Showing 27001 words to 30000 words out of 139192 words

Chapter 10 - Kanwata Book One Complete Hausa Novel

Jiddah   

27 Sep 2025

897

jiya tana kuka take tambayarta me Fadila tayi ake dukanta? Yarinyar tace wai kisan kai tayi ta kashe mutumin daya d'aukota, gudu Amrah tayi taje wurin Fadila ta riko kafafunta tana kuka tace "Adda meyasa zakiyi haka? Nice nayi Abu kuma ke zaki karb'i hukunci?"

Fadila girgiza mata kai kawai takeyi, Da sauri Amrah taje wurin Guyson tace "wallahi nice nayi kisan ba itaba ka yadda dani"

Wani dariyan mugunta Guyson yayi yace "na lura yarannan kunaso Ku rainamin hankali, ita tayi kisa na kamata dumu dumu kizo kinacemin kece kikayi?"

Amrah tafara rantse rantse ganin tana raina mishi hankali yasa yabar mata wurin gaba d'aya ko magana baiyi mata ba, Baby kuka take tsakani da Allah tana rokansu su kyale Fadila amma saida sukaga ta daina numfashi kafin suka kyaleta, kuka Baby takeyi ganin Fadila ta daina numfashi, haka ta kwanta a gefenta har bacci ya d'aukesu dukansu, Fadila ta rufe idonta ne sabida hankalin Baby ya kwanta amma yanda takeji bazata iya bacci ba jikinta rad'ad'i yakeyi mata, gashi hannunta yana ciwo kuma ba damar kuncewa, haka har garin Allah ya waye musu, yanda Fadila taga rana haka taga dare, saida Guyson yaga ta galabaita jikinta yagaya mata yasa yace a kwanceta, ana kwanceta tafad'i ta sume ihu Baby tayi ganin Fadila bata motsi, tazata ko mutuwa Fadila tayi ganin yanda tafad'i, Fatima da Zainab ne sukazo suka taimaka mata tareda d'agota suka kaita d'aki Baby sai kuka takeyi, Fatima ce tafara bata hakauri har tad'an sauko, kwantar da Fadila sukayi akan gadon har tayi bacci da kyar take fitarda numfashi.

   

        "Amrah yau satinta biyu agidansu Kamal ba abunda yake shiga tsakaninsu sai aisuwa dukda wani lokacin idan ta gaidashi baya amsawa wani lokacin kuma yana zama har suyi hira sama sama, yau takama litinin Kamal ne yayi shirin zuwa office cikin bakin Riga da wando fari, jakarshi ya rayata ya juya wurin Amrah wacce ta xuba mishi na mujiya, d'aga mata gira yayi yace "lafiya?"

Amrah dukar da kanta tayi tace "kayi kyau yaya Kamal"

'Dan murmushi yayi sannan yace "kema kinyi kyau" yana fad'an haka yafice, wurin madubi ta nufa tana duba kanta daga sama har kasa, wandone a jikinta Wanda yad'an wuce gwiwanta da kad'an sai Riga me hannun vest Wanda bai rufe cibiyarta ba sai ulan net data tumbusa gashinta Wanda bata tajeba aciki, murmushi tayi Wanda yakarayi mats kyau lokaci d'aya takuma had'e fuska ko me ta tuna oho.

      "Kamal tuki yakeyi cikin nishad'i, baisan meya sameshi ba a 'yan kwanakinnan yaji soyayyar Smrah yadawo mishi sabo dal bayan wasu shekaru da suka wuce, lumshe ido yayi tunawa da yanda yabarta tana sakin murmushi Wanda shikad'ai yakejin abinda yakeji duk lokacinda Amrah tayi murmushi, yamutsa fuska yayi a lokaci d'aya dariyanshi ya koma ciki, kome ya tuna shima oho.

         " jikin Fadila yayi sauki, sun koma gidan jiya na aikin bauta a cikin gidan, yauma kamar kullum Fadila ce take shara kasancewar yanzu itace kad'ai take share cikin gidan kuma ta d'ibo ruwa shine hukuncin da Guyson ya bata, Baby tana mugun tausayawa Fadila wani lokacin Idan Fadila tana aikin saita rakub'e jikin bango wajenda tasan babu wanda zai ganta tayita kuka harta gode Allah, bayan isha'i Guyson yashigo gidan yace musu gobe zasuyi many an Baki wata kilama gone dukka 'yammatan gidan zasu kwashe, jin wannan maganar ya rud'a 'yammatan sun tsorata matuka, bayan ya tafi Fadila ta mike tace "yanzu haka zamu karashe rayuwarmu anan gidan? Yakamata munemi mafita run kafin dare yayi mana koya kuka gani?"

