Showing 60001 words to 63000 words out of 139192 words

Chapter 21 - Kanwata Book One Complete Hausa Novel

Jiddah   

27 Sep 2025

883

kud'in Ai Ko?" gid'a mishi Kai tayi alamar ta Sani, tafiya suka fara zuwa Inda tafad'a mishi, Sunyi tafiya me Nisa sosai Fadila ganin tagaji yasa ta had'a kanta da gwiwa tafara gyangyad'i ahalin Yanzu Ko kuka batayi idanunta sun bushe bata tsoron faruwar Wani abu,  tunanin Amrah ne yafad'o Mata Arai "Auzubillahi" shine Abinda tace azuciyarta tana neman tsari da tunanin Amrah tana addu'ar kada Allah yakara Had'ata dame irin suna Ko Kamar kanwarta, hancinsu da ake cewa iri d'ayane da Amrah jitake Kamar ta yanke batason Abinda yashafi kanwar Tata, daidai Wurin cross suka Tsaya ganin goslow Yayi yawa,  Fadila tad'an jingina da kujerar baya tana kallon titi, Wani d'an sanda ne yazo ya Leka motar ya kallesu Sama da kasa yacewa Fadila Tacire face mask d'in, cirewa tayi ya kalleta sosai Kafin Yabar Wurin, Wurin Wani yaje da alama Oganshi ne sukayi Wani magana tsakanin Kunne da Baki Kafin suka Kira waya, atake 'yan Jarida suka cika Wurin auna tambaya Kamar Haka (yallab'ai shin zaka iya nuna mana fuskokin wad'anda suka aikata wannan mummunar Abun?)

'Dan sandan Yayi gyaran murya yace sunyi Kokarin gudu amma Yanzu Mun kamosu Ku biyomu don ganinsu, Fadila tana zaune a Mota 'yan Jarida suna zuwa wurinsu dafari tayi Zaton Ko tambayarsu zasuyi sai taga 'yan Sanda sun zagaye daidai Wurin motarsu, zuciyartace tabada sautin dumm, Ganin Haka yasa tafara Salati tana kallonsu,  tambaya 'yan Jarida suka Farayi musu "malama shin me zakice gameda laifin da kika aikata?"

Fadila dasuka fito daga motar itada driver cikin Tashin hankali tace "ban fahimceku ba me kuke magana akai".

       Amrah rufe Idonta tayi Kamar me bacci amma a zahiri ba baccin takeba, tunanin mafita kawai take Kafin garin Allah ya waye, itafa ta tsani Adda Fadila duk itace sanadin shiganta wannan halin, kuka tafashe dashi sosai wayarta ta d'auko takira numban Guyson cikin sa'a taji ya d'auka cikin kuka tace "Guyson Ina kashiga? Kamal ya sakeni Nashiga uku"

Tsaki Guyson yaja yace "shine Dan wannan d'an macen ya sakeki zakiyi kuka?, Kinga da ALLAH malama idan bakida Abin fad'ine nakashe wayata Dan Yanzu Haka akwai Yammata akasa"

Cikin kuka tace "Aa Dan Allah kayi hakuri Kabani mafita Narasa yacce zanyi da Mama da Abba"

Guyson yace "Kinga Kice musu wanine yatakura miki shine Kamal yafara zarginki daganan zamusan abinyi" kashe wayar Yayi kitt Amrah tabi wayar da Kallo idanunta yana zubda hawaye.

