu je jihar Adamawa daurin auren kanin wani abokin aikina a Yola, zan samu abokiyar kwana a dakina? Bana jin dadin jikina, ina tsoron kada cikin dare zazzabi ya rufe ni.
Kunkuni ta hau yi tana zumburo baki,kaji wani sabon batu, ya kasa jin me ta ke cewa.
Sake matsowa ya yi ya zauna a gefen gadon daidai hannunta. Da sauri ta janye hannun, Aah Hafsah na fara cizo ne?
Ta yi masa shiru.
To zan samu yar tayin kwanan?
Sunkuyar da kai ta yi tana magana ciki-ciki, sauka ya yi daga gefen gadon ya zauna a gabanta sosai ko ya fahimci me take cewa. Ta yi saurin ja da baya. Da mamaki yake kallonta, ta sunkuyar da kai ta ki yarda su hada ido.
Wani abu ya faru ne bayan na fita? Ya tambaya da murya ta nutsuwa.
Girgiza kai ta yi, Ba abin da ya faru.
Ya ce, Na ga kina ta guduna ne, Hafsat yaushe ta kaimu da haka?
Kwalla ya hango ta taru a gefen idonta tana ta kokarin maida ita. Kafin ta ankara ya dago fuskarta sai kawai ta sake su ta ba su damar silalowa.
“Yaa Sattaru Sutrukal jameel. A fitata da dawowata na yi wani abu da ya bata miki rai?
Girgiza kai ta yi.
To tashi mu je na ce ki taya ni kwana, ina da tafiya gobe da asuba saboda a yammacin gobe za mu dawo.
Mikewa ta yi ba don ranta na so ba sai don a dan zamanta da shi ta fahimci shi mutum ne mai naci a kan abin da ya sa kansa, ba ya niyyar abu ya fasa. Wardrove dinta ta bude ta dauko kayan barci masu kauri ta shige toilet, brush ta fara yi sannan ta yi wanka ta sanya su. Kanta cikin shower-cap ta fito sai digar ruwa ta ke. Fatar jikinta ta kara yin fresh, ga mamakinta har zuwa wannan lokacin yana zaune a gefen gadonta, wayarta da ta sanya a caji ce rike a hannunsa, gallery din wayar ya shiga. Hotunansa ne duk a ciki wadanda Ismael ya turo mata da wadanda bai san a ina ta same su ba. Ga kuma na dinner dinsu da aka yi a A-Class.
Dagowa ya yi da zummar tambayarta inda ta same su, amma sai ya ji harshensa ya sarke. Kai ka ce ta fito ne daga jinsin Somali. Wayar ta subuce daga hannunsa ta fadi kasa. Turo baki ta yi tana tambayarsa don me yake mata bincike a waya? Budar bakinsa sai cewa ya yi, Don na isa!
Ta sake cuno bakin ta tsugunna a gabansa za ta dauki wayarta, ya ce, Wallahi ki ka sake cuno min baki I will kiss it...
Yadda ya ja lafazin kiiiiiissss din ya sanya ta ba shiri maida bakinta daidai. Za ta mike ya take hannunta mai rike da wayar. Wata yar kara ta saki, Yayan Haleem za ka ji min ciwo.
Ki gaya min abin da ki ke fadi don na ce ki taya ni kwana.
Ta runtse ido don zafi don sosai yake murje mata yatsu da yatsun kafarsa. Da sauri ta ce, Ba fa wani abu na ce ba, cewa na yi sai dai in a kwanta kai da kafa.
Me ye kwanciya kai da kafa?
Don Allah ka daga min hannu, sai in maka bayani.
Tausayi ta ba shi sosai ganin yadda idonta har ya tara hawaye. Hannun ya kamo ya rike cikin nasa yana murza mata, abinki da farin mutum har ya yi jajawur. Ta matse kwalla da hannun hagunta, So sorry! Ya ce, sake zumburo baki ta yi. Amma data tuna abinda ya fada yanzunnan tayi maza ta gyara shi.
Yi min bayani ina jinki, mene ne kwanciya kai da kafa?
Ka sanya kanka inda na ajiye kafata, ko ni in sanya inda ka ajiye kafarka.
Dariya Abdulazeez ya yi, Saboda me to?
Ta yi shiru tare da kwace hannunta ganin ya fara canza yanayin murza mata yatsun, wayarta ta dauka ta yi gaba. Ya bi bayanta.
Sai da ya rufe koina na gidan ya kashe wuta da kayan wuta, sannan ya same ta a dakin. Ta jefa filo a kan resting chair ta yi kwanciyarta ta rufa da zanin atamfarta. Yana shigowa ya ce,
Me ya yi zafi na kwana a kujera Hansatuwa Addar Mammanta? Na yarda a yi kwanciyar kai da kafa.
