Showing 66001 words to 69000 words out of 139192 words

Chapter 23 - Kanwata Book One Complete Hausa Novel

Jiddah   

27 Sep 2025

885

d'iba suka Gama Kaiwa toilet Kafin Baby tafice tabar Fadila a toilet d'in taje d'auko omo da sabulu, Fadila ruwa ta kunna tasa babban bath tana tara hannunta tasa tana wasa da ruwan,  bud'e kofar akayi tace "Baby Kinga abinda kikaja mana Ko?  Yanzu ace wannan tulin wankin Zamu Wanke?  Ko agida Wallahi Amrah ce take mana Wanki tsabar yacce natsani Wanki, Ke kika fara neman fad'ana daga tashi a bacci saikice wai zai rungumeni wannan Mugun Ai saidai ya tsagani biyu Da fuskarshi Kamar kunun tsamiya ba sugar d'in, dole Kiyi shiru Ai Tinda kinsan Bakida gaskiya"

Juyowa tayi taga Mutum tsaye a Bayanta ya rungume hannunshi a faffed'an kirjinshi yazuba Mata Ido yana sauraran abinda take fad'a, jikintane yafara rawa ganin yanda yazuba Mata Ido, cikin in Ina tace "um.. um kaine.."

Baiyi magana ba sai Ido daya zuba Mata, ganin Haka yasa ta rab'a ta gefenshi zata gudu, riko hannunta yayi be juyoba, hawayene yafara bin Idonta tace "Dan Allah kayi hakuri"

Saketa Yayi yaje bakin Kofa yasa key ya kulle toilet d'in, cikin gigita ta d'ago kanta tana kallonshi  baice komai ba, kuma be saki hannunta ba, janta Yayi zuwa Wurin wankin yace sunkuya Ki Wanke kayannan kada kisa omo Ko sabulu Haka zaki Wanke kuma kada naga datti Ko d'aya aciki, idan sun bushe Ki gogesu kisa a wardrobe yau, Ko ruwan Sama akayi Ki tabbatar sun bushe"

Yana fad'an Haka ya d'ale kan Wani drower yana kallonta, sai b'ari jikinta Yake gashi kayan bacci ne ajikinta duk jikinta ana Kallo kanta babu d'an kwali gashinta bata Gyaraba,  ita ba wankin bane ya dameta yanda ya zuba Mata Idone yasa takasa Sakat, idontane yakai kan Wani jallabiyanshi me dogon Hannu,  d'auka tayi tad'aga ta Kalla sannan ta juya ta kalleshi ganin hankalinshi Akan waya yasa ta Sauke ajiyar zuciya da sauri tad'aga riganta Sama tacire, Allah ya taimaka tanada skin tirt da sauri ta zura jallabiyan tana tana gyarawa, duk abinda take yana kallonta hankalinshi yana kanta ganin yanda jallabiyan Yayi Mata yawa yasa ya kawar da Kanshi gefe yana had'e fuska, Fadila sai Yanzu taji hankalinta ya kwanta amma Rashin d'an Kwalin yasata kara zama a takure, alebo d'inshi ta d'auko tana Kokarin d'aurawa akanta amma gashinta yaki taruwa wuri d'aya sai kiciniyar d'aurawa take yakiyi, jitayi ya rike alebo d'in da sauri ta Sakar mishi, nad'ewa Yayi biyu ya riko kanta a hankali ya mayar Mata da gashin baya sannan yasa Alebon ya d'aura Mata da sauri ta saki kanta yajuya yakoma Inda ya tashi, shiru tayi tafara Wanke kayan tana shanyawa, tin tanayi bata gajiba harta fara rufe Ido tanajin bacci, Baby data jima a bakin Kofa  tanaji kuma tana Leko abinda Yake faruwa da sauri tabar cikin falon ganin yana bud'e Kofan, fita Yayi yazauna a falo Ita kuma Fadila tanata Wanki tana rufe Ido,ta Gaji harta galabaita, Bayanta konkosonta hannunta duk suna ciwo hannun Yayi ja sosai,

