Showing 99001 words to 102000 words out of 168255 words
farko ba ka yi wa Hafsat alkawarin rayuwa mai dorewa da ita ba, kuma ta san wannan. Abu daya ka ke yi wa shi ne SABO! Ba mutuwa ake yi wa kuka ba sabo ne, da sannu zai gushe tamkar ba a yi shi ba. Babu mai mara maka baya ka auri Muazatu kana tare da Hafsat. Matsayin da Hafsat ke da shi babu soyayyah sai emotion. Wani irin emotion na can karkashin zuciya. Wanda a kullum yake da nauyi kamar ansababban dutse an danne shi. Zuciya mugun nama.. ta ci gaba da angiza shi da cewa... Muazatu na jiranka Abdulazeez da tarin soyayyah mara algus..... za ku shimfida rayuwa mai maana irin wadda ka ke buri..... soyayyah irin wadda ka ke mafarki... yadda ta yi maka tanadin kanta tsawon shekarun nan ta tsayar da soyayyarta a kanka kai kadai, ta cancanci ka watsar da komai ka cika alkawarin da ka daukar mata... sai ka rabu da Hafsat ne za su dubi alamarinka da Muazatu da idanun basira.
Hafsat duk wasu alkawururruka da ka daukar mata a yau Allah ya nufa ka cika mata su. Abu daya ya rage ka damka ta a hannun MAHAIFINTA, wanda in Allah ya so Ya yarda wannan ya zama tarihi. Zuciyar ta ci gaba da qawata masa komai na Muazatu ya fi na Hafsat sau dubun dubata. Hafsat har gobe kamata ya yi a ce tana gaban iyayenta suna ci gaba da rainonta... yadda ka shirya rayuwa da matarka ta aure da tarin bukatar gangar jiki da zuciya,me Hafsat za ta iya dauka a ciki? Wane martanin soyayya kake tunanin samu daga gare ta? Muazatun dai! Ita ce daidai da rayuwarka, wadda za ta zage ta nuna maka soyayya dakwanji, da jiki da zuciya.
Haka zuciyarsa ta yi ta kawo wahayi iri-iri na kyakkyawar rayuwar da zai shimfida da Muazatu in ya same ta. Bangaren kyakkyawan tunani ya toshe, idan ma akwai, to son cika alkawarin da ya dauka ya rinjayi komai... A ganinsa in ya cika wannan alkawarin ne zai kubuta daga sahun munafukai, makaryata, mahaintakuma rayuwarsa ta zauna lafiya.
Duk sanda zuciyarsa ta kawo masalaha ga rayuwar ita Hafsat din, daya zuciyar sai ta hambare. Da hujjarta na cewa, ita yar gata ce yanzu... mai iyaye, yan uwa da kakanni babu abin da zai dame ta don ta rabu da kai... Mammah kuwa in za ta yi adalci ai ka yi mata biyayya, lokaci ya zo da za ta karbi naka zabin ta ba ka yancin da Ubangiji ya ce ta baka. A zaman da ka yi da yarta ba ka taba cutar da ita ba... ba ka taba bata mata ba sai ko bisa ajizanci irin na dan adam, ko ka yi kuskuren ma kana kokarin gano kuskurenka da kanka ka yi repenting. Idan ba a gode maka ba a rikon da ka yi wa Hafsat, to a kalla ba za a yi maka tofin Allah tsine ba......!!!
Da wannan kwarin gwiwar Abdulazeez Hamza Atiku ya dauke ido daga kallon Hafsat, ya karasa shiga cikin falon. A lokacin ne Hafsat ta ankara da shigowarsa. Wani irin dadi ta ji a ranta domin sosai ta yi kewarsa a gidan tun fitarsa. Rashin abin yi ne ya sanya ta yin assignment din kuma map din ya yi kyau sosai kamar ba ita ta yi ba. Ga mamakinsa ya kasa hada ido da Suhaanah a yau, kai tsaye ya nufi dakinsa ba tare da ya ce da ita komai ba.
Hafsat ta yi dan jimm! Me ke damun Yayanta Abdulazeez? Ko wani ne ya bato masa rai a waje? Mikewa ta yi da niyyar binshi dakin, amma sai ta dakata. Sun dade da daina shiga dakin junansu. Sannan a lokacin da miji yake cikin fushi matarsa nesa-nesa ya kamata ta yi da shi. Damuwarta shi ne, ta shirya masa abinci mai rai da motsi da za ta so ya ci kafin ya shiga barci. Amma haka ta hakura ta soma tattara kayan zanenta don barin wajen.
A wannan daren mai cike da rudani ga Abdulazeez Dakata daga shi har Hafsat kowanne ya kasa barci. Cikin sulusin dare ya samu takarda ya yi rubutu ya ninke ya adana a lokar gefen gadonsa. Wata irin ajiyar zuciya ya saki ya maida kansa ya jingina a kan filo. Amma ga mamakinsa ya kasa runtsawa. Ya rasa takamaiman abu guda da kwakwalwarsa za ta kama, gabadaya ta hargitse, ta cukwikwiye, duk kuwa da ya yanke hukuncin da zuciyarsa ta fi amincewa da shi din. Kamata yayi ace ya samu (peace of mind) bayan zartas da hukuncin amma kamar ya kara hargitsa kwakwalwar sa fiye da baya.
Hafsat kuma damuwarta me ke damun Abdulazeez ne? Ba ta taba ganinsa cikin wannan yanayin ba. Ko ba ya jin yin magana zai gaya mata ba ya son magana ta yi harkarta ta kyale shi. Amma a yau ko alfarmar hakan ta kasa samu balle ta ga kwayar idanunsa. Ga shi da alama yana cikin rudani irin wanda ba ta taba ganinsa a ciki ba. Ta samu kanta da mikewa ta dauro alwala ta dasa sallar nafila cikin daren. Addua ta ke ko mene ne matsalar Abdulazeez Allah Ya ba shi kyakkyawar mafita, Ya iya masa abin da ba zai iya ba, Ya shige masa a gaba a kan alamuransa (Allah sarki Hafsat).
******
Wani barci ne mai nauyi ya sure ta gabanin asubahi, bayan ta idar da sallar asubah. Ba ita ta farka ba sai wayewar gari tangararan. Lokacin tuni Abdulazeez ya tsufa a office. Takaicin kanta ne mai tsanani ya kamata. Haka ta mike ta yi wanka ta shiga kicin don sama wa cikinta abin da zai ci.
Abdulazeez bai dawo gidan ba har ta yi shirin barci, gidansu ya tafi a can ya ci abinci. Hatta Mammah ta lura cikin damuwa yake, amma da bai furta ba sai ta kyale shi. Yana gidan har karfe goma, Mammah ke tambayarsa ko ya gaya wa Hafsat maganar tafiyarsu Yola? Ya ce, abubuwa sun masa yawa, ya manta. Amma da ya koma zai gaya mata. Fada sosai Mammah ta hau yi masa na ba ya daukan abubuwan kowa da muhimmanci sai nasa. Hakuri ya ba ta ya kuma tabbatar mata yau zai gaya mata.
Da ya dawo ta dade da shigewa daki ta kashe wuta ta kwanta. Ko ta yi barci ko ba ta yi ba, ba zai iya cewa ba. Text ya yi mata a ciki ya ce ta shirya kayanta da na bukata wanda zai yi mata sati biyu za su tafi jihar Adamawa jibi dukkansu, har su Mammah.
Washegari tana kunna waya abin da ta fara gani kenan. Sai kawai ta ji gabanta ya fadi, me za su je yo wa a Yola? Wa suka sani a can? Har kuma sati biyu? Allah ya so ta hutunsu na sati hudu ne. A hakan dai cike da zullumi ta soma shiri tun a lokacin.
Karin kumallo mai kyau ta shirya ma Abdulazeez a safiyar ranar. Amma sai tsintar bude masa get da fitarsa ta yi tun kafin lokacin da ya saba tafiya office ya yi. Jikinta ya kara yin sanyi fiye da yadda yake a mace tun daren jiya. Haka ta kare wunin sukuku tana shirya kayanta cikin travelling bag.