Jiddah Ce

08144818849

[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸

    *K'ANWATA*

  🌸🌸🌸🌸🌸

    Na

Jiddah S Mapi

*Chapter 43*

         ~Mama ce tayi sallama tana kallon Amrah da Sauri Amrah ta d'ago kanta tana goge hawayen Tareda b'oye wayar a karkashin filo, cikin yanayin tausayi mama takaraso ta zauna a bakin gado gefen Amrah hannunta ta d'ora a kafad'arta tace "Nasan Zafin dakikije na sakin da Kamal Yayi miki to amma nakasa zaune nakasa tsaye tunanin rayuwata na baya nakeyi shin akwai Abinda Nayi lokacin yarintata wanda Yake bin 'ya'yana ne? Amsar itace Banyi ba, kidubi Halinda Addarki take ciki sannan kidubi halin da Kema kike shiga, Inason kifad'amin gaskiyar Abinda Yake faruwa"

zuciyar Amrah ne yabuga tana tsoron fad'ama Mama gsky Dan ta tuna Abinda yafaru tsakaninta da Kamal, murza idanunta tafara Tacusa lips Nata na kasa cikin bakinta tafara Ciza, mama kallonta Tayi tace "idan Baki fad'amin damuwarkiba wa zaki fad'a wa?  Fadila da kike Matukar so bata nan Dan Allah Kidaure Ki fad'a min kinji?"

Kuka tafashe dashi tafad'a Jikin Mama.

      "Bayin Allah Me mukayi muku?" Abinda Fadila take iya fad'a kenan tsabar tsinkewar zuciya, Wani d'an jaridane yace "Baiwar Allah me yasa kika saida d'anki Keda mijinki sannan kuke Kokarin gudu shin bakiji Zafin haihuwar bane?" Fadila cikin Tashin hankali ta d'ago kanta tazuba mishi manyan idanunta masu Kama da shape d'in kwai, muryanta yana hard'ewa tace "wa wa wane yaro kuke magana akai?" Wancan d'an sandan ne Yakutsa cikin 'yan Jarida yana turesu shida 'yan Uwanshi suka shigo Wurin suka rike hannun Fadila da driver sukasa musu ankwa Fadila tana turjewa amma Haka akasasu a Mota akayi Gaba dasu d'an sandan yahana suyi magana da 'yan jarida, kuka ma yadena Zuwama Fadila sai idanu datake bin mutane dashi Gara zamanta gidansu Baby da wannan Sharrin da ake shirin maka Mata Ko kuma aka maka Mata, Wani d'an sanda ne da hausanshi baya fita yace "kidubi yarinya me Kyau amma ta aikata wannan laifin zakici ubanki"

Fadila Ido ta zuba mishi tace "ba ubana ba"

Yace "me kikace?" tace "nace ba ubana ba"

Kallonta Yayi yace "daga Gani Bakida Hankali amma zan Koya miki hankali".

       Baby ihunta Yayi yawa Abdul dayake kwance Akan makeken gadonshi tunanin maganganun yarinyar ya addabi zuciyarshi lumshe idonshi yayi yana tuno yanda tafad'a jikinshi "uzubillahi" shine Abinda yace, shiru Yayi yana Jiyo ihun Baby yasan Halinta tun tana yarinya idan abu ya dameta saidai ta zauna tayita ihu kuma dai ba shine ya lallab'ata ba tofa bazatayi shiru ba, ganin zata iya fasa mishi Kunne yasa ya Mike dagashi sai jallabiya a Hankali ya tura Kofar ya tsaya cak yana kallon yanda Baby take kuka tana Birgima akasa ranshine ya b'aci sosai yasan tana kukane Akan Wancan yarinyar cikin Tsawa yace "Baby tashi Anan!!!"

Ko juyawa batayiba taci Gaba da kukanta

"ba magana nakeyi miki ba? "

Cigaba da kukanta tayi ranshi Ab'ace yanufota ganin haka yasa ta Mike da gudu tayi hanyar d'akinta Tsayawa Yayi yana kallonta Dariya tabashi sosai, dakin Tsaya Ai da jikinki Yayi tsami banza kawai"

Baby tana shiga d'aki tafad'a kan bed tana rizgan kuka Tabbas data Sani dabata cewa Fadila suzo gidansu ba da mutuncinsu yafi Haka Yanzu babu mutunci Sam Sam a tsakaninsu momy ta zubda girmanta a idon Adda Fadila Kunya takeji sosai idan tahad'a Ido da Fadila, wani tunanine yafad'o Mata Tamike tanufi Wurin drower wayarta ta d'auko takira numban Dady ringing biyu Dady yayi receive lokacin yana Zaune a office, "Hello Mamana ya akayi?"

