Showing 39001 words to 42000 words out of 139192 words

Chapter 14 - Kanwata Book One Complete Hausa Novel

Jiddah   

27 Sep 2025

889

ta kalleshi tace "meyasa ka katse wayar?"

Numfashi ya sauke a hankali yace "nagama ne shiyasa" wani kallo tayi mishi kafin tace "okay muje"

Key yasa suka d'au hanyar gida babu me magana acikinsu, kowa da abinda yake sakawa musamman Amrah dataji kalaman Mama sun matukar d'aga mata hankali "idan Addu'ar mama ta karb'u sai d'an kampai na"

Kamal ne ya kalleta yace "magana kike?"

Da sauri tabugi bakinta tace "Aa meka gani?"

Kamal yace "naga bakinki yana motsi"

Ajiyar zuciya ta sauke tace "aa idonka dai yaga hakan"

Baiyi magana ba har suka iso gida, da sauri ta bud'e motar tanaso tashiga gida ta kwanta tayi tunani tukun, Umman Kamal tagaji zaune abakin kofa tanayi mata wani irin kallonta, dabarcewa tayi kamar bata ganiba tace "sannu da hutawa Umma"

Amma batace komai ba tamike tashiga b'angarenta tanayiwa Amrah wani kallonta data kasa fahimtarta, Amrah tsayawa tayi tana tunani wannan kallonfa? Na menen? Tab'e baki tayi alamar ko ajikinta.

_kowa ya sani a addu'a pls_

Jiddah Ce

08144818849

[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸

   *ƘANWATA*

🌸🌸🌸🌸🌸

Na

Jiddah S Mapi

*Chapter 27*

        ~Saida tashiga d'aki ta kwanta agado kafin maganganun Mama suka fara yawo a kwakwalwarta, da ker bacci b'arawo ya saceta, Kamal yana shiga yaga tayi bacci Toilet yashiga yyi wanka tareda alwala yazo yayi raka'a biyu ya kwanta a bayanta tareda kashe wutar d'akin, Asuba tagari".

       "Fadila yau sun tashi cikin murna gobe zasu koma garinsu su had'u da iyayensu dukda fargaba da Fadila take ciki bai hanata

Nuna murna ba, kayansu Wanda sarki yabasu suka harhad'a acikin bagco, Baby murna kamar tayi hauka jitake kamar bazata iso gida ba gobe hakan yasa idan akayi mata magana saidai tayita washe hakwara, sarki yakirasu yabaiwa kowa dubu hamsin sukayi godiya, Yarima ma yabasu dubu d'ari d'ari, sannan yakira Fadila gefe daniyan suyi magana, yace "Fadila naso ace kece na Aura amma hakan baiyi ba, sabida kinyi alkawari dawani kuma babu kyau nema cikin nema, tunda hakan bai faruba watakila shine mafi alkhairi amma inaso ki karb'i wannan numbana ne duk Inda kike zaki iya Nemana sannan idan kun koma inaso kihad'ani da wancan kanwar taki zan Aureta nasan hakan bazai zama matsala ba"

Fadila share hawaye tayi haka kawai taji Yarima yashiga ranta dukda batason Amrah yanzu amma insha Allah saita had'asu Aure domin zasu dace, "nagode Yarima nagode da kulawarka ka yafemin wulakanci danayi maka abaya kuma da yaddan Allah idan nakoma gida zan had'aka da Amrah zaka Aureta"

Murmushi yayi yace "nagode Unty Babba"

Harara ta sakar mishi tace "banason iyaye fa saina fasa"

"Aa ayi hakuri Unty a yafemin na tuba"

Dariya kawai sukayi Fadila ta koma wurinsu Baby tana murna, har Baby tagano cikin tsokana tace "ooh wannan yariman yayi nasara Babba daya sato zuciyar yayata a lokaci d'aya"

Fadila ta kalleta da mamaki tace "me kike nufi"

Baby tace "abinda nace shinake nufi"

Fadila tace "Ammade Kinsan zuciyata ta mutum d'aya ce ko? Wannan ba kowa bane sai Kamal shikad'ai nakeso kuma shikad'ai zan iya zama dashi amatsayin miji"

Baby tace "zadai mugani idan tusa zata hura wuta"