Baby  tarasa yanda zatayi idan taje tasan Tabbas ze koreta kuma batada mafita, Wani tunanine yafad'o Mata da sauri tanufi dakin momy,  tana zuwa tafad'a kan gado, kallonta momy tayi tace "yau kika Ga daman zuwa Wurina kenan? Ina sabuwar uwar taki? "

Dan karamin tsaki Baby taja tace "tana Wurin Yaya ya kirata tana toilet nashi shima yana ciki Ko Wanki takeyine Kome sukeyi oho musu"

Da sauri momy ta kalleta yace "toilet kuma? "

Baby tace "Eh kuma ya rufe da alama Wanki yasata amma kada Kafada mishi Nina fad'a miki"

Momy tace "to tashi kije"

Tashi Baby tayi da murna Dan tasamu mafita, waya momy ta d'auka takira number d'in Abdul, tace "hello Son kazo kaje Kauye ka karb'amin magani kirjina yafara ciao sosai" takarasa Maganar tana tari, da sauri Abdul yafara cewa Sannu, kaya yacanja da wuri yad'au makullin mota yafice har yayi Nisa yatuna da Fadila komawa Yayi ya kulle side nashi yabarta aciki, Baby data lab'e jitayi Kamar ta Tsala ihu ganin ya rufe kofan ita datayi haka Dan ta taimakawa Fadila shine ze rufe side nashi? Tsani taja tace "Adda Fadila Kin hadu da Mugun miji wlh"

Fadila tawuni Akan Wanki sannan tafara guga, saida ta Wanke ta goge Tass sannan ta jera a wardrobe tafesa turare, jirine yafara d'ibanta Dan batason Wurin guga Ga Gajiya gashi bataci komiba sai ruwa datasha, Kamar zata Fad'i da kyar ta Iso cikin falonshi ganin da datti yasa ta share ta goge Kamar yacce tayiwa toilet da bedroom turaren wuta tasa sannan tafad'i Akan sofa sakamakon Jiri daya kwasheta atake jikinta yayi zafi kanta yafara bugawa tafara jin amai amai, Idonta yafito Sosai,  Sanyi takeji bakinta yafara rawa bazata iya mikewa ba sabida zata Fad'i, jikinta ma gaba d'aya yad'au rawa tana Kwance kawai Kamar ranta zai fita,

Baby data kasa zaune takasa tsaye tin safe Yaya ya kulle Adda Fadila gashi har mangrib yayi be dawoba, jitayi Kamar tafad'awa Dady amma tana tsoron kada yayi fishi da Yaya abin ze mishi yawa, da sauri tafito jin motar Abdul yashigo gida yayi parking, d'akin momy yawuce da bak'ar Leda saida yabata yayi Mata Sannu Kafin ta juya yanufi side nashi, Baby takasa Tsayawa da sauri taje bayanshi ta Tsaya, yasan Meya kawota Hakan yasa beyi Mata magana ba, da gangan yaki dawowa da wuri saida yaje gidan abokinshi yasha fira Yayi sallan mangrib Kafin yadawo, yana bud'e kofan yashiga itama Baby tabishi abaya, "Adda ina kike?" jin shiru yasa ta nufi toilet ganin bata ciki yasa tafito a rud'e tana kiran Sunan Fadila, shikuma riganshi yacire yarage dagashi sai vest da dogon wando,  nutri milk me Sanyi ya d'auko a frij yazo yazauna Akan Sofa yabude a hankali yanasha, d'aga kafanshi Yayi zai d'aura Akan center table yaji Kamar yataka abu, kallon Wurin Yayi da sauri ta waro Ido ganin Fadila kwance tana rawar Sanyi, da sauri ya sauko Akan sofan ya d'agata Sama ya d'aurata Akan three seeter Baby ganin Haka yasa ta bud'e Baki zata saki ihu Wani Kallo ya banka Mata atake tayi tsitt, Fadila bata gane kowa Rikeshi tayi sosai  taki sakinshi dama Sanyi takeji ganin Mutum yasa ta rungume taki sakinshi, shikuma ganin Haka yasa yayi shiru ya kyaleta"