Kuka Baby tafashe dashi, cikin Tashin hankali dady yace "Meya faru Meya sameki kike kuka? "

Cikin kuka tace "Dady Momy ta daki Adda Fadila kuma ta Koreta agidan"

"what!!!" Dady yafad'a da Karfi har Saida Baby ta tsorata takara kallon Wayan, katse wayar Yayi yafita da sauri zuwa parking space, Motarshi yashiga da sauri yanufi hanyar gida ranshi a matukar b'ace,  Momy kwance take Akan gado tana choice chat a group sai Dariya take sosai Dan wata kawartace take bata labarin 'yar aikinta sanadin mijinta dayake lallab'awa yana zuwa Wurin 'yar aikin, Momy cewa tayi "ke kika yadda Wlh aini nan Bana d'aukar iyayi da raini Koshi Alhaji tsorona Yake sosai..." garau taji an bud'e Kofa a Rikice tajuya tana kallon Ko Wayene ganin Dady tsaye yana Huci yasa jikinta yabata, dakewa tayi tace "Sannu my Sweet" cikin b'acin rai Dady yace "yau Ko Alawa zaki kirani bazaki kara kwana a gidannan ba sai Kinje Kin dawo da Fadila"

Momy tace "Akan wannan yarinyar kakemin barazanar Barin gidanka?"

Ran Dady ne yakara b'aci yace "zaki bar gidanma Gaba d'aya"

Momy cikin tsiwa tace "Anya Alhaji babu Wani b'oyayyen Al'amari tsakaninka da yarinyarnan?"

Da Yatsa dady ya nunata yace "Wlh kinji na rantse yau idan Baki dawo da yarinyarnan ba saidai Ki koma gidan me saida Goro"

Momy tace "Meya kawo mahaifina cikin wannan Maganar? Akan wannan talakar banzan kake Zagin mahaifina?"

"ke gidanku masu kud'ine? Kina 'yar malam Shehu kike Zagin wata talaka Wlh kifita a idona idan nad'au mataki akanki bazakiji dadi ba, kibar ganin Ina rufa miki asiri a gidannan kina rayuwar jin dadi, wlh idan na sakeki yau ba karamin wulakanta zakiyiba, maganata ta karshe shine kificemin agida kada Ki kuskura kidawo saida Fadila"

Hanyar Kofa yanufa yarufe gum Kamar ze b'alla, zuciyar momy ne ya tsinke jikinta yafara rawa Tinda take da Alhaji be tab'a cimata mutunci irin na yauba, Maganganunshi sunyi tsauri kuma Tasan halinshi idan yafad'i magana d'aya baya maimatawa, "Nashiga uku ta Ina zan fara nemo yarinyarnan?"

Sakonnin watsapp ne suketa shigo Mata batako kulaba Dan tana cikin Tashin hankali.

         "tun mama tana tambayar Amrah Meyafaru harta hakura ta kyaleta shima Abba Yayi iya bakin kokarinshi Dan ganin yaji Meya had'ata da Kamal amma tirr Amrah taki Fad'i, kwance take a falo tana kallon TV hankalinta kwance, gefenta goran Faro ne da Banana juice  a cup sai cake datakeci kad'an Kad'an, yau Mama tafita unguwa gidan kawarta Shikuma Abba yaje Wurin sana'a ta maida hankalinta kan news taga an nuno hoton wata Mata da namiji a gefenta fuskarsu rufeda bakin Kyalle, mai bada labarin ne yace "Kamar yadda kuke Kallo wannan itace matarda ta kashe d'anta ta saida idonshi da harshenshi dakuma yatsunshi wa Wani attajiri a garin Abuja tareda had'in bakin mijinta, ku saurara zakuji bayani daga bakinsu kasancewar babban jami'in d'an sanda ya nemi alfarmar a rufe fuskokinsu"

Damm gaban Amrah yabada sauti ganin yanayin Jikin Kamar na Fadila, bata kuma tsorata ba saida taji an fara tambaya Kamar Haka,

"Baiwar Allah Yaya sunanki?