Tashi ta yi tana murmushi jin sunan da ya kira ta da shi, Ka yi alkawari?
Alkawarin me?
Ba za ka canza position din kwanciyar ba.
Na yi alkawari Hafsat, amma in kafata ta tsokale miki ido ba ruwana.
Kana juye-juye ne in kana barci?
Juye-juye kai! Har da mirgine-mirgine.
To ni zan je karshen gado, kai kuma ka zauna a farko, kuma still kai da kafa.
In aka yi hakan bargon ba zai ishe mu ba.
Dauko wani, kowa ya rufa da guda daya.
Ya marairaice fuska, Ga shi kuma guda daya ne Babana ya sai min, ke ce Mammanki ta saya miki da yawa.
To bari in je in dauko nawa.
Ok, go.
Ta mike ta nufi kofa ta murda ta fita. Da dan banzan gudu ta dawo ganin wani uban duhu. Gabadaya fitilun gidan ya kashe bai bar ko guda daya ba. Dariya sosai Abdulazeez yake yi. Ya mike ya isa ga dan firjinsa, madarar oldenburger fresh milk ya zubo a kofi ya kawo mata. Zama ta yi a gefen gadon tana ta fushin dariyar da yake mata.
Mika mata ya yi, Karbi ki sha, ba kyau kwana da yunwa, daga ni har ke ba mu yi dinner ba.
Ba musu ta karba ta kwankwade, ya kara mata ta shanye ta ba shi kofin ta haye can karshen gadon ta nufa da zanin atamfarta. Zama ya yi a farkon gadon yana shan madarar a hankali.
Dauki duvet din ki rufa ke daya na bar miki.
Ta kuwa janye ta kudundune a cikinsa. Shi ina zai iya rufa da wani quiltbayan zai kwana cikin zafi babu AC sabida ita? Dama tsokanar ta yakeyi. Sai da ya gama abin da zai yi, ya yi addua, sannan ya yi (light off) ya kwanta.
Shi ya tashe ta da asubah suka yi sallah tare. Cikin sauri ya yi wanka ya shirya cikin farar shaddah kal yar ciki da babban riga, ya kafa hula zanna-bukar ya daura agogon rolex a damtsen hannunsa duk Hafsat na kallonsa. Lokar jikin gadonsa ya janyo ya dauko wani tsohon envelope da yake ta boyonsa ya sa a aljihunsa.
Turare ya dauka yana fesawa sai ganin Hafsat ya yi a gabansa, ta mika hannu ta karbi turaren daga hannunsa ta shiga fesa mashi. Daga shi har ita murmushi suka kama yi, wanda ba su san dalilinsa ba. Sai da ya rike hannunta mai turaren don ya yi masa yawa. Kallon juna suka yi na yan sakanni kafin Hafsat ta sunkuyar da kanta. Horn din mota suka ji diiiit-diiit! daga bakin gate Sagir na jira. Da sauri ya saki hannun Hafsat ya sumbaci goshinta ya juya da sauri ya fita.
Shafo wajen ta yi, ta sa wa yatsun ido tana kallo. Ba ta san dalilin murmushinta ba. A fili ta ke yi musu adduar dawowa lafiya. Gadon Abdulazeez ta koma ta haye ta yi kwanciyarta tare da nannadewa cikin duvet dinsa wadanda ba sa komai sai tashin kamshinsa.
A yinin ranar bakidaya kasa tsinana komai ta yi, kewarsa ta ke yadda harshenta ba zai iya bayyanawa ba.
*****



To fah! Ga AUREN KWANGILA ya dauko wani sabon salo, ko yaya zaa kare??? Ni kaina ban sani ba!!!
Nayi muku alkawarin cigaban bazai jima ba.







SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI
07030137870

*Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama* ***
A JIMETA
Jirgin Arik ya sauke Abdulazeez da Sagir a Jihar Adamawa (Yola), karon Abdulazeez na farko da zuwa Adamawa a rayuwarsa. Kai shi a jihohin Nigeria bakidaya zai iya kirga wadanda kafarsa ta taka, wadanda karatu ya kai shi (Ibadan, Lagos), sai ko mahaifar iyayensa (Kanon Dabo) sai kuma yau da ya taka kafarsa a Adamawa a dalilai guda biyu. Na farko abokinsa Sagir wanda yake abokantaka da shi da zuciya biyu; kyakkyawan tsammaninsa na cewa yana da alaka da Hafsat da kuma aiki da ya hada su wuri guda. A yau kuma ya zo Adamawa ne don amsa gayyatar Sagir da ya yi masa na daurin auren dan Yayarshi Modibbo da kuma son yin kyakkyawan bincike a kan Sagir da ahalinsa don tabbatar da wannan zargi da zuciyarsa ta riga ta mika wuya da shi.
