Showing 90001 words to 93000 words out of 139192 words
aka kirani matata batada lafiya kuma an kira doctor ɗin dazatayi mata aiki amma doctor tace bazata samu fitowa ba saita basu wata number wai na kanwarta ce,to ita kuma kanwar da aka kirata tace gaskiya kanta yana ciwo shiyasa raina ya ɓaci sosai Emergency ne kuma suke irin haka, kiyi hakuri da tsawan danayi miki"
Amrah da jikinta yayi sanyi tace "gaskiya wannan doctorn anyi mara imani wannan wani irin rashin imani ne? Amma ba musulma bace ko?"
Mutumin yace "musulma ce wallahi kawai de sabon buɗewa ne asibitin"
Amrah tace "to Allah ya shirya ya maida mata aniyarta Allah kuma ya baiwa matarka lafiya"
"Amin dan Allah bani number ɗinki idan ba matsala"
Amrah tace "banida waya gaskiya"
Kallonta yayi yace "to ina gidanku?"
Kwatance tayi mishi sannan yace ya gode da haka suka rabu, Amrah a zuciyarta taji jnama ace ita takai matar asibiti da babu abinda ze hanata zuwa gidan likitan taci mata mutunci, da wannan tunanin harta iso gida, Mama dake zaune tana baiwa Abba kunu tace "lafiya kika dawo da wuri yau?"
Amrah tace "Mama kaina keɗan ciwo shiyasa"
Mama tace "sannu jeki ki kwanta"
Amrah tace "to ya jikin Abba?"
Mama tace "gashi dai da sauki"
Amrah shiru tayi sai idanunta daya cika da hawaye tawuce ɗaki.
_Jiddah Ce_
[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸
*ƘANWATA*
🌸🌸🌸🌸🌸
Na
Jiddah S Mapi
*Chapter 60*
~Akwana atashi jikin Abba sai gaba yake cikin Amrah ko sai girma yake, yau yakama Alhamis Amrah tayi shirin zuwa bakin hanya wurin kuluwa amma sam jikinta yaki sakinta sai faɗuwar gaba takeji sosai, da kyar dai ta lallaɓa ta tafi tareda yiwa Mama sallama, kuluwa da ganinta tace "lafiya kuwa Amrah?" Amrah giɗa mata kai kawai tayi, dahaka har suka gama tuya suka koma gida, sallan Mangrib sukayi gaba ɗayansu suka zauna akan tabarma sunacin abincin dare, karan tsayuwar mota sukaji wanda yasa amrah taji kirjinta kamar an ɗaura mata katuwar karfe, babu sallama sukaga mata da wani a gefenta, Waro ido Amrah tayi ta dafe kirji tareda sakin salati ganin Umman Kamal da Kuma Kamal wanda ya lalace ya kanjame ya fita a hayyacinshi, da gudu ta karasa wurinsu ta zube a kasa tana rokansu kada su tona mata asiri, Umman Kamal ce ta bugeta gefe cikin tsawa ta nunata da yatsa tace "zan koya miki hankali idan kika kara taɓa jikina ko kuma na ɗana"
Amrah rike kafarta tayi tana rokanta, janye kafarta tayi da karfi, Mama ce ta fito daga ɗaki itada Abba zata kaishi toilet, ganin ana hayaniya yasa ta karasa tana tambayar meyake faruwa?
Umman Kamal ta nuna Amrah da yatsa tace "wannan zaki tambaya meyake faruwa bani ba, nayi dana sanin haɗa zuri'a daku wallahi, ku duba kuga yanda Kamal ya lalace sabida soyayya, wallahi bazan yafe muku ba har sai kun nemo mishi Fadila kun Aura mishi"
Mama cikin ɓacin rai tace "mune dai mukayi dana sanin haɗa zuri'a daku, sannan kidaina aibatamin yarinya Kamal kuma be fara ganin rayuwa ba tunda wulakanci ne aikinshi, kuma kin taɓa ganin inda aka auri Kanwa sannan a auri yaya? Wannan ai kin nuna jahilcinki a fili"
Umman Kamal cikin fushi tace "akwai jahilai irinku? Kunsan addini kuma kuka take sani ai gwara nida bansan addini ba balle na take sani"
Abba ganin bazasuyi shiru ba yasa a hankali yace "ki kyalesu su zauna"
Umman Kamal tace "banga wurin zama ba a gidannan wannan bolar zan zauna ko wancan karamar karfen?"
Kamal kam yana gefe sai sharan kwalla yake harda jan hanci, idanunshi sun rine sunyi jaa, ya rame sosai soyayyar Fadila ne yake mugun azalzalar rayuwarshi, Umma da rnata ya ɓaci sosai tasa hannu taja kunnen Kamal sannan ta ranƙwashi kanshi tace "kaima kamar maye, nafaɗa maka kafita a harkar ƴan gidannan kaki jina zakaji dashi"
Abba ne ya karaso wurin da tafiyarshi na mara lafiya ya riko hannun kamal ya zaunar dashi a bakin kofar ɗaki yace "ɗana ka faɗamin abinda yafaru kuma dan Allah kada kayimin karya kaji?"
Kamal kallon Amrah yayi wacce take faman ɗaga mishi hannu sama alamar ya taimaka ya rufa mata asiri fuskarta duk hawaye, ganin zai faɗi gaskiya yasa taɗan ɗaga mishi riganta cikinta daya girma kaɗan ya bayyana tayi mishi alama da ya taimaka mata albarkacin cikin jikinta, Kamal sunnar da kai yayi kasa idan be faɗi gaskiya ba zasu ɗauka mahaifiyarshi makaryaciya ce to amma idan yafaɗi gaskiya wannan yarinyar tana cikin tashin hankali ta fice a kammaninta,
Abba yace "dan darajan manzon Allah (S A W) kafaɗan gaskiya"
Kamal jin haka yasa yafara kuka yana irgawa Abba abinda yafaru tun daga ranar haɗuwarshi da Fadila har ranar rabuwarsu, kuka ne yaci karfinshi lokacin dayazo wurinda suka kori Fadila da Unty Sadiya, Mama cikin Kuka da ihu tayi tsalle ta damƙo Amrah wacce ta durkusa a wurin kamar bata motsi, wani itace ta ɗauka tafara maka mata kota ina, Kamal ganin Amrah zata Hallaka yasa ya mike zeji ya kwatota Ummanshi ta rike hannunshi cak ya tsaya, "idan kasa hannunka ajikin wannan yarinyar Allah ya isa"
Kallon Umma yayi sosai yanaji yana gani Mama takusan sumar da Amrah, Kuluwa da baso tasa baki a maganar tayi sauri taje tana kwatan Amrah amma Mama tayi mata mugun riƙo, dukan datakeyi mata kamar bata hayyacinta, Kuluwa ganin za'ayi kisan kai yasa tafara ihu tana kiran makota, Umma. kamal ce tayi wurin kofa tasa sakata yacce babu me iya shigowa gidan, Kuluwa wurin Abba tayi da gudu tana cewa "kana ganin za'ayi kisan kai bazakayi magana ba?"
Ganin yayi shiru yasa ta girgizashi tana cewa "Abba!!! Abba!!!"
Ɗan tureshi tayi taga ya faɗi kasa warwas kamar babu rai, wani uban ihu takuma kurmawa tace "Abba ya mutu"
Kamal da sauri ya kwace hannunshi yayi kan Abba, Umma tace "idan ka taɓashi zan ɗaga maka nono"
Cak ya tsaya yana kallon yanda idon Abba ya kafe, Mama saida taga Amrah ta daina numfashi kafin tashiga ɗaki ta ɗauko hijabinta jikinta duk yana rawa ta nufi wurin Abba ta yayyafa mishi ruwa a hankali ya buɗe idonshi, Umman kamal ce ta janye hannun Kamal suka fita a gidan, Kuluwa kuwa ta ɗibo ruwa ta watsawa Amrah amma shiru bata mike ba, ganin haka yasa tafara ku, takara sa mata ruwa har yanzu shiru, Bokiti ta ciko da ruwa ta juye mata ajikinta kafin tasaki ajiyar zuciya a hankali tafara buɗe idonta tana sakin numfashi da kyar, Mama ganin haka tayi wani kukan kura ta ɗauko icen takara zabga mata, ta ko ina take dukanta har saida Amrah takara wani dogon suma, kuluwa sai ihu take tana cewa "Allah na tuba"
Abba sai kallonsu yake amma babu bakin Magana, Ganin haka yasa Mama tanufi waje takira me adaidaita tazo ta duki kuɗi a ɗakinta tariko Abba suka nufi general Hospital, Kuluwa tayita zubawa Amrah ruwa amma taki farkawa sai addu'a take Allah yasa ba mutuwa Amrah tayiba, janta tafara daga varanda zuwa ɗaki da kyar take janta jikin Amrah sai ciwo yakeji sakamakon duwatsun cikin gidan ita kuma Kuluwa bazata iya ɗagata ba tayi mata nauyi, Da kyar dai takaita ɗaki ta kwantar da ita akan tabarma tareda sa mata filo, sannan taɗau mahuci tarinka fifita ta.
