Showing 126001 words to 129000 words out of 139192 words

Chapter 43 - Kanwata Book One Complete Hausa Novel

Jiddah   

27 Sep 2025

887

/>
Shiru Kabir yayi mishi, hannu yasa akan maranshi yana shafawa tareda runtse ido har wahalallen bacci ya ɗaukeshi,

Abdul shiru yayi yana tunanin hukuncin da zaiyiwa Baby, tukunna ma ina takoyi wannan karatun? Yasan Fadila ce kaɗai zata iya koya mata, tashi yayi a zafafe ya nufi fali, Baby ta rakuɓe jikin Fadila sai zazzare ido take tasan yau takaɗe har ganyenta, Abdul ne yace "ke!!! Zo nan"

A tsorace ta tashi taje, pink lips ɗinshi yaɗan ciza kaɗan sannan yace "waya koya miki wannan iskancin?"

Jikintane yafara rawa, da zafinshi ya matso wurinta ya kifa mata mari, Fadila tashi tayi taje wurinshi tarike hannunshi tareda cewa "me tayi maka?"

Cikin ɓacin rai ya zaro manyan idanunshi yakalli Fadila da kyau kafin yace "zaki rama mata ne?"

Fadila tace "tambayarka nayi"

Yace "oh nagane kece kike koya mata raɓan jikin maza ko dan nasan da batayin hakan"

Ran Fadila ne ya ɓaci cikin zafi tace "dashike gidanmu su suka kawo karuwanci duniya shiyasa, kuma ashe abin ba daɗi kaida kake zama da Nabila harta zauna a cinyarka bakaji haushi ba saida yafaru akan kanwarka? To idan baka sani ba Kama tu Dini tu dan, abinda kayi sai anyi maka"

Tana faɗan haka ta ɗau hijabinta da wallet nata tafice tabar gidan, Baby sai satan kallonshi take burinta kada ya daketa, kallonta yayi yanayinshi yaɗanyi sanyi, hannunta yariko ya zaunar da ita akan sofa, cikin sanyin murya yace "Babyna abinda kikeyi babu kyau kada ki kara sai kunyi aure kinji?"

Giɗa mishi kai tayi a tsorace, yace "yawwa good gal, tashi ki shirya kitafi gida to nizan kula dashi"

Sum sum tamike tasa Takalminta taɗu jakarta kasancewar basuzo da motarsu ba yasa yabata kuɗin transport, a hanya takira number ɗin Fadila yafi a kirga Fadila ko kallon wayar batayi ba, text naban hakuri ta tura mata,

Abdul zama yayi yana tunanin maganganun Fadila tabbas a rayuwa duk abinda kayiwa wani kaima sai anyi maka, yaga zahiri a lokacin daya kusanci Fadila, yayiwa wata fyaɗe shima anyiwa matarshi, gashi kuma hakan yana faruwa akan Baby, dukda ya yadda da Kabir bazai taɓa cutar mishi da kanwa ba amma yasan akwai sharrin shaiɗan, jingina kanshi yayi da jikin sofa ya runtse idonshi, lips nashi na kasa ya tura cikin bakinshi a hankali yafara tsotsa yana tuna yarinyar daya yiwa Fyaɗe dolene ya nemeta koda tayi aure saiya bata hakuri, haka yayita tunani har Kabir yatashi yayi wanka saida Abdul ya kula dashi kafin yace "Dude zan tafi gida"

Kabir yace "ka gaida matarka"

Abdul yace "zataji"

Kallonshi kabir yayi kamar akwai abinda yake damunshi amma yayi shiru kawai ya kyaleshi, tafiya Abdul yake amma tunaninshi duk akan yarinyar ne, tunanin kiranshi da "yaya me nayi maka" yafaɗo mishi a rai, hannu yasa yafara yamutsa lallausan gashin kanshi, da karfi yace "forgive me"

Haka ya iso gida parking yayi yafita zuwa ɗakinshi, wanka yayi ya shirya cikin kananan kaya, bayajin yunwa ko kaɗan amma yana bukatar Coffee, waya ya ɗauka yadanna number ɗin Fadila, Fadila data zauna a gefen gado tana karanta text message na Baby take taji jikinta yayi sanyi meyasa tayi mishi haka? Be kamata tayi mishi hakan a idon kanwarshiba, take taji kunya ya kamata, kiranshi ne yashigo wayarta ɗagawa tayi batace komai ba, shima shirun yaɗanyi daga bisani yace "i need Coffee"

Tashi tayi takashe wayar gani take tasamu dama dazata bashi hakuri, Wardrobe taje ta ɗauko wani wando three kwata, jinx ne ya matseta sosai, riganta me raga raga tasa ta taje tulin gashin kanta sannan ta fesa turare, flat shoe tasa taje tahaɗa coffee ɗin tayi hanyar ɗakinshi, da sallama a bakinta tashiga, ɗago kai yayi ya kalleta sannan ya watsar, gabanshi takai cup ɗin ta ajiye, zama tayi akan cinyarshi tana kallon fuskarshi, ɗauke kai yayi yana danna waya, Fadila hannu tasa ta juyo da fuskarshi, haɗe rai yayi ya ɗauko Cup ɗin ya ɗaura a bakinshi, saida ya shanye ya ajiye yana kokarin sauketa daga jikinshi yaji tace "Am sorry"

Shiru yayi mata dan gaskiya bayaso ta rainasa, Hannunshi tariko tasa yatsarshi a bakinta da sauri ya ɗago yana kallonta, tsotsa take tana kallon cikin idonshi, Abdul ji yayi kamar jinin jikinshi take tsotsewa, sunyi minti goma ahaka kafin tace "Yaya kayi hakuri"

Ras ras yaji gabanshi yafaɗi jin maganar yayi kamar daga bakin yarinyar yafito, babu abinda yatuna sai kukan datake tana cewa yaya kayi hakuri, Fadila sanin haka yasa tayi luff a jikinshi, "Fadila!!!"