Sai shirya kaya sukeyi sunata murna a karshen kayanta tasa number da Yarima yabata, Washe gari bayan sun idar da sallar Asuba suka fara shirin tafiya domin gari dayawa zasuje sai an sauke kowacce agarinsu, sarki yace sauran akaisu tasha sushiga mota mutane hud'u saisu kaisu gida, haka kuwa akayi saida suka kai sauran tasha bayan zasu tafi ananne kuka yafara kowacce ta rungume 'yar uwarta suna kuka da kyar suka rabu, Fadila da Baby sai Fatima dawata 'yar Gombe sune a motar, sai kuka suke suna d'agawa 'yan uwansu hannun harsukayi nisa, jisuke kamar suyita zama tare sunashan wahalar amma ba dama iyaye ba wasa ba, Gombe akafara bi har kofan gida aka kai Fatima nanne kukan yaci nada, Fatima taki sakinsu sai kuka take harda ihu shima driver wannan karon saida yayi hawaye Dan yaran sun bashi tausayi, da kyar suka b'amb'are Fatima a jikinsu badan sunso ba, itama d'ayar tace zata sauka domin basuda niya zata shiga keke napep ta karasa gida, Fatima tana kwance akasa tana kuka harsu Fadila da Baby suka tafi suna kuka suke, musamman Baby datake tunanin yau zata rabuda Fadila rungume Fadila tayi tana kuka kamar ba gobe, itama Fadila shiru tayi tanajin zafin rabuwa dasu, sai mangarib suka iso Abuja da kwatancen Baby har suka iso wani Babban gida me Latin get da Ado ajikin Get d'in wutar kofar gidan kamar rana, har allura zaka d'auka idan yafad'i, Fadila Kallon get d'in takeyi taji Baby tace "mun iso nanne" har saida driver yajuya yana kallonta ganin gidan data nuna, Dan gidan kamar na shugaban kasa, lalle yau saiya shiga gidannan wayaga bati yabari? Fadila jitake dabata zauna da Baby bagashi tanason yarinyar gashi yarinyar tafi karfinta nesa ba kusaba, Dan ta tabbata ko 'yar aiki bazata samuba agidannan, Baby ce ta katse musu tunani ta hanyar cewa "yanzu dai dare yafara idan kun tafi bansan yaushe zaku iso ba Ku kwana a gidanmu idan yaso gobe da safe saiku tafi" da sauri driver yace "to to to ba damuwa yarinya" Fadila Kallon gidan takumayi takara Kallon Baby sannan tace "kin tabbata nanne gidanku?"

Dariya abun yabaiwa Baby tace "idan nayi karya Adda Fadila ribar me zanci?"

Fadila fita sukayi a motar suka nufi bakin get megadi ne ya leko yana tambayar waye? do ya zaro ganin Baby yace "Amrah dama kina raye Alhaji da Hajiya kullum suna cikin tunani wannan yayan naki me shegen Girman kanma ya sauke yafara nemanki Ido rufe lalle yau akwai shagali agidannan na tabbata sai an karamin albashi iko sai Allah" Amrah ganin surutun ba karewa zaiyi ba yasa tace "baba abud'e mana mushiga da motarmu"

Da sauri yabud'e musu driver yashiga, Amrah suna shiga taji hawaye a idonta babu shakka tayi missing magida, riko hannun Fadila tayi wacce tazama 'yar Kallo tace "Adda mushiga ciki" Fadila binta take kamar jela driver yazauna awurin megadi sunfara cin abinci tare (nace driver anga Bajau)

Amrah suna shiga ciki tafara kiran Mommy, Daddy, Yaya, Kakus ina kuke?"

Daddy ne yafito yana waya, wayanne ya sub'uce mishi ganin Amrah tsaye tayi duhu ta lalace da gudu Amrah taje ta rungumeshi tana share hawaye shima hawayen ya share yana Kallon Fadila wacce itama take share nata hawayen, cikin tsananin murna ya mikawa Fadila hannu alamar itama tazo, a hankali tafara takawa harta iso, rungumesu yayi gaba d'aya yana murna, da karfi yace  "Hajiya, Mama kufito kuga ikon Allah"

Waya matace fara Tass guntuwa zata wuce shekara talatin tafito cikin wani leshi baki Wanda ya matukar amsar jikinta, ganin Alhaji rungume da 'yammata guda biyu yasa ta tsaya turus, Amrah ce ta juya tana Kallon Mommynta da gudu takarasa wurinta ta rungumeta mommy gani take kamar tana mafarki kuma wannan mafarkin bazataso ta fara ba, Daddy ganin Fadila tsaye yasashi cewa "kije kema baiwar Allah"

Fadila a hankali takarasa wurin Amrah tajata jikin mommy, da sauri Mommy ta janye Fadila a jikinta tana kallonta wata useless haka zata rungumeta ba gaira ba dalili? Amrah Kallon mommy tayi da mamaki tace "mommy tarefa Muke da ita yayatace"

Da sauri mommy tasa mata  hannu abaki tace "shii yayanki yana d'aki yana bacci biyoni muje"

Jan hannun Baby tayi zuwa wani b'angare Baby tana cewa "Mommy Fadila fa?"