"A hankali take juye abincin cikin flask tarasa meyasa tun safe gabanta yake faɗuwa duk abinda taɗaga sai taji jikinta ya mutu, zuciyarta ta tsinke kirjinta ya buga sosai, yau kwata kwata tanayin abu kamar mara lafiya, Abdul yadawo daga wurin aiki yau da wuri kasancewar yau friday ne, yana lura da yanayin Fadila sosai amma yarasa ta ina zai fara tambayarta, harga Allah bazai iya sharing na damuwarshi dawata ba, amma dolene ita tayi sharing na damuwarta dashi sabida ita matarshi ce, Tashi yayi a hankali ya nufi kitchen ɗin yana tunawa da maganar Kabir, Fadila bataji shigowarshi ba taji an rungumeta ta baya, ihu taso ta kurma yasa hannu ya toshe bakinta da sanyin muryarshi yace "ke nine fa"
Shiru tayi ta tsaya da aikin datake, gashin kanta ya maida baya a hankali yasa kanshi daidai wuyarta ya zagaye hannunshi a cikinta, yana shafawa a hankali yana shakan kamshin dayake fita a gashinta, Ganin takasa yin aikin yasa yariko hannunta yafara wanke plate ɗin, Fadila shiru tayi dan takasa yin komai, cikin sanyin murya yace "meyake damunki? tun safe naganki cikin damuwa"
Fadila tace "kaima baka faɗamin damuwarka nima ba dolene nafaɗa maka tawa ba"
Da karfi ya rungumeta saida tayi kara kaɗan kafin yaɗan saketa yace "damuwata bata shafeki ba ni kaɗai tashafa kuma idan nafaɗa miki bazaki iya bacci ba"
Fadila tace "nima hakane, amma zan baka girmanka na mijina, tin safe kirjina sai bugawa yake har yanzu bansan dalili ba"
Ba zato ba tsammani taji ya ɗaura hannunshi a kirjinta da sauri tafara kokarin kwatan kanta amma ko gizau beyi ba, yace "Nan ne yake bugawa?"
Fadila idonta yacika da hawaye tace "please ka sakeni"
"La haula wala kuwwata illa billah, ki rinka karantawa kinji?"
Sakinta yayi yafice daga kitchen ɗin, tsaki taja taci gaba da aikinta, tana gamawa takira Baby sukasha fira, ganin har yanzu bata daina ji ba, yasa tafara karanta "lahaula wala kuwwata illa billa"
A hankali taji nutsuwa yana sakko mata, rufe idanunta tayi tana ɗan tunani har bacci ya saceta.
Washe gari yakama Saturday babu zuwa aiki Fadila ce takira Baby tace dan Allah tazo su ini, da kyar Baby ta yadda akan zatazo da karfe 10, Da karfe goma ko saiga Baby da murna da tsalle Fadila ta rungumeta, "Baby yanaga kin rame?"
Baby shiru tayi batace komai ba, Fadila ganin tayi shiru yasa tagane akwai matsala, riko hannunta tayi ta zaunar da ita akan Sofa, tashi tayi taje ta ɗauko juice da Cup, zama tayi a hannun kujerar da Baby take, gyallen datayi rolling Fadila ta zame mata tace "Baby na ga wannan kisha"
Baby da idonta yacika da hawaye ta sunnar da kai tana wasa da yatsunta, Fadila ɗan murmushin gefen baki tayi ta tsiyaya juice ɗin a glass cup ɗin, sannan ta ɗago kan Baby tafara bata, Baby a lokacin hawaye suka fara sakko mata, tabbas tayi saurin cewa Dady Fadila suna soyayya da Abdul gashi tashiga tsakanin Fadila Da Kabir to amma yaya zatayi? Son Kabir ne ya ɗarsu a zuciyarta, gashi Fadila tana sonta sosai kamar ciki ɗaya suka fito,
Fadila ganin Haka yasa ta ajiye Cup ɗin ta rungomo Baby a jikinta tana shafa bayanta cikin sigan lallashi tace "Sorry kiyi shiru"
Baby shiru tayi batace komai ba,
Abdul ne yafito da brush a hannunshi zeji kitchen ko me ze ɗauka ne oho, Da Mamaki yake kallo. baby da Fadila yanda take lallashinta kamar wata karamar yarinya, "mtswwwww" yaja wani dogon tsaki "yarannan wawayene wallahi"
Hanyar kitchen ya nufa yakara fitowa yawuce ɗakinshi,
Baby ɗago kai tayi tace "ki yafeni Adda Fadila..."
Fadila rufe mata baki tayi da hannu tace "kada kidamu bakiyimin komai ba, muna zaman lafiya da Abdul saide abinda ban fahimta ba shine, yana yawan zama cikin damuwa sannan yana yawan kuka a keɓantaccen wuri nakasa gane meyake damunshi"
Baby ta share hawayenta tace "tabbas Dady yasha tambayarshi amma sai yace ba komai wannan yariga yazama jinin jikinshi"
Fadila tace "to Allah ya kyauta, yanzu dai tashi mushiga bedroom ɗina kiga wani abinda nasiya"
Da sauri Baby tamike tace "muje"
Zuwa bedroom sukayi Fadila tace "rufe idonki"
Baby rufe idonta tayi, Fadila ta ɗauko wani babban Jaka pink color ta buɗe sannan taciro wani gadon yara me kyaun gaske tace "buɗe"
Baby Buɗe ido tayi tace "wow Adda gadon yara"
Fadila signal tayi mata tace "Nafara tara kayan yara sabida ina mugun son yara a rayuwata, kjma koda badan haka ba inada burin ganin ɗan uwana na kusa dani kinga kuwa dole saina haihu kafin naji daɗi a raina, Baby akwai ciwon da har yau yakasa yin sauki acikin zuciyata, Baby wallahi inaso yaro kodan ya maye min gurbin ƴan uwa dana rasa"
Baby kallonta tayi tabata tausayi sosai, tace "Adda Fadila kodai yaya yayi ajiya ne?"
Fadila rufe fuska tayi tace "Aa wallahi amma vary soon"
Baby tace "uhmm nima zan tqyaki tara kayan yara"
Rungumarta Fadila tayi tace "you are the best Sister in the world"
Baby tace "gaskiya kinason yara jibi yanda kike murna"
Fadila dariya tayi tafara cire kayan cikin jakan masu kyau, suka gama kallo ta mayar cikin wardrobe sannan ta dawo suka cigaba da hira.
_Jiddah Ce...✍️_
[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸
*ƘANWATA*
🌸🌸🌸🌸🌸
Na
Jiddah S Mapi
*Chapter 61*
~Amrah kwana tayi batasan wayake kanta ba, Idonta a rufe amma zuciyarta a buɗe tana tsoron buɗe idonta dan batasan wani tashin hankali zata gani ba, Kuluwa ce taketa zirga zirga itama tarasa tayi tsoronta kada Amrah ta mutu, "wannan wani irin rayuwa ne?"
Ruwa takuma ɗebowa a bokiti tazo ta kwararawa Amrah sakin ajiyan zuciya tayi me karfi ta buɗe idonta dasukayi nauyi suka kumbura, gefen ɗayan idon har yayi jaa, Rungumeta Kulu tayi tace "Alhamdulillah"
Amrah ɗaga hannunta tayi itama zata rungumeta taji hannunta kamar an zare jijiya tsabar azaba, Ihu ta kurma tana kallon hannunta dan son tabbatar da ko yana jikinta ko kuma babu, ganin yana jikinta yasa ta saki kuka tana kiran "Umma"
Kuluwa tace "sun tafi asibiti"
Zaro ido Amrah tayi tace "Waye ba lafiyan?"
Kulu tace "Abba ne dan ya suma kuma bansan asibitin da sukaje ba"
Amrah sai a lokacin tafara tuno abinda yafaru, kuka tafashe dashi sosai, Kuluwa tace "Amrah na ɗaukeki a matsayin kanwa, inaso kema ki ɗaukeni a matsayin yaya ki faɗamin Gaskiyan abinda yafaru"
Amrah cikin kuka tace "duk abinda Kamal yafaɗa gaskiya ne Baba Kulu saide maganar bin maza wallahi ba halina bane na rantse miki da Allah"
Kuluwa numfashi ta sauke da karfi kafin tace "tabbas kin zalinci yayarki a halin yanzu kuma bakisan inda take ba balle ki roki afuwa a wurinta"
Tureta Amrah tayi tace "koda tazo gidannan yau wallahi bazan nemi afuwa a wurinta ba"
Kuluwa tace "sabida me?"
