Showing 168001 words to 168255 words out of 168255 words
ko don hotonta da ya shekare mata a falo. Ko taji wani abu a ranta yau kam tafi karfin kishin ta. Duba da cewa Muazatun bata nuna komai ba sai kauna da kulawa ga yayanta. Itama sai ta ja nata a jiki har sukayi hotuna tare.Sun zo ne musamman tun daga jihar Lagos don halartar wann kasaitaccen bikin karin girma da kasar Nigeria ta baiwa Justice Abdulazeez Dakata sakamakon jajircewa da sadaukar da kai irin nasa na tsahon shekaru ga kotunan Nigeria, ba kuma karkashin gayyatar kowa ba sai kasancewar su karkashin umbrella guda na aiki da proffession. Justice ABDULAZEEZ HAMZAH ATIKU da HAFSAT-SUHAANAH nima ina fatan alkhairi.
-Takori
June, 2019
Masha Allah laquwwata illa billah.
Nan na kawo karshen littafin AUREN KWANGILA. Kuskuren da ke ciki ku taya ni rokon Allah Ya yafe mini. Darussan alkhairin da ke ciki Allah Ubangiji ya hada mu cikin ladan ni da ku baki daya.
Sai mun hadu a sabon littafina AALIMAH nan ba da jimawa ba insha Allah. AALIMAH sabon salon rubutu ne a cikin jerin littattafan Takori. Idan nace yafi min sauran ko nayi kuskure to kadan ne don ina ji da shi (on its own). Mu hadu da Aalimah Mansour Raazee a cikin littafin AALIMAHdon jin irin nata kaddarorin and her journey to diaspora..
Taku har abada,
Takori.