Showing 39001 words to 42000 words out of 168255 words

Chapter 14 - Auren Kwangila Book 4 Hausa Novel Complete

Takori   

12 Dec 2024

297

mai sunan Addar?”
Shiru ya sake yi, bai ga amfanin ya sake magana akai ba, tunda babu wanda zai fahimce shi. Magana ce ta SO; love... feelings.... devotions...... emotions.... to ba ya jin ko daya a kanta. Ba ya sonta ba ya kaunarta, bata da abinda zai kaunata. Bai da wani feeling a kanta ko da na kanwa, (sai ko na dan gida da ‘yar aikin gidansu). Don haka daga yanzu ya dinke bakinsa, ya daina wahalar da kansaneman taimakon kowa, they will never understand him; cewa yana cikin soyayya wadda ta hana shi gane kome suke son ya gane. They only want to excercise their power ta iyaye a kansa, su dakushe masa farin cikin rayuwa, zai yi abin da ya ga dama, zai nema wa kansa mafitar da za ta raba shi da wannan bakar kaddara da ake neman daura masa. Ya samu abin da zuciya da ruhinsa ke so (Mu’azatu) ba tare da ya batawa iyayensa ba, ba tare da ya bata wa kowa ba har ita yarinyar. A matsayinsa na wanda ya san hakkin dan Adam da ‘yancin da Allah ya ba shi ya san ita ma mutum ce kamar kowa, ba zai zama azzalumi a kanta ba. Ba zai bata wa iyayensa saboda ita ba, shawarar da zuciyarsa ta yanke masa ta karshe shi ne daidai.
Mikewa tsaye ya yi, kansa a sunkuye ya zuba dukkan hannayensa a aljihu, “Ku yi hakuri Kawu, na yi alkawarin yi muku biyayya. Na yi kuskuren yin jayayya da ku, na amince zan aure ta Kawu, ku yi hakuri, ku sa min albarka”.
“Allah ya yi maka albarkar duniya da lahira. Allah Ya shige maka gaba a kan duk abin da ka sa gaba, ko kai fa Abdul’azeez? Na ji dadi kwarai, that’s my grandson!” Ya fada yana bubbuga kafadunsa. Shi kuma ya yi murmushi.
Har mota ya rako shi, bai koma office ba sai da ya ga hawansa kan kwalta da bacewarsa.