Mommy batako kalli Fadilar ba suka tafi, Fadila jitayi jikinta yayi sanyi tsayawa kawai tayi tarasa abinyi, Daddy da murmushi a fuskarshi yace "'yata samu wuri kizauna kinji? Kinada babban kyauta a wurina tunda kuka kawomin ita har gida, bari nakawo miki ruwa da lemo kinji?" Gid'a kai tayi tana mamakin yanda yake da kud'i amma yanada saukin kai, ya nuna mata sofa yace "zauna anan" bata zauna akaiba ta zauna a kasa tareda sunkuyar da kanta tana wasada Capet dayake shinfid'e a kasa, Bata jimaba Daddy yakawo mata ruwa da memo da snacks, bataciba sai Kallon d'akin take.

        "Baby ce tafito daga d'akin tayi wanka ta janza kaya zuwa Jada baki Riga da wando tayi kyau sosai, tana zuwa tafara baiwa Fadila hakuri, Fadila tace "karki damu ba komai"

Baby tace "bari Yayana yafito kafin kije kiyi wanka a d'akina saimu huta sabida mun gaji..." bata karasa maganar ba Fadila taji wani kamshin turare me tafiya da hankali yana tunkarota d'aga kai tayi tanason ganin me wannan turaren, wani gaye tagani Wanda ko a television bata yawan ganin irinsu Shiba fari sosai ba kuma Shiba Baki ba, d'an daidai yake, fuskarshi kewaye dawni saje Wanda yakara fitar da kyaunshi yanada tsayi kuma yanada d'an kauri idonshi kamar na mage idan yana kallonka kamar bakai yake Kallon ba jikinshi kana gani kaga d'an Hutu Wanda kud'i ya zauna mishi, atakaice dai yayi kama da mazan da ake kira MIJIN NOVEL.

Jiddah Ce

08144818849

[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸

   *ƘANWATA*

🌸🌸🌸🌸🌸

Na

Jiddah S Mapi

*Chapter 28*

        ~cikin takun kasaita ya karasa tareda zama akan sofa ya d'aura kafanshi akai fuskarshi a had'e tamau da alama bai cika yin dariya ba, Fadila ganinshi taji tsoronshi mutum baya dariya haka? "Ina wuni" shine abinda tace, kallonta yayi sau d'aya ya watsar a hankali kamar bayason yin magana yace "Lafiya" daganan bai kara cewa komai ba yaciro wayarshi yana dannawa, Baby bataji dad'in yanda ya Amsawa Fadila ba, riko hannun Fadilar tayi tace "muje kiyi wanka sai muyi sallah muci abinci kafin kakata ta tashi saiku gaisa ko?"

Fadila gid'a kai tayi batace komai ba, Har d'aki Baby takaita d'akin Babynma abin kallo ne, toilet ta nuna mata tashiga tayi wanka tareda alwala, tana fitowa taga Baby takawo mata kayan bacci me kyau,  wurin dressing mirror taje Wanda yake cikeda kayan mai da turaruka, batasanma wani mai zata shafa ba Dan dukansu sunyi girma, Baby ce takaraso tareda d'auko mata wani mai mai suna Cocoa Butter, amsa tayi tana murmushi tafara shafawa Baby sai kokarin hira take mata ita kuma tunanin gida take gaba d'aya yau tazama so silent, bayan tayi sallah aka kawo musu abinci sukaci kafin Daddy yakira numbern d'akin yace "Babyn Yaya idan kun gama kuzo falo"

Da "to" ta amsa tace "Adda Fadila muje inji Daddy" Fadila badan tasoba ta mike suka tafi Dan ita gidanma tana Allah Allah gobe yayi ta tafi tsoro suke bata, suna zuwa Baby taga kakarta da gudu ta rungume ta tana murna, da sauri kakar tad'an tureta tace "matsa anan da Allah bayan tafiyarki ko abinci banaci gashi dukna rame ko jambaki nashafa bayamin kyau"

Dariya Baby tayi Fadila ma saida tad'an murmusa, Baby tace "haba Kakus bagashi nadawo ba? Ai yanzu zaki murmure" kakus ce ta kalli Fadila wacce take faman murmushi tace "Amrah ina kika d'ibo wannan" Amrah jikintane yayi sanyi sosai tama kasa had'a Ido da Fadila, Daddy ne ya kawar da maganar ta hanyar cewa "Ina kike Amrah tsawon wannan lokacin?"