Kowa yace ya yadda amma basusan wani mafita zasu nema ba, Fadila tace "had'e kai zamuyi waje guda musamu mufidda mutum d'aya a cikin gidannan taje tayiwa 'yan sanda bayani, wata kila musamu mafita"

Kowa yace ya amince.

     "Da dare bayan sun shirya wani katone yashigo d'akin domin kiransu, Fadila wacce ta b'uya a bayan kofa da Sauri taciro hijabin dayake hannunta ta rufa mishi a fuska, sauran ma suka fito zainab ce ta d'auko tsumma suka taru su uku suka danne bakinshi da hancinshi har saida ya daina numfashi, ganin haka suka janyeshi, Baby ce tacire Mayan jikinshi da taimakon sauran suka baiwa Fadila, Shiga band'aki tayi tasa kayan tafito tana kuka, Dan batada tabbacin zata tsira da ranta wata kila tayi rai wata kila ta mutu, suma kuka suka fara har sunajin kaman su fasa yin wannan dabarar domin zaman dasukayi nad'an lokaci sun saba sun zama 'yan uwan juna baza su so rabuwa ba, Baby tafi kowa yin kuka domin Fadila ta zame mata komai yaya, Cikin karfin hali Fadila tace "idan mutum ya mutu lokacinshine yayi, mutum baya mutuwa idan lokacinshi baiyi ba, muyafi juna" kowa yace ya yafe, Baby ce ta kara rungumeta tsam kamar za'a kwace mata ita, A hankali Fadila ta janye jikinta tajuya tafice daga d'akin.

 

_Jiddah Ce....✍️_

08144818849

[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸

   *ƘANWATA*

🌸🌸🌸🌸🌸

Na

Jiddah S Mapi

*Chapter 18*

      ~Tana fita tasa handkerchief ta rufe fuskarta dashi, sauran mazan tagani tsaye sunashan taba zuciyanta ne yafara bugawa da karfi tana Addu'ar Allah yabata sa'a, suna kallonta babu Wanda yace kala don sunsan d'an uwansu ne, saida taje bakin Get taji bugun zuciyarta ya tsananta, bud'ewa tayi me gadi yace "kai tsaya ina zuwa haka ba tareda oga ba?" Rasa abin fad'i Fadila tayi sai kifkifta ido kawai takeyi, matsowa yafarayi yana tambayar ta, jikintane yafara rawa da kyar ta d'aga hannu tayi mishi alamar tanajin Amai, washe hakwara yayi yace "ok ok jekayi amanka watakila kasha Wanda yafi karfinka ne" da Fadila taji haka a take ta kwasa da gudu batako juyawa,  batasan ina zatajeba batasan waye zai taimaka mata ba, Addu'a kawai takeyi a ranta Allah yakawo mata d'auki, Allah yasa ta had'u da mai taimaka mata ba mugu ba, hawaye taji yafara bin fuskarta tunawa da tabar sauran 'yan uwanta a cikin wani hali, tana gudu tana goge hawaye idonta yayi jaa fuskarta tayi kura Dama ga dattin data tara tayi putu putu kura duk yab'ata mata jiki da fuska ta fita a kamanninta, saida tagaji ta zauna karkashin wani bishiya tana hutawa, kallon yanayin kasan takeyi akwai ni'ima sosai mutanen ciki basu damuda mutum ba kowa harkan gabanshi kawai yakeyi, tana kallon duk wani me wucewa ta wurin, daga nesa ta hango wata yarinya 'yar kimanin shekara gomasha uku dakuma karama 'yar kimanin shekara goma, karamar ta zauna a kasa tana kuka babban sai hakuri take bata tana lallab'ata karamar sai kara sautin kukan take tana buga kafarta a kasa, Fadila batasan lokacin data mike ba, wurinsu tanufa gadan gadan tanajin wani zuciya na d'ibanta, tana isowa ta sunkuya ta zabgawa Karamar mari, Babban ganin haka yasa tafara Jan Fadila tana tureta, Fadila juyowa tayi tana kallon yarinyan tasan koda tayi mata bayani bazata fahimta ba kasancewar yarensu ba d'aya ba, amma bari tayi mata turanci wata kila zata fahimta, cikin b'acin rai Fadila tace "wannan wacece?" Yarinyan da mamaki itama ta mayar mata da turanci tace "she's my little sister"

