Showing 30001 words to 33000 words out of 139192 words

Chapter 11 - Kanwata Book One Complete Hausa Novel

Jiddah   

27 Sep 2025

894

nace kazo kayi" tana magana tana matsowa wurinshi da idanunta Wanda ya canza kala daga fari Tass zuwa jaa, ganin yanda take nufoshi yasa yafara ja dabaya yana kokarin gudu riko riganshi Fadila tayi ta jashi baya ta zuba mishi ido saida jikinshi yafara rawa ganin abinda ke cikin idon nata, da karfi ta furata "kasan waya sani a wannan rayuwar? To idan Baka saniba yau zan Sanar maka, KANWATA itace tasani a rayuwarnan nasota fiyeda tsammani shine ta sakamin da haka, inaji a jikina zan zama muguwa zan zama marar imani musamman idan nakoma Nigeria kasan meyasa? Sabida anyimin mugunta an kusa a b'atamin rayuwa kuma nasha wahala manyan kasarmu sunada sa hannu akan safarar 'yammata da Guyson keyi, kuma tsafi sukeyi damu bayan sun gama abinda zasuyi saisu kara d'ibo wasu sabbin 'yammatan domin su samu kud'i dayawa"

Share hawayenta tayi ta kara kausasa muryanta taci gaba dacewa "kuma wallahi nayi Alkawarin saina Addabi manyan kasarmu saina cutar da yaran masu kud'i fiye da adadi" juyawa tayi ta kalli Baby tace "banason in fad'a miki abunda yafaru amma yazama dole yau in fad'a miki, akwai ranar da akazo aka tafi dake kina kuka, nima Ina kuka sai nakasa taimaka miki, to bayan fitanku shine Guyson ya dawo ya jawoni wani d'aki ina kuka ina rokanshi amma yakiji saida yakaini d'akin yayimin fyad'e na jiggata nafita a hayyacina naga wasu masu kud'in sunzo da farin kyalle jinin daya fita a jikina shinaga sun shafa ajikin kyallen suka tafa suna dariya suna fice, naki fad'a miki ne sabida karki Shiga damuwa amma rayuwata an Riga an b'ata, nima kuma nayi alkawarin saina b'ata rayuwar mutane" wani iron kuka takeyi nakin karawa ji takeyi zuciyarta ya bushe zata iyayin komai yanzu ciki harda kisan kai idan ta tuna yanda take kula da mutuncinta lokaci d'aya a lalata shi saitaji inama ta kashe kanta, jikin 'yan sanda yayi sanyi har kunya sukeji idan suka had'a ido da 'yammatan, zama sukayi a gefe suna Rokan gafara Fadila tace "zamu yafe muku amma da sharad'i guda d'aya"

Da sauri sukace kifad'a mana sharad'in rankin shidad'e domin suna tsoron kada sufad'awa oga, Fadila tayi murmushi tace,

Zaku bud'e mana kofa acikin darennan mu tafi dan ban yadda da DPO ba ina kyautata zaton dasa hannunshi a lamarinnan idan nayi bincike kuma nagano hakan kashinshi ya bushe"

Sukace "to amma idan safiya tayi muce ya kuka gudu?"

Fadila tace "Ku kwanta kamar kun suma sannan idan kun farfad'o kuce da black magic muka gudu"

Sukace to Allah yabada sa'a, hakan kuwa akayi suka bud'e musu kofa tareda d'aga musu hannu dukka 'yammatan suka fice a station d'in batareda sanin Inda zasuje ba, ga duhun dare ga yunwa ga gajiya musamman Baby, da Fadila taga haka saita sunkuya Baby tahau bayanta, sai dariya takeyi ganin ita babba an goyata, b'angaren Fadila yanzu bata fiye yin dariya ba saidai idan taga abun mugunta sai tayi d'an murmushi kawai, a haka suka yada zango a wata kango me cikeda sauro da duhu, Fadila taciro d'ankwalinta ta rufawa Baby a jikinta.

         "Amrah ce zaune akan Sofa hannunta na Dama d'auke da waya na hagun kuma d'auke da glass cup Wanda yake cike da juice tana sipping a hankali, wandone (Plazo) ajikinta bud'ad'd'e da wata Riga baka 'yar karama, Neman wata number takeyi amma takasa samu sai yamutsa face kawai takeyi, Kamal ne yashigo d'akin sanye da jallabiya me hla brown color yana yamutsa fuska shima alamar ya tashi daga bacci, wurin Amrah yanufa ya zauna akan sofan ya kwantar da kanshi a kafad'arta yace "Amrah yunwa nakeji"

Amrah murmuahi tayi tashafa kanshi cikin muryanta siriri tace "okay Kamal bari naje kitchen na had'a maka delicious ko?"

'Dago kanshi yayi ya kalleta yace "I love you Amrah"

Murmushi tayi tamike tana cewa "I know Kamal"

Janyota yayi tafad'a kanshi a hankali tace "wash zaka karyani"

Dariya yayi shima ya kwaikwayi muryanta yace "wash zaka karyani"

Sunkuyar da kanta tayi, a hankali yasa hannu ya d'ago kanta yazuba mata ido na 'yan lokaci sannan yace "meyasa idan nave Ina sonki said kice kin sani ko kuma kice kin gode amma ke baraki cemin kina sona ba why?"

Idonta ne yacika da hawaye ta d'ago tana kallonshi tace "bazan iya cewa ina Sonka ba Yaya kamal sai naga kamar naci amanar Adda Fadila ne"

Cikin tausayawa Kamal yace "bakida laifi Amrah hasalima Fadila muguwace batada tausayi, batayi tunanin halinda zata barni ba batayi tunanin halin dazata bar iyayenta ba batayi unanin halinda zatabar Kanwarta kuma KAWATA  ba, Amrah Allah yasani naso Fadila tsakani da Allah Amma Tafi amana ta Allah ya isa tsakanina da Ita"

Saurin toshe bakinshi tayi da hannunta tana girgiza mishi kai hawaye yanbin fuskarta tace "no Yaya Kamal karkace haka"

Rungume Amrah yayi yanajin soyayyarta yana ratsa duk gab'b'in jikinshi dafari idan kaganta zakayi zaton batada hankali batada kunya Naughty Girl amma saika zauna da ita zakasan Innocent ce batada matsala.

08144818849

[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸

   *ƘANWATA*

🌸🌸🌸🌸🌸

Na

Jiddah S Mapi

*Chapter 20*

      ~cikin dare Fadila suna kwance kowa da abinda yake sakawa a zuciyarshi, Baby ce tace "Adda Fadila akwai maganar danakeso muyi amma idan bazai b'ata miki rai ba"

Fadila shiru tayi kafin tace "to tinda kinsan zai iya b'atamin rai meyasa zaki fad'amin Babyn Yaya?"

Baby itama tayi ahiru nad'an lokaci kafin tace "Adda maganar yanada matukar anfani shiyasa"

Fadila tace "to ina jinki"

Baby tace "Adda nasanki da hali me kyau kinada nutsuwa da kamun kai gakida tawakkali, meyasa zaki rama mugunta da mugunta? Ai kamata kirama mugunta da Alkhairi koba komai zakiyi confusing na makiyanki, Amma nayi mamaki da kikace zaki rama mugunta da mugunta, manzon Allah (S.A.W) ya zauna da makwabci kafiri, kullum idan akayi shara agidan makwabcin sai a zubawa Manzon Allah datti a cikin gidanshi, haka zai hakura bazaiyi magana ba, wata rana yana zaune sai yaga basu watso dattin ba, sai yayi sallama yashiga gidan, yana zuwa ya tarar da wannan mutumin bashida lafiya, saiya gaidashi, mutumin yace kazone kayimin rashin mutunci akan abinda nayi maka? Manzon Allah yace Aa naga yau baka zubo da sharan ba shiyasa nace bari induba ko lfy? Shine na tarar bakada lfy Allah yakawo sauki, mutumin yafara kuka yaroki gafara akan manzon Allah ya yafe mishi, Manzon Allah yace babu komai Allah ya yafe mana gaba d'aya, daganan mutumin ya karb'i kalmatushahada, Adda Fadila? Manzon Allah ya zauna lafiya da mutane kai waye da bazaka zauna lafiya dasuba? Manzon Allah yayi hakuri da mutane kai waye da bazakayi hakuri ba? Kiduba Abu akan maganar nan"

        "Ba Fadila ba gaba d'aya 'yammatan saida jikinsu yayi sanyi jin maganar daya fito daga bakin Baby"

Kuka kawai Fadila ta fashe dashi ace yarinya karama ce take fad'a mata abinda Ita ta kasa tunawa? Ya Allah ka yafemin bazan kara ayyana wani mugunta a raina ba, Allah na tuba, haka taci gaba da kuka tana rokan gafara a wurin ubangiji, saidai har yanzu tanajin zafin abinda Guyson yayi mata.

        "Da dare Amrah ce kwance akan gado tana kiran numbern Guyson amma baya d'auka, hankalinta ya tashi sosai tarasa meyasa kwana biyu baya d'aukan kiranta, wani number ta lalubo takira ana d'auka tafara zagewa meshi ruwan matsifa da bala'i tana cewa "meyasa baya d'aukan kirana? Nafishi rashin kunya da fitsara wallahi, ya tabbata ya turamin kud'ina ko kuma nayi mishi sharri sharri irin na mata kuma kunsan zan iya"

Tana fad'an haka ta gintse wayar, Kamal ne yakaraso cikin d'akin Wanda yanzu zuwanshi kenan, yace "me akayi miki kiketa matsifa haka?"

Amrah rud'ewa tayi tarasa me zatace mishi, tafara in ina tana cewa "Am...Yaya Kamal kud'in d'inkina zasu turomin tin ranar Auren nabasu amma basu d'inka ba kuma sun karb'i kud'ina"

Kamal dariya abun yabashi yace "nawane kud'in d'inkin da kud'in zanin?"

Ajiyar zuciya ta sauke tace "zanin dubu bakwai ne d'inki dubu uku"

Kamal yace "Yakama nawa?"

Shiru tayi tana irga yatsu alamar tana lissafi, karasowa yayi wurinta domin hakan datayi saida yatuno mishi da Fadila duk lokacin da zata fad'a mishi Abu na lissafi saita irga yatsu, riko hannunta yayi duka biyu ya kankance murya yace "d'an wannan lissafin saikin irga yatsu?"

Amrah gid'a mishi kai kawai tayi, yayi murmushi Wanda ya bayyana dimple nashi yace "dubu bakwai ahad'a da dubu uku Yakama dubu Goma, kinada account?"

Amrah tanaso tace eh amma tana tsoron Kara tambayeta ko kuma yayi zargin metakeyi dashi?  sai tace "Aa dana Mama nake anfani"

Kamal yace "bani account number d'in to"

Murmushi tayi ta dukar dakai kasa tace "kabarshi kawai yaya Kamal ba komai na yafe Allah yanason me yafiya"

Kamal ji yayi Amrah ta zarce Fadila da abubuwa da dama adane bai saniba amma a yanzu yana kan fahimta rungumeta yayi yanajin tausayinta yana ratsa ko ina na jikinshi bata sonshi amma ta daure tarufa mishi asiri ta Aureshi bazai tab'a mantawa da ita ba a rayuwarshi.

   _bayan kwana uku_

  "Su Fadila ne zaune abakin wani ruwa sauran suna kwance sauran suna wanke kafarsu da alama sunyi tafiyane me Nisan gaske domin da kaga fuskarsu zakaga suna cikin matukar gajiya da yunwa, Fadila wacce fuskarta yazama baki na dole ta rame ta kod'e idan ka ganta bazakayi zaton ita bace, ta juya wurin Baby tace "Babyn Yaya kuna ganin zamu iya wannan tafiyar me Nisan? Inaji kamar mutuwa zanyi"

Baby cikin kuka tace "kidaina fad'an haka Adda insha Allahu zamu koma gida mu had'u da iyayenmu lfy"

Fadila ma hawaye ta share bata kara cewa komai ba, don tagaji iya gajiya zuwa Nigeria da kafa ba wasa ba, yau kwana uku amma ko alama babu, Fatima itama tagaji sosai ta kod'e tayi bak'a tace "Allah ya isa tsakaninmu da wad'annan mugayen Allah yashige mana gaba, babu shakka idan na koma Nigeria saina bud'e gidan Marayu saida nasha wahala kafin nasan halinda marayu suke ciki, Allah ubangiji ka taimaki duk wani musulmi na fad'in duniya ka rabashi da Sharrin mugayen mutane"

Kowa ya Amsa da "Ameen"

       "Amrah rashin d'aukan kiranta da Guyson yayi ba karamin tashin hankali tashiga ba, yauma sai kai kawo takeyi acikin falon gidan, Umman Kamal ce tashigo da ledoji a hannunta Da Sauri Amrah taje ta sunkuya ta karb'i ledan tanayi mata sannu da dawowa, kallonta Umma tayi da mamaki tace "ke Lafiyarki kuwa?"

Amrah tace "lafiya lau, tunani kawai nakeyi"

Zuciyar Umma ne yabada sauti dumm da sauri tace "tunanin me kikeyi da tsakar ranan nan?"

Amrah tayi mamakin yanda Umma ta Amsa mata maganar duba da yanda suke zama zama irin na rashin jituwa, Hajiya Turai ce ta bud'e kofar tashigo tana bala'i tana zage zage, Umma ce ta kalleta tace "lafiya Hajiya?"

Da masifa tace "ina lafiya kuwa yaronnan na kula idan ya zauna agida bayason fita watarana sai matarnan ta hanashi zuwa ko ina, da idonta kamar na mayu" tafad'a tana kallon Amrah, Umma batace komai ba ta kwashi ledojinta tashige ciki, Amrah ce ta juya ta bankawa Hajiya Turai harara ita Sam matarnan ba kaunarta take ba, itama cikin b'acin rai tafice yana kara kiran numbern Guyson cikin sa'a kuma ya d'auka amma dagajin muryanshi Kasan akwai matsala, da Sauri tace "lafiya Guyson?"

Tsaki yayi yace "ina lafiya wannan yayar takin  takai report wa 'yan sanda da kyar nasha"

Amrah cikin rashin fahimta tace "ba kaiba yanzu ina take?"

Cikin b'acin rai Guyson yace "wato baki damu daniba kinfi damuwa da yayarki ko?"

Amrah tace "kai ai gakanan muna waya amma kafi kowa Sanin idan Adda Fadila ta dawo Nigeria akwai Babban matsala ko"

Guyson yace.

         "Fadila sun gudu hasalima bansan India sukaje ba na nemesu sama da kasa nasa 'yan gidana su nemesu amma ko alamunsu babu, Nina ina cikin tashin hankali KANWATA, amma nasan bazasu tab'a tsallake kasar Sudan ba sabida ko kud'in jirgi basuda, kuma anakan nemansu"

Amrah ta rud'e iya rud'ewa amma tasan tunda batada kud'in jirgi to bazata dawoba dahaka taji sauki a ranta tana addu'an Allah yasa karta dawo tafad'a kowani haline amma karta tako Nigeria domin idan ta dawo Nigeria data rabata da masoyinta kuma shine abinda bazai tab'a Faruwa ba Indai tana numfashi.

    "Tafiya yayi tafiya Fadila da sauran 'yan uwanta sunyi tafiya ba wasa, Zainab ce wacce kafarta ya kumbura ga yunwa suna cikin tafiya ta fad'i, da gudu suka iso wurinta suna tashinta, Zainab babu bakin maganar, sai motsi kawai bakinta yakeyi, Fadila ce ta kai kunnenta saitin bakinta tanason jin metake cewa a hankali taji zainab tana cewa "Ruwa!! Ruwa!!" Juyawa tayi tana kallon gefenta  Babu alamar ruwa a wannan dajin ga sauranma sun jiggata sosai musamman Baby wacce take numfashi kasa kasa rasa abinyi tayi kawai ta tashi  tafara gudu tanason tanemo ruwa ko a inane tana gudu tana zana layi a hanya gudun karta manta hanya, saida tayi nisa dasu kafin taga wani d'an karamin rami da ruwa aciki amma ruwan duk datti, wani gora ta d'auko ta d'ibi ruwan tamike da gudu tanabin Layin data zana murmushi ta saki data hangosu a nesa, tana murmushi tana gudun ta isosu, turus ta tsaya ganin sun taru akan zainab suna kuka, jikintane yafara rawa ganin yanda Baby take kuka, da gudun bala'i ta karasa tana turesu, d'ago Zainab tayi tana kiran sunanta Amma babu alamar motsi ga idonta daya kafe, ihu Fadila tayi tana tashinta Amma ina Zainab Allah yafisu Sonta, Fadila kuka kawai takeyi tasan itama da kyar ta iso gida sabida wahalan yayi yawa yau kwana hud'u kenan suna tafiya babu ci ba wanka duksun fita a hayyacinsu, daurewa tayi ta tsayar da kukanta tayiwa Zainab addu'a sannan ta rife mata ido, tace "kubar kukan haka kutashi mu musan abinyi, mikewa sukayi kowa yana share hawaye Suka nemo itace masu karfi suna tona Rami sauran suka nemo duwatsu, saida suka tona sukayi taimama sukayi mata sallah, sannan sukasata a Ramin suka binneta suna kuka, Fadila ce tad'au wani d'ankwalin Zainab ta aje akan kabarin ta juya tana share hawaye tace "mutafi"

Baby cikin Kuka tace "bazamu iya tafiya mubarta ba"

Fadila tace "idan kun zauna dawowa zatayi? Idan munyi kuka dawowa zatayi? Annabi Muhammad (S.A.W) yace Allah ya tsinewa mata guda uku na d'aya mata masu Bayyana tsiraicinsu, na biyu macen datake kauracewa mijinta a shinfid'a, na uku mata masu Kururuwa akan gawa ma'ana masu ihu idan anyi mutuwa, kunaso Allah ya tsine mana ne?"

Cikin mutuwan jiki suka mike suna tafiya amma basu daina kuka ba.

(Allah yasa mucika da imani saina tuna wata mata agidan rasuwa bayan an tafi da gawa kenan sai aka dawo da markad'an tumatur, tana cikin kuka ta tab'a wata kawarta tace "Hmmm gobe idan nahad'a miyan stew d'innan sai antambaya waye yayi tsabar yanda zaiyi dad'i, Allah dai yakaimu gobe")

       " Unty Sadiya tana cikin bincike har yanzu saidai bataga wani alama ba, harta d'an rame Abbansu Aisha kullum yana cikin korafin yanda tazama lokaci d'aya, saidai tabashi hakuri amma tace bazata iya Barin bincikeba sai ranar da Fadila ta dawo, a haka shima ya hakura yana tayata Dan yasan yanda suke da Fadila".

        "Mama ce zaune akan tabarma suna hira da Abba Wanda yadawo daga kasuwa yanzu Mama ce takalli Abba tace "Malam nifa har yau bana bacci sosai idan na tunda Fadila, bamusan halinda yarinyarnan take ciki ba, mu sanar agidan redio akara dubawa watakila zamusameta kaga idan ta dawo saimu San matakin dazamu d'auka akanta koba haka ba?"

Abba cikin matsifa yace "bakida hankali kekam idan zaki zage kiyi bacci to kizage kiyi bacci yaran zamanin nan basuda kunya zasu iya yin abinda yafi haka ma, da farko na yadda da Fadila nafidon Fadila akan Amrah Amma yanzu Fadila tacire duk wani son danakeyi mata, wallahi idan Fadila ta sake ta tako gidan nan saina yi mata rauni, ba duniya ba? Taje gata gashi ya ishi kowa Riga da wando"

Shiru Mama tayi Dan tasan halinshi idan ranshi yab'aci bayida sauki.

08144818849[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸

   *ƘANWATA*

🌸🌸🌸🌸🌸

Na

Jiddah S Mapi

*Chapter 21*

       ~Tafiya suke tafiyan da basusan hanya ba, idan lokacin sallah yayi saidai suyi taimama su idar kafin sukara tashi suci gaba da tafiya, babu abinda sukeci sai 'ya'yan itatuwa Wanda Allah ya taimaka sunayi awannan lokacin,  gaba d'aya sunata korafin sun gaji Fadila kallonsu tayi tace "naga Alamar kamar mun kusa mu iso boda, to amma idan munje boda dole zasu tambayemu wasu properties dabamu dashi suma idan mukayi rashin sa'a saimu had'u da 'yan iska suzo sunayi mana maganar banza ya kuke ganin zamuyi ko dai zamu juyane mu koma, kasar da muka fito?"

Fatima tace "haba Fadila irin wahalan da mukasha a wannan kasar kinaso mukara komawa? Ai gara musha wahala a kasarmu damusha a kasar wasu, naji Babana yace akwai wasu mutane dasuka shigo Nigeria ta karkashin Boda amma da aka tsawaita bincike an gano basuda kud'in guzurine, to mu meze hana mubi ta karkashin bodan mu koma kasarmu?"

Fadila shiru tayi tana tunani sauran 'yammatan sukace gaskiya yakamata muyi hakan, Fadilan ma ta yadda amma hankalinta bai kwanta ba, awani daji suka yada zango, yini sukayi suna shawarar yanda zasu shiga Nigeria.

       "Amrah dukda Guyson yace yanakan nemansu amma hankalinta Sam Sam yakasa kwanciya, zaune take akan drawer tana rike da waya sai text take turawa Guyson kwata kwata hankalinta ba akwance ba, Kamal ne yaturo kofar yashigo kallonta yayi yana mamakin yanda kwana biyu take acting kamar wani abu yana daminta, a hankali ya taka zuwa inda take yana zuwa yariko hannunta dukka biyu yayi kneeling a gabanta, kallon fuskarta yayi Wanda take murmushi amma daka gani zakasan na karfin hali ne, cikin sanyin murya yace "Kanwata me yake damunki kwana biyu naganki kamar mara lafiya?"

Amrah rasa abinda zatace mishi tayi kawai tafara kuka a hankali ta zamo daga kan drawer ta rungumeshi tsam tsam, Kamal jiyayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login