"Sunana Fadila"

"Ke 'yar Wani garine?"

"Ni 'yar adamawa ce"

"Meyasa kika kashe d'anki da hannunki?"

Cikin sheshekar kuka Fadila tace "niban kashe d'ana ba hasalima ban tab'a Aureba yauma tsautsayine yafitar Dani"

"Shin Ina iyayenki?"

"Iyayena sun mutu tun Ina yarinya"

"to Ina kannenki?"

"banida kanne ni kad'ai iyayena suka haifa kuma Bana rokon Allah yasa ace Inada k'anwa Ko k'anne" tana Maganar zuciyarta yana zafi Kamar tasa hannunta ta zaro daga kirjinta, Haka aka Gama Mata tambayoyi aka dawo kan driver shima yabada amsa yacce Fadila ta bada, Amrah mikewa tayi da sauri ta kashe TV jikinta yana rawa Tarasa abinyi sai yarfa Hannu take, ganin batada mafita yasa ta zare d'an Kwalin kanta tayi jifa dashi atake dogon gashinta ya bayyana har gadon Bayanta, zufane yafara Wanke Mata goshi, Mama ce tayi sallama tashigo ganin Amrah Haka yasa ta Mugun firgita Badai Jinnu ne suka shiga Jikin d'iyar Tata Bakam da sauri taje Wurin Amrah Tareda rikota a lokacin Amrah hawaye yazo Mata fad'awa tayi Jikin mama tana rabza kuka, Mama tace "Meya sameki?"

Cikin kuka Amrah tace "Mama Adda Fadila tab'ata mana suna acikin TV naga an nunota wai an kamasu agidan Karuwai dake garin Abuja shine akace Ina iyayenta tace wai Kun Mutu, kuma batada k'anwa, Mama Tsoro nake kada Adda Fadila tasa Ku Mutu sabida bakin ciki" kuka Takuma fashewa dashi mama tsabar haushi yasa tace "mune wai Muka Mutu?"

Amrah tace "Eh Ina tsoron kada Ki mutu da gaske"

Mama tace "kwantar da hankalinki bazamu mutuba sai lokacinmu yayi kinji? "

Gid'a Kai Amrah tayi tace "Mama kibarni Nayi bacci a jikinki Wlh na Mugun tsorata"

Janyota mama tayi zuwa kan sofa a hankali take shafa kanta har saida tayi bacci Kafin ta zame a hankali zata Mike taji Amrah tarike hannunta gam gam Kamar zata tsaga, murmushi tayi sannan ta janye a hankali tabar Wurin.

08144818849

[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸

    *K'ANWATA*

  🌸🌸🌸🌸🌸

    Na

Jiddah S Mapi

*Chapter 44*

         ~Abdul ne zaune agaban Dady sai masifa Yake mishi Kamar zai dukeshi cikin zafi Dady yace "Wlh Wlh kaji Nayi rantsuwa saika auri Fadila kuma Bazan maida rantsuwana kaffaraba, yaushe aka haifeka? Dazaka had'a Baki da mamanka Ku Kori baiwar Allah, yarinyar nan Kunsan matsayinta a Wurina kuwa?"

Cikin Mamaki Abdul yace "Aa Dady ban saniba"

Cikin zafin nama dady yamike yanunashi da yatsa Tareda cewa "idan ka sake ka kara gayamin magana cikin Isa saina Wanke wannan fuskar taka me Kamada jikakken Kashin Mari, shiru Abdul Yayi Dan yau ya mugun tsorata da Dady be tab'a zaginshi ba amma yau Harda su Mari, da gudu Baby tashigo tana kiran Dady!!! Dady!!! Juyawa sukayi dukka suna kallonta, muryanta na rawa tace "Daddy ka kunna news kaji Meyake faruwa, kunna TV Yayi yashiga news Dan yasan Ko tambayarta Yayi bata hayyacinta bale tabashi amsa, cikin ikon Allah sai gashi an kara nunasu Fadila sai Maimaita zancen ake Kamar da Gaske, waya Dady ya Ciro daga aljihunshi yakira Wani number yace "Wani zancen banza nakeji a news Yanzu? Kunsan yarinyar da kuka rike kuwa?  Daga gidana tafito yaushe tayi aure harta haihu Harta kashe d'anta? Wani station take? "

Kitt ya kashe wayar yace "Abdul Baby kushirya mutafi"

Baby Ko Gyale bata Saba daga ita sai dogon Riga da karamin d'an Kwali Mota suka shiga driver yazo suka nufi station, suna Isowa Dady yabud'e yafice cikin station yawuce kowa yana Mika mishi gaisuwa, Hannu kawai yake d'aga musu, yana shiga yace "Ina take? "

Fadila tana zaune acikin kanta Sai kuka take rabzawa tana rokon su saketa, ganin dady dasu Baby yasa tafara ihu tana kiran sunansu, da gudu Baby taje Wurinta Tareda riko hannunta tana kuka,  Dady yace "Ku saki yarinyarnan Kafin nakai magana gaba"

Babban d'an sandane yace "kufitar da ita kada kowa yasani"

Cikin b'acin rai Dady yace "harda shi wanda kuka Kama tare"

Tare aka sakesu batareda Anja zance ba sabida Sunsan Dady tsarai, Abdul tsaye Yake agefe yana shan kamshi sai had'e rai Yake yana kallon Fadila Tabbas daba Dady awurin dayasa Anyi Mata Dukan tsiya, Kallonshi Dady yayi yace "Kai Abdul Zoka rike hannun Fadila ka kaita Mota Ina zuwa"

Had'e rai Yayi yafara tafiya a Hankali Kamar ana turashi yana kunkuni, Dady yace "Kai do Allah Kayi sauri da Wani wando sai kace b'era yaci"

Dariya Baby da Fadila sukayi Dan Maganar tabasu Dariya harara ya banka musu Tareda kad'a Kai alamar zan had'u dakune, "muje" Abinda yace Musu, suka shiga hanya Baby rikeda Fadila, Dadi bakin Mota yace "tsaya" cak Fadila ta Tsaya amma bata Juyaba, matsowa Yayi Dab da ita ya kalleta Sama da kasa sannan Yayi nuni da Wurin Fanfo yace "wuce can Ki Wanke jikinki dan banason wari" kallonshi tayi Ido cikin Ido ya kawar da Kai, Tafiya tafara zataje tayi Abinda ya umurceta, Baby tace "muje na rakaki Adda"

"ita kad'ai zataje" yafad'a Ko kallonsu beyi ba,  Baby jikinta ne Yayi Mugun Sanyi ganin Fadila tayi gaba zuwa bakin Fanfo,  Meyasa 'yan gidansu sukeyiwa Fadila hakane? dady ne yafito yanata masifa Akan Abinda akayiwa Fadila,  ya Kallesu yace "Ina Fadila? "

Baby ta bud'e Baki zatayi magana Abdul ya kalleta yace "taje Wanke jikinta nace tashiga Mota taki wai saita Wanke jikinta daga Bayama batayimin magana ba" murmushi Dady yayi yace "Allah sarki yarinya me tsafta batada Hayaniya Hala tanaga Kamar inta shiga cikin motar zata cutar damu da Warine shiyasa tace bari ta Wanke jikinta"

Ran Abdul ne Yakuma b'aci Dady ya d'aurewa yarinyarnan Gindi Wlh, Baby kuma sai murmushi take ganin Dady  ya yabi Fadila, Mota Abdul yabud'e yashiga sai shan kamshi Yake, Fadila tana Wanke jikinta tanufo wurinsu tana murmushi tad'an durkusa tace "nagode Dady" Dady bece komai ba yashiga mota itama da Baby suka shiga driver yazo yajasu, bayan wasu Mintuna suka Iso gida, Wanka sukayi Gaba d'aya sukaci abinci, Dady yacewa  Baby kiramin momynku da Abdul zamuyi magana,