Daga filin jirgin saman (Yola Airport) shatar taxi suka yi (drop) har garin JIMETA kofar gidan iyayen Sagir da ke unguwar DEMSAWO.
Demsawo unguwa ce mai tsohon tarihi a Jimeta. Babban gida ne irin na extended family (gidan Gandu) wanda ya tuna masa da nasa gidan kakannin da ke Kano. Tun isowarsu wajejen karfe goma na safe suka tadda jamaa sun fara taruwa a kofar gidan wanda dakali guda biyu suka sanya shi a tsakiya. Karfe goma sha daya na safe za a tafi gidan su yarinyar inda za a daura auren, nan gidan su Sagir shi ne wurin haduwa (meeting point).
Sai yi musu barka da zuwa yan uwan Sagir ke yi har suka samu damar shiga cikin gidan. Wuce wannan lungu, shiga wannan sashe har suka tadda bangaren iyayen Sagir wanda ke can karshen gidan. Abdulazeez zai iya rantsewa ya ga fuskoki na mata da maza masu yanayin zubin halitta ko kamanni na fuska da matarsa Hafsat sun kai guda goma. Tazbihi kawai yake yi wa Allah Sarkin kaga halitta wanda ya halicci wannan family ya kuma sanya kamanceceniya mai tsanani a tsakaninsu da Hafsat wadda idan har ba ta jini ba ce, to hakika imaninsa ya karu da Ubangijinsa.Mai yin halitta yadda ya so a tsakanin alummar Annabinsa Muhammadu (SAW). Alamarin ya kara rikirkita shi a lokacin da suka kuke ga isowa kuryar gidan zuwa dakin dattijuwar da ake ta kira da Daada a bakin manya da yara.
“Daada adon nderna (Dada kina ciki)? Sagir ya tambaya a kofar dakin, yana mai zura rabin jikinsa ciki.
“Mido nder Sagir, yottu nder (ina cikiSagiru, karaso ciki).
Bismillah Barrister mu shiga daga ciki.
Ya gusa ya bai wa Abdulazeez hanya. Tare suka shiga dakin suka zazzauna a kan tabarmar kaba da ke shimfide, suka fara gaida Daadan, wadda ko kusa Hausa ba ta zauna a kan halshenta ba.
Shi ne abokina da nake gaya miki Barrister Abdulazeez Dakata.
“Jabbama-jabbama Abdulazeez, Allah ya kara albarka a gare ku da iyalanku, barka da zuwa garin Jimeta.
In ji dattijuwa Daada, cikin tattausar muryarta mai cike da nutsuwa. Irin dattijan nan ne da yawan ibada da kula da sallah ya sanya musu kamala, dattaku da nutsuwa ta musamman a rayuwar girmansu.
Abdulazeez dago ido ya yi yana kallon Daada, wannan karon zuciyarsa neman hantsilowa waje ta yi. Hakika baa mutuwa a dawo, kuma har da shi aka binne Habibah a birnin Jeddah, idan kuma aka hada shekarun Habiba a sanda ta ke raye tare da su zuwa yanzu shekaru goma sha takwas ko kusa ba za ta yi shekarun wannan dattijuwar ba. Ba don haka ba da ya ce Habiba ce ba mutuwa ta yi ba, Nigeria ta dawo. Hatta wata tawwadar Allah da ke gefen hancin Habiba ga ta nan a gefen hancin Maman Sageer. Bai gama farfadowa daga tunanin da ya lula ba ya lura da wani enlargment na wani hoto a gabas maso kudu na dakin, wanda ya gama warware duk wani tunani da zargi da ya saura masa.
Wani farin Dattijo ne tare da Daada, da yaya maza da mata sun kai goma har da Sagir tun bai wuce shekaru sha takwas ba, a cikin jerin matan ga wadda zai iya kira HABIBAH ko daga barcin mutuwa aka taso shi Habiba ce wannan.
Jikinsa har rawa yake yi, yana kallon Sagir da Dada na magana yana kallon hoton. Kafin ya sauke idonsa an cika gabansu da akusan abinci kala-kala. Muryar Sagir ya tsinkaya a tsakar kansa,
Tunanin me ka ke haka ina ta magana ba ka jina? Mu ci abinci maza mu tafi lokaci na tafiya Abdulazeez.
A hankali ya sauke idonsa a kan Sagir ya sake daga su ya kalli hoton sannan ya kalli mahaifiyar Sagir. Tunani ya yi gara ya bar komai a cikinsa kada ya bata musu rana, bayan suna da abin farin cikin da suka shirya yi. Wannan tunanin ya sa shi daidaita fuskarsa ya maido hankalinsa ga Sagir, wanda ya ciko kofi da farin kunun gyada mai kyawun gani a ido ya miko masa, ya kuma dauki plate ya cika musu da wainar shinkafa da kuli (maasa) ya sanya a tsakiyarsu suka fara ci. Dada na tambayarsa ko yaransa nawa?
