Showing 12001 words to 15000 words out of 139192 words
Amrah cikin kuka tace "Adda Fadila ke kam kin samu Wanda zai Aureki ma har kina kuka hmmm"
Fadila cikin kuka tace "Amrah kema lokacinki ne baizo ba, idan yazo zakiyi"
"Mubar maganar nan yanzu yaushe kike ganin zamuyi dinner?" Cewar Amrah
"Dinner sai ranar Friday idan an d'aura Aure sai muje kinga lokacinsu Fatima sunzo daga Gombe ko?"
Amrah tace "Dama su Fatima zasuzo? Shine babu Wanda yafad'amin"
Fadila tace "wallahi yanzuma sub'utar bakine dama nacewa mama zanyi miki surprise"
Amrah tsalle tayi ta dire a gado tace "Allah yanunamin Ranar Auren nan abun zai bada citta"
Fadila dariya tayi tace "d'azuma munyi waya da Baba Sadeeq yace tun alhamis zasuzo"
(Baba Sadeeq kanin babansu ne dayake zaune a Gombe yanada yara uku Fatima da Nana sai Hafeez, Fatima itace 'yar fari sai kanwarta Nana sai Hafiz d'an Auta)
Amrah Murna kawai takeyi domin tana matukar son Nana yarinyar halinsu d'aya batada tsoro haka har sukayi bacci.
_Jiddah Ce_
08144818849
[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸
  *ƘANWATA*
🌸🌸🌸🌸🌸
Na
Jiddah S Mapi
*Chapter 9*
  ~ranar laraba Amrah sun dage suna shirye shiryen kayan Kamu domin gobe alhamis za'ayi Kamu, Amarya zatayi fitan blue and white kamar yanda angoma zaiyi fitar blue and white kawayen Amarya da kawayen Amrah zasuyi futan yellow na dogon Riga da bakin gelle, sai Kanwar Amarya wacce zatayi fitan Light blue na kaya, su Zee da sauran kawayenta na school ne sukayi ankon, Abokan ango suma yellow na kaya suit zasusa, za'ayi Kamu ne a Wetline dake garin Adamawa.
   "Me kunshi ja da baki aka kira da me kitso har gida sukazo akayiwa Amarya da Kanwarta, dama dukansu ga hasken fata lallen yayi musu kyau ba wasa, kitso kuma da akayi gashi har gadon bayansu, Fadila dama anayi mata gyaran jiki irin na 'yan Maiduguri, sai haske takeyi, Unty Sadiya sai bata kayan gyara na mata takeyi kala kala har Fadila taki karb'an sauran Da Fad'a suka gama.
_Ranar Kamu_
  "Wurine me kyau Wanda aka kayata da kayan kyale kyale sai yalk'i da sheki kawai gurin yake yi fad'in irin yanda wurin ya had'u b'ata lokaci ne, Kawayen Amarya duk sun karaso sunyi kyau kowa ya zauna akan kujerarshi an aje musu drinks da snacks, Abokan angoma hakane,
Amarya da ango yanzu suka karaso cewar MC atake aka d'au tafi a wurin, Kamal ba karamin kyau yayi ba kamar yanda Fadila ma tayi, Amrah ce a gefen Fadila rike da hannunta sai taku suke kamar kasace ka gudu, A haka aka fara gudanar da Kamu Umman Kamal da kawayenta ma sun halacci wurin, an d'auki hoto anyi rawa".
_washe gari_
  "Yakama jumma'a da safe bayan 'yan biki sun tashi daga bacci kowa sai leka d'akin Amarya yake yana tambaya ina Amarya? Amrah ce take cewa tashiga band'aki, Kusan karfe goma Unty Sadiya tashigo gidan kasancewar ta kwana a gidan makotansu sabida ba wurin kwana baki sunyi yawa, tambayar Amrah tayi ina Amarya? Amrah Jan hannun Unty tayi suka Shiga wani lungu acikin gidan, cikin tashin hankali da firgici tace "Unty Sadiya tun jiya da muka dawo daga wurin dinner naga ran Adda Fadila a b'ace nace mata Adda meya sameki? Adda tacemin wai nayi mata shiru ko kuma taci mutuncina shine nayi mata shiru, yau da Asuba natashi banganta ba na duba kota ina lungu da sako babu ita, Nana ma ta tayani nemanta amma bamu ganta ba, banason fad'awa Mama sabida kar hankalinta ya tashi" ta karasa maganar tana kuka, Unty Sadiya Ido ta zuba mata cikin rud'ani tace "Fadila ta gudu kenan?"