*****
Washegari daidai wancan lokacin da suka zauna wato karfe goma na dare, yau din ma tun kafin cikar karfe goman Mammah da Daddy ke zaune a falon suna dakon shigowarsa. Goma na bugawa da minti biyar Barrister Abdul’azeez ya yi sallama ga iyayensa.
Sosai Mamma ta bi shi da kallo, so ta ke ta karanto yanayin da yake ciki, fuskarsa kadaran-kadahan ta kasa karantar komai, sai dai ta fahimci ba ya cikin damuwa kamar wancan lokacin. Kyakkyawan sajen nan ya kara kwanciya a kan fuskarsa kamar wani bako daga Qatar. Shadda ce (Getzner) ruwan kasa a jikinsa, kansa da hula mai launin ruwan kasa mai haske. Dole duk macen da ta san ciwon kanta ta yi wa kanta sha’awar hada rayuwa da Abdul’azeez Dakata, domin baiwarwakin da Allah ya yi masa suna da yawa, don haka bata ga laifin wannan yarinyar ‘yar Lagos data yi masa kamun kazar kuku ba, gata take so ta yiwa kanta. Mammah ta fada a zuciyarta.
Gefen kafafunta ya karasa ya zauna. Daddy ya dube shi yana murmushi.
“Yau tun safe ban ganka ba”.
Ya dan muskuta, “Na fita ne Daddy, ban jima da dawowa ba”.
Sautin muryarsa kadai suka ji suka fahimci babu sauran damuwa a tare shi.
A tare Daddy da Mammah suka sauke ajiyar zuciya.
“To ya ya? Ina maganarmu ta kwana?” Prof. Dr. Hamzah Dakata ya tambaya cikin raha. Mammah ba ta tsoma baki ba.
Ya sunkuyar da kai, “Mammah na amince ki aura min duk wadda ki ke so ko da sun kai goma, na hakura da Mu’azatu na karbi zabinki Mammah, ki yi hakuri da jayayyar da na yi da ke ranar bana cikin hayyacina. Mammah na amince, ku sa min albarka”.
Kura masa ido ta yi cikin kallo na kurilla, ita dole so ta ke ta karanto zuciyarsa, da ta kasa fahimtar komai sai ta furta abin da ke zuciyarta.
“Amma ya aka yi ka canza ra’ayinka haka da sauri Abdul’azeez? Na fa sanka farin sani, na sanka a kan ra’ayi da akidarka, anya babu wata makarkashiya a zuciyarka? Ba fa zan yarda a cutar min da Adda ba, daidai da kwayar zarrah!”
Ya hadiye wani miyau ji kake, mukut. Mammansa sau tari haka ta ke kamar psychologist, she reads their minds easily, duk wani motsinsu ta sani. Ya kara zama serious ya sunkuyar da kansa.
“Mammah dole ne in yi muku biyayya kowanne ra’ayi nake da shi. Na bi Allah, na bi umarninku. Zancen Mu’azatu na ajiye shi a gefe ba don na daina sonta ba, da ma iyayenta ba so suke su aurar da ita yanzu ba sai ta gama (Law School). Amma Mammah ita din ta yarda ta amince za ta aure ni?”
Har yanzu kansa a sunkuye yake, bai dago ba yake yin maganar cikin tsanaki. Hajiya maryam ta ce, “Sunanta ne ba ka sani ba?”
Murmushi ya yi, ya ce, “To Mammah sunayen nata ne sai mutum ya rasa na kamawa...”
Dariya ya ba su sosai.
“Zabi guda daya wanda ya fi kwanta maka a ciki ka dinga kiranta da shi, kai kadai”. Inji Daddy.
Cikin alamun jin kunya ya sadda kai bai ce komai ba.
Hajiya Maryam ta rufe zaman nasu da cewa.
“Sai ka koya mata amincewa da auren naka, tunda ka fita hankali, daga ranar da aka daura muku aure”.

*****
A daki ta samu Suhaana tana ninke fararen (innerwears) dinta da ta wanke tana jerawa a sif din da ta ware musu. Tunani ta ke yi a zuciyarta tun dawowarsu Nigeria Mommah ba ta kara yin zancen karatunta ba. Bayan ta san babban burinta shi ne ci gaba da karatun, tana matukar burin yau a ce ta zama wani abu a dalilin karatu, ta tsaya da kafafunta ta fuskanci rayuwa mai cike da kalubale da ke gabanta. Tun ba ta kawo haka ba ta san ita ba ‘yar Prof. Hamzah ba ce, ba ta san ubanta ba, ba ta san ta inda ta shigo hannunsu ba. Ba ta son yarda da gaskiyar da ke a bude “ita ba ‘yar Mommah ba ce”, amma dole ta yarda, rashin zama ‘yar Prof. Dakata na nufin rashin zama ‘yar Maryam Dakata, iyakar gaskiyar kenan.
Ta share hawayen da suka cika mata ido da bayan hannunta, Mammah ta ce sai ta cika shekara goma sha takwas za ta gaya mata komai da ya kunshi rayuwarta. Tana so ta nemo uban nan da uwar nan nata ko ta samu cikakken farin ciki irin na kowa. Hakan kuma ba zai zama mai sauki ba sai ta yi ilimin zamani mai zurfi, ta yadda ba sai ta nemi taimakon kowa ba a sanda ta tashi aiwatar da wannan jan kalubale da ke gabanta.
Cikin wannan halin na zurfin tunani Hajiya Maryam ta same ta, har ta zauna kusa da ita ba ta sani ba, sai da ta kai hannu ta kama nata ta rike gam cikin nata. A sanyaye ta sauke idanunta a kan Mammah kwalla cike da idanunta. Hankalin Hajiya Maryam ya tashi, ta ce.
“Addah tunanin me ki ke yi haka har da hawaye? Har na shigo na zauna ba ki sani ba”.
Ta kai hannu ta dauke hawayen ta kakalo murmushi.
“Mammah ina tunanin yaushe zan ci gaba da karatu ne?”
Hajiya Maryam ta yi jimm! Sannan ta girgiza kai, “Shi ne kuma har da hawaye? Kayya, in kuwa shi ne ki yi hakuri, rana ta farko da zan gaza wajen yi miki abin da ki ke so, sai dai hakan ba yana nufin ba za ki yi ba kwata-kwata a rayuwarki. Za ki yi idan mijin aurenki na so, kuma ya amince ki yi a dakin aurenki, ki yi hakuri Addahta, ina da dalilai na masu yawa da ba zan iya barinki karatun jami’a a gabana ba, na fi gane in bi umarnin Ubangiji in yi miki AURE sai hankalina ya kwanta ya tsumma a randa. Abin da kuma na zo in nemi amincewarki a kai kenan. Hafsatu aure zan yi miki”.
“Aure Mommah?” Ta tambaya cikin mamaki, da alamun kuma cikin sautinta da fuskarta ba ta gama fahimtar me Mammah ke nufi ba.