Hamdala tayi ganin ta iya turanci, tace "yanzu kinashan wahala akanta saita girma tasaki a rana, kicire son kanwarki a zuciyarki, kanne basuda imani basuda tausayi sannan basuda tunani, kidaina gajiyar da kanki akanta domin wata rana zakiyi Dana sani, kamar yanda nima nake dana sani"

Da kallon mamaki duk suke binta, wani mutum ne yakaraso da sauri jin kalaman Fadila, hannun yarinyar yariko yana tambayarta meyafaru? A hankali ta labarta mishi, kallon Fadila yayi d'aga sama har kasa yaga irin dressing nata kama Dana terrorist, ID card nashi yaciro yanuna mata yace "you are under Arrest" Fadila da firgici take kallon mutumin ganin shi d'an sandane yasa tahad'a hannunta biyu tana bashi hakuri, tace "Dan Allah karka kamani wlh sauran 'yan uwana suna cikin matsifa da bala'i idan ban taimaka musuba waye zai taimaka musu, na yadda idan na taimaka musu sun samu sun kub'uta d'aga hannun wad'annan mugayen ka kasheni, Amma Dan Allah ba yanzu ba" jikinshine yayi sanyi jin maganar datayi, hannunta yariko yace "biyoni" juyawa yayi wurin babban yace "Mulka riko hannun mulli kubiyoni mota" riko hannun kanwar tayi sukabi bayan baban nasu, suna shiga mota ya kunna suka d'au wani hanya me tsayin gaske, daidai kofar wani gida d'an madaidaici suka tsaya hannun Fadila Yakuma rikowa suka shiga cikin gidan, har d'aki yakaita ya zaunar da ita akan sofa, juyawa yayi wurin yaran yace "mulli kawo ruwa me sanyi a frij" karamar ce tajuya rana hararan Fadila itama Fadila harara take bankawa yarinyan domin tun kallo d'aya datayiwa yarinyan tagane cewa ita Naughty babban kuma Innocent, ruwa ta d'ibo tazo ta aje a gaban Fadila tana yamutsa fuska, Babansune yad'ibo ruwan a cup yamikawa Fadila yace "karb'a kisha" babu musu Fadila ta karb'a tad'aura a bakinta saida ta shanye tass kafin ta sauke Cup d'in, Kallonta yayi yace "relax And tell me what is happening"

Fadila cikin kuka tafara basu labarin duk abinda yafaru dakuma abinda yakekan faruwa, saida tazo karshe tace "shiyasa banason kanne a rayuwata na tsani kalamar Kanwa" gaba d'aya d'akin saida sukayi kuka bama kamar Mulli ba wacce taji Fadila tashiga zuciyarta sosai, Mulka ma kuka takeyi karasawa tayi wurin Fadila ta rungumeta tana kuka, Babansu ma goge hawayenshi yayi yace "It's okay Ku zauna anan dasu Mulka zanje office nabada report gobe sai ayi shiri me kyau aje musu, saboda wad'annan mutanen sunada hatsari sunsan me suka taka, ba banza zasu zauna a kasarnan ba akwai me d'aure musu gindi, Amma dolene sushiga hannun hukuma gobe"

Fadila cikin kuka tace "nagode sosai"

Tashi yayi yafita a gidan, Mulli ce tazo wurin Fadila ta safe kafad'arta tace "kiyi hakuri da farko nayi muki mumunan zato nazata bakya sona ne amma tunda naji labarinki naga kinyi daidai"

Fadila tace "ba komai" bata yadda magana me nisa ya had'ata da it's domin haka kawai yarinyar take tuna mata da Amrah, itama Mulli dataga haka saita daina ahige mata, sai Mulka ce tace "tashi muje kitchen kiga kalan abincinmu" ba musu Fadila ta mike tabita kitchen, abinci kala kala suka dafa Mulka tana nuna mata yanda akeyi ita kuma tanayi har suka gama, Abinda yabawa Fadila mamaki shine wake da aka Ciro acikin frij da sanyi harya fara daskarewa wai dashi za'aci abinci, itakam da kyar take tura abincin don't bawani sabawa tayi dashi ba, yau kad'ai harsun saba da Mulka da Munni amma sabawansu yafi yawa da Mulka, hira sukeyi sosai had sunajin kamar karta tafi, cikin Hiran suke fad'a mata mamansu ta mutu tun suna yara shiyasa suke zama su kad'ai da babansu, Fadila ta tayasu bakin cikin rashin uwa sannan tabasu shawara akan Susa Babansu yayi Aure watakila zasu daina yawan tuna maman nasu, shawaran ta yayi musu sosai had suka kudiri aniyan au zasu fad'awa Babansu, tun suna hira Suns jiran dawowan Babnsu had bacci ya d'aukesu bai dawoba, Fadila ma bacci yayi awon gaba da ita.

