Showing 138001 words to 139192 words out of 139192 words
meyafaru? Tace "wai nakaiwa Baby zoɓo inji Yaya"
Abdul karɓan wayarta yayi yakira number ɗin yace "bazata kawo ba batada lafiya"
Kabir yace "ban ganeba ko batada lafiyan takawo Baby tanason sha yanzu"
Abdul yace "bawa Baby wayan"
Kin bata wayan yayi dan yasan yanzu zaiyi mata faɗa, yace "ban isa da Fadilan bane? Ta tashi tahaɗa ko naje nafasa mata baki"
Abdul yace "kana fasa mata baki zan fasa bakin Baby"
Katse wayar Kabir yayi, yakalli Baby cikin lallashi yace "kuyi hakuri gobe zan siya miki"
Baby buɗe baki tayi tafara kukan gaske, wayar yaɗauko yakara kiran Fadila cikin lallami yace "Ƙanwata! Kiyi hakuri ki kawo mata zoɓon kinji ko?"
Fadila tace "tom"
Kashe wayar yayi, nan Fadila tahaɗa mata zoɓo me sanyi tasa a gora Baba takai mata, Baby tace "tnx"
Ko kallonta Fadila batayi ba ta zajna sukayita fira da Kabir, Baby tana shanyewa tace "i need more"
Fadila cikin jin haushi tace "nabi more da gudu ba wando bazan kara ba"
Kabir yace "tunda tanaso kiyi mata mana"
Nan Fadila tafara gunguni da kyar tahaɗa mata wani zoɓon, Baby tana ɗanawa ta tofar tace "ba daɗi"
Kabir yace "ki karayi mata wani"
Kuka tafara tana shiga kitchen takira number ɗin Abdul tafada mishi abinda yafaru, nan yaso gidan da gudun tsiya yaja hannun Fadila yace "aiba baiwarku bace"
Tafiya sukayi saida Kabir yatashi yahaɗa zoɓon.
"Guyson ne yake kwance akan cusion hankalinshi akan wayarshi yana kallon hoton yanda aka gyara gidan marayun shi, Nabila ce tashigo tana yatsina fuska tareda turo baki, jikinta sanye da riga daidai gwiwa daga sama ta ɗaureshi, sai hula net cap data tara gashinta aciki,
zama tayi a gefenshi takalli tv taga Bollywood yake kallo, film ɗin sanam teri kasam, matsowa tayi ganin hankalinshi baya kanta, kwantar da kanta tayi akan cinyarshi, hannu ɗaya yasa yacire hulan dayake kanta, a hankali ya cusa yatsunshi zuwa tsakiyar kanta, nan yafara shafawa amma hankalinshi yanakan waya, Nabila lumshe ido tayi ta lafe a jikinshi, ganin baiyi magana ba yasa cikin shagwaɓa tace "Habibi?"
"Um" shine abinda yace, tashi tayi ta wafce wayar, da sauri yace "please kibani inayin abu"
Kallon screen ɗin tayi tace "yanzu time ɗina ne bana Waya ba"
Yace "sorry reply ɗaya zanyi kinji Babyna?"
Girgiza kai tayi tana kallon cikin idonshi tace "no"
Janyota yayi yanaso ya kwace tafara dariya tana ɓoyewa, da kyar wa wafce yayi reply ɗin tareda rufe data ya juya ya kalleta yace "nagama"
Haɗe face tayi alamar tayi fishi, matsowa yayi yace "haba Babyna nasan bazakiyi fishi dani ba, Ranar monday fa zamuje honeymoon a dubai kinaso aga amarya bata dariya ne?"
Ɗan dariya tayi tace "da gaske?"
Janyota jikinshi yayi yace "da gaske nake kinga acan zamuje mu zauna har saimun samo Baby kafin mudawo"
Sa hannunshi yayi yana shafa cikinta yace "wannan karamin cikin Baby's nawa zai ɗauka?"
Nabila tace "huɗu"
Dariya yayi yace "saide daya"
Tace "huɗu dai"
Yace "no"
Nan tafara kuka adole saida ya yadda akan huɗu ɗinne.