Fadila tace "um"

Yace "meyasa kika faɗamin magana me ɗaci agidan Kabir?"

Tace "babu kayi hakuri kaji?"

A hankali yace "bazan iya fushi dake ba na hakura"

Shafa sajen fuskarshi tayi tace "nagode"

Shiru yayi kawai yanajin yanda take shafa fuskarshi, a hankali ta sakko da hannunta zuwa bakinshi zagaye pink lips ɗinshi take tana shafawa, ɗago lumsashen idonshi yayi yace "Do you need it?"

da sauri ta giɗa mishi kai tace "Umm"

Jinginar da ita yayi jikin gadon, bakinshi yakai kan nata a hankali yasa lips nashi nakasa cikin bakinta, jin tayi shiru yasa yace "Suck it"

Kamar jira take tafara tsotsa, jikinta yafara yawo da hannunshi harya samu nasarar cire riganta, shafa ko ina na jikinta yake, itama hannu tasa ta ɓalle bottle ɗin gaban riganshi, kirjinshi tafara shafawa tana yawo da hannunta jikinshi, Abdul badan yaso ba yakeyin hakan duk da yana enjoying amma bayaso yaci aman princess ɗinshi, saide yana tsoron kada Allah yakamashi da laifin kin biyawa matarshi bukatarta, nan nafice nabarsu.

               "Baba kulu saura sati biyu na haihu, murna nakeyi saura sati biyu na huta da wahalar ciki, kinga daganan saina shiga duniya na nemo ƴan uwana tunda natara kuɗi daɗan yawa"

Kulu tana murmushi tace "gaskiya kam kin kusa zama momy kin kusa samun ƴarki ko ɗanki na kanki"

Amrah shiru tayi tana tunani, Kulu tace "ki daina tunani kinji?"

Amrah tace "tom"

Komai na haihuwa sun haɗa sun adana komai rana kawai suke jira, har yanzu basa magana da Ahmad duk yaɗau karan tsana ya ɗaura mata, sai Umar ne yakeɗan kwantar mata da hankali yace tayi hakuri komai na rayuwa me wucewa ne.

_Rana bata karya..._

Gobe ne ɗaurin auren Kabir da Baby, gidansu Abdul makil yake da dangi da abokan arziki, Baby tasha dayis da kitso me kyau, ga Fadila ma ba'a barta abaya ba tayi lalle da kitson, Baby rike take da waya tana chart da Kabir sai dariya take tana rufe baki, Fadila ko tana guga tace "lafiyanki?"

Baby tace "kalau"

Shiru Fadila tayi mata dan batajin daɗin jikinta ta rasa meyake damunta tun safe takejin gabanta yana faɗuwa, Baby tace "naga kamar bakida lafiya Adda kibar gugan ni zanyi"

Fadila tace "ba rashin lafiya bane Baby wallahi tin safe nakejin faɗuwar gaba"

Hawaye ne yafara zuba mata batasan na menene ba amma a zuciyarta tasan bana lafiya bane, Baby sakkowa tayi daga gado ta zauna gefen Fadila tace "kiyi ta addu'a kada kiyi kuka kinga yau ranar farin cikina ne gobe zamuyi aure da Kabir be kamata kina kuka ba kinji?"

Fadila giɗa kai tayi still hawaye yana zuba mata tace "Baby jinake kamar wani abu wanda babu kyau ze faru dani, ban taɓajin hakan a rayuwata ba gaba ɗaya bana hayyacina"

"Kiyita addu'a kinji?"

Haka Fadila ta daure tanayin murmushi dakuma aiki cikin gidan saide gaba ɗaya tanayi ne dan kada ayita tambayarta meya faru, amma a zuciyarta ita kaɗai tasan abinda yake damunta.

             "Amrah zazzaɓi me zafi ne ya ritsata, gaba ɗaya jikinta sai zufa yake tun safe bataci komai tafita a hayyacinta, Kulu da kaka ne suke dubata sai sannu kaka takeyi mata, Kulu tace "Kaka idan bazaiyi ba mutafi asibiti mana"

Kaka tace "ba yau zata haihu ba wannan alamun haihuwan yakusa zuwane kawai"

Kulu tace "Sannu Amrah"

Amrah hannun Kulu tariko tace "idan na mutu ki ɗau Asusu na ki nemi ƴan uwana kibasu kuɗin nasan zaiyi masu anfani"

Kulu cikin kuka tace "Aa Amrah bazaki mutu ba"

Amrