Showing 102001 words to 105000 words out of 168255 words

Chapter 35 - Auren Kwangila Book 4 Hausa Novel Complete

Takori   

12 Dec 2024

638

yake ya fasa aurena daga dukkan alamu.

Kakansa ya lalata komai yarinya!.

Gabadaya suka dago a firgice suka dube shi.
Wani farin dattijo mai farin gemanya, mai tarin shekaru rututu. Yana can Arewacin Najeriya yana karya duk wani sammu da ke jikinsu ba tare da su kansu sun sani ba!!!.
Idanun Muazatu suka firfito cikin tashin hankali.
Yanzu ba wani taimako da za ka yi min ya aure ni? Ta fada cikin son kecewa da kuka.
Ko mun yi zai sake lalatawa, amma akwai aiki guda daya wanda ba yadda zai yi da shi sai dai daga gare ki amincewar take.
Fadi ko mene ne wallahi zan iya in dai ba zan rasa Abdulazeez ba. Muazatu ta fada tana kuka tare da zubewa a gaban Chiwonzhu.
Zai iya zama mai tsauri a gare ki, amma ina tabbatar miki kamar yankar wuka yake. Kuma ba a jikin jikansa zai zauna ba balle ya karya, a jikinki zai zauna har gaban abada.In ba ni ba babu mai iya karya shi.
Rokonsa Muazatu ta shiga yi ya yi mata wannan aikin, ko nawa ne za ta biya. Ita dai burinta ta auri Abdulazeez ko ta halin kaka.
Chiwonzhu ya ce, Aikin ba ya bukatar ko sisinki. Magani ne zan shafa a jikina in sadu da ke, idan ba a yi auren nan cikin sati biyu ba, kada ki kara dawowa inda nake.
A hankali Muazatu ta soma ja da baya, Regina ta soma harararta, Me ye a ciki? Ba kanki aka soma ba, na kwanta da shi ya fi sau goma, me ya ragu a jikina?
Girgiza kai Muazatu ta shiga yi tana kara ja da baya, Im a virgin Regina, aladarshi ba daya ta ke da tamu ba. Idan na je masa babu budurci ba zan taba yin daraja a idonsa ba....
Kuma aka ce miki haka za mu kyale shi bayan an yi auren?
Kamar ta ce da ita, An zo gurin, maganar Mamana ta tabbata;in aka farabinsu ba za a daina ba. Nikuma ba zan iya jura ba, ko zuwa wajen nan kadai balai ne balle hada jiki da wannan kazamin mutumin.
Shi dai boka wasu harkokinsa ya shiga yi a cikin kogon ya manta da su ita da kawarta suna ta jayayya. Da suka fara isarsa ya ce, idan ba ta amince ba su tattara su bar gabansa. Muazatu ta wawuri jakarta ta mike kan su ce me ye wannan har ta kai kofar kogon. Chiwonzhu ya dube ta cikin takaici, Ki sa a ranki ke da wannan mutumin har abada! Ba zai taba aurenki ba. Kina iya gwada wani bayan ni, don ki tabbatar da abin da na fada.
Da kuka wiwi Muazatu ta fito daga kogon Chiwonzhu, ta soma kokarin saukowa daga dutsen, ga rashin nutsuwa ga tashin hankalin abin da ya fada. Santsin dutsen da ta ke kokarin bi a hankali ya kwashi sassalkar kafarta ta yo suuuufa tun daga sama har kasa ta fadi a kan kwankwasonta.
Wata azababbiyar kara ta saki Regina na kallonta daga saman dutsen ta yi tsaki ta ci gaba da saukowa a hankali har ta sauko tsaf, ta kama ta ta mikar tana zuba ihu a haka suka karasa motarsu. Regina ta watsa ta kujerar baya ta tuka motar suka tafi.
Kwananta uku tana jinyar Muazatu wadda ko zama ba ta iya yi sai kwanciya, amma Regina don mugunta ta ki kai ta asibiti. Kwana ta ke kuka tana gaya mata pelvic-girdle dinta (kashin kugu) ya karye. Da ta gaji ta tattara ta ta sa a jirgin Lagos ta koma gida.
A wheel-chair maaikatan jirgin suka turo Muazatu zuwa reception. Nan ta fiddo waya ta kira Babanta ya turo a dauke ta tana filin jirgi ta karye. Da kansa ya zo cikin tashin hankali har da Mamanta suka kwashe ta sai wani babban asibitin kashi. Likitoci suka duba ta sosai, nan suka gayawa Babanta ta samu tsagewar kashi a kashin kugunta za a yi mata aiki. Ya yi addua kada abin ya taba lakarta (spine). Hankalin Attorney General ya yi mummunan tashi, Mamanta sai kuka.
Bayan an yi aikin an fiddo ta Babanta da Mamanta suka sanya ta a gaba ta gaya musu inda ta je ba da saninsu ba kwana hudu ta karye. Tana kuka cikin zafin ciwo ta gaya musu tun zuwansu na farko wajen Chiwonzhu da Regina a kan Abdulazeez har kawo na wannan karon da abin da ya rikitata har ta sulmiyo. Ran Attorney ya yi mummunan baci, idanunsa ya yi jazir ya ce.
Wato duk tsawon lokacin nan charming din Abdulazeez ki ka yi don ya so ki? Na raine ki kan ki zamo mai son kanki ki zama heartless Muazatu? Ina ki ka kai darajar da Allah ya yi miki ta diya mace? Shin daga kan Abdulazeez aka ce maza sun kare a duniya? Mene ne farin cikinki na zama da wanda ki ka san ba don Allah yake sonki ba? Kina tsammanin akwai abin da ba kararre ba a wannan duniyar? Muazatu kin san azabar da ki ka gana wa zuciyarsa tsayin wannan lokacin? Kin san ya ya zuciyar tunkiya ta ke? Haka ake nufin ki maida zuciyar mijin aurenki. To ina batun samun aljannan kuma tunda kin maida zuciyarsa ta tunkiya? Yau da kin ba wa bokan nan kanki da na yi tirr da haihuwar ki. Afuwar da zan miki kenan tunda ki ka tsira da wannan hankalin. Kin san halin da ki ka jefa zuciyarsa tsayin wannan lokacin Muazatu?
Gaskiya na ga iyayensa na yin baya-baya da maganar aurenki, ashe su suka san abin da suke gani daga gare shi a kanki. To bari ki ji in gaya miki aure zan yi miki karshen watan nan. Ba irin maneman da Allah bai baki ba kina wulakanta su kike tsaye nacin wanda baya son ki. Jinina yafi karfin irin wannan auren. Ko a waya ki ka kara kiran Abdulazeez ban yafe miki ba duniya da lahira!
Kuka Muazatu ta sa, Daddy kada ka yi min haka, wallahi tun kafin hakan yana sona, tun kafin in je Kadunan muke tare.
Mamanta ta kai hannu ta buge bakinta. Ban ce kada ki taba bin bokaye ba a rayuwarki? Ban gaya miki adashin da babu dauka ba ne? Ban gaya miki in aka fara baa dainawa ba? Kin biyewa arnan kawayenki kafirai wadanda su basu san Allah shi ke sawa Yake hanawa ba? To wallahi ni ma na fada ko shi ya saura namiji a duniya ba za ki aure shi ba! Abin da ba ki sani ba ma iyayensa sun dade da yi masa aure, jiya wata kawar Mamansa ta gaya min mun hadu a wajen conference, ke ya mayar sakarai, shashasha.
Kuka Muazatu ke yi har ta ji babu dadi, Mummy na sani fa! Ya yi min alkawarin zai sake ta in na gama law-school mu yi aure.
Ga mamakinta daga uwar har uban sai suka bushe da dariya, So he is playingwith your senses duk da asirin naki? Ya dauke ki mai kwakwalwar yar tsana. Tunda ki ke kin taba jin wannan almarar? In ji Maman.
Attorney ficewa ya yi don takaici bai kara dawowa asibitin ba har bayan kwana biyu. Shi kadai ya san me yake shirya mata.
Akwai wani Grand Khadi abokinsa tun na karatu, dansa Barrister Muntada ya dade yana son Muazatu ba ta ma sani ba. Yana aiki a court of appeal ta jihar Lagos. Mahaifinsa ya biyo ta kan Daddynta yana nema wa dan nasa izinin a bashi dama ya fara nemanta. Attorney ya ce ya dakata saboda akwai maganar wani studentdinsa a yanzu a hannunsu, amma bai san me Allah zai zaba mata ba. A lokacin ya fadi hakan ne ganin tsohon Ambassador Hamza na yin baya-baya da zancen. To a ranar da ya bar asibitin bai kwanta ba sai da ya nemi Grand Khadi Akilu Lawal ya ce ya baiwa Muntada Muazatu, ko yaushe suka shirya su fito. Alkalan sun shirya komai a tsakaninsu ba tare da Attorney ya kara bi ta kan Muazatu ba a wannan lokacin, don ya fara tunanin bayan buguwar tata a kwankwaso kanta ma ya bugu ta fara fita daga seti a kan Abdulazeez.
Wannan kenan.

******
Kwanan Hajiya maryam biyar a asibitin DIFF sannan ne aka samu jikinta ya sauka taji sauki sosai likita ya ba su sallama tare da kaidojinsa cikin buhu, hatta abincinta ya canza shi ya mayar da shi zuwa na masu lalurar hawan jini. Duka jamaar gidan Dr. Ya hana su zuwa tun zuwansu na farko ya ce hutu ta ke bukata, don ranar da suka zo sai da jininta ya kara hawa. Hafsat ce kawai tare da ita, ita ma ba wata hira suke ba don mafiya yawan lokuta ma tana barci.

Shi kadai ya san cikin yanayin da ya kwana a wannan rana, zai iya rantsuwa cewa idanunsa ba su runtsa ba. Yana da tabbacin Mammah za ta yi fushi duk ranar da ya karar da auren kwangilarsa amma bai yi zaton alamarin zai yi girman da har zai taba lafiyarta ba. Their Mum is always healthy and vibrant, always busy taking care of them and their Dad, yau bakin cikinsa ya jaza mata cuta ya kwantar da ita a kan kafafunta. Ba ta sani ba, ya fi ta shiga damuwar abin da ya aikata. Ya runtse ido ya aikata ne don ya tserar da kansa daga tozarta alkawari.
Zan yi repenting Mammah... Ki ba ni dama! One last chance! Ya fada a fili ya fi sau shurin masaki.
Washegari har ofishin Ahmad ya tadda shi, kallo daya ESQ Ahmad Kutama ya yi masa ya tabbatar alamarin bai tafi yadda suka so ba.
“Be a man. Abin da ya fara ce da shi kenan.
Komai ya cabe Ahmad,yadda bazan iya gyara shi ba. Mammah ta ji. Shes now on admission. Na tabbata ni ne sanadi.
Ga mamakin Ahmad sai ga hawaye sun sauko a fuskar Abdulazeez shar-shar! Hannunsa Abdulazeez ya kama ya ce, What will I do now? In Muazatu ce na fasa aurenta, ba ni da wani sauran buri a kanta. I need my wife back, and my Mums forgiveness.
Ahmad ya jinjina kai kafin ya ce Daga yau ka daina jayayya da iyaye, ka kasance mai godiya da abin da Allah ya baka ko baka sonshi komai kankantarsa, ka daina zurfafawa a soyayya ko kiyayya, komai mai iya canzawa ne a duniya banda mulkin Allah da ikonSa a kanmu. Ba duka abin da muka kallafawa rai muna so bane alkhairi a garemu. Wasu alkahairan na rayuwar mu a lullube suke bamu san dasu ba amma Ubangijin da ya halicce mu ya yi mana tanadinsu in munyi hakuri mun bi iyayenmu zasu tadda mu har inda muke. Mu daina cewa lallai sai mun mallaki abinda muke so ko ta halin kaka. Mu roki Allah zabinsa ba zabin zuciyarmu ba. Abdulazeez ina mai fada maka da babbar murya ka yi kuskure! Ba Mamanka kawai ka sabawa ba har da Ubangijin da ya halicce ka. Aure ba abin wasa ba ne, umarni ne na Ubangiji. Amma ka yi shi ba da tsarkakkiyar niyya ba, duk auren da aka yi shi babu ikhlasi kuma aka kayyade masa waadi bai inganta ba a shariah. Bana tunanin ko ka rufe zancen nan ka karbe takardarka daga hannun Hafsat ka ci gaba da zama da ita auren ku ya gyaru duk da dai ni ba malami bane. Ka kwashe fiyeda shekara ba ka sauke hakkin aure da Allah ya rataya a wuyanka ba, wanda shi ne gundarin auren. Wasu malaman ma sun ce watanni uku babu saduwa tsakanin maaurata kuma babu hujja ta rashin lafiya ko tafiya, auren ya lalace.
Don haka sanin da iyayenku suka yi ina ganin shi ne daidai. Su zasu nemi yadda zasu gyara muku auren idan sun huce. Ka roki Allah gafarar wannan zunubin da tuba nasuuhan. In aka ce tuba nasuuhan wato a yi shi da niyyar ba za a sake maimaita laifin ba.
A yanzu kam, ai kada ma ka doshe su da bukatar su maida maka Hafsat, hakan zai zamo tamkar zubawa wuta fetur ne. Suna kan tsinin fushinsu, kuskure ne ka riga ka tafka, sun maka zabin da suke ganin shi ne daidai da rayuwarka da raayin su ka ce ba su iya ba, kai ne ka iya. Saboda sun tsaya maka kayi karatun zamani har kana ganin ka fisu sanin zamanin. Sai ka jure duk wani punishment da za ka fuskanta daga gare su, ka kwantar da kai kawai ka amshi laifinka da hannu bibbiyu, duk wani bayani da zaka yi musu bazai gamsar dasu ba a yanzu, amma ga wata shawara... ka nemi hadin kan matarka.
A sanyaye Abdulazeez ya dago, cikin ransa yarda yake da duk kalaman da ke fita bakin Ahmad, ya ce. Kutama, Suhaana ta yanke duk wani communication gap da ke tsakaninmu. Daga ranar da muka rabu ba ta kara amfani da wayarta ba. Ina jin kunya in je gidanmu in ce zan ganta, ban da nan din kuma ban san inda zan ganta ba, ba ta zuwa koina Ahmad, ko da makaranta.
Dariya Ahmad ya yiya ce Haba Abdulazeez kaman ba namiji ba? Kada ka bada maza, mazan ma mafiya hikima da sarrafa fasaha (lauyoyi). Kai za ka nemo hanyoyin communicating da ita. Kada ka manta weakness din mata daya ne (soyayyah). Balle kai dinnan (brainlliant and handsome hunk Abdulazeez) wanda na tabbata Hafsat ta dade da macewa akan ka. Ka fi Romeo iya soyayyah, ka fi (William Shakespeare) iya sarrafa harshe wallahi za ka sha mamaki.
Sai da ya sa Abdulazeez murmushin da bai shirya ba amma bai ce masa komai ba. Damuwar dake cin sa a zuci ta hana shi bawa zancen nasa muhimmanci.









**SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI
07030137870

*Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama*
****
Tunda suka dawo gida daga asibiti Hafsa ke hidima da Mammah, ta hana ta yin komai na gidan, girki ita ke yi, nasu daban na Mammah daban. Baba Azumi na taya ta da gyaran gida da tsabtarsa, wanke-wanke da shara. Ga Ismael na debe mata kewa da hirarrakin budurwarsa da yake matukar so Wasila, in ya je zance ya dawo duk hirar da aka yi a kunnenta za ta kare. Duk da baa gama hirar ba tareda sunyi fada ba saboda wasan kanin miji irin na Ismael mai ban takaici. Su ba yara ba ne daga shi har Usman, ganinta a gida da halin da Mammah ke ciki lokacin da suka dawo ya fahimtar da su abin da ya faru ba tare da kowa ya zaunar da su ya gaya musu ba. A zuciyar Ismael bai yi mamaki ba in ya tuno abin da ya faru tsakaninsa da Yayan nasa kafin auren. Ya tuno zuwansu na farko gidan nasu, da yadda aka yi kan hoton budurwar falo wadda ya tabbata budurwar Abdulazeez ce don ya tuna inda ya ganta bai fada bane a lokacin saboda Mammah. Ranar call tothe bar ceremoney ne na Yayan nasu. Ita ce ta kawo musu abinci. Ba tun yau ba ya san Yayansa is very selective and ideal a kan macen aure. Amma bai ga inda wadannan halaye suka yi proving kansu a gare shi ba in dai a Muazatu ya kare. Ko ta ina ba su daidaita ba, tarbiyyah, aladu, dabiu da halayya. Daga ganinta girman kudu ce, kuma sakakka, ba kunya ba kamun kai, ba aladun Malam Bahaushe ko daya a tare da ita. Da ya kalle ta sosai ma sai ya ga kamar ba bahaushiya bace. Suhaanah kuwa ai matar manya ce ko shi ba zai gaya mata komai ba banda zurfin ilmi wanda in yayi hakuri nata na tafe yanzu take nemansa. Sun samu labarin ganin dangin Suhaanah da aka yi kafin dawowarsu. An ce fadan da babu ruwanka dadin kallo gare shi. A kwayar idon Yayansa ya ga alamari mai girma a kan Suhaanah ranar da ya sanya ta gaba da tsokana a gidansu. Don haka ya san ko ma mene ne wannan ba shi ne karshen auren Yaya Azeez da Hafsat-Suhaanah ba. Shi Usman dama dan ba ruwana ne, bai kawo komai a ransa ba kuma bai tambaya ba, shi ya ma dauka zaman da ta ke yi a gidan din jinyar Mammah ta ke yi.
Yau kwanansu biyar da dawowa daga asibiti Hajiya Maryam ta dan fara sakin ranta, har suna hira da ita. A daren ranar ta shiga ta tadda Hafsatun a dakinta tana shirin bacci. Irin zaman da ta yi a gefen gadonta da yanayin fuskarta ya tabbatar mata muhimmiyar magana ta kawo ta. Barin komai ta yi ta zo ta zauna a gefen kafafunta. Hajiya Maryam ta daga ido ta dube ta, kullum kara ramewa ta ke a tsaye kamar kudin guzuri. Ta juyar da kai cikin takaici ta ce, Zuwa na yi mu yi magana Addah.
Kanta ta sunkuyar tana sauraronta.
Kina da iddarshi a kanki?
Dagowa ta yi ta dubi Mammah cikin rashin fahimtar Hausarta, har gobe Hausa mai tsauri na yi wa Hafsat wuyar ganewa. Hajiya Maryam ta fahimce ta sai ta maida bayanin nata gwari-gwari.
Na ce ya taba kwanciya da ke?
Kasa ta kara yi da kanta kamar tace da kasar ta hadiyeta ta huta, kunya, daburcewa da kidimewa babu wanda babuwannan lokacin a tareda ita. How could she say to his mother something like that (ta ya ya za ta iya fadawa mahaifiyarsa wani abu kamar wannan)? Da za ta iya da ta ce da ita, sam ita ba ta sani ba. Ya sha kai hannunshi gare ta,he even kissed her, but they had never have it. In wannan shi ne abin da ta ke son ji.
Maimakon hakan sai ta soma shesshekar kuka. Ba ta son tuna komai da ya dangance shi, zuciyarta ba ta da karfin dauka. Haushi ya kama Hajiya Maryam, da babbar murya ta ce Addah!
Ta dago kai idanunta jage-jage da hawaye, ta ce. Tambayarki nake yi don in soma lissafa kwanakin iddarki, na ce ya taba ki?
Girgiza kai ta yi alamar aah. Wani bacin rai ya kara mamayar Hajiya Maryam, kiyayyar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login