Haka ya yi ta zillewa haduwarsu har zuwa ranar tafiya. Ba su hadu ba sai asubahin ranar da ya fito cikin shiri da nashi jakar kayan marasa yawa. A falo ya same ta a shirye don kusan kwanan zaune ta yi saboda zuciyarta ta kasa sukuni balle ta yi barci. Jikinta ne kawai yake ba ta canjin Abdulazeez yana da nasaba da wannan tafiyar.Ya kalle ta kasa-kasa yace ta koma daki ta canza mayafi wannan yayi shara-shara, nan ta ajiye hand-bagdinta ta koma dakin don bin umarninsa. Mamaki fal ranta don ita bata ga laifin mayafin data yafa ba, yanada kauri ba laifi kuma yanada girma, ita data fi amfani da abaya ma da dan mayafinsu bai taba cewa komai ba sai yau akan babban gyale. Tunda suka shiga mota ta gaishe shi, ya amsa bai kara ce mata komai ba. Nauyin da zuciyarsa ta yi kawai ya ishe shi.
A Asokoro ma ba su bata lokaci ba kowa a shirye yake. A motoci za su yi tafiyar. Manyan jifa-jifai uku na Dr. Hamza, sun biya sun dauki Uncle Abdulkarim da yaransa, za su tsaya a Kano su dauki su Adda Hafsatu don Anty Zuwaira ta ce ita kam ba za ta samu zuwa ba. Sanin halinta mijin bai takura ta ba.
Wajejen karfe sha daya na rana suna cikin Kano. Babu bata lokaci su Adda ma sun shirya su kawai ake jira su iso. Motar farko Abdulazeez ke ja, Hafsat da Mammah, Baba Azumi da Adda Hafsatu da Daddy ne a ciki, ta biyu Baffa Atiku, Dr. Idris Dakata, matarsa Dr. Tawheedah, matar Ibrahimada Minister Abdulkareem da dansa Ramadan ne a ciki, Ibrahima ke jan su, ta karshe su Aunty Luba, Murja, Mariya, Furerah, Usman da Haleem dasu Farhan, direban Daddy Salisu ke janye da ita suka kama hanyar Adamawa. Daddy ya ce, ba za su daura musu nauyi ba, Hotel zai kama musu gabadaya in sun isa.
Ana ta hirarraki a motar banda Hafsat da Abdulazeez, wanda ke tuki cikin nutsuwa da kwarewar tuki. Daddy ne a gefensa, a kujerar baya ta farko ita da Mammah ne, a ta biyu Baba Azumi da Adda Hafsatu. Hafsat kwantar da kanta ta yi a kujerar gabanta tun tana tunane-tunane har ta rasa na kamawa, barcin da ta ci bashinsa ya yi awon gaba da ita. In lokacin sallah ya yi suna tsayawa a gidan mai su yi sallah su ci abincin da Mammah ta yo musu guzuri sannan su ci gaba.
Akai-akai suna waya shi da Sagir har Allah ya kai su Jimeta lafiya, misalin goma na dare. Don haka ya gaya wa Sagir ba za su samu shigowa a daren ba sai gobe da safe sun wuce masauki. Sagir ya yi korafin cewa, don me ba za su karaso su sauka gidansu ba? Ya ce, suna da yyawa ne, sannan shi ma ba tsarinsa ba ne tsarin Daddy ne su yi hakuri. Sagir ya ce ya fada masa sunan hotel din da suke, zai kawo abincin da aka tanadar musu. Ya gaya masa sunan (Jireh Suites).
A reception din hotel din ya tarbi Sagir, ya karbi kabakin abincin ya kakkai musu, Mammah da Daddy daki daya suke, Baffa Atiku shi kadai. AbdulkarimDakata shikadai a dakinsa, Dr.Idris da matarsa Dr. Tawheedah daki daya, Usman, Uncle Ibrahim,Haleem dasu Farhan daki daya, Sauran yan tafiya duka mata ne daki guda suka hada. Daga reception Sagir ya koma.