        "Amrah yanzu tanajin dad'in yanda Kamal ya sauko suna hira wani lokacin har wasa sukeyi sosai suyita d'aukan  photo saidai har yau takasa ganewa shin yana son Fadilane ko kuma ya daina sonta?

Yauma kamar koda yaushe zaune take akan sofa ta d'aura kanta akan cinyar Kamal shikuma yanata yamutsa mata dogon gashinta wai yana mata kitso, Amrah d'an janye kanta tayi kad'an tace " Yaya Jamal?" Ummm shine abinda yace, Amrah tace "Dama nason muje gidansu Mamane yau mu gaidasu nayi kewarsu wallahi, gashi ban rabu dash a lokacin da nayi niyya ba" tafad'a cikin muryan kuka,

Kamal tausayin yarinyar ne yakamashi yasan Fadila ta cuceta, a hankali ya d'agota ya rungumeta sosai yace "kidaina kuka KANWATA"

Amrah jin haka yasa ta kara fashewa da kuka tace "Yaya Kamal ni banida Wanda yake sona tinda make babu Wanda yatab'a furtamun Kalmar so nasan haka rayuwata zata kare"

Jamal dayaji tausayin Amrah yana nema ya fas mishi kirji da karfi ya kankameta yace "I love you Amrah" Amrah jitayi numfashinta yana Neman d'aukewa a hankali tace "me kace Yaya Kamal?"

A hankali yace "I love you Amrah"

Amrah wani dad'ine ya rufeta jin maganar daya fito daga bakinshi ta tabbata tayi nasarar sace zuciyar Kamal, Shima Kamal wani dad'i yakeji sabida ya furtawa Amrah abinda ya jima yanason furta mata, sai sauke ajiyar zuciya kowannensu yakeyi, Kamal ne yad'an raba jikinshi da nata yace "bari nayi wanka ina zuwa" Amrah cikin kasala tace "to Yaya Kamal"

Shafa fuskarta yayi yace "bazaki rakani ba?"

Rufe fuskanta tayi da hannunta alamar kunya, dariya Kamal yayi ya wuce zai fita, Da Sauri Umma ta matsa daga jikin kofar tanajin zuciyarta yana Neman tarwatsewa, rakub'ewa tayi a jikin bango har Kamal ya wuce bai ganta ba, hannu biyu tasa ta dafe kirjinta cikin tashin hankali tace "Kamal yana nema ya gama dani, me yake nufi da yanason Amrah? Nashiga Uku ni Mariya Asirina ya tonu, ina zansa kaina inji sauki?"

A hankali tafara silalewa daga jikin bango zuwa kasa, tanajin bugun zuciyarta yana tsananta, saida taji tad'an samu sauki kafin ta mike tanajin jiri yana son d'ibanta, wucewa tayi zata shiga bedroom taji muryan hajiya Turai tana cewa "lafiya Mariya? Keda zaki kira Kamal kuma saiki shigo d'aki kamar 'yar kwaya?"

Umma a daddafe tace "yana zuwa" tana fad'an haka tafad'a d'aki ta kwanta akan gado tareda janyo bargo ta rufa a jikinta Wanda harya fara rawan d'ari, runtse ido tayi tanajin jikinta yana zafi, a hankali har wani wahalallen bacci ya d'auketa.

  

        "Washe gari Babansu Mulka da Mulli ne yashigo gidan yace Fadila ta shirya da wuri zasu wuce, Mulka ce tafara kuka tace "Daddy kabari mana ta kara koda kwana ukune" Babansu yace "aa My dear Kinsan tabar 'yan uwanta a can bai kamata ta zauna anan suna can suna  Jiran tsammani ba"

Mulli ma kuka takeyi Itama Fadila sai taji ba dad'i yaran sun bata tausayi, rungumesu tayi d'aya bayan d'aya tana kuka tace "Allahn daya had'amu yanzu idan yaso zai had'amu wata rana" Babansu ma sai yaji duk ba dad'i da Alama sun saba sosai daga jiya zuwa yau, hakuri yabasu yariko hannun Fadila suka fita tana d'aga musu hannu, suma hannu suke d'aga mata Suna hawaye harta tafi, rungume juna sukayi suna Kuka sai a lokacin sukaji kewanta sosai amma ba abinda zasuce sai Allah ya had'asu a haske ko kuma a aljanna.