Jiddah Ce

08144818849

[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸

    *K'ANWATA*

  🌸🌸🌸🌸🌸

    Na

Jiddah S Mapi

*Chapter 48*

         ~Ajiyar zuciya take sakewa ajikinshi ganin Haka yasa ya rungumeta yana kallon fuskarta Baby sai raba Ido take, a hankali taja kafarta ta Iso Wurin Hannu tasa tana Kokarin d'ago Fadila be kalletaba yace "bakya ganin tana Kwance a jikinane?"

Shiru tayi batace komiba Dan haushi Yake bata sosai, "d'aukomin first aid box a bedroom"

Turo Baki tayi taje ta d'auko, d'an janye Fadila yayi a jikinshi yad'an tab'a wuyarta yaji zafi, da sauri ya d'auke hanunshi, Baby tace "Zafi Ko?"

Ko kallonta beyi ba yafara duba Fadila saida yagama dubata ya d'auko magani yace "oya shanye"

Yatsina fuska tayi alamar bataso "bud'e bakinki" yafad'a a tsawace, da kyar ta rufe Ido ta bud'e Bakin ya watsa Mata maganin saida ta k'ank'ameshi Kafin ta had'iye, slim ta Konta awurin Sai bacci, so yake ya janye jikinshi amma taki sakinshi shiru ya zauna da ita, ganin Baby ta Tsaya akansu ta Kura musu Ido yace "Ki zauna Ko Ki fita"

Zama tayi tana kallon Fadila har Idonta ya cika da hawaye.

saida Fadila tayi bacci sosai Kafin ta farfad'o tana kallon d'akin da Baby da Abdul, cikin disashiyar murya tace "Baby Ina d'an kwali na?"

Kallon gefen Abdul baby tayi tace "gashi can"

Hannu Fadila tasa zata d'auka Abdul yayi sauri ya d'auke had'e gira Yayi yafara d'aura Mata, yana gamawa yace "tashi Ku fitamin a d'aki"

Kamar Jira suke dama sukayi wuf har suna rige rigen fita "Ku dakata" cak suka Tsaya ba wacce ta juyo yace "idan kuka fad'awa Dady abinda yafaru saina b'ata muku rai, kuna jina?"

Eh suka fad'a a take Tareda fita a d'akin.

        "Banji Dadin Koran Abba da'akayi a Wurin Aiki ba, to tayaya zai kula damu musamman Nida nake d'auke da juna biyu, Tabbas akwai Matsala gobe da Kaina zanje Nayi Binciken Meyasa suka koreshi Nasan Abba akwai zuciya kuma Nasan bazaiyi abinda babu Kyau ba, dole akwai dalili"

Mama ce ta turo kofar tana kallonta cikin sanyin Jiki ta karaso bakin gado ta zauna,  tacewa Amrah "zauna"

Zama Amrah tayi tana murza yatsun hannunta, kallonta Mama tayi tace "Amrah Ki fad'amin gaskiyar abinda ya had'aki da mijinki harya sakeki Dan Naga alamar Rashin gaskiya a tare dake, kinsan ta Yaya nagane?