Amrah tace "satoni akayi aka kaini wani kauye Allah ne yahad'ani da Fadila ta taimakamin shine harta kawoni gida" Fadila kallon Amrah tayi jin maganar datake tsan tsan karya ne, Kashe mata Ido Amrah tayi alamar tayi shiru, Dady ne yace "an gode Amrah kinada kyautar miliyoyin kud'i da mota sannan kuma da gida, zansa da Amrah su maidaki gida gobe kinji?"

Gid'a kai tayi batayi magana ba, Daddy yarinyar tana birgeshi sabida batada hayaniya, saida aka gama maganar Fadila suka koma d'akin Baby duk sukayi bacci Asuba tagari.

      "Washe gari, Fadila tayi wanka tasa kayan Baby me kyau da babban gyalle Babyma tayi wanka me kyau da gyalle sai Abdul Wanda yasa bakin jeans da farin Riga yayi kyau sasai saidai ba dariya yahad'a fuska kem da alama bayason zuwa dolene Daddy yasashi, suna shiga motar yajuya ya kallesu Fadila saida jikinta yafara rawa ganin irin kallon dayake mata, Cikin muryanshi me dad'i yace "ni driver d'inkune dazaku zauna abaya?"

Amrah tace "yaya kayi hakuri banason barinta ita kad'ai abaya"

Harara ya banka mata Wanda saida cikinta yayi kuka da sauri tabud'e motar takoma gaba badan taso ba, Fadila jikinta sai b'ari yake "dama wannan shine yayan nata data dameni dashi? Wannan ai mugune" shine abinda take fad'a a ranta, tafiya suke kamar kurame babu maganan cin Abinci saida suka iso welcome to yola kafin yaciro wani swan yamikawa Baby, Karb'a tayi tamikawa Fadila kallonta yayi baice komai ba yaci gaba da tuki, Fadila jitayi zuciyarta yana bugawa batasan mezata tarar agida ba, batasan yaya zasu fahimci zancenta ba, addu'a kawai take Allah yasa abin yazo mata da sauki. Sai bayan mangarib suka iso unguwar ganye road, daidai kofar gidansu tace "nan ya isa" baby tana murmushi tace "gani agidansu Adda Fadila kema zakiyi murnar danayi jiya" fita sukayi, Kamal yaja motarshi zaibar wurin da gudu Amrah ta tari gabanshi "yaya ina zakace kuma" baiko kalletaba yace "a hotel zan kwana gobe zanzo na d'aukeki" yana fad'a yaja motar da gudu kamar zai bangajeta ihu tayi ta runtse Ido kwana yayi yabar Layin, Fadila ta matso tareda rike hannunta tace "muje ko?"

Tafiya sukayi abakin kofa Fadila ta tsaya tace "bansan mezan Tarar ba Baby haka kawai nakejin kamar na koma kada in shiga" Baby ce ta kwantar mata da hankali ta hanyar kalamai masu kyau, sallama sukayi Mamace ta amsa tana cewa "kushifo"

Shiga sukayi hannunau sarke Dana juna, Mama ganin Fadila yasa ta saki butar hannunta tana salati  cikin murna tace "Fadila kina Raye?"

Muryar Abba sukaji yanacewa "Wace Fadilar?"

Da karfi Fadila tace "nice Abba Fadilarku"

Abba yace "okay jirani ina zuwa"

Sai a lokacin Fadila taji sanyi a ranta, Mama nufota tayi zata rungume Abba yafito daga d'akin rikeda wani babban sanda, kan Fadila yanufa a zuciye ya buga mata, jin zafi yasa ta kwala ihu bai tsayaba sai kwala mata yake tana ihu, Amrah kwatanta take itama Abba ya kwala mata d'aya baya tayi tafad'i tana Susa bayanta, da kyar sukaja jiki suka fita agidan mama sai ihu take tana bashi hakuri amma ko saurarenta bayayi, cikin tsawa yace "ba'agidana ba karuwanci kije can kiyi karuwancinki badai anan ba na yafeki wa duniya"

Fadila tashin hankali yasa takasa magana da kyar tace "Baby kije bayan nan kikira mana adaidaita sahu muje gidan Unty Sadiya mu kwana acan"

baby tashi tayi taje takira musu, suna zuwa gidan unty sukayi knocking bud'ewa akayi ana tambayar waye, Unty wani irin tsalle tayi ta rungume Fadila, Fadila hawaye sai wanke mata fuska yake, a hankali tace "Unty kibamu kud'i mubiya me napep"

Jansu ciki tayi tace "muje zan kawo mishi yau inada babbar bakuwa" dukda ta fahimci akwai matsala amma ta dake tamayar kamar bataga komai ba, saida tabiya mai Napep ta dawo tanayi musu sannu, Fadila kuka ta fashe dashi tace "Unty meyake faruwane? Ina Amrah take?"