“Eh, aure irin nawa ni da Daddy, ki bar gidan nan ki koma gidan mijinki, ku rayu tare ki haifo min jikoki in yi ta raino. Ku yi zamanku lafiya ke da mijinki, mu da ke sai ziyara, haka Allah da manzonsa suka ce a yi wa kowacce ‘ya mace idan ta kai munzali, kuma kin kai, kin fahimce ni?”
Idanunta suka yi rau-rau, gab ta ke da ta saki kuka, muryarta na rawa ta ce, “Mommah karatuna fa? Mommah in na rabu da ke da Baba Azumi ni da wa zan zauna?”
Murmushin kwantar da hankali Hajiya Maryam ta yi mata tare da dafa kafadunta, cikin idanu ta ke kallonta. Kwayar idanuwanta na nuna zahirin kaunar da ta ke mata.
“Kwantar da hankalinki Addah, aure abu ne da kowacce ‘ya mace ta gada, kuma gaba yake da kowanne burinta. Shi fa wannan karatun na zamani ba Allah ne ya ce a yi shi kafin a yi aure ba. Duka da haka shi ma abu ne mai amfani, amma ko kusa amfaninsa bai kai aure ba. Ki fahimci abin da na fada miki a baya dalla-dalla, za ki yi karatun jami’a idan mijinki na so, kuma ya amince a gidanki. Amma yanzu aure zan yi miki, za ki bar mu ni da Baba Azumi ki zauna a gidan mijinki yadda kowacce mace da ki ka sani ke zaune a gidan miji. Amma na yi miki alkawarin duk sanda ki ka so ki ganmu za ki ganmu, zan zo gidanki ko cikin dare ne kin ji Addahta?”
Ta gyada kai alamar ta fahimta, sai kuma ta fada jikinta ta saka kuka.
Bayanta Hajiya Maryam ke shafawa tana lallashinta.
“Yi hakuri kin ji Addahna? Ba zan kai ki inda za ki cutu ba, ba zan bari a bata miki rai da gangan ba sai in ba na raye. Ki yi hakuri ki yi min biyayya yadda shi ma da ya fi ki shekaru ya yi mini. Na yi miki alkawarin insha Allahu dukkanku ba za ku yi da na sani ba, sai kun yi alfahari da wannan aure naku, sai kun gode min watarana”.
Baba Azumi daga falo tana shara ta ke jin tashin muryar Mammah da alamun kukan ‘yar gidanta. Ta ajiye tsintsiyar ta taho. A bakin kofa ta tsaya tana kallon ikon Allah.
“Kukan me ta ke yi? Ke fa abin kuka ba ya miki wuya, don Mamarki na shagwaba ki?”
Murmushi Hajiya Maryam ta yi, “Wannan kukan mai dalili ne. Yau Mommah ta yi laifi dole ta ke lallashi, kukan aure ne na rabuwa da Mammah da Baba Azumi, ko Suhaana?”
Ta daga kai ta ce, “Eh”.
Duk sai ta ba su dariya.
Mammah ta share mata hawaye, Azumi ta ce “To ai mijin na gida ne, ba za ki yi nisa da mu ba. Ni na taba ganin auren gata ma irin naki Hansai? Babban Yaya gabadaya fa, uban gida magajin gida, lauya na al’ummah na Hansatu bada kanka a sare, Yayan Isma’ila, Yayan Usmanu, Da daya tamkar da goma Mammah ta zabo miki duk cikinsu. Daina kuka kin ji? Yi farin ciki ki gode wa Mamarki, ita mai sonki ce”.
Nan fa Hafsat ta hau zazzare ido tsakanin Mammah da Baba Azumi tana so su yi mata karin bayani, wane Babban Yayan Baba Azumi ke nufi?
Sai dai ba ta samu komai daga karin bayanin da ta ke son jin ba don Mammah ficewa ta yi kawai tana murmushin wannan kirari da Azumi ta yiwa Abdul’azeez.Da yake tayi maganar da ita tun jiya. Inda ta bada goyon bayanta dari bisa dari da kyakkyawar addu’a. Baba Azumi kuma ta wuce ta ci gaba da shararta suka barta cikin ci-da-zuci, sakar zucci da tunanin zuci mai nauyi. Ba dai wannan ‘baren’ (total stranger) na cikin ‘ya’yan gidan nan ba? Ba dai wannan wanda ya fi kowa odd hali cikin gidansu ne ake nufin zai zama mijin nata ba????
*****