Idan Mutum yana yawan lab'ewa yaji abinda ake fad'a to bashida gaskiya, sau uku Ina ganinki kina labewa kiji abinda muke fad'a da mahaifinki to yau Inason sanin gaskiya"

Zuciyar Amrah ne yafara Lugude tarasa Wani Karya zata had'a Yanzu tafad'awa mama, kawai tafara kuka, mama tace "ba kuka nace kiminba gsky nace kifad'amin"

Cikin sheshekar kuka tace "Mama zargina Yake wai Inabin maza kuma na rantse da Allah ban tab'a zina ba Tinda nake, Kema kinsan tarbiyyar da kika bamu Nida Adda Fadila"

Shiru Mama tayi Kafin Daga bisani tace "to Meyasa yayi zarginki yaganki da namiji ne Ko meyafaru"

Mama Wlh be Ganni da kowa ba, mama Kema kinsan halina"

Cikin Tsawa Mama tace "sanin halinkine yasa nake tambayarki, Fadila tafiki hakuri da biyayya, Ke Bana yadda dake kwata kwata Amrah, tin lokacin da Fadila take nan naga alamar kina rufa rufa idan kinyi laifi sai kisata tace itace, kina cutar da ita da hakurinta, Nasan Tabbas kinsan wani abu daya Shafi b'atan Fadila ranar Aurenta, musamman yanda naga jikinki yana rawa Akan Kamal, Amrah nicefa na haifeki ba kece kika haifeni ba, tun kuna yara Nasan abinda zaku iya Nasan wanda Bazaku iyaba, da Fadila ce kika b'ata ranar aurenki Wlh babu Ko shakka data suma yakai sau biyar, da har Yanzu bamu gane kanta ba,  Amma narasa Dalili Kullum idan na kwanta sai Nayi wannan tunanin Nayi niyan nabari sai Kin haihu Kafin muyi magana gudun kada kisa damuwa a ranki amma Ki gafarceni nakasa hakura abin yana cimin rai ashiga hakkin Mutum me hakuri Kamar Fadila, ban saniba Ko akwai Wani b'oyayyen Gaba tsakaninki da Yayarki, Don ba tare daku nake kwana ba kuma batare muke yawo ba, amma a yanda nasani babu Gaba tsakanin Yaya da K'anwa wacce suka fito ciki d'aya"

Sulalewa mama tayi daga kan gadon ya durkusa kasa gaban Fadila tace "Dan Allah Ko Sanar dani gaskiya a matsayina na mahaifiyarki na durkusa kan gwiwana Ina rokanki Kitaimaka kifad'amin gaskiya"

Zufane yafara zubowa daga kwantaccen Gashin Amrah zuwa wuyarta da goshinta, sai Rawa jikinta da bakinta suke ganin Mama durkushe a gabanta ba karamin Tashin hankali ya sataba, itama kasa ta durkusa tafara Kokarin d'ago mama cikin rawan murya tace "Dan...dan Allah mama kitaimakeni Ki Mike Dan Allah Ko rufamin asiri kada kisa mala'ku su tsinemin Ki Mike mama Dan Allah"

Mama cikin kuka tace "Bazan mikeba saikin fad'amin gaskiya Amrah zuciyata zata fashe 'yata aka salwantar wa duniya bansan Halinda take ciki ba bansan Awani duniyar takeba, ban San Ko tana halin nagari ba Ko nabanza"

Amrah juyawa tafara tana kallon Kofa batason mutane sushigo su gansu Ahaka, "Wlh Mama zan gaya miki gaskiya amma saikin mike"

Mama tace "kinyi alkawari"

Gid'a Kai tayi tana kuka, mama tace "magana nakeso kiyimin Amrah"

Amrah da kyar ta bud'i Baki tace "eh"

A hankali Mama ta Mike ta zauna bakin gado sannan tace "Ina jinki"

Ganin Haka Amrah taja numfashi taki Sakewa, a hankali Tafara yin kasa zata Fad'i da sauri mama ta tareta tana Kiran sunanta, a sume tafad'i jikin mama Idonta yakafe yana kallon Sama, ihu mama tayi tace "na hakura Wallahi Bazan kuma tambayarki ba, na tuba Ki Mike Dan Allah idan bakida laifi Shikenan Nayi hakane Dan nagano Ko kinada laifi Ko Baki dashi, Ki tashi Dan Allah kada Nayi biyu babu"

Bud'e labule Abba Yayi yana kallon Mama Wani iri "Kin huta Ai Ko?"

