Showing 57001 words to 60000 words out of 139192 words

Chapter 20 - Kanwata Book One Complete Hausa Novel

Jiddah   

27 Sep 2025

860

"Allah na rokeka kada kasa inyi nadamar abinda nayiwa Fadila Allah kada kasani na rokeka" kula takeyi tana yin addu'ar Kamal ne yashigo d'akin ya tsaya abakin kofa yana jinta addu'ar datkeyi ya tsaya mishi a wuya me tayiwa Fadila? Karasawa yayi wurinta ya zauna ya lank'wasa kafarsa kamar me d'aukan karatu yakalli Amrah yace "me kika yiwa Fadilar?"

A razane tajuya tana kallonshi bakinta yana rawa tace "ba komai fa"

Rarrafawa yayi zuwa wurinta yana Kallon cikin idonta yace 'zaki fad'amin ko saina yankaki na dafaki na cinye?" A firgice take kallonshi tace "banyi mata komai ba nikam" murmushi yayi kana yace "banza batakai zomo kasuwa Amrah nasan akwai wani Abu akasa yau sekin fad'amin idan bahakaba zan kasheki"

Zazzare Ido takeyi tarasa mema zata fad'a mishi tarasa ta inama zata fara a zuciyarta tace "hande min boni hande min babbi"

Jiddah Ce

08144818849

[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸

   *ƘANWATA*

🌸🌸🌸🌸🌸

Na

Jiddah S Mapi

*Chapter 41*

      ~karasawa yayi cikin d'akin ya zauna a gefenta manyan idanunshi ya zuba mata, atake taji jikinta yana rawa ba karamin kwarjini yayi mata ba ta tsorata matuka dataga yanda yake kallonta, Kamal lips nashi na kasa yad'an ciza kad'an dama ya jima yana zargin wani Abu gashi kuma yana ganin rashin gaskiya a idonta yanzu, "zaki fad'amin ne ko kuma"

rau rau tayi da idanu tana kallonshi cikin rawan murya tace "um um nikam fa babu abinda nayi mata"

Matsowa yayi dab da ita har suna iya jiyo numfashin juna kura mata Ido yayi yanda jikinta yake rawa yasan akwai Abu akasa, a hankali ya kwantar da murya cikin son gano gaskiya yace "Autan Mama ki fad'amin me kikayiwa Fadila kinji"

'Dago kai tayi ta zuba mishi idanunta me d'auke da wani sirri tace "Yaya Kamal saidai idan nafad'a maka bazaka fad'awa kowaba"

Gid'a mata kanshi yayi yace "naji"

Tace "sai kayi min alkawari tukun" yace "nayi"

Sunkuyar da kanta tayi tana kallon dogayen yatsun kafarta, hannunta ya riko cikin sanyi yace "ina jinki kinyi shiru"

Hawayene yafara bin kumatunta a hankali tace "nice na cuci Adda Fadila nice nasa aka saceta ranar kamu wallahi nayi hakane sabida ina sonka kuma nasan itama tana sonka Dan Allah kada kafad'awa kowa" shiru Kamal yayi sannan yace "kin tabbata hakan"

Amrah tace "Eh na tabbata"

Ciro wayarshi yayi yace "duk abinda kika fad'a nayi recoding kuma saina fad'a a idon kowa dama na dad'e ina zargin hakan amma idan nafad'a banida hujja yanzu nasamu hujja me kyau kuma kisani bazan zauna da muguwa kuma fasika ba" mikewa yayi zai bar d'akin riko kafarshi tayi da hannu biyu tasaki kuka "Dan Allah yaya Kamal ka rufamin asiri na tuba wallahi na tuba ka taimaka min kodan cikin dayake jikina" bugeta yayi da kafarshi tafad'i kasa idanunshi yana zubar da hawaye yace "kinyi asara bazakiga haske a rayuwarki ba kuma na sakeki saki uku"

Kanta ta d'ago a firgice tana kallonshi tace "ba'a fa saki da ciki"

"Cikin banza cikin wofi ai dai ba cikina bane bale kice na aikata haram ke kikasan inda kika d'ibo"

Rashin hankali yahana Amrah yin magana gefe d'aya kuma cikin yafara murd'awa, Kamal yec"kafin nan da minti goma kitara kayanki kibarmin gidana"

"Dan Allah Dan Annabi kayi hakuri wallahi baba zai kasheni ka gafarceni" Kamal jiyake kamar tana zazzaga mishi ruwan dalma a zuciya haushin dayakeji kamar ya dab'a mata wuka yakeji, janta yafarayi dama da hijabi a jikinta hangar wake yanufa da ita tana ihu tana rokanshi amma  ina, Umma ce tafito daga side nata tanajin ihun Amrah da sauri takarasa tana tambayar Kamal meya faru, cikin kuka yafara fad'a mata abinda yafaru harda maganar cikin bai bar komai ba, Amrah sai kuka take tana basu hakuri Subari sai gobe takoma gida, Umma kallonta tayi tace "nasani shiyasa banaso Kamal ya rab'eki tun ranar Auren ina ganin yanayinki wallahi kibi duniya a hankali sannan kitashi kibar mana gida idan ba haka ba wallahi sainayi miki dukan tsiya"

Amrah rarrafe tayi taje wurin Umma rike kafarta tayi tana bata hakuri Mari Umma tayi mata me lafiya tace "zaki fita ko ko?"

Kamal ne yazo wurin yajata akasa har kofar gida turata yayi yarufe kofar megadi sai ganin ikon Allah yake, Kamal yana rufe kofar ya zauna a wurin dafe da kirjinshi sai hawaye yafara bin fuskarshi a hankali ya had'a kanshi da gwiwa yafara kuka, Umma ce tazo wurin tareda dafa kafad'arshi cikin sanyi tace "ba kuka zakayi ba addu'a yakamata kayi"

"Umma ya zanyi? Na lalata rayuwata tun daga farko Umma kitaimaka min yaya zanyi?"

Rungumeshi Umma tayi tanad'an buga bayanshi cikin rarrashi tace "kadaina kukan haka ya isa Allah yasa hakan shiyafi Alkhairi"

Shiru yayi yana sauke ajiyar zuciya,

Amrah yana fitar da ita tahad'a kanta da jikin Get d'in tafara kuka yanzu idan taje gida tasan Umma zata kasheta idan tayi dalilin zuwan nata to amma idan bataje gidan ba ina zataje? Ganin dare yana nisane yasa takama adaidaita tashiga zuwa ganye road saida suka iso tacewa me napep batada kud'i yayi hakuri, ai kuwa yayi parking a gefe yafito cikin masifa ya nunata da yatsa yace "kin isa? dama kinsan bakida kud'in napep kika hau? Ki bani kud'ina ko nayi miki rashin mutunci" hakuri tafara bashi Dan tasan idan taje gida Mama taji abinda yakawota ba kud'i zata bata ba, rike hijabinta me adaidaitan yayi yace saita bashi kud'inshi sai kokarin kwacewa take amma yafi karfinta, cikin masifa itama tace "malam nifa matar Aurece ka sakarmin hijabi"

Yace "kinsan ke matar aurece kika nemi arike miki hijabin?"

wani mutum ne yazo wucewa yaga halinda suke ciki karasowa yayi yace "lafiya kuwa?"

Me adaidaita yace "napep nawa tashiga wai batada kud'i"

"Nawane kud'in maka?"

Yace "kud'ina d'ari uku ne"

d'ari uku yacira yabashi kafin ya sakar mata hijabin, bayan yatafi ne mutumin yakalli Amrah yace "bakiji kunya ba? Ace kina mace namiji ya tsareki haka akan kud'i ai tun farko saiki fad'a mishi yanzu wani bazai San gashi abinda ya had'aku ba sai yayi zaton wani Abu daban gaskiya ki kiyaye"

Cikin share kwallah tace "na gode Baba Nima bada sona hakan tafaru ba kuma bazan karaba"

Murmushi yayi yace "Allah yayi miki albarka"

"Ameen" tace kafin tawuce zuwa gida tsayawa tayi abakin kofa tana kuka tarasa mezatace ya dawo da ita a wannan daren, Abba ne ya dawo daga masallaci hannunshi rike da carbi dakuma toci salati yayi ya haska inda yaji kukan yana fitowa ganin Amrah tana kuka yasa yace "lafiyanki kuwa?"

A firgice tajuya tana kallonshi ganin Abbba ne yasa kukan nata yakara karuwa, Abba yakaraso wurin yariko hannunta yace "tashi mushiga ciki kidaina kuka"

Tashi tayi tabishi har cikin gida, lokacin mama tana salla zamar da ita yayi akan tabarma yace "bari nakawo miki ruwa kisha" ruwan ya d'ibo yakawo mata a hankali takarb'a ta aza a bakinta saida ta shanye Tass kafin ta sauke, Abba yayi mamakin ruwan data shanye yace "akaro miki" gid'a kai tayi alamar eh, karo mata yayi shima saida tayi rabi kafin ta ajiye cup d'in, mama tana idar da sallah ta dafe kirji tace "lafiya kamar Amrah ko?"