Unty shiru tayi Dan batasan mezatace ba, saida Fadila tafara bubbugata kamar bata hayyacinta tace "please Unty kifad'amin meya faru"

Unty taja numfashi tace "abubuwa dayawa sun faru amma zanso kijira gobe idan Allah yakaimu zakigani da idonki yanzu banason wani magana daga bakinki idan har kin d'aukeni a matsayin 'yar uwa"  Fadila kuka takeyi me  tsuma zuciya, Unty takaisu d'akinsu Aisha sukayi wanka taja musu kofar, Baby ce tafara bacci sabida gajiyan hanya, Fadila yanda taga rana haka taga dare, tunani kawai takeyi.

        "Washe gari Fadila tasa Unty agaba da kuka saida fad'a mata meyake faruwa, unty saida tayiwa yaranta wanka tashiryasu aka kaisu gidan makota kasancewar babansu yayi tafiya sannan tace "Muje kigani da idonki" da sauri tamike suka fita itada Baby da Unty, mai adaidaita suka kama sannan suka shiga, tafiya sukeyi kowa da abinda yake ranshi, daidai kofar gidansu Kamal Unty tace "tsaya anan yayi" tsayawa yayi suka biyashi tareda nufan cikin gidan.

Jiddah Ce

08144818849

[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸

   *ƘANWATA*

🌸🌸🌸🌸🌸

Na

Jiddah S Mapi

*Chapter 29*

        ~Amrah ce zaune a gefen katifa yau da rigima ta tashi Sai tura baki takeyiwa Kamal, shima Kamal zaune yake a gefenta hannunshi rikeda robar ice cream Sai hakuri yake bata ita kuma ta had'a baki da hanci taki karb'a, bud'e robar yayi cikin muryan lallashi yace "haba Auta na ki karb'a mana yaufa da asuba kika sani fita saida nasiyo miki yanzu kuma kiki karb'a? Please bud'e bakin kinji?"

kara turo baki tayi tace "saidai idan zaka goyeni zuwa bakin get"

Numfashi ya sauke alamar ta gajiyar dashi yace "akan wannan tashi to"

Tashi tayi tahau bayanshi yafara tafiya da ita daidai bakin kofa yace "wash bayana sauka nad'an huta"

Tana sauka ya ruga da gudu itama ganin ya gudu tafara binshi zagaye gidan suke da gudu megadi Sai d'auke kanshi yake wai yanajin kunya, daidai bakin get Amrah Tamika hannu zata rikoshi saitaji tariko bakin Abu da sauri ta d'ago kanta Dan ganin meta kama, Hijabin Fadila ne rike a hannunta suna had'a ido tasaki wani razannannen ihu tayi baya tabufad'a bayan Kamal ta rikeshi kem tana runtse ido, jikin Fadila da bakinta Sai rawa yake idonta ya kafe bakinta abud'e tana kallonsu, Unty Sadiya ce ta karaso wurin Fadila tace "da ace jiya nafad'a miki na tabbata bazaki yadda ba amma yanzu tinda kin gani da idonki nasan zaki Amince"

Fadila batajin maganar unty bakinta yana rawa da kyar ta had'a kalma tace "Unty rikeni kaina zai fad'i"

Unty riketa tayi tanayi mata sannu, Baby ma tazo wurin tariketa tana tausayawa Fadila, Kamal ne yacire Amrah daga jikinshi a zuciye ya iso wurinsu Fadila yanuna Unty da yatsa tareda cewa "bance karki kara zuwa gidannan ba? Ubanwa yabaki izinin shigowa gidana da karuwa?"

Had'a hannu biyu yayi alamar roko yace "please kifitarmin da abunnan agidana kafin in rasa hankali na zanyi muku illa dagake har ita"

Da gudu Amrah takara zuwa bayanshi ganin irin kallonda Fadila takeyi mata, juyawa yayi ya rungumeta yana shafa kanta ya kwantar da murya yace "Babyna kidaina tsorata babu abinda zasuyi miki ina tare dake kinji?" Gid'a kai tayi a tsorace tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login