Riko Amrah yayi yafara tafiya da ita Mama da sauri tariketa ta gefe Abba yace "kyaleta kada Ki tab'ata kije kirike Fadila amma ba Amrah ba, idan kinaso ma zamu raba yaran Ke kibi Fadila ni zan kara aure narike Amrah"

Yana fad'an Haka yawuce Falo da Amrah ya kwantar da ita Akan carpet sannan yaje ya dibo ruwa yazo ya shafa Mata a fuska, ajiyar zuciya tasaki a hankali ta bud'e Idonta tana kallon Abba cikin sanyin Jiki tace "Abba Ina Mama? Tace Nafad'a Mata gaskiya, Nikuma zan fad'a Mata iya abinda nasani"

Shafa kanta Abba Yayi yace "Kiyi shiru Ki kwanta kinji? Idan kika fad'awa Mamanki abinda Yake faruwa ban yafeba domin Nasan Tabbas idan ya takuraki zakiyi Karya Ki kwanta Ki huta kinji? "

Wani ajiyar zuciya ta Sauke a b'oye Kafin ta Kalli mama da gefen Ido tace "to Abba"

Rufe Idonta tayi tafara bacci hankali kwance.

    

*bayan Kwana biyu*

     Yau Yakama Alhamis gobe Jumma'a Yakuma d'aurin Auren Abdul da Fadila idan Allah ya Kaimu, 'yan uwan momy ne acikin gidan sunata Aiki yayinda wasu sunata cin abinci Dady da Abdul ne suka fito Daga mota hannun Abdul rikeda Wani Leda fari, cikin gida suka Nufa suna gaisawa da kowa, Sai neman tsokanan Abdul ake ago kasha kamshi, daurewa kawai yake yana d'an murmushi shi kad'ai yasan abinda Yake damun zuciyarshi, daidai kofan Dady wata Mata take zaune Tanacin jellof rice Ko sanin su Dady sunzo batayi ba, ta zauna d'ai d'ai tana sakin loma saida Abdul yad'an bubbugata cikin tsokana yace "Hajiya abamu hanya"

'D'ago Kai tayi takalli Dady da sauri tafara gyara zamanta tace "Sannu da dawowa Alhaji "

Dady yace "Yawwa"

Kafin suka gaisa suka wuce, acikin falo Dady yakalli Abdul yace "wannan uwarsu d'aya ubansu d'aya da Momynku gashi ta zauna sai cin abinci take Kamar na gobe, sai fitsara da Rashin Kunya Kamar 'ya'yan wasu, da Anyi magana suce anayi musu gori narasa da irin zuri'arsu Wallahi"

Abin yabaiwa Abdul Dariya amma ta dake yakiyi Dan kada dady ya zageshi, saida yafita Kafin yadara.

08144818849

[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸

    *K'ANWATA*

  🌸🌸🌸🌸🌸

    Na

Jiddah S Mapi

*Chapter 49*

         ~yana cikin Dariya Fadila tabiyo Baby da gudu Danta cinye Mata chocolate Nata, Baby tana gudu tana Dariya ita kuma Fadila sai Haki take Dan dama akwai ragonta batason wahala Ko kad'an, Baby ganin Fadila zata kamata yasa tayi hanyar d'akin Dady mutane sai kallonsu suke ba Wanda ya kulasu sai momy datake had'e rai wai ace wannan wawiyar ce zata zama surikarta? "God forbid"

Dab kofar Dady sukayi Karo da Abdul d'ago Kai dazasuyi sukayi Ido hud'u Ai atake suka juya aguje suna rige rigen Barin sashin, Abdul kallonsu Yake Dan shi dariyama suka bashi musamman yanda Fadila take ture Baby to wai me hakan? Yanzu wannan wawayen zan zauna dasu gida d'aya ba babban ba ba karamar ba duk wauta yaci kansu mtswww yaja Wani tsaki Naban haushi Kafin yajuya yatafi d'akinshi Kwanciya yayi Akan gado yace "Nasan Yanzu kinyi wayo princess Allah ya karemin Ke aduk Inda kike"

Hawaye ya goge tareda kifa kanshi jikin filo yana tunanin rayuwarshi.