Amrah tace "nice mama"

Tashi mama tayi daga sallayan tace "meya faru?"

Kuka Amrah tafara Abba yace "barta mana ta huta zuwa gone saimu tambayeta amma yanzu bakiga a gigice take ba"

Mama tace "bazan iya jira zuwa gobe ba hankalina ya tashi Amrah daba kuka take yiba sai Abu yaci tura itace yau take wannan kukan?"

Abba yace "komadai menene abarta zuwa gobe"

Mama tace "to" tareda riko Amrahn suka tafi d'aki kan gado ta kwantar da ita tareda rufeta da blanket, runtse Ido Amrah tayi tana Allah Allah kada gari ya waye Dan batasan me zata fad'a musu ba ta tabbata idan sukaji abinda yadawo da ita sai sunyi mata abinda tafi na Kamal da mamanshi, Mama kuma tana zuwa d'akin Abba tafad'a jikinshi tana kuka "meyasa abubuwa marasa dad'i suke faruwa da yarana?"

Abba yace kidaina kuka komai yayi tsanani yana tareda saukinshi, da kyar dai ya lalkab'ata tayi shiru.

        "Fadila damuwar me garin yawa tashiga yanzu waye Daddy zai aura mata cikinsu Uba da d'a, addu'a take Allah yasa ya tambayi ra'ayinta wallahi batason koda d'aya a cikinsu, Number Yarima Takara gwadawa kamar dawasa taji an d'aga shiru akayi ta d'ayan b'angaren cikin sanyin murya tace "salam alaika"

"Wa alaikissalam"

Shiru tayi bata kara cewa komai ba sai filo dataja ta matse a kirjinta jin muryanshi daya daki zuciyarta, "wake magana" yafad'a kamar bayason yin magana, cikin sanyin murya tace "Fadila ce" ta d'ayan b'angaren Kabeer mikewa yayi daga kwancen dayayi cikin muryan mamki dajin dad'i yace "My Deelah" da sauri ya buge bakinshi yace "ayya sorry"

Lumshe Ido tayi Takara bud'ewa tunawa da Kamal datayi Kamal ne kad'ai yake iya kiran sunanta har taji shauki a ranta idan tana way a da Kamal wani lokacin sai taji kamar ta had'iye filon dayake gefenta tsabar shaukin dayake sata, gashi yau Yarima yasata acikin yanayin data jima bata shiga ba, a hankali tace "Ba komai Yarima na"

Yarima wani dad'i yaji a zuciyarshi jin tace mishi yarimana, "ya kk ya kwana tirim shine kuka kini ko?"

Tace "Aa ban kika ba yanayi ne ya kika amma kana raina"

Yace "Nina kina raina Fadila wallahi na kasa mantawa dake har Adamawa naje na nemeki wallahi ban sameki ba kullum sake nake kwana a raina mai martaba yasa a nema mishi ke sabida yaga damuwar danake ciki amma ba'a sameki ba Fadila ki taimakawa rayuwata kada bugun zuciya ya kamani"

Shiru tayi tana saurarn zazzakar muryanshi har wani lumshe Ido take, haka sukayi waya yace "anjima zan kiraki ko zaki d'ibemin kewan Dana jima inayi yanzu me martaba ya aika akirani, Amma kafin nakashe ki fad'amin kalma guda d'aya dazai jima a zuciyata"

Fadila shiru tayi tarasa me zatace mishi, sai can tad'an rage murya tace "I miss you"

Wani irin dad'i ne ya ziyarci Kabeer jiyake kamar kada ya kashe wayar, kitt Fadila ta katse Kallon screen d'in yayi yasaki murmushi, itama murmushi tayi tana Kallon wayar, Baby ce tashigo idonta yad'an kumbura kad'an ganin Fadila tana Kallon waya tana murmushi yasa takarasa wurinta ta zauna cikin son kawar da damuwarta tace "meyasa Adda ta murmushi?"

Fadila tace "Yarima ne Yarima bai manta ni ba Baby hasalima soyayya yakemin me zafi, danaji muryanshi sai naji kamar an bani kyautar aljanna ne shima na tabbata hakan yaji domin alamu sun nuna" murmushin dole Baby tayi ta d'auke kanta gefe kamar tana kallon wani abu so take tamayar da hawayen dayake kokarin zubowa muryanta yana cracking tace "lalle kama yayi kyau gaskiya"

Kallonta Fadila tayi a hankali yasa hannu ta juyar da kanta tana kallon idanun Babyn Ganin tana sunkuyar da kanta gashi idonta ya kumbura yasa tace "lafiya Baby? Badai fad'an su Daddy kikasa ranki haka ba?" Sai alokacin Baby tasamu damar Rungumeta kuka tafashe dashi Fadila tana bata hakuri har tayi shiru ta kwanta lub tana sheshshek'a, Fadila tayi zaton fad'an Mommy ne yasa Baby kuka ita kuma Baby tana kuka ne sabida yanda son Yarima yake azalzalar zuciyarta, dahaka kowa ya kwanta yana sake sake a ranshi.

Washe gari

Mommy ce taje d'akinsu Fadila ko karyawa batayi ba tsabar masifa tana zuwa ta tarar da Fadila tafito daga wanka jikinta d'aure da 'yar karamar towel ta baza gashinta sakamakon wankeshi datayi dryer ta d'auko ta jona tana kokarin busar da gashin, kallonta Mommy takeyi daga sama har kasa lalle idan tasake Daddy ya aura wannan santaleliyar yarinyar to babu shakka zata zama 'yar kallo wannan diri da gashi ga kyaun har ina? tab akwai akwai aiki a gabana, Fadila taji ajikinta ana kallonta juyawa tayi ta kalli kofar ganin momy ta zuba mata Ido yasa tayi sauri ta d'auko zundumemen hijabi tasa ajikinta durkusawa tayi tace "ina kwana Hajiya"

Mommy tace "ban kwana ba tashi sama nayi har gari ya waye biyoni d'akina yanzun nan"

To tace tareda mikewa ko shafa mai batayi ba tasa Riga dogo me guntun hannu tanufi d'akin Momy sallama tayi lokacin momy tana bedroom tace "shigo nan" karasawa tayi tasamu tana zaune akan gado tana girgiza kafa, zama tayi a gefenta ta sadda kai kasa momy tace "Ke d'ago ki kalleni"

Kasa d'ago kai tayi "ba magana nake miki ba?"

'Dago kai tayi ta kalli momy tareda kuma sauke kanta momy tace "wato kinje kinyi tsafi kinbi malamai kinzo gidana zaki kwacemin iyalaina ko? To bari kiji nafad'a miki zuru batacin zuru saidai suhad'a zuru suci zuru zuru, kinyi kad'an wallahi inaso anjima kije kisamu Akhaji da kanki kice akyason Auren sabida Abu biyu bazasuyiba a lokaci d'aya gudu da Sosa gindi dolene  ayi gud'a d'aya ko gudun ko kuma Sosa gindi, baza mu taimaka miki kizo kici amanar mu ba, baki isaba idan kuma bazaki iya fad'a mishi ba kisan inda dare yayi miki ki tattara ni zan baki kud'in mota okay ashema kinada mota zan baki kud'in mai harda kud'in wani motar kai har saudiyya zan kaiki da Dubai duk idan kinaso sannan zan sallamaki da kud'i masu yawa Wanda zasu isheki rayuwa dake da iyayenki Dan nasan sune suka aika ki nan nidai burina da rokona shine kitaimaka kibarmin iyalaina"

Hawaye Fadila take zubarwa masu d'umi ba hawayen maganar da momy ta fad'a mata take ba aa hawayen abinda Amrah tayi mata har tasa ana zagar mata iyaye take, a hankali cikin zanyi tace "to momy Amma inaso kisan wani Abu guda d'aya kaddara tanakan kowa sannan duk Wanda yayi Aure mijinshi ya aura wani baya auran matar wani idan Allah yace zan auri Daddy babu yadda na iya dole na yadda domin Allah baya tambayan ra'ayi, sannan zan bar gidannan kamar yanda kikace amma saina sanar da daddy sabida karyace na gudu Dan banason maganarshi" mikewa tayi zata fita momy taja hijabinta ta baya kasa tafad'i ta fara kuka, duka momy tafarayi mata tana sauke haushinta akanta, koda wasa batayi ihu ba bale mutane sushigo abaiwa momy laifi sai kuka datake tana kokarin kwace kanta.