Amrah tace "ina ganin hakane Unty"
  "To ai bamuga tazama ba dole a sanarwa mutane ko wata kila a dace"
Unty Sadiya ce taje ta sanarwa Mama abinda ake ciki batayi tsammani hankalin mama zai tashi haka ba, sai gani tayi mama ta suma, mutanene suka taru akanta suna tambayar meya faru? Unty Sadiya cikin kuka ta zayyanawa kowa abinda yake faruwa, Inna Falmata ce tace "To wannan maganar ya tsaya a cikin gidannan domin fa akwai matsala idan mutanen waje da mutanen ango sukaji, Wallahi sunan gidannan b'aci zaiyi, Yanzu tinda tanada kanwa sai tayi fitan Amare a d'aura Auren da ita akan yarjejeniya idan yayar tadawo sai ya saki kanwar koya kukace?"
Mutane sun amince da maganar Abbansu ma ya yarda domin ya tara mutane dayawa na birni dana kauye yana gudun abin kunya, haka maganar yayi tsit saidai ana Neman Fadila a hankali yanda bakowa zai fahimta ba, Amrah sai kuka takeyi mutane suna lallb'ata ana bata hakuri Amma ina numfashinta har yankewa yakeyi tsabar kuka da tashin hankali, Unty Sadiya ce ta lallab'ata tayi wanka tareda sa kayan Amarya rufe kanta tayi da mayafi yanda masu zuwa biki bazasuga fuskarta ba, haka aka d'aura Auren Kamal da Amrah, Shi Kamal lokacin da ake d'aura Auren be karaso ba har aka d'aura kafin yazo.
Da yamma kusan mangarib aka tafi dinner Amrah sai hawayene suke sauka a idonta jitake kamar ta d'aga mayafin Ko zataga Fadila,
Kamal yarike hannunta sai washe hakora yake yana d'agawa Abokanshi hannu.
  "An fara dinner wurin ansa mishi disco light sai canja colour yake daga ja zuwa blue zuwa purple wuri ya k'ayatu sosai, Amrah da Kamal sune zaune a saman kujera irin na Amarya da Ango, Maman Kamal da Kawayenta sunyi anko kowa yayi kyau, MC yakira Amarya da ango sun fito fili suna rawa sai lik'i akeyi musu harda dala,
Wurin d'aukan hoto akace dole sai Amarya ta d'aga kanta, tofa Unty Sadiya da sauran dangin Amarya sai juye juye suke sun rasa mafita, Amrah tafisu Shiga tashin hankali "ya zanyi ne?"
Ganin batada mafita yasata juya tacikin mayafi taga babu me kallonta A hankali tafara bin kasa tana sulalewa harta fad'i, Lokacin mutane suka lura da hakan, Kamal ne ya sunkuya ya nad'e hannun riganshi ya d'agata sama sai cikin mota, mutane sun tsaya sai mamakin abinda yafaru suke Amarya ta suma.
  "A motarshi yasata yana d'an buga bayanta a hankali Amma bata tashi ba, ruwa ya d'auko cikin Goran swan ya shafa mata, Amrah tana jinshi batayi yunkurin yin komai ba, fuskanta rufe yake da mayafi, daidai kunnenta yakai bakinshi cikin muryanshi me sanyi yace "my Deela meya sameki? Kodai kinajin kunyata ne?"
Amrah jin sunan daya kira yasataji wani Abu ya tsaya a makoshinta hannunshi ta lalubo ta rike gam a nata, Kamal jin haka yasashi sakin murmushi domin yasan tanajin kunyarshi ne, Matsowa yayi dab da ita har suna jiyo numfashin juna, hannu yasa akan mayafinta yafara cirewa a hankali, Knocking akayi musu da sauri ya saketa tareda yin baya, bud'ewa yayi yaga Ummace tsaye hankalinta atashe tace "ya Fadilar take? Meya sameta?"
Kamal d'an dariya kad'an yayi yace "Ummana babu komai tana bukatan Hutu ne kawai"
Umma tace "to kabarta ta huta mushiga ciki a karasa dinner, ina wannan kanwar tata me kama da Aljanu Mara take ko Amrah?"
Kamal dariya yayi yace "Umma nikam bansan meyasa bakwa shiri da Amrah ba, nima ban ganta ba maybe tana hanyane kinsanta da ra'ayi"
Umma tace "koma dai menene ita tasani ita yashafa"
Rass Rass gaban Amrah yafad'i "me matarnan take nufi dani? Ok Fadila takeso? To zanga tayanda zata had'u da Fadilar harta sota"
Kamal ne ya katseta da tunanin ta hanyar riko hannunta yace "my Deela bari nashiga ciki idan an sallami baki zan dawo kinji?"
Amrah gyad'a kai tayi, fita yayi a motar ya kulle mata, sai a lokacin ta d'ago kanta tacire mayafin ta saki ajiyar zuciya me karfi, wata siririyar dariya tayi Wanda ya Nuna tana cikin farin ciki kallon fuskarta tayi jikin madubin motar taga yanda tayi kyau tayi haske, gyara mayafinta tayi tace "Adda Fadila kiyafemin naso in danne zuciyata akan Kamal Amma hakan ya faskara, tun lokacin da kina had'u da Yaya Kamal naji zuciyata ta Kamu da sonshi ina cikin soyayyarshi sai kuka nasamu hujjar Auren shi kasancewar banida saurayi, ki yafewa Kanwarki masoyiyarki Kamal natane ita kad'ai da ita yafi dacewa bake ba, niban d'auki shawarar Zee ba asali inada wannan niyar a zuciyata Allah yasani Adda Fadila" kwantar da kanta tayi jikin marfin motar tana kuka me ratsa zuciya da gangar jiki.
Jiddah ce
08144818849
[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸
  *ƘANWATA*
🌸🌸🌸🌸🌸
Na
Jiddah S Mapi
*Chapter 10*
    ~kuka take tanajin zafin rabuwa da 'yar uwarta "me kikayi haka Amrah? Zaki cutar da 'yar uwarki akan namiji dakuma damuwarki Wanda yazame miki kaddara?" Da sauri ta d'auko wayarta takira wani number ana d'agawa tace "ku dawo da ita nafasa"
'Dayan b'angaren akace "Hajiya ai bakin Alkalami yariga ya bushe mun Riga mun aiwatar da abinda kika samu, yanzu hakama jirgi yatashi"
"La'ila ha illahu, jirgi yatashi? Dan Allah ka dawomin da ita nayi nadama"
Wani irin shu'umin dariya akayi kafin yace "ni Guyson banayin Abu kuma in kara maidawa ke kika kawo wannan shawarar kisani idan kika yadda kika tona mana asiri kamar wa kanki kika tona domin ni kurkuku yazama min gida kece da wahala" kitt yakashe wayarshi, Amrah idonta ne ya kafe babu hawayen ma yanzu, tunanin abinda yafaru tafarayi cikin k'unci.
 *Throw Back*
A wurin Kamu Amrah ce aka kira a waya lokacin tana zaune a gefen Fadila sunan guyson shine ya bayyana akan screen d'in, kallon gefenta tayi taga hankalin Fadila a wurin Kamla, mikewa tayi ta fice zuwa bayan wani mota, d'aga wayar tayi tafara magana a hankali kamar haka "guyson ya kake kirana a cikin mutane bayan kasan banason kowa yasan abunda yake tsakaninmu?"
Guyson yace "nakirakine domin in baki handkerchief dazakiyi anfani dashi idan kun koma gida, ni bazan cutar da yayarki ba, ke kuma nasan kinason Kamal dolene kiso Aurenshi, banaso shirinki ya b'aci shiyasa nake bin komai a sannu"
Amrah tace "yanzu fad'amin ina kake"
Guyson yace "ina bayan motar da kika jingina na rufe fuskata da bakar kyalle banaso kowa yaganni"
Amrah tace "ok ganinan zuwa"
Amrah juyawa tayi taje wurin guyson bata handkerchief yayi yace "wannan sai tana bacci zakisa mata saiki kirani zanzo, nayi waya da drivern jirgin yace zai kaita Lagos idan kuma za'a bata kulawa harsai ta manta da Kamal kafin tadawo gida"
Amrah dariyan jin dad'i tayi tace "nagode guyson da kulawa Amma Dan Allah kada a cutar da ita"
Guyson yace "OK"
Nan suka rabu kowa yatafi, bayan an tashi a Kamu ne sun koma gida kowa yayi bacci Amrah tasawa Fadila handkerchief a hanci tana sheka ta suma, janta tafarayi har zuwa kofar gida, takira Guyson awaya yazo ya d'auketa.
*Throw back finished*
 "Hawayen fuskarta ta share tanajin inama data hakura tabar 'yar uwarta ta Auri masoyinta, Amma ina soyayyar Kamal bazai barta ba, share hawayen daya fito mata tayi ta kwanta a cikin motar bacci yayi awon gaba da ita,
Cikin hall kuma su Unty Sadiya sai ajiyar zuciya suke saukewa Dan bakaramin tashin hankali zasu shigaba idan maman Kamal ta kunyata a idon duniya dahaka har aka kammala dinner ango sai rawan kai yake burinshi yaje ya samu Fadilarshi, wani abokinshi ne Abdul ya leko fuskarshi yana dariya yace "How fer ango? Ka matsu mu kaika wurin amarya ne? Naga tun d'azu kana wani lumshe ido to babu Inda zamuje sai bayan isha" ya karashe maganar yana dariyan mugunta don yasan Kamal baiki ace yanzu yana jikin Fadilarshi ba, Kamal had'a face yayi yana kallon Abdul, can yaga Ummanshi tana wucewa riko gyallenta yayi ya karyar da kai yad'an lumshe ido yana kallonta "meya faru my Son?"
Ido yazuba mata a hankali yace "Ummana I want to go and meet my Deelah"
Umma murmushi tayi tad'an shafa kanshi tace "Fadila tana bacci yanzu idan kajema tashinta kawai zakayi son kayi hakuri a gama dinner saiku tafi kaji?"
Langwab'ar da kai yayi yace "to Umma"
Dariya tayi mishi a zuciyarta tace tin yanzu yafara zama Mara kunya to idan yazama angon kuma ya za'ayi?, sharewa tayi taci gaba da kula da mutane, sai bayan isha aka tashi daga dinner motoci masu lafiyane suka d'aukan kawayen Amarya, Kamal ko jiran abokanshi baiyi ba yaje yasamu Fadilarshi a mota yatarar tayi bacci kanta a sunkuye, murmushin daya bayyana dimple nashi yayi yaja motar suka wuce gidansu Amrah, Sai bayan sun iso Kamal ya d'agata yana kiran sunanta "Fadila Fadila tashi mun iso"
Firgigit Amrah tafarka daga baccin daya d'auketa Wanda cike yake da mafarkin Fadila, Kamal ne ya matso kusa da ita sosai har yanajin saukar numfashinta, hannunta yariko yanad'an matsawa a hankali lumshe idonshi yayi Wanda yad'an kankance sabida gajiya, a hankali kamar Wanda bayason yin magana yace "Baby na nayi missing naki nad'an lokaci kad'an dukda kin hanani ganin fuskarki amma ba matsala zan hakura har zuwa gobe Wanda za'a kawomin ke inyi ta kallonki harsai nagaji" jikin Amrah ne yafara rawa jin sweet muryanshi yanayi mata kalamai masu dad'i, kallon hannunta dayake rawa yayi yad'an jawota kusa dashi, wani irin runguma yayi mata yanajin Lamar ya mayar da ita ciki, Amrah rawan jikinta ne ya tsananta dan bata tab'ajin irin wannan yanayin a jikinta ba, shiru tayi tana sauraron bugun zuciyarshi, A hankali tad'aga hannunta ta d'aura abayanshi itama ta rungumeshi tanajin soyayyarshi yana kara Shiga zuciyarta, sun kai kusan Ten minute a haka kafin tazare jikinta a hankali tana kokarin bud'e mortar, fizgota yayi zuwa jikinshi cikin muryanshi daya fara rawa yace "Baby na please kibini muje gida mukwana tinda kin Riga kin zama matata"
Amrah da Sauri ta janye jikinta tafita a mortar tana dariya, Dama haka yaya Kamal yake bashida kunya?
Karo tayi da mutum a bakin kofar Shiga gida, da Sauri ta d'aga gyallen kanta tana kallon ko wayene, Unty Sadiya tagani tsaye tanayi mata kallon tuhuma, jikinta ne yad'an fara rawa muryanta yana cracking tace "Unty Lafiya kuwa? An samu Fadilar ne?"
Kallonta Unty Sadiya tayi daga sama har kasa tace "me kukeyi a cikin mortar?"
Amrah jitayi zuciyarta ta buga d'ago many an idonta tayi tana kallon Unty da kyar ta harhad'a magana bakinta yana rawa tace "Unty Yayi niyan ya rungumeni shine na matsa tafita da gudu shiyasa kikaji ina dariya"
Unty Sadiya tayi Jim tana nazarin maganar tace "Amrah ki rike amana karki cutar da yayarki, kinsan yanda Fadila takeson Kamal bazata yafe miki ba kuma bazata yafe mana ba idan har wani Abu yashiga tsakaninki da mijinta sabida lokacin zai haramta a gareta, Aurennan anyishine domin hankalin maman Kamal ya kwanta sabida matar batada kunya, kiyimin alkawarin babu abinda zai Shiga tsakaninki da Kamal har Allah ya bayyana Fadila"
Amrah ido tazuba mata tana kallonta da mugun mamaki A hankali tabud'i baki zatayi magana Mama ta kwala mata kira, ajiyar zuciya ta sauke ta rab'a ta gefen Unty Sadiya zata wuce, carab Unty Sadiya tarike gyallenta tana kallonta ido cikin ido, Amrah ce tafara janye idonta da sauri tasa hannu tajanye gyallenta daga rikon da Unty Sadiya tayi mishi, sauri sauri gudu gudu tawuce cikin gida tana sauke ajiyar zuciya, Mama ta tarar a cikin gida tsaye hankalinta a tashe, da sauri takarasa wurin tana tambayar mama meya faru?
Mama cikin kuka tace "Amrah Fadila ta cucemu Fadila taci Amanarmu Allah ya isa tsakanina da ita, duk irin tarbiyyar da muka bata saida ta lalata, Ashe saurayi tabi suka gudu..." Mama ta karashe maganar tana kuka me tab'a zuciya,
Amrah takaraso wurinta ta rungumeta tsam tace "Mama me kike fad'ane akan Adda Fadila kinfi kowa sanin tanada nutsuwa"
Mama cikin kuka tace "Amrah ada kece muke yiwa kallon Mara hankali Ashe ba haka abin yake ba Fadila ce batada hankali, yanzu suka kirani a wayar itada saurayin nata wai sunanshi gubson kuma wai mucireta a zuciyarmu Dan tayi mana nisa sannan afad'awa Kamal yacireta a xuciyarshi tana fad'an haka ta gintse wayar"
Amrah cikin tashin hankali tace "Gubson kuma Mama? Kodai Guyson?"
Mama cikin kuka tace "yawwa yanda kika kira haka sunan yake"
Amrah kukane ya kubce mata cikin zuciyarta tace meyasa Fadila tayi haka? Kodai tagane nice nasa ayi mata haka, Unty Sadiya ce ta karaso wurin tace "Mama nifa kidaina jawa Fadila Allah ya isa kika sani ko dole aka sata tayi maganar?"
Amrah d'ago kai tayi ta bankawa Unty Sadiya wani irin banzan harara tanajin matar tafara fita a ranta, mikewa tayi cikin kuka tace "Unty yanzu mama kike nufin tayi karya? Itafa aka kira kuma tabbas inajin Adda Fadila tana waya da saurayi guy son amma ban tab'a kawo komai a raina ba sabida na yadda da yayata hundred percent amma taci Amana"
Unty Sadiya kallonta takeyi ita haka kawai Amrah bata kwanta mata a rai ba, juyawa tayi cikin share hawaye itama tashige d'aki, Amrah ce tariko mama takaita har kan gado ta kwantar da ita tareda bubbuga bayanta har tayi bacci, Tashi tayi ta tafi d'aki ta kwanta akan gado lokacin su Fatima dunyi d'ai d'ai akan gado suna bacci, Wayarta ta d'auko tayi dialing na numbar guyson yana d'agawa yace "congratulations amarya Allah yabada zaman lafiya"
Amrah dariya tayi tace "Aikinka yana yyau nawan Yanzu da kyar na lallashi Mama tayi bacci ta kunnu iya kunnuwa nake fad'a maka"
Dariya yayi yace "sai gobe baki tambayi yayarki ba"
Itama dariya tayi tace "nasan tana cikin koshin lafiya tunda nabaka kud'i masu yawa Wanda za'ayi mata hidima dasu, bazata zauna da yunwa ba, miliyan goma ba wasa ba"
Wani irin dariyar mugunta Guyson yayi yace "Hajiya Amrah Allah yakara tsayin rai" kit yakashe wayar, Amrah mirginawa tayi a hankali tazubawa gefen katifar ido Fadila take gani tanayi mata murmushi, lumshe idonta tayi a hankali tabud'e su jin wayrta yana ringing da sauri tamike tana kallon wayar zuciyarta ne takusayin bindiga ganin Yaya Kamal ya bayyana kan screen nata, rasa abinyi tayi ta langwab'e akan gado ta d'aga wayar tana nishi sama sama, "Kanwata ina Yayarki tashigane nakirata taki d'auka?" Amrah cikin wani irin murya tace "Yaya Kamal cikinaaa wayyo zan mutu ka taimaka min"
Kamal