Fadila da Baby atare suka shiga d'aki Tareda sa sakata suna sakin nishi, cikin Gajiya Baby tace "daya rike d'aya acikinmu dayau tayi bayani kutt"

Fadila tace Saide ya rikeki amma baniba Wallahi Nifa Bazan tsiya yana cin zalina ba ehe"

Dariya Baby tayi Harda Rik'e ciki tace "shiyasa naga rannan yasaki Wanki kuma kinyi, sannan yau naga Kin tureni Kin gudu"

Dundum Fadila ta sakarwa Baby abaya, baby tace "wash Allah ya isa"

Saida suka gama yarintarsu Kafin kowa yasamu wuri ya zauna, Baby ce takalli Fadila tace "Adda Fadila na"

Fadila tace "Na'am Baby na"

Baby tace "Kinsan Ina sonki sosai da sosai idan kunyi Aure da yayana kada Kice mishi Babyna ni kad'ai nakeso Ki kirani da Baby na kinji"

Fadila a zuciyarta tace "Dama ba sona yakeba niba ba sanshi nakeba biyayya zamuyi inani Ina kiranshi da Baby?" amma a fili tace "hmmm kinsan nafara sanshi Wlh Babyna zance mishi Ke Ai kinamin raini"

Cikin jin Dadi Baby tace "da Gaske Kin fara sonshi?"

Fadila datake ninke kayanta tace "yes Ai duk gidannan Ina sonku sabida Kun min halacci Allah dai yabiyaku, shikuma Yaya Abdul yatab'a karb'amin fad'a a school Kin manta? "

Baby tace "oh yes Kice tun lokacin kika fad'a soyayya da yayana"

Harara Fadila ta sakar Mata,  kofarsu akayi knocking cikin Tsoro Fadila tace "waye"

"ubanki ne" sukaji muryar wata, zaro ido Fadila tayi tace "Baby tashi Ki bud'e"

A hankali Baby ta Leka Kafin ta bud'e da gudu tayi rungume yarinyar datake tsaye, sai kuma wata datake Bayanta tana yauki tana taunar cingum, "kushigo My Girl"

Shigowa sukayi wacce tayi Zagin tace "har kina tambayana waye Baki gane Muryana bane Kome? "

Rungumeta Baby tayi suka fad'a gado tace "Haba my Girl rabonmu dake tun shekara uku dasuka wucefa Ai dole muryanki yad'an b'atamin"

Marinta tayi a kumatu tana Dariya, Baby tace "Ya London? Dafatan karatu yana shiga Ko? "

Yarinyar tace "Aa gaskiya soyayya yafi shiga nifa kinsan Dady ne ya takurani Nayi karatun amma nafison Aure"

Baby tace "Shegiya har Yanzu Baki daina iskancin ba"

Dariya sukayi suka kara tafawa, Baby ce tajuya takalli d'ayan tace "Sannu da zuwa Unty Nabila"

Cikin yanga da yauki Kamar me ciwon Baki tace "Yawwa Baby"

D'auke Kai Baby tayi taci Gaba da hira da Yarinyar me fara'a Dason Dariya, Fadila ce tafito daga toilet tana lekawa Dan gudu tayi tana tsoron kada momy ce tayi Zagin, ganin 'yammata guda biyu yasa ta saki Jiki tace "Sannunku da zuwa"

Cikin Sakin fuska karamar tace "yawwa Ko ba'a fad'aba Nasan wannan ce Untyn Tamu amma gaskiya ta had'u sosai Yaya Abdul Yayi sa'an mace wallahi"

Fadila kawar da kanta tayi tanad'an murmushi takalli Babban tace "Sannu da zuwa"

Wani banzan Kallo yarinyar ta watsa Mata bata amsa ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login