Showing 45001 words to 48000 words out of 139192 words
d'aura d'ankwali saimuje" pink na wandone ajikinta da farin Riga me yankakken hannu, tayi kyau sosai pink d'in d'ankwali ta d'aura tariko hannun Baby suka nufi Babban falo, Daddy ne zaune akan sofa sai Mommy datake gefenshi Abdul kuma yana zaune a gefen kafarsu yana aikin nashi wato danna waya, Baby ta zauna a gefe guda itakuma Fadila tsabar yanda take tsoron Mommy batasan lokacin data zauna a gefen Abdul ba, Daddy ne yace "Mamana idan Allah yakaimu gobe Abdul zaikai Fadila makarantarku zatayi karatu a can, inaso Ku bud'e kunnuwanku da kyau kijini, zan kafa muku doka me guda biyu nafarko babu kula saurayi harsai kunyi candy na biyu babu yin latti zakuyi shiri da wuri domin makaranta bayason latti, sannan zan kawo muku malami Wanda zai rinka koyar muku da karatun addini, kunsan Allah idan kuka tsallake dokata saina sab'a muku kuna jina?"
Da sauri sukace "eh Daddy" yace "ban yadda da driver yakaiku makaranta ba Abdul zai rinka squeezing na time nashi yana kaiku"
Abdul ne ya d'ago kanshi yana kallon Daddy fuskarshi a had'e, Daddy yace "eh ko bazakayi bane?"
Sunnar da kai yayi baice komai ba amma alamu sun nuna bayaso, Mommy Sai hararan Fadila take dasun had'a Ido sai Fadila taji dum a kirjinta, Daddy yaciro kud'i me yawa yamikawa Baby yace "anjima kuje kuyi shopping naduk abinda kuke bukata banda rawan kai kunajina?"
Fadila sukace "Eh" dahaka taro ya watse, Mommy ce tariko hannun Baby wacce take shirin bin Fadila janta tayi zuwa d'aki ta zaunar da ita akan gado itama ta zauna a gefenta fuskarta da alamar tanaso suyi maganar gaskiya ta kalli Baby tace "Babyn Yaya shin bakiga yanda d'an uwanki ya sauya bane? Bakya ganin yana cikin damuwa ne? Meyasa bakya kula dashi Bacin kinsan yana bukatar taimakon naki? Meyasa kika zab'i wancan yarinyar akan yayanki? naga sai wani rawan jiki kike da ita kinsan mutanen yanzu ba'a yadda dasu zakayi musu inuwa sukuma zasu kaika rana, kibar ganin tanayi miki kalar tausayi idan ta falle ta waye saikinyi kuka da kanki, ki saki hanyar yarinyarnan ki kulada yayanki d'an uwanki, kinajina?"
Baby tace "haba mommy wani irin magana kikeyi ne? Itafa Adda Fadila tana bukatar taimakona sabida nima ta taimaka min, kuma gaskiya bazan iya barin ta...." Kafin takarasa maganar mommy ta buge mata baki da karfi, ihu tayi tana tab'a bakinta ko yayi jini, mommy tace "banaso ina dukanki amma wannan maganar taki yazama dole ayi miki hukunci, meyasa zaki fifita bare akan d'an uwanki? Abdul fa yayanki ne ni kaina ina tausaya mishi akan irin halin dayake ciki nalura ko abinci baya yawanci"
Baby cikin kuka tace "to ai dama shibaya yawan cin abinci"
Mommy taja numfashi tace "hmmm nalura har yanzu ke yarinyace bazaki fahimci halinda yake ciki ba, tashi kibani wuri kafin inyi ferfesunki yanzun nan, Dan naga alamar raina kawai zaki b'ata"
Da gudu Baby tafice Dan tasan halin Mommy, tana fita sukaci karoda Abdul yanason shiga d'akin yaji duk maganar dasukayi, kallonta yayi sau d'aya ya watsar zai Shiva d'akin tayi sauri ta rikoshi ta baya, shiru yayi bai jiyo ba, tace "Yaya Adda Fadila tana bukatar taimakona banyi maganar da manufa ba, nasan kana cikin damuwa Amma Adda Fadila tafika damuwa kayi hakuri na zab'i na kula da ita akan nakula dakai, Amma kasani kana zuciyata domin komai d'an uwanka yayi maka dolene kaji sonshi a zuciyarka d'an uwa ba wasa ba" tana fad'an haka ta sakeshi tabar wurin, Abdul yayi mamakin yanda tace zata kula da wata bashiba ita wannan Fadilar me tayiwa Baby ne?" Da tunanin yashige d'akin Mommy, yana Shiga ya hango Mommy zaune ta zabga tagumi, karasawa yayi ya kwantar da kanshi akan cinyarta, mom murmushi tayi mishi, a hankali ya rungume kafarta ya lumshe ido, mom shafa kanshi take a hankali har bacci yayi awon gaba dashi.
08144818849[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸
  *ƘANWATA*
🌸🌸🌸🌸🌸
Na
Jiddah S Mapi
*Chapter 32*
    ~washe gari Yakama Monday Fadila tunda tayi sallar Asuba tashirya cikin bakin Riga abaya da mayafinshi baki, batayi kwalliyaba lip balm kawai tashafa a bakinta tayi kyau sosai, Baby bacci take kamar bazata farka ba, duka Fadila ta nad'a mata s firgice ta mike tana mitsika ido ganin Fadila tashirya yasata dira akan gadon tashige toilet da gudu Dan tayi zaton sunyi latti, saida tafito ta duba agogo taga karfe shida tsaki taja tace "haba adda Fadila nazata 8:30 yayi har kika sani gudu? Shi Yayan ma ai yanzu yana bacci" komawa tayi zata kwanta Fadila ta jawota tace "bakisan yanda nake zumud'in zuwa makarantar nan bane Dan Allah kitashi kishirya"
Jin tahad'ata da Allah yasata mike tafara shiri badan baccin ya isheta ba, itama abaya tasa amma nata arsh color ne da mayafinshi arsh, sunyi kyau sosai, Fadila tace "muje mugaida Hajiya da Daddy" kallonta Baby tayi tana mamakin yanda takeson gaida mommy dukda momyn ba amsa mata takeba, kawar da tunanin tayi tace "okay muje"
Hanya suka nufa zuwa d'akin Daddy a zaune suka sameshi yanashan coffee hannunshi rikeda jarida yana dubawa fuskarshi da medicated glass, sallama sukayi ya amsa musu, zama sukayi akasa tareda gaidashi, cikin fara'a ya amsa musu, kud'i yaciro yamika musu, Baby ce ta amsa sukayi godiya sosai kafin suka fita zuwa d'akin Mommy, tare suka samu Mommy da Abdul, Mommy tasashi agaba da breakfast tace dole saiyaci shikuma ya had'a face yaki ci, sallama sukayi Baby tafad'a kan mommy tana dariya, Mom ma dariya tayi tace "yau kece kika shirya dawuri haka Auta?"
Tace "eh mana mom ai Adda Fadila ce ta tasheni" had'a fuska mommy tayi Dan batason yanda Baby take yawan ambaton Adda Fadila d'innan, Fadila ce tace "Ina kwana Hajiya"
"Lafiya" shine abinda mommy tace, shiru tayi Sai daga baya tad'an d'ago kai tace "ina kwana yaya Abdul"
"Lafiya" shima shine abinda yafad'a, daganan Fadila bata kara magana ba ta zauna a takure sai Baby ce take d'an sata acikin maganarsu, shima saidai tayi murmushi, saida Abdul yashirya kafin suka tafi makarantar, cikin sa'a akayi mata register bayan anyi mata interview, makarantar na karatun doctor ne, Baby zata zauna a school ita kuma Fadila zata koma gida, sallama sukayi da Baby kafin taje bakin motar tarasa aina zata zauna gaba ko baya? Jikintane yafara b'ari ganin Abdul yana zuwa dawasu takaddu a hannunshi, kallonta yayi ya watsar tareda Shiga mazaunin driver, baya ta bud'e ta zauna Dan tana ganin batada matsayin dazata zauna a gaba, wani kallo yawatsa mata kallon waye driver d'inki? Da sauri ta bud'e motar ta koma gaba ta kame jikinta kamar mejin sanyi, ko kallonta band yi ba yaja motar, daidai bakin cross suka tsaya kasancewar akwai go slow dayawa, Abdul ya kwantar da kanshi jikin stiyari itakuma Fadila ta zauna dab'as kamar me karb'an karatu Dan a tsorace take, knocking na glass akayi a tsorace ta bud'e tana kallon kowaye lokacin Abdul ya d'ago kanshi wani soja tagani hannunahi rikeda bindiga, ihu tayi tana salati tareda runtse idonta Dan batason ganin soja tsoro suke bata, tsaki Abdul yaja yaciro wani paper yanunawa sojan, hannu soja ya d'aga mishi da hausanshi Wanda baya fita yace "matanka yanajin tsoro"
Tsaki Abdul yaja ya zabga mata harara, ita kuma idonta a rufe ta toshe hanci Dan warin giya sojan yake, saida yarufe musu motar ta bud'e idonta da hancinta tana maida numfashi kamar wacce tayi wasan tsere, ruwa a roban swan yamiko mata baima kalleta ba, karb'a tayi tabud'e ta kwankwad'e tass batasan lokacin datace "wannan sojan anyi kazami" ba, kallonta yayi da mamaki "wato dama tana magana iya shegene kawai", dahaka har aka d'aga musu hannu alamar pass, wucewa yayi.
     "Amrah lamarin Kamal yana d'aure mata kai ya shareta kuma bai fad'a mata laifin datayi mishi ba, yaufa ta kudiri aniyan sauya fad'a mata ko kuma suyita ta Kare, Santa a b'ace ta sameshi yana kwance akan sofa kunnenshi da waya sai murmushi yakeyi, da matsifa ta wupce wayar takara a kunnenta ikon Allah saiga muryar mace kamarma bataji Hausa sosai ba cikin matsifa tace "matarshi ke magana munafuka yanada Aure idanma bai fad'a miki ba Toni zan fad'a miki karuwar banza ballagaza mebin maza"
Kamal ne ya wupce wayar ya kashe kafin ya nunata da yatsa yace "baki kai wannan matsayin ba kinyi nad'an kizagi wasu karuwai bayan gidanku shine sansanin karuwai, nan kika nuna mana videon yayarki da wani kato akan gado ashi kema nan karuwarce domin tin ranar Dana sanki a mace Nagano hakan, sabida haka karki kara kuskuren kiran wasu da karuwai"
Gidanmune karuwai? Yana nufin nima karuwa ce? Tayaya hakan yafaru? Batayi mishi magana ba tajuya zuwa bedroom tanason tuno yaya akayi tazama karuwa Dan tsaf ta fahimci maganar Kamal, kwanciya tayi akan gado tarufe idonta tanason tuno ya akayi haka?
Duk tunanin duniya tayi amma takasa ganowa.
    "Fadila tafara zuwa school kuma tana fahimtar komai, saidai zamanta agidansu Baby yanasata a takura tana samun saukine a wurin Daddy da Baby, yau Sunday babu makaranta Daddy ya tashi da zazzab'i tin safe Fadila take zirga zirga akanshi, dayayi tari saita tambayeshi meyafaru? Dukta susuce akanshi don't shine gatanta yanzu shine yake kula da ita kamar yanda yake kula da yaran daya Haifa, bazataso wani Abu ya sameshi ba, zama tayi a gefenshi tana kuka kallonta Daddy yayi yace " kidaina kuka haka cutan Diabetes yake insha Allahu zan samu sauki kinji?" Share hawaye tayi tace "to Daddy, in kawo maka Tea?" Daddy yace "eh"
Mikewa tayi da sauri harda d'an gudu danufin zuwa kitchen karo sukaci da Abdul Wanda taji labarin rashin lafiyan Daddy yanzu, ta bugeshi amma ko juyawa batayiba burinta tad'ibo wa Daddy shayi kawai, kallon bayanta yayi yana ganin yarinyar tafara rainashi, Fadila said a tad'ibo shayin a wani glass cup da karamin plate tanufi d'akin, lokacin Abdul yana zaune a gefenshi, bata kalli Abdul ba sai hawayen datake sharewa tanufi wurin Daddy tareda d'agoshi kad'an tasa mishi filo a bayanshi, shayin Tamika mishi tace "gashi Daddy" karb'a yayi yanayi mata murmushi ya d'aura cup d'in a bakinshi da sauri ya tufar jin zafin da shayin yayi, Abdul ne yamike ya kofa mata mari cikin tsawa yace "banida hankali ne? Yaya zaki kawo mishi shayi me zafi haka?" Fadila ko kallonshi batayiba tanufi wurin Daddy tanayi mishi sannu, da gudu tafiya ta d'auko wani cup d'in tazo tana fifita mishi har yayi sanyi Tamika mishi, Daddy yarinyar tabashi mamaki a mareta kuma tayi shiru? saida Daddy ya kwanta kafin Fadila takalli Abdul tace "kayi hakuri nima babana ne yanda ka d'aukeshi haka nima na d'aukeshi" tana fad'a haka tafice a d'akin ranta yana suya, Daddy ne yakalli Abdul yace "baga irinta ba yanzu kamareta a banza, kadaina saurin hannu watarana zakayi Dana sani, kumani bazanso kayi Dana sani ba"
Jikin Abdul yayi sanyi sosai shiru kawai yayi.
     "Fadila tana Shiga d'aki ta mayar kamar ba abinda yafaru, Baby tana bacci Dan tasaba da wannan baccin, tashinta tayi tace " jeki dubaDaddy bashida lafiya" da sauri Baby tamike takalli Fadila tace "meya sameki a fuska naga yayi jaa"Â
Kawar dakai Fadila tayi tace "ba komai kuka nayi danaga jikin Daddy"
Baby tace "ai haka yake mishi har India an kaishi amma jikin idan ya tashi ba sauki, Alladai yabashi lafiya"
Fadila tace "Ameen"
Ba ta yadda sun kara had'a ido da Baby ba Dan idonta cike yake taff da hawaye.
08144818849
[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸
  *ƘANWATA*
🌸🌸🌸🌸🌸
Na
Jiddah S Mapi
*Chapter 33*
    . ~Baby taje taduba jikin Daddy taga da sauki sannan tayi mishi sannu takoma d'aki book tafito dashi takalli Fadila tace "Adda Fadila nifa abinda Mommy takeyi bayamin dad'i kiduba kigani yaufa Daddy bashida lafiya maimakon ta zauna a gefenshi saitaje d'aki tanata sharan bacci fisabilillahi hakan datayi tayi daidai?"
Fadila tace "baiyi ba amma ai wata kila tanada uzuri shiyasa" Baby tace "babu uzurin dayakai na lafiya ai nikam Addu'a nake Allah yasa Daddy yakara Aure" mommy ce tashigo d'akin fuu tayi kan Baby, duka ta had'a mata abaya tace "ba Ameen ba Dan Ubanki, ina uwarki shine addu'ar dazakiyimin? Wallahi Baby kifita a idona na rufe na lura tinda kika dawo kika d'au wani karami tsana kika d'aura min, fatan kishiya kikemin" tafashe da kuka Dan mommy akwai bala'in kishi, Fadila ta tsorata sosai ta sunkuyar dakai tana addu'a bata ankaraba taji mommy tariko kunnenta tace "nasan kece kike zigata wallahi yaran nan kufita a idona" had'asu tayi wuri d'aya tana jibgarsu sai ihu suke saida tagaji Dan kanta ta kyalesu tafice a d'akin, jikin Baby da Fadila yayi tsami.
     "Kamal yafara baiwa Amrah tsoro rashin hankalin nashi yayi yawa yanzu takai karanshi wurin Ummanshi Umma tace yarantane zai daina itafa abun yafara isanta, tin yana waya da 'yammata harya fara kawo 'yammatan gidanshi yanaji tana gani zasu shige bedroom nata babu daman magana, wani lokacin da dare har video call yake da 'yammata suyita maganganun banza harta gaji ta fice, abinda yafi damunta yanzu shine shan giya dayake saiyasha yazo yayita Amai kuma dole itace zata kwashe, yau yana kwance a falo tayi wanka cikin Riga da wando gashin kanta tabaza bata d'aura d'ankwali ba dukdan taja hankalinshi, tasameshi yana video call zuwa tayi wurinshi tad'an leka wayar "wa iyazubillahi" shine abinda tafad'a ganin mace ba kaya ajikinta tanayi mishi dariya, kallonta yayi ya watsar yaci gaba da wayarshi saida yakai minti talatin yanayi kafin yakashe wayar, ya kwanta, Amrah cikin kuka tace "Yaya Kamal meyake damunkane? Kasan hukuncin Wanda yake kallon tsiraicin macen daba tashiba kuwa? Yaya Kamal zinan idofa kakeyi innalillahi wannan wani irin bala'i ne"
Kamal yace "kinga dalla malama idan kinzo kicikani da surutu ne to nagode zaki iya tafiya"
Amrah tace "hmmm dama nazone in fad'a maka kataimakeni kadaina shan giya wallahi banaso kamutu kashiga wuta Allah yace meshan giya baya Shiga aljanna"
Kamal a zafafe ya mike yace "idan makullin aljanna yana hannunki to idan nazo Shiga kihanani" bar mata wurin yayi, tafashe da kuka me ratsa zuciya.