“Kina ina Mu’azatu?”
“Har yanzu ina Apo, sai gobe zan bar abuja, mene ne? You sound worried?”
“A ina zan same ki? Magana ce mai muhimmanci da ba ta bukatar distraction, gidan Anty kuma ba ya rabo da jama’a”.
“To ko in zo office dinka yanzu? Sai direba ya kawo ni, ina ganin za mu iya tattauna kowacce irin magana a can”. Ta fada cikin faduwar gaba, jin muryar Abdul’azeez na rawa, abin da ba ta taba ji daga gare shi ba. “Alright” Kawai ya ce ya kashe wayarsa.
Mota kirar matrix ta sauke Mu’azatu Rufa’i a Federal High Court da ke kan titin (OAU Quaters, Kashim Ibrahim Way Maitama, Abuja), cikin tafiyarta mai kama da tana taku a kan kwai ta karasa zuwa ofishoshinsu. Daya bayan daya ta ke wucewa tana duba sunayen da ke rubuce jikin wani dan karfe a saman kowacce kofa har ta zo inda ta ke nema.
‘Barr. Abdul’azeez H. Dakata’. Shi ke rubuce a saman ofishi mai lamba (24). Ta kwankwasa daga ciki ya amsa, ta murda ta shiga.
A kan doguwar kujerar leather ruwan kasa yake zaune cikin daya daga kujerun tattaunawa da baki da ke ofishin. Sanyin air-condition ya ratsa ta kamar yadda ya mamaye ofishin da kamshin turaren mamallakinsa.
Mu’azatu na mamakin son sanyi irin na Abdul’azeez a gida ne, a mota ne, a ofis ko yaushe za ka same shi ya kure A.C shi ba wanda ya yi rayuwa a kasar sanyi ba.
“Koma ki yi sallama malama, sannan ki shigo”. Ya fada cikin sanyin murya.
“Ai na yi knocking ka ce in shigo”.
“To ni bana son knocking saboda ni ba arne ba ne, sau nawa zan gaya miki?”
Ta zumbura baki, ta koma ta yi sallamar ya amsa. A ranta tana fadin “yana cikin damuwar ma ba ya fasa ba da order, order dai! Da kyar nan gaba in bai zama Alkali ba”.
Kusa da shi ta zauna suka zuba ma juna ido, idanunsa sun kada sun yi jajir. Ba ta taba ganinsa cikin rashin nutsuwa irin na yau ba. Duk ya birkice kamar ba shi ba (smart-guy) mai tafiya da imaninta, yau har wani cukurkudewa gashin kansa ya yi ga wani gashin fuska ya karu na babu gaira babu dalili.
“Wai me ke faruwa ne Abdul’azeez? You look worried. You sound worried, ni ma ka dugunzumar min da hankali, da ina da hawan jini na tabbata da yanzu kafin na iso ofishinnan ya hau”. Ta fada a jere ko numfashi ba ta tsaya ta shaka ba.
Tana rufe baki ya ba ta amsa.
“Duk a dalilinki ne Mu’azatu”.
“A dalilina? To me ya faru?”
“Kin yarda ina sonki Mu’azatu?”
“Na yarda, amma me ya kawo wannan tambayar?” Ta fada da hanzari.
“Na tambaye ki ne saboda ki yarda da ni, ki yarda da abin da zan gaya miki babu karya ko yaudara. Ba ni da nufin su gare ki shi ya sa na yanke shawarar gaya miki gaskiyar halin da nake ciki da iyayena a yanzu, kada ki ji a wani wuri daban ki yi wa zancen fassara a baibai ko ki yi tunanin na yaudare ki, amma in muka hada kai muka amince da juna za mu shawo kan mastalar, mu samu cikar burinmu a lokacin da ya dace da burin iyayenki. Kin yarda da ni Mu’azatu?”