Jiddah Ce

08144818849[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸

    *K'ANWATA*

  🌸🌸🌸🌸🌸

    Na

Jiddah S Mapi

*chapter 42*

          ~duka momy takeyiwa Fadila Kamar zata aikata Lahira amma Ko kit Fadila batayi ba sai kukan zuci datake tana Sauke ajiyar zuciya, saida momy tagaji Dan kanta Kafin ta kyaleta a hasale tace tashi kifitamin a d'aki Kafin na kasheki, Fadila mikewa tayi zata fita idanunta sun cika da hawaye karamin bakinta sai rawa Yake a hankali hawaye suka fara Sauka daga Ramin Idonta zuwa kumatunta kafartane ya riketa daidai bakin k'ofa tayi baya baya Kamar zata Fad'i Abdul daya Dad'e tsaye a bakin Kofa ne yayi saurin rikota ta fad'a jikinshi Fadila ganin Abdul yasa kukanta ya tsananta don Gani take Kamar zai kara dukantane Akan wanda momy tayi Mata, k'ank'ameshi tayi sosai tana kuka, Abdul tsareta Yayi da manyan idanunshi yana kallon yanda lips Nata Yake rawa a hankali yaji jikinshi yanayin Sanyi cireta Yayi ajikinshi ya Zabga Mata harara ganin momy tana Aika mishi Mugun Kallo yace "stay away from here" Fadila kallon cikin idonshi tayi tace "Bama nanba gidan zan bar muku Gaba d'aya Bazan iya zama dakuba Wallahi nagaji da wulakanci Ku sanifa ni Macece me rauni Allah yace Ku tausayawa Mata sabida Mata Abun tausayine Dalilin Haka yasa Allah yace Ku auri Mata daga d'aya zuwa biyu zuwa uku zuwa hud'u (Fankihu ma d'aba lakum Minannisa'i Masna wa salasa warba'a fa'in Khiftu fawahidatan awma malakat aimanukum) Allah ya Fad'i hakane sabida maza su Kula da Mata sosai musamman idan Allah Yayi maka bud'i, Mata munada tausayi sosai Saide Wani lokacin kishi yanasa Muzama Kamar mahaukata Yanzu ace Kamar ni Fadila yarinya Karama Dani wacce Bazan wuce shekara 19 ba Ina fuskantar wannan rayuwar? Badan Allah ya Yini da d'an ilimi ba da war Haka Ai dana Dad'e dazama Karuwa me lasisi, amma Ina Godiya wa Allah daya samin tsoronshi a zuciyata bayin Allah Ku tausayamin Ku tausayawa rayuwata..."

      Jikin Abdul ne Yayi Sanyi sosai shifa bayason Yaga mace tana hawaye a rayuwarshi kawar da Kanshi yayi gefe ganin Fadila tana Kokarin Karya mishi zuciya, momy ta tsaya tsaye Kem Kamar botarami takasa motsi kalaman yarinyar sonso suyi Tasiri a zuciyarta amma tana tsoron faruwar Hakan, Fadila d'akinsu da Baby ta wuce Baby tana zaune Abakin gado taga shigowar Fadila Ko sallama batayiba tawuce Wurin akwati shiru tayi tana kallonta saida Fadila ta zab'e kayanta tas Kafin tad'au makullin motar da Dady yasaya Mata towel d'in ta zame ta Saka bra da dogon wando Wani dogon Riga me roba roba tasa tad'auko Wani hijabi pink colour tasa face mask Baki ta d'auko awata 'yar Karamar Jakarta da glass fari tasa yanda fuskarta ya rufo babu me ganinta ya ganeta, kallon Baby tayi wacce tayi tagumi tazuba Mata na mujiya, had'a face tayi taja akwatinta daidai bakin Kofa tace "sai Watarana idan kina Kaunar Allah da Annabi Muhammad (S.A.W.) kada Ki Dakatar Dani Kibarni natafi cikin rufin Asiri ba Tareda kowa yasan me ake cikiba" tana fad'ar Haka tabud'e Kofar tawuce, Baby ganin da gaskefa Fadila take tafiyar zatayi yasa ta Diro daga kan bed tanufi Kofa Jan hijabin Fadila tayi baya tace "Adda Fadila Kin Raina Daddy ne dazaki fita bacin yace kada Ki kuskura kifita batareda saninshi ba?" fisge Hijabinta tayi Ko magana batayiwa Baby ba taci Gaba da tafiya Dan yau ta kuduri aniyar bazata sake kwana Agidan ba, Baby sai Binta take Kamar zautacciya tana magana amma Fadila Ko kallonta batayiba, Da Baby taga ba sarki sai Allah tafara ihu tana kiran taimako, Fadila ganin Haka yasa ta ajiye akwatin tafara gudu batason zaman gidan ta gwammace tabar Baby dukda son datakeyi Mata Akan ta zauna tana fuskantar wulakanci agidan, saida ta Iso bakin Kwalta Kafin ta tsaya da gudu Wani me Taxi ta tsayar shiga tayi tace "malam ka kaini bayan gari" kallonta Yayi yace Amma kinsan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login