      "Makarantar Fadila yana tafiya yanda yakamata kamar dawasa yau tayi shekara d'aya saura shekara d'aya tagama duk wani all amari daya shafi Adamawa ta manta dashi, ko a school aka kawo maganar Adamawa shiru takeyi batason jin sunan garin, kewan iyayentane kawai yake damunta sai wani lokaci datakejin kewan Amrah (d'an uwa yawuce wasa)
Abdul yana kokari wurin kaisu makaranta dukda baya dariya amma wani lokacin yanad'an yiwa Fadila magana, yauma suna cikin school Fadila tana zaune ita kad'ai kamar yanda tasaba idan Baby tana class bata takura mata, wani yarone me suna Haruna yaron ya takurawa Fadila bawasa tayi mishi a hankali yabarta yakiji tayi mishi tsawa yaki yaron kamar maye, zuwa yayi ya zauna a gefenta yace "sannu sarauniy"
Fadila juyawa tayi takalleshi tsaki taja ta tashi zatabar wurin yariko hannunta, da Sauri yajuya tana kallonshi, cikin tsawa tace "kasakar min hannu"
Langwab'e kai yayi yace "haba Beauty danna rike hannunki shine laifi?"
Mari Fadila ta sauke mishi a fuska, waro ido yayi yana tab'a gefen face nashi cikin b'acin rai yace "ni kika Mara?" Fadila tace "an mareka kayi abinda zakayi"
D'akin hannunta yayi yace "zakisan kin mareni kinsan nid'an gidan waye a garinnan?"
Fadila tace "ina zan sani tinda kaiba d'an gidan karuna bane"
Cikin b'acin rai yazaro belt na wandonshi watsawa Fadila yake kota ina sai Jan Allah ya isa take, dataga zaiyi mata illa ta d'auko dutse babba ta rotsa mishi aka, mutanene suka taru a wurin babu Wanda ya iso Dan suna matukar tsoron yaron Baby ce takaraso wurin da gudu ganin Fadila tana kuka gashi jikinta yayi ja fuskarta da shatin bulala, kasa tad'iba tafara watsawa yaron tana zaginshi da kyar mutane suka janyesu, fad'an har gaban shugaban makaranta ankai dama yaron yasaba fad'a da mutane amma dashike babanshi mugun don ne yasa aka kashe case d'in, bayan an tashi daga school ne Abdul yazo d'aukansu ganin duk jikinsu a mace Ga fuskar Fadila yayi jaa yasashi cewa Fadila tazo gaba ta zauna, daidai lokacin data zauna hawaye yafara bin fuskarta, kawar da kanshi yayi kamar be ganiba, ta madubi ya kalli Baby ma tana share hawaye, saida suka iso gida kowa yafita Abdul yace "kubiyoni d'akina"
A firgice Fadila takalli Baby, Baby takashe mata ido d'aya binshi sukayi har zuwa d'akin nashi, saida yagama iya abinda zaiyi yaja lokaci kafin yazauna akan sofa yace "idan kukayimin karya saina b'allaku meyafaru yau a makarantarku?"
Baby takalli Fadila, Fadila takalli Baby Fadila tace "Um...Umm..dama damadai"
Baby ma tace "dama wannan ne..su wannan"
Wani harara ya zabga musu yanuna Fadila yace "ke nasan bakya karya meya faru?"
Fadila tace "wani yarone ya dukeni shine muka kai kara shugaban makaranta ta kashe maganar"
Abdul yace "idan naje naji labarin ya bambanta sainayi miki bulala ishirin ke kuma" ya nuna Baby yace "sainayi miki bulala ishirin da biyar, kutashi kubarmin d'aki"
Da gudu suka fice a d'akin, Daddy dake tsaye ajikin window yayi dariya "wato yarannan sun had'a Kansu kamar 'yan uwa".
    "washe gari Abdul daya kaisu makaranta Shiga sukayi gaba d'aya kiran wata yarinya yayi yace taafad'a mishi gaskiyar abinda yafaru, zayyana mishi tayi yace shikenan ya gode, office na shugaban yaje yace sai anyiwa yaron hukunci, da shugaban yaga Abdul d'an rikici ne yakira yaron dasu Fadila a idonsu aka baiwa yaron hutun sati biyu, sallamansu akayi kowa ya koma class, Abdul ma yatafi,
Fadila zaune take a class ta buga tagumi tana tunani karo na farko kenan da aka karb a mata 'yancinta lalle yau taji dad'i sosai batayi tsammanin tanada matsayin da za'abi mata hakkinta ba, sai murmushi take sakarwa ita kad'ai, Baby ce tazo wurinta ta dafata tace "Adda Fadila abu yayi yau Yaya Abdul yashiga fad'a kwanaki danayi fad'a a makaranta zuwa yayi ya zaneni agaban mutane lalle kinci sa'a yau"
Murmushi Fadila ta saki tace "hmmm sa'a ba d'aya bama sa'a har