Jikinta a sanyaye ta ce, “I trust you ka sani, ko mene ne ka gaya mini zan fahimta. Amma don Allah kada ka ce Mu’azatu ba zan aure ki ba...!!!” Sai hawaye.
Karo na farko da ya yi kuskuren kai hannu ya rungumo Mu’azatu a jikinsa. Nasa idanun na fidda kwalla. How he wish Mammah za ta fahimci karfin wannan soyayyar? Ba zai iya barin Mu’azatu saboda wata mace ‘yar uwarta ba, wadda ya tabbata ba ta da abin da ya fi na Mu’azatun, ba ta fita da komai ba. Sai ma dai ace bata kaita ba.
Ko ma ta fitan shi son da yake wa Mu’azatu (has no reason), wato babu dalili. Abin da ya sani kawai yana sonta, ita ma tana sonshi, ba don uwa-uwa ba ce sai ya ce wannan abun da da ta yi masa zalunci ne. Ba ruwanta da feeling dinsa, ita dai kawai a biya mata tata bukatar. Kwalla mai zafi ta gangaro masa, ya yi saurin dauke ta kafin Mu’azatu ta gani. A lokaci guda kuma ya sake ta ya janyo ta suka kalli juna.
“Ba zan taba cewa ba zan aure ki ba, it’s a promise. Zan aure ki komi runtsi, yanzu dai ki ba ni hadin kai ki ji damuwar tawa, kina kara min damuwa da fitar hawayenki Mu’azatu, bayan na kira ki ne don mu fahimci ta yadda za mu billowa matsalar, ba fa wata gagaruma ba ce (we can overcome it)”.
Mu’azatu ta share hawayenta, ta ba shi hankalinta.
“Mu’azatu, kin san girman iyaye, kin san karfin ikonsu a kanmu, kin san tsattsauran umarnin Ubangiji a kanmu na mu yi musu biyayya, Ya ce (Ubangiji)‘Wa qada rabbuka alla ta’abudu illa iyyahu Wa bil walidayni ihsaana’, Ya kara da cewa, ‘Wala taqul-lahuma uffin walaa tanhar humaa wa qul-lahumaa qaulan-kareema’(Isra’i). A wata ayar ya kara cewa, ‘Daga bautarsa sai kyautayi ga iyaye.......’
Allah (SWA) ya kara cewa ma mu dinga nema musu gafara ko suna raye, kamar yadda suka ji kanmu muna kanana.
‘Wakhfidh lahuma janahazzilli minar rahmati Wa qul rabbir-hamhumaa kama rabba yaani saghira... (Isra’i).
Mu’azatu duka wannan kadan ne daga ayoyin Ubangiji da suka yi umarnin mu zamo masu kyautayi da biyayya a gare su, wallahi Mu’azatu duk da wannan sanin sai da na sa kafa na take, na yi PROTEST (tawaye). Na yi jayayya da su a kanki, na shiga na fita ta wasu hanyoyin duk don in kaucewa umarninsu in tsira da ke.......”
Mu’azatu ta shiga girgiza masa kai alamar, “A’ah”.
Ya ce, “Yes, ban yi nasara ba ai, don haka na amsa wa bukatarsu. AURE za su yi min Mu’azatu da wata macen ba ke ba.....!!!”.
Girgiza kai kawai Mu’azatu ke yi, numfashi na neman dauke mata, tana neman shidewa. Tallafo ta ya yi ya rungume suna amfani da nasa numfashin. Kawai sai ga kira a wayarsa da ke gefe, juyawa yayi a hankali yana kallon sunan da ke yawo a fuskar wayar ‘Precious Mammah’. Da sauri ya saki Mu’azatudon gani ya yi kamar itace tsaye a kansa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login