Amrah tace "na barwa zuciyata wannan amsan"
Kuluwa shiru tayi bata ce komai ba, Amrah kwanciya tayi akan gadon ta rufa kanta da bargo tana tunanin dawani ido zata kalli Mama da Abba? Tashi tayi kamar an mintsineta tayi hanyar waje, Kuluwa tana tambaya ina zaki? Amrah shiru tayi ta nufi ɗakinsu, kayanta ta kwashe acikin wata babbar akwatinta tasa komai datake bukata, wani asusu ta ɗauko na katako ta fasashi tafara kwashe kuɗin datake tarawa akan idan ta haihu zata siyawa Baby kayan bukata dashi, hawaye ta share kafin ta irga ba yawa amma tasan zasu biya mata bukatarta, jan kayan tayi zuwa waje, Kuluwa tana ganinta ta zabga ihu tace "ina zaki Amrah?"
Amrah tace "tafiya zanyi bazan iya haɗa ido da Abba ba"
Da gudu Kuluwa taje taja akwatin zata komar ɗaki, Amrah da jikinta ba kwari tayi sauri tarike tana ɗan lumshe ido alamar tanajin jiki, Kuluwa tace "kibi a hankali kinada ciki zaki iya kama low Bp"
Amrah jan akwatin take, sukaji sallama, Mama ce rikeda Abba suna tafiya a hankali da alama abba yanajin jiki sosai dan yanda sukaga Mama acikin ɓacin rai, Kuluwa sakin akwatin tayi tace "Mama sannunku dai ya jikin nashi?"
Mama tace "Da sauki mun gode Allah"
Kulu tace "dama Amrah ce wai zata tafi tin ɗazu nake hanata taki hanuwa"
Mama tace "to Allah ya kiyaye hanya"
Amrah data kasa ɗago kanta tayi shiru tana sauraron su, tsoronta kada mama takarayi mata irin dukar mutuwar datayi mata jiya, Sakin hannun Amrah kulu tayi, Amrah naganin haka taja akwatin tayi hanyar waje, Abba yace "idan kika fita nanda bakin kofa Allah ya tsine miki albarka"
Jiri ne yafara ɗiban Amrah jin abinda mahaifinta yafaɗa akanta, Tunda take da iyayenta basu taɓa ambatar kalmar tsinuwa akanta ba sai yanzu, faɗuwa zatayi Kulu ta rikota tace "Mama kudaina haka tanada ciki fa, damuwan zaiyi mata yawa idan tazo haihuwa zai kawo mata matsala"
Mama tace "to ta mutu mana saime? Akanta aka fara mutuwa? Ko akanta za'a kare mutuwa?"
Shiru tayi Mama tawuce da Abba ɗaki ta kwantar dashi akan gado, itama Kulu tawuce da Amrah ɗaki ta kwantar da ita akan gado.
"Yaya Abdul nasan baka sona kuma nima ba sonka nakeba, amma dan Allah kabari aurenmu yayi koda wata biyar ne kafin kayi wani auren"
Cewar Fadila data dukar da kai kasa tana kuka, ba kukan Auren da zaiyi take ba, Aa kukan Kada matar tazo tanayi mata gorin rashin dangi da ƴan uwa take,
Abdul daya haɗe Fuska yace "kinsan darajar yarinyar danakeso a zuciyata kuwa? Ko ba agabanki Dady yace na aureta ba? Aurena zanyi nanda sati biyu, kuma bari nafaɗa miki idan tazo gidannan kika nuna mata wani hali saina kasheki"
Ɗago kai tayi ta kalleshi yace "i mean it" daganan ya mike yabar mata ɗakin, Fadila kifa kai tayi da jikin sofa tafara raira kuka, wannan kaddarar Amrah ce ta jawo mata, "Allah ka cireni a wannan rayuwar ya ubangiji ya ɗauki rayuwata cikin gaggawa banason wannan duniyar Allah ka ɗauki rayuwata"
Kuka take me ratsa zuciya dahaka har bacci ya ɗauketa,
Abdul yana shiga ɗaki ya kifa kanshi da jikin bango cikin damuwa da tarin hawaye a idonshi yace "Am sorry Kabir bazan iya ba wallahi bazan iya ba, inaso princess na cuci rayuwarta dole sai nine zan gyara bazan iya wannan alkawarin ba banason Fadila i can't pretend, to amma meyasa Zan karya alkawrinka?" Buga kanshi yayi da bangon yace "zanci gaba da pretending tunda wani lokacin we can pretend that we can never pretend bazan taɓa faɗawa Fadila na tsaneta ba, damuwan sunyi mini yawa ina bukatar me lallashi na"
Kamar me taɓun hankali ya buɗe kofar ya nufi ɗakin dayabar Fadila, Ganin tana bacci yasa ya ɗagata sama, buɗe idonta tayi a hankali ta zuba akanshi, "ya.." yatsarshi yasa a bakinta yace "shiiii"
Shiru