"Kamal yakamata kayi aure yanzu kaga komai ya canja yanzu"
Umma ce take faɗawa Kamal wanda yasa kanshi akan cinyarta, yace "Umma Dady ma yamin maganar ɗazu amma naɗan barine saina manta da tsohuwar mata wato Amrah"
Umma cikin tausayi tace "Kamal ka daina sa kanka acikin damuwa wanda yamutu yariga yamutu"
Kamal yace "hakane amma zanso ace tadawo duniya koda sau ɗayane na nuna mata so saide hakan is too late"
Umma tace "Allah yaji kanta"
"Amin" yace, Pinky ce tashigo da uniform ɗin school ganin Kamal yana kwance akan cinyar Umma yasa ta kwaɓe fuska kamar zatayi kuka tace "Yaya katashi ni na kwanta dan nagaji a school"
Kamal kin tashi yayi, da sauri tazo tana tureshi shikuma sai dariya yake mata, Umma tace "katashi to kato dakai kazo ka kwanta a cinya"
Kamal yace "itama ai katuwa ce"
Pinky tace "niba katuwa bace wallahi"
Nan tasa kanta a gefenshi suka kwanta tare Umma sai dariya take musu,
Dady ne yashigo yace "Kamal zo"
Kamal yaje Dady yace "ga waɗannan takaddun ka ɓoyemin su"
Kamal yace "to Dady" a halin yanzu babu abinda be saniba akan dukiyar Dady, dan Dady yajashi jiki sosai ya nuna mishi kan dukiyarshi sannan yahaɗashi da Allah koda bayan ranshi ne Kamal ya duba Nabila da Pinky sabida Kannenshi ne"
Kamal yace zaiyi insha Allah tareda yiwa Dady fatan nisan kwana me albarka.
"Alhaji da gaske zakayimin kishiya?"
Momy ce tasa Dady agaba tana tambaya harda kukanta, Dady yace "eh"
Momy tace "wallahi na daina cin abinci dayawa idan kana ganin karya ne to kafara zama agida"
Dady yace "sabida ke saina fasa fita neman halaliyana ko?"
Momy tana kuka tace "Aa" saida tabashi tausayi kafin yace "idan baki gyara halinki ba wallahi saina karo mata, nan Momy tafara godiya tace "wallahi zan gyara"
Da yamma tayi ferfesun kifi tasa a flask guda uku ɗaya ta aika gidan Abdul wa Fadila, ɗaya kuma gidan Guyson ɗaya kuma gidan Kabir, kiranta Fadola tayi awaya tayita mata godiya, Baby haka sukayita fira, Nabila ma takira sukasha fira, a halin yanzu babu abinda take bukata illa taga jikoki daga jikin Abdul da Fadila, Baby da Kabir sannan Nabila da Kaseem, hakan yasa take kula dasu daidai gwargwado.
"Sadiya nagode da ɗawainiyan dakikayi dani amma kema ki ɗauki wannan zaiyi miki anfani"
Umty Sadiya ce zaune agefen Mama, Mama taciro bandir bandir ɗin dubu ɗaya ta ajiye mata wai ala dole saita ɗauka, Unty Sadiya tayi godiya tace "Mama idan na tuna wani abu har kunyan kaina nakeji"
Mama tace "menene kuma sadiya?"
Unty Sadiya idonta ne yaciko da hawaye hoton gaban wayanta ta kalla wanda ɗauka Amrah da Fadila ranar da sukaje gidanta a sallah, Amrah tana dariya sai Fadila data haɗa rai dan Amrah ta tsokaneta, tace "Mama inama a dawo da Amrah koda sau ɗayane na nuna mata soyayya"
Mama saukar da kanta tayi kasa ta share hawayen dasuka zubo mata tace "bakida laifi Sadiya, a yanda abin yazo ba kowane zaiyi tunanin tanada gaskiya ba sabida ta ɓoye, amma ko nima nayi mata wulakanci ashe baiwar Allahn soyayyar yayartace yasata cikin wannan damuwan"
Hawaye suka share duka sukace "Lalle Fadila tasamu Ƙanwa wacce ta nuna mata so"
Unty Sadiya tace "Allah yaji kanki yasa aljannace makomarki, sannan yakai haske kabarinki Amrah yarinyar kirki, in Allah ya yadda zanje Abuja naga Little Fadila ɗiyar da Amrah ta haifa da kanta, Allah ya rayata"
"Ameen"
Mama tace.
"Fadila data idar da sallah tana zaune akan sallaya ta ɗaga hannu sama tace "ya Allah kaika halicci sammai da kassai kaine kake kashewa kuma kake rayawa, Allah nayi tawassali da sunayenka tsarkaka, ya Allah nayi tawassali da alkur'ani me girma, ya Allah kajikan ƘANWATA, ka kai haske kabarin ƘANWATA, sannan kasa ƘANWATA agidan aljannatul firdaus, Kasa shine iya wahalan datasha kenan, Ubangiji ka amsamin rokona badan halina ba, saidan ƘANWATA.
_Tammat Bihamdillahi_
Anan nakawo karshen littafin ƘANWATA, kuskuren dake cikinta Allah ya gafarta mini, tunatarwa dayake cikinta Allah yabani ladanshi.
*JIDDAH CE TA RUBUTA✍️*
08144818849