Murmushi ya yi. Dada auren nawa ko shekara bai yi ba.
To Allah ya kawo masu albarka.
Amin Dada.
Sosai ya ji dadin abincin nan, don ya jima bai ci irinsa ba. Kuma basu karya ba suka fito. Da suka gama Dadan ta miko masa kwanon sha cike da sabuwar madarar shanu mai dumi. Ya karba ya sha sosai, da doki mai yawa. A lokacin angon ya shigo wanda Sagir ya kira da suna Modibbo, ya sha manyan kaya sai kamshin turare yake. Sai Abdulazeez ya kara tsinkewa, tsinkewar da bai yi a baya ba na zaton da dangin Hafsat ya ke tare. Yanzun ne ya karasa mika wuya.
Wannan saurayin bafillace wanda alamu sun nuna ya samu ilmin boko mai zurfi bai bar komi na Habibar da ya sani ba. Mika musu hannu ya yi suka yi musabaha, ya ce da kawun nashi, wato Sagir ya tashi su wuce unguwar su amaryar inda za a daura auren.
Bayan an daura aure sun dawo aka yi liyafar cin abinci a wani babban falo da ke gidan na mahaifin su Sagir. Suisu ne family din gidan maza zallah. Ko abokan ango ba su da yawa, daga nan jamaa suka soma watsewa.
Booking dinsu na komawa Abuja na karfe biyar na yammacin ranar ne, don haka cikin gidan Sagir ya ja shi suka koma. A lokacin mahaifin su Sagir da suke kira da Malam Babbah ya dawo yana shigifarsa wadda ke kusa da dakin Dada, can Sagir ya ja shi suka gaisa da Malam. Ya gabatar da shi a matsayin amininsa a wajen aiki.
Malam Babba malami ne na sosai, malamin Alkurani masanin addini wanda gwamnatin jihar ta Adamawa ta san da zamansa, ta ke kuma damawa da shi a kan alamuran da suka shafi addini a jihar. Kamalarsa da kwarjininsa a bayyane suke na malaman kwarai maabota dimbin ilimi. Sosai yake jan Abdulazeez a jiki don ya sake su yi hira, kasancewar Abdulazeez bai saba shiga irin wadannan wuraren ba sosai yake nuna bakunta, ga kuma nauyin da zuciyarsa ta yi. Amma duk da haka ya saki jiki da Malam Babba sun yi hirar iyayensa da kakanninsa da ke Kano.
Ba karamin dadi Abdulazeez ya ji ba lokacin da Sagir ya ce su koma dakin Dada su yi mata sallama, su yi haramar wucewa airport.
“On warti na (kun dawo)? Dada ta tambaya.
Ai tun dazu muka shigo muna tare da Malam Babba. Sagir ya ba ta amsa cikin fulatanci shima.
Wasu abubuwa cikin jarka ta turo gaban Abdulazeez. Ga man shanu da kindirmo ka kaiwa maidakinka. Ga kuma masa sabuwa an yi muku ita ma ka tafida ita, na lura kana sonta sosai.
Murmushi ya yi, ya ja jarkokin gabansa yana godiya, Sagir na taya shi.
Idonsa ya mayar kan hoton nan da ke kafe ya ci gaba da kallonsa. Har Dada ta lura ya kurawa bangare guda ido, ta juya don ganin abin da yake kallo.
Kana kallon yan uwanka ne? Ta fada da hausarta mai rauni, fulatanci shine harshen da ya kama harshenbakinta, tsilli-tsilli take jefa hausar wadda ma dalilin Abdulazeez din take yin ta.
Mikewa ya yi ya isa ga hoton ya bambaro shi daga bangon ya dawo ya zauna kusa da Dada da shi a hannunsa.
Dada yanzu duk ke ki ka haife su?
Murmushi ta yi, amma saboda alkunya irin ta Fulani sai ba ta ce masa komai ba. Sagir ya matso kusa da shi ya soma yi masa bayanin jamaar cikin hoton.
Wannan shi ne babban yayanmu Yaya Tijjani, wannan Yaya Yushau, wannan kuma Yaya Habiba... sai Maiwada, Saade, Fusam, Haladu, ni Sagir da autan Dada Nuru. Duka mu tara ne yayan cikin Dadanmu.
Yatsansa (ibham) ya dora a kan fuskar Habibah ya ki daukewa, har Sagir ya lura ya ki dauke yatsansa daga kan fuskar ta. Kamar yana bukatar karin bayani a kanta, amma bai furta hakan da bakinsa ba. Sagir ya kara matsowa kusa da shi sosai.
Ita wannan da ka ke gani a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login