Sun ci sun sha daga abincin fulanin usli, sun sha fura da nono kindirmo har sun gode Allah, sannan kowannen ya nemi makwanci don huta gajiya. Abdulazeez na tare da Baffa Atiku, Hafsat na tare da su Aunty Luba, Daddy dai ya dauka daki daya Abdulazeez din ya kama musu shi da Hafsat din tunda shi ya kakkama dakunan,ko kusa ba wanda ya gaya mata abin da ya kawo su wannan gari mai dumbin albarka.
Shi da Baffa Atiku suka kwana, wannan kadai ya debe masa kaso hamsin na daga damuwar da ke nukurkusar zuciyarsa. Domin dai Baffan kusan kwana suka yi yana ba shi labarin kuruciyarsa, ya gaya masa hesbrave, genius, and patriotictun yana yaro, babu abin da ke girgiza shi a kan raayinsa da determinations dinsa na son zama babban lauyan gwamnati. Yana so ya ci gaba da zama hakan a yanzu da ya zama cikakken mutum mamallakin iyali. Ya cigaba da amfani da wadannan qualities din akan aikinsa da iyalinsa.
Ji ya yi gwiwoyinsa sun yi wani irin sagewa... Does these qualities are still with him? Da sauri ya girgiza kai cikin musanta hakan da cewaNo,they areabsolutely not. Hes only brave on Muazatu yanzu, but not on anybody and anything else. Juyar da kai ya yi ya ci gaba da sauraron labaran da Kakansa ke ba shi na rayuwarsa ta baya, yana diba yana zuba su a sikeli yana auna su da rayuwarsa ta yanzu.Sai ya ga cewa; ratar da ke a tsakani mai tsananin fadi da girma ce tunda ya kasa yi wa kowa bravity da patriotic din sai Muazatu!!!
A dakin iyayen, Mammah na shirin kwanciya ta ce da mijinta Dr. Hamza. Ko ka lura da sauyin yanayi a tare da Abdulazeez da Addah? Tunda muka taho ba sa magana da junansu har muka iso. Sannan da ya zo kama daki bai kama musu tare ba ina lura. Haka kawai sai in ji gabana yana yankewa ya fadi in na kalle su tun tahowarmu.
Daddy ya ja bargo ya rufa ya kashe fitila mai haske.
Tsohuwar nan kin fiya sa ido, ina ruwanki da tsakanin miji da mata? In kuma fadan masoya ne suka yi a tsakaninsu fa? Ko harshe da hakori ai ana sabawa. Don Allah kada ki bata min daren yau da Psychological Investigations dinki. Kanwar Haleem nake so mu samo tunda gobe za a kwace Hafsat.... Ya fada yana murmushi don son gusar mata da damuwarta.
Fuska ta yi sosai jin fatan da yake mata (gobe zaa kwace Hafsat), sannan ta isa gare shi tana fadin,
Mai raba ni da yata ko girgizar kasa albarka. Mu je dai su ganta su san da zamanta, su san labarin tasu diyar, in koma da abata.
SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI
07030137870
*Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama*
******
Tafe suke cikin kwazazzabo cikin farar mota hilux mai hawa kowanne irin tudu da kwari cikin wani kauye wai shi Kufana a Southern Kaduna. Muazatu na ta korafi, Regina ta ce, Dadina da ke wutar ciki Muazatu, garaje da rashin hakuri. Tunda na ce miki matsala aka samu kuma zai gyara ki adana min wannan rashin hakurin naki har mu isa.
Dole Muazatu ta yi shiru ba don ta so ba. A ganinta Regina tana daukar alamarinta da wasa don ba ita ta fada cikin abin da ta fada ba. Har suka iso karkashin wata bishiyar kanya nesa da wani hawan dutse. Regina ta faka motar. Tare suka fito ta sa mukulli ta rufe motar, fili ne fetal ba gida gaba ba gida baya, sai wani dogon dutse a tsakiyar filin. Wannan dutsen Regina da Muazatu suka nufa har suka iso gabansa, kowacce ta tattare zani suka fara hawa dutsen nan kamar kadangaru daya na zamowa daya na tallafo ta har suka iso bakin wani dogon kogo na rarakakken dutse, Muazatu takalmi, dankwali da mayafi duk a hannu saboda wahala, har hawaye ta ke yi. Zuwanta wannan wajen na biyu kenan bayan Regina ta ce in ka zo sau daya ba ka kara dawowa bukatarka ta gama biya.
