Showing 63001 words to 66000 words out of 168255 words

Chapter 22 - Auren Kwangila Book 4 Hausa Novel Complete

Takori   

12 Dec 2024

302

yana bakin aiki, in tana gari suna tare, in ba sa gari daya koyaushe suna manne a waya.
Don haka washegari Hafsat ba ta sanya Abdulazeez a idanunta ba ya fice ofis da sassafe. Da ya tashi office gidansu ya wuce, a can ya ci abinci. Sai da Mammah ta ga karfe tara ta yi ba shi da niyyar komawa gida ta ce ya tashi ya tafi. A nan yake gaya wa Mammah zai saya wa Hafsat waya tunda ta ki zuwa gidansu, kuma ta hana shi kawo ta.
Ta yi murmushi cikin ranta ta ce, Mu je zuwa... wai mahaukaci ya hau Kura.
A (Bannex) da ke Wuse 2 ya tsaya ya yi cinikin wata karamar (Iphone) ya saya da sunan Hafsat. Har jikin (receipt) Hafsat Dakata aka rubuta.
Sanda ya iso gida ta dade da kulewa a daki. Ya so ya tadda ita a falon ya ba ta wayar, hakan bai yiwu ba. Ga shi kuma ya sa wa kansa takunkumin daina shiga dakinta.
Sai washegari zai fita ita kuma ta fito daga kicin suka hada ido, rabon da ta ganshi tun shekaranjiya. Shi ya fara dauke idonsa, zuciyarsa na harbawa. Akwai wani maganadisu mai kama da magnet a cikin kwayar idanunta, wanda duk lokacin da ya yi kuskuren hada ido da ita sai ya ji shi a jikinsa. Neman kujera ya yi ya zauna, ya dafe kansa ya kasa ce mata komai. A sanyaye ta zagaye kujerar bayansa, ta tsugunna a gabansa, ta ce.
Good morning.
Da ka ya amsa ta hanyar daga kansa da ke cikin hannayensa, amma ba ta yi nasarar samun kallo daga gare shi ba. Inda sabo ya ci a ce ta saba, don haka ba ta wani damu ba ta mike za ta wuce. A sanyaye ya cira kai daga cikin hannayensa ya ce, Hafsah?
Dakatawa ta yi ba tare da ta juyo ba. Cikin mamakin wai ashe ya san sunanta?
Dauki wayar nan taki ce.
Dawowa ta yi ta dauki wayar ta duba, sai kuma ta mayar ta ajiye ta a inda ta dauke ta tana girgiza kai.
Ba abin da zan yi da ita Yaya Azeez.
Cikin mamaki ya ce, Ba za ki dinga kiran Mamanki ba? Ni ma zan dinga kiranki in ina office.
Ga mamakinsa, sai hawaye suka balle mata. Ta ya ya za ta gaya masa cewa, mahaifiyarsa ta daina sonta? Tunda ta kawo ta nan ta aje yau kusan watanni hudu ba ta kara waiwayarta ba. Sai ta mike kawai tana share hawaye ta nufi dakinta.
Haushi, takaici, mamaki su suka taru suka rufe Abdulazeez. Bai san lokacin da ya bi ta dakin ba a fusace. Tana zaune a kujerar gaban mirrow ta kifa kanta a kan madubin tana kuka. Hannunta ya fizga ya mikar da ita tsaye suna fuskantar juna. Kafadunta biyu ya rike ya girgiza ta.
Na yi kama da saanki Haleem da za ki dinga kawo min raini?
Ta fiddo jajayen idanunta tana dubansa cikin firgici.
Ya sassauta rikon da ya yi mata ganin ta tsorata sosai yadda yake so, ya ja hannunta ya zaunar da ita a gefen gado, ya ci gaba da tsayuwa a kanta. Muryarsa akwai sassauci a sailin da yake cewa.
Jiya na yi miki abin arziki na ba ki system dina, ki ka saka min da rashin kunya. Ban daddara ba yau na sake yi miki abin arziki na sayo miki waya don ki dinga magana da Mamanki da yan uwanki ni ma in dinga jin lafiyarki, in daina tunanin na jima a office ban san halin da ki ke ciki ba, shi ne za ki yi min rashin kunya again wai ba kya so?
Cikin girgiza kai hawaye na ci gaba da fita ta ce, Ba rashin kunya ba ne. Yanzu misali in ba ka system dina, kana kunnawa ka ga hoton namiji ya ya za ka ji? Waya kuma abin da ya sa na ce maka bana bukatarta saboda da ma don Mammah nake sonta, kuma Mamma ta dade da mantawa da ni, ta daina sona... tunda ta kawo ni ba ta kara nemana ba alhalin ta san ba ni da kowa sai ita... Ta kifa kanta cikin cinyoyinta, ta ci gaba da kuka sosai mai taba zuciya.
Hannun Abdulazeez ta ji a saman kafadunta ya cira ta tsaye, kokari yake ya raba tafukan hannayenta da fuskarta, amma ta ki bari. Ya ce, Suhaana, in kin yarda ni Yayanki ne Azeez kamar yadda ki ka fada dazu ki dube ni...
Sosai ta rage kukan domin abin da ba ta zata ba ne. Hannunsa ya kai habarta ya dago fuskarta daidai tashi, ya shiga share mata hawayen da yatsun hannunshi. Runtse idanunta ta yi sakamakon jin wani sabon alamari na bin illahirin gangar jikinta.
Bude idonki Suhaana ki dube ni, magana za mu yi.
A hankali ta ke bude idon, amma ta kasa bude su gaba daya ta dube shi cikin ido, kamar yadda yake nufi. Yana da wani irin girma na musamman a idanunta ba tun yau ba. Burinta ya daina kai hannu saman fuskarta don haka ta bude idon. Janta ya yi suka zauna a gefen gadonta yana kallon agogo, da mamaki yau shi ne har karfe tara na safe a gida saboda diyar Mammah.
Sai da ya ga ta nutsu sosai ya ce, Ashe mutum yana fushi da iyayensa Hafsat
Kai ta girgiza masa.
Amma ke ki ke fushi da Mamanki?
Sunkuyar da kai ta yi tana kallon yatsun kafarta.
Mikewa ya yi ya koma falo, ya dauko wayar ya dawo ya dora mata a saman cinyarta,
Common, call your Mammah....







SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI
07030137870

*Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama*

******
Kiran lambobi masu tsayi ne ya tashe ta daga barci bayan ta yi sallar asubah ta koma. Code ne na kasar Amurka. Barcin idonta ya wartsake nan da nan sai dai kafin ta amsa kiran, ya katse. Ta ciji yatsa za ta kira, kiran ya sake shigowa. Wannan karon ta yi nasarar amsawa.
Bride of the year. In ji (Brothern) da babu kamarsa a wajenta.
Illaila... Ta amsa tana dariya.
Sunan da ta ke kiransa kenan tana yarinya, ba ta iya cewa Ismaeela ba.
Mammahs doll (yar tsanar Mammah). Shi ma ya rama, kafin ya rufe baki ta rama, Bachelors of the century...
“Brides of the moment. Ismaeel ya amsa cooly, muryarsa cike da kulawa ga yar uwar tasa wadda ya shafe watanni bai yi magana da ita ba. Ya yi-ya yi Mammah ta ba shi lambarta ta ce ba ta da waya, Yayan nasa kuwa tunda ya bada masa kasa a ido a kan bukatarsa na a hada baki da shi a yaudari Mammah a kan sistern da bai da kamarta ya kulla gaba da shi. Jiya kamar daga sama kawai sai ga lamba Mammah ta turo masa, wai ta Suhaanah ce. Tun a lokacin ya so kiranta ya yi tunanin dare ne sosai a wajensu, haka ya yi ta daurewa har gari ya waye.
He so much missed her, she so much missed him. Akwai wata irin shakuwa a tsakaninsu wadda ta samo asali tun lokacin da suke taya Mammah rainon ta a Jeddah.Ta san da suna tare da ba ta shiga damuwar da ta shiga a baya ba. Hira suka shiga yi, amma ko kadan ban da zancen aurenta ko halin da auren ke ciki, hirarsu suke irin wadda suka saba tun ta yarinta. Ta tambaye shi ina labarin Usman, ya ce yazo America daga Brussels suna tare, ya je excursion birnin Orlando. Tana jin fitar motar Abdulazeez wajejen karfe takwas na safe, ba su yi sallama ba sai da cajin wayarta ya kare, wayar ta kashe kanta.
Ta sauko daga gadon ta sanya wayar a caji. Ta duba agogo, karfe takwas na safe. Bandaki ta shiga ta yi wanka, wanke baki, alwala sannan ta fito. Ta samu kanta da yin kwalliya sosai da (lace) mai tsananin taushi, kalar pusher pink da ratsin baki. Sosai kalar da leshin suka karbeta suka kwanta a sassalkar fatar jikinta. Ta fesa turare (christian dior) ta fada kitchen ta daura apronta hau girki.
Wata zuciyar na cewa, ta dafa da Abdulazeez, wata na cewa aa, ko kin dafa da shi ba ci zai yi ba, ina ma ki ka ganshi? Motsi ta ji ana zura mukulli a jikin kofar falon, ko kadan ba ta ji karar shigowar motarshi ba, domin ta kure qiraar Abdurrahman Sudaith a gidan gabadaya cikin Suratul Maidah, ko ba don haka ba motar Abduazeez GMC Terrain ba ta kara, sai in shi ya yi horn.
Ba ta fito ba ci gaba ta yi da abin da ta ke yi, tana mamakin me ya dawo da shi a wannan lokacin? Misalin karfe goma sha daya na safe.
Zama ta yi ta ci dankali na turawa da agadan data soya da farfesun kaza, ta wanke hannunta da liquid soap ta cire apron din ta adana a mazauninsa ta kora da gwangwaninfantasannan ta fito zuwa falon.
Ya watsar da gown dinsa da wig a tsakar falon, hatta briefcase din ta yi nata wurin. Kwance yake a kujerar da ta fi kowacce tsayi a falon, ko takalmin kafarsa da socksbai cire ba,he dont even loose his tie, kwanciyar da daga gani za ka fahimci ba ta lafiya ba ce ya yi. Ji ta yi gabanta ya yi mummunan faduwa, ta rabe ta bayan kujerar da yake kwance ta wuce dakinta ta rufo kofa a hankali.
Amma ga mamakinta ta kasa zaune ta kasa tsaye, so ta ke ta san me ya same shi, sai dai ta san ba ta da wannan matsayin. To amma ai ko babu aure Abdulazeez dan uwanta ne kamar Ismaeel, tunda Mammah ce ta haife shi, ba za ta taba son wani mummunan abu ya faru da shi ba, ko rashin lafiya. A haka lokacin sallar azahar ya yi mata, da ma tana da alwala ta matsa wajen ibadarta ta tada sallah.
Samun kanta ta yi a cikin sujjadarta tana yi wa Abdulazeez addua har da hawayenta, a kan ko ma me ye ke damunshi, Allah ya sa ya zo masa da sauki. Da ta idar tana so ta fito falo ta ga halin da yake ciki, amma ta kasa. Zama ta yi ta hada kai da gwiwa sai a lokacin ta tuna da wayarta, ko Mammah za ta kira ta gaya mata ya dawo a cikin wani irin yanayi ba lokacin da ya saba dawowa ba? Wata zuciyar ta ce.
Akul! Ki je ki tabbatar da abin da ya same shi din tukunna, yanzu haka ma ya bar gidan.
Mikewa ta yi cikin sanda kamar marar gaskiya ta bude kofa ta fito falon. Yana nan yadda ta barshi awanni uku da suka wuce, ko juyawa bai yi ba. Ya yi rub-da-ciki a kan hannayensa. Is touching him a crime? (Taba shi zai zama laifi?) Ta tambayi kanta. Ba ta sani ba, don haka ta je ta tsaya a kansa tana tunanin abin yi.
Lokacin sallah ya yi. Ta fada muryarta na karkarwa.
Ko motsi bai yi ba, sai ta tsugunna ta kai hannunta kan goshinsa. Zafi rau! Ta taba wuyansa shi ma kamar garwashi don zafi. Kawai sai ta durkushe a wurin ta sanya kuka.
Da kyar ya cira kansa daga kwancen ya bude idanunsa da suka kankance suka yi jawur yana kallonta. Ta dago fuskarta suka yi wa juna kuri da ido.
Wane taimako zan iya ba ka? Abinda ta iya tambayarsa kawai kenan cikin karkarwar murya.
Duk halin da yake ciki sai da ya yi murmushi,shes very soft-hearted. Ki duba lokar jikin gadona akwai paracetamol ki dauko min.
Dakin a bude yake?
Ya lumshe ido tare da daga kai, shi bai ma taba rufe kofar dakinsa ba wai don zai fita, ashe ba ta taba shiga ba? Mikewa ta yi da hanzarinta har tana tuntube zuwa dakin. A tsayin rayuwarta ba ta taba ganin dakin barci mai ban shaawa irin wannan ba. Yafi nata tsaruwa ninkin ba ninkin. Ko kuma idonta ne ya ga hakan? Bazata iya cewa ba.
(English Bedroom) komai fari da ruwan toka (white and ash), hatta labulayen. Ba ta wannan ta ke ba, drower din ta nufa kai tsaye ta debo kwayar maganin ta fito. Kicin ta koma ta samo gorar ruwa mara sanyi ta dawo. Taimaka mishi ta yi ya tashi zaune, ta sa mai kwayar maganin a hannunsa ya watsa su a baki ta kafa mai robar ruwan a bakinsa.
Komawa ya yi zai kwanta ta rike masa hannu, dan dago ido ya yi da kyar ya dube ta da idanun tambaya.
Kada ka kwanta a nan, ka koma daki.
Ba zan iya ba. Ya ce da ita a wahalce.
Ill help. Ta ba shi amsa.
Ciwo ya ci karfinsa, amma a ransa ta ba shi dariya sosai. Dube ta yar ficika da ita, ko ya za ta iya daga kato irinsa? Da zai iya doguwar magana da ya tambaye ta hakan.
Ki bari in kwanta kadan forsome minutes tunda na sha magani zan koma.
Ba ta ce komai ba ta koma ta zauna a gabansa, zuciyarta a jagule. Ya maida idonsa ya rufe sai bacci.
Da ta ji yana sauke numfashi irin na bacci, sai ta samu kwanciyar hankali, ta koma daki ta yi sallar laasar. Kicin ta koma ta hado duk abin da ta soya a kan tray ta dafa shayi baki da lipton din tetly tea, ta zuba kayan kamshi su kani fari da citta kadan ta tace ta dauko ta dawo falon da su, ta ajiye a gefensa. Baccinsa ya yi nisa sosai, don haka sai ta koma daki ta kwanta tana ci gaba da yi masa adduar samun sauki.
Cikin dan barcin da ya soma figarta ta ji kamar ana kiran sunanta. Ta bude ido sosai, daga falo ne Abdulazeez ke kiranta. Da sauri ta fito, ya tashi yana zaune dafe da kansa da hannun damansa. Zama ta yi a gefensa ta hau zuba masa shayi ta zuba zuma, ta juya ta mika masa. Bai yi musu ba ya karba ya soma sipping a hankali.
Tana kokarin zuba agada da chipsya ce.
Bar wannan. Ba ni farfesun kawai.
Ta zuba a dan bowl na tangaran ta tura gabansa. Tana so ta ce ya cire suitdin mana saboda sai zufa yake yi, amma ta yi shiru, kada ta wuce makadi da rawa.
Kafafunsa ya mika mata bayan ya ajiye bowl din a gefe ba don ya gama ba.Cire min.
Dago ido ta yi cikin wata irin siga ta kalle shi. Kwayar idanunsu suka sarke da na juna. Ta ya ya za ta iya kama kafafunsa ta cire masa takalmi da safa? Aikin ya so ya yi mata tsauri. Shi kuma ba da wata manufa ya fadi hakan ba, zazzabin jikinsa ya sauka ne, zafi yake ji sosai. Ganin umarninsa ya jefa ta a gajeren tunani, sai ya fara kokarin cirewa da kansa.
“Sorry, you can go (za ki iya tafiya).
Sai ta ji ba dadi, mene ne a cikin cire safa da takalmi da ta kasa? Bashi da lafiya shine dalili. Bayan wannan ba wani abu.Mikewa ta yi kamar wadda kwai ya fashewa a ciki ta nufi daki zuciyarta babu dadi.
Da ya cire takalman ci gaba ya yi da shan farfesun kadan-kadan. Girkinta yana da wani sinadarin dandano irin na Mammansa. Ya fahimci hakan tun sanda yake cin abincinta, lokacin da tana amarya. Ganin cin abincin nata da yake yi zai haifar da wani bond na daban a tsakaninsu shi ya sa ya daina, ba don ba ya so ba. Auren da ba mai dorewa ba bai kamata ya bari ya yi tasiri mai yawa a zuciyarsa ba.
A nan ya bar bowl da spoon din da ya sha farfesun ya tattara shirginsa ya koma daki. Bai kara fitowa ba, wanka ya yi, sannan ya yi sallolin azahar da laasar da ke kansa, ya bi lafiyar gadonsa ya kwanta bayan ya kashe wayoyinsa.
Tufka da warwara yake, na yadda rayuwarsu ta gaba za ta kasance tsakaninshi da ita.

******
Ta ci abincin dare ta yi shirin kwanciya, amma anya za ta iya barcin nan mijinta na gefe ba shi da lafiya? “Ki daina kiranshi mijinki fa, mijin Mu’azatu dai”. Wata zuciyar ta gyara mata.ď
Har yanzu hotonta da ya kafa musu a falo yana nan. Ta shafa wa kanta lafiya ne ta daina kallon bangaren da hoton yake.
Abdulazeez bai cancanci ki tausaya masa ba, saboda ba sonki yake ba, ko yau din ma da ya kula ki don ba shi da yadda zai yi ne, ba shi da mai taimaka masa. Manta da shi ki yi barcinki.
Amma abin mamaki ta kasa bin wannan shawarar ta zuciya mai gaskiya. Ko ba ya sona Dan Mommah ne, duk wani jininta amana ne a gare ni, ba za ta ga Da na ba lafiya ta kauda kai ba. Ni ma ba so nake ya so ni ba, amma tunda ya fara kyautata min, dole in kyautata masa ko da ba zai gode ba.
Saukowa ta yi daga gadon ta bude wardrove dinta, ta dauko wadataccen mayafi ta lulluba. Kicin ta nufa ta gasa masa karamar kazar gidan gona data yiwa hadin kayan kamshi dana dandano sosai ta yayyanka akan farantita hada da gwangwanin maltinata kinkima a kan tray ta yi dakin nasa.
Tsayawa ta yi a bakin kofar ta yi sallama, kirjinta na dukan uku-uku. Tana jin sautin muryarsa kasa-kasa kamar yana waya, Come in. Ya fada yadda za ta jiyo ci gaba da wayarsa.
Murda kofar ta yi ta shiga, sanyin A.C har ya yi yawa, kamshin turaren da yake yawan amfani da shi (creedaventus) ya gauraye da sanyi da kamshin A.Cn ya bada wani atmosphere mai dadi da sanyaya zuciya.
Karasawa ta yi ta janyo wani dan teburin gilashi karami ta dora tray din hannunta, ta matso da shi gabansa. Wayarsa ya ci gaba da yi, bai ce mata komai ba. Cikin hirarsa ta ji yana fadin, Iv never lost a case, but I lose it today Muazatu. (Ban taba faduwa a shariah ba amma na fadi yau Muazatu). Yanzu haka a kwance nake ba ni da lafiya tun safe.....
Tsaki ta yi ta juya za ta fice, sai jin hannunta ta yi cikin na Abdulazeez, ya riko hannunta ta baya.
Kasa juyowa ta yi, zuciyarta na wani irin tafasa, ita ba ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login