Momy sai zarya take acikin d'aki tarasa me zatayi, sallamar Baby ne yasa tajuya tana kallon Baby, "lafiya!?" baby tace "Dady ne yake kiranki yana falo"

Cikin Tashin hankali Momy tace "ranshi a b'ace Ko? "

Kafin takarasa tambayar Baby Tafice tarufe Kofa gif,  dafe kirji tayi da Kyar ta d'aga kafarta zuwa falo, ganin duk sun taru amma babu Fadila yasa taji kafarta Yayi Nauyi awurin ta durkusa sabida tana kara taku d'aya zata fad'i

          اكار حكري دن

Jiddah Ce

08144818849

[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸

*K'ANWATA*

🌸🌸🌸🌸🌸

Na

Jiddah S Mapi

*Chapter 45*

~Kamal!!! Kamal!!! Idan harni na haifeka Katashi kasha tea d'innan, Kamal dayake lullub'e cikin bargo jin Kanshi Yake Kamar zai tsage biyu, Umma cikin b'acin rai tafara magana "Kasan Bazan d'auki wannan Abunba, gidansu Amrahn zanje Dan bazasu d'aurawa d'ana cuta Sukuma suje suna zaune lafiyaba never, Kamal da Kyar yamike yana Rik'e da Kanshi, zama Yayi kad'an a gefen Umma yariko hannunta muryanshi yana hard'ewa yace "Dan Allah Umma Ki Auramin My Deela Wlh ita Nakeso ba Amrah ba Ki taimaki Rayuwan d'anki Tilo, Badan Halina ba"

Kuka yafashewa Umma dashi, tausayi d'anta Yake bata a halin Yanzu wannan shegiyar yarinyar tab'ata komai da komai, tace "Kayi hakuri Kamal babu aure tsakaninka da Fadila sabida idan babu iyayensu yau Fadila ce Uwar amrah kaga kenan ba aure tsakanin d'a Dakuma uwa, sabida Haka kacire Fadila a zuciyarka"

Kuka Yakuma fashewa dashi me ratsa zuciya yace "dan Allah Umma Ki taimakeni na rokeki"

Umma Jitayi Kamar ta kwashi hijabi taje gidansu Amrah takamata tayi Mata Dukan fitan rai, da kyar de ta lallab'a Kamal harya yadda yasha tea kad'an daganan Yakoma Yayi bacci, Umma Mikewa tayi Tsaye tana zagaye bedroom d'in tunanin abinda zatayiwa su Fadila da Amrah wanda zasuji duniyarma tá ishesu takeyi taji labarin Fadila ta tafi yawon karuwanci Tabbas saita d'au mataki Akan Amrah da iyayensu wad'anda suka d'aure mata gindi, waya taciro a aljihun riganta d'inkin Buba wanda yaji tsones Wani number Takira cikin kafiya tace "Kafin gobe inaso a binkicomin gidansu Amrah matar d'ana Abdul shin haya Suke Ko gidan Kansu ne? Idan gidan Kansu ne a binkicomin wanda yasiyar musu gidan sannan Inason sanin miye sana'ar Babansu Dakuma Wurin sana'ar tashi"

Kashe wayar tayi tace "MUZUBA MUGANI".

"Amrah bacci takeyi sosai dan Tanason bacci a rayuwarta wayartace tafara ringin hannu tamika ta d'auko cikin gigin bacci tace "Hello"

"Amrah Ikon Allah har kuka Rabu da Kamal bazaki fad'amin ba? "

Tsaki Amrah taja tace "Kinga Zee Nifa bacci nake banason damuwa"

Zee tace "Lalle kam kurabu da Kamal santalelen miji Haka Kice kina bacci?"

Cikin Gajiya da magana Amrah tace "to me zanyi idanba baccin ba?"

"daminshi zakiyi awaya harsai yafara kulaki kirinka kissa da kisisina irin tamu ta mata, idan so samune har

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login