Haduwarta ta farko da Abdulazeez Dakata a ofishin mahaifinta ta fara sonsa kamar ta ciro rai ta ba shi. Ba irin kyautata masa da ba ta yi ba don ya so ta, bata taba tunanin neman soyayyarsa ta wata hanya bayan kyautatawa ba. Amma sai ya bada mata kasa a ido, ta hanyar nuna mata shi babu wannan a gabansa, yana da abin da ya kawo shi Law School ta yi hakuri ya ci gaba da bata girman da yake ba ta na kasancewar ta yar malaminsa. Duk wasu dabarunta sun kare, ta kasa canza wannan murdadden lauyan data fahimci ba abinda ke canza masa wani irin raayin rikau irin nasa.
Regina abokiyar karatunta ce wadda ta fito daga jihar Benue. Hira ta yi hira a tsakaninsu irin ta shaqiqan aminairannan sai ta ke gaya mata yadda ta samu kanta a kan Abdulazeez da raddin sa gare ta, da kuma matsanancin halin data ke ciki akan hakan. Ba da wata manufa ta fadawa Regina ba sai don ta rage radadin dake ranta, irin wanda dan adam ke samu idan ya raba damuwarsa da wani nasa. Wani sakaran kallo Regina ta yi mata ta ce.
Ke wa ya gaya miki yanzu ana tarar namiji haka zikau, a ce ana sonsa ba tare da an tabbatar an kama shi a hannu ba?
Muazatu ta ce, ita ba za ta iya biye-biyen malamai ba, saboda in aka fara baa dainawa, ta ga Mamanta na yi amma ita ta hane ta, ta sha ce da itaadashi ne wanda baa dauka. Regina ta ce, Ina da inda zan kai ki a yi miki aiki a kansa, in aka je sau daya babu komawa, kuma aikinsa na har kabari ne (har wanda aka yi wa ya mutu). Idan kuma na ce ki kara komawa kada ki kara kallon inda nake.
(Mafarin zuwan Muazatu Rufai wajen boka Chiwonzhu a Kaduna-South, kauyen Kufana).
A kan idonsu ya kamo tunkiya ya kalli kudu ya farke mata ciki, zuciyar tunkiyar ya tsigo tana yararin jini ya dora ta a kan wani kasko ya zuba hayaki a kai ta hau tiriri har sai da jinin jikinta ya kone. Bata zuciyar ya yi a tafin hannunta ya ce ta gutsire ta sau goma sha biyu, duk gutsira daya ta ambaci sunansa har ta cinye. Duk kyankyamin da Muazatu ke ji haka ta cinye danyar zuciyar tunkiyar nan. Ya hada ta da wani garin magani ya ce a ciyar da shi a abinci tsayin kwana talatin ba tsallakewa. Wanda ta nufa da wannan asiri ba zai taba samun nutsuwa da kwanciyar hankali ba har sai ya aure ta. Zai iya ja da kowa a kanta, in yace kowa yana nufin kowahar sai ya aure ta.
Wannan shi ne makasudin Muazatu na fara ciyar da Abdulazeez abincin gidansu, daidai da rana daya ba ta taba kuskurewa ba, har zuwa cikar waadin da boka ya debar mata.
Dawowarsu a yau tsibirin boka Chiwonzhu ga su a gabansa, tun shigowarsu yake dawurwura a kansu yana zagaye su. Yana bugun kan Muazatu da wani gashi yana wasu maganganu da ba sa fahinta kafin ya yi zaman yan bori a gabansu. Idan ya yi hakan, yana jira ka fadi abin da ya kawo ka ne, ya gama duba matsalolinka.
Ya daina damuwa da ni, ya ki zuwa mu yi aure, ya daina kirana, ya daina amsa nawa kiran. Nema