      "Babban station dake kasar Sudan aka kai Fadila, da babban d'an sanda aka had'a ta tanayi mishi bayanin abinda yake faruwa da yaren Hausa kasancewar shi d'an Sanda ne dole ya iya yare daban daban, saida ta dasa aya kafin Yakure mata kallo da farin glass dake idonshi cikin hausanshi da baya fita yace "Idan munyi binshike muka gane kayi muna karya zakashi Ubanka"

Fadila jitayi kirjinta ya buga to me zaisa suci ubanta da gaskiyanta? "Kaji mune?" Shine abinda yakara fad'a, Fadila a hankali ta gid'a kanta, cikin tsawa yace "kana d'agawa d'an sanda wuya? Bud'e Baki kayi zance"

Fadila tafara tsorata da mutumin daga ganinshi mafad'acine sosai, a hankali tace "eh na yadda"

Kara kallonta yayi yace "da ihu zakace kowa yaji"

Fadila tace "oh ni yau nahad'u da jaraba"

Kamar yadda yafad'a haka tayi,

Takadda ya ciro yabata tayi sign.

Jiddah Ce

08144818849

[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸

   *ƘANWATA*

🌸🌸🌸🌸🌸

Na

Jiddah S Mapi

*Chapter 19*

        ~daganan aka d'ibo motan 'yan sanda yakai goma akasa Fadila a ciki suka d'au hanya, saida suka fara tafiya Fadila taji zuciyarta tana bugawa Addu'a Take Allah yasa suyi nasara akansu, daidai wani lungu suka tsaya akace Fadila sufita dawani wanda bashida uniform daga baya sauran zasu biyosu haka akayi kuwa Fadila ce a gaba shikuma yanabin bayanta suna zuwa megadi ya d'aure Fadila da mari cikin tsawa yace "kinsan abinda kika jawomin kuwa? Kinsa zasu koreni a aiki?"

Fadila idonta yayi rau rau ga tsoro gashi d'an sandan yaki magana sai kallonau yake, megadi yakara d'ago hannunshi zai mari Fadila da sauri yariko hannunshi yaciro bindiga yace you're under arrest, hannu megadi yad'aga sama bakinshi yana rawa idonshi sun fito, lokacin sauran 'yan sandan suka karaso suna zuwa suka bud'e kofar suka  kutsa kai cikin gidan, da 'yammata suka fara cin karo duk sun rame sun shanye kamar wasu masu cuta, Guyson ne yafito da yana sauri da waya a kunnenshi ganin 'yan sanda yasashi yayi Baya baya yakoma d'akin daya fito, ta baya yasamu yafita yagudu, bincike aka farayi acikin gidan ana Neman Guyson ba'a sameshi ba, babban ne yacewa 'yammatan sufita su tsaya a kofa, duk sun Fita sun tsaya a kofa, mai gadi da sauran muatanen duk an kamasu sun tafi police station duka da 'yammatan, Fadila da Baby sai murna suke Allah yaciresu a wahala da Azaba, da dare an basu d'aki babba acikin station d'in akan su kwana sai gobe asan yanda za'ayi, suna cikin bacci sukaji karan bud'e kofa, Fatima ce ta mike tanason ganin ko waye, 'yan sanda dasuke duty na dare tagani suna shigowa cikin sand'a, shiru tayi ta toshe bakinta gudun kartayi ihu, ganin suna kokarin d'aga hijabin Baby yasa ta sake bakinta ta buga ihu me kara, a firgice sauran suka tashi suna salati, da sauri Fadila ta mike ta kunna wutar d'akin saiga 'yan sanda da uniform sunkai Goma a kansu, ja dabaya suka farayi suma suna binsu suna washe hakwara, Fadila tace "Dan Allah bayin Allah Ku kyalemu haka muhuta a can bamu hutaba nanma bazaku barmu mu huta ba fisabilillahi?"

Wani me dogayen hakwarane yace "Baby mu bazamuyi muku fyad'e ba had'in kai muke bukata a wurinku muyi a sirrance babu me ganinmu"

Fadila da zuciyarta ta bushe ita yanzu ta daina tausayi ta taina son mutum a rayuwarta jitakeyi yanzu zata iya kisan kai babu abinda ya shafeta ta bud'e baki cikin tsawa tace "had'in kai? Had'in kai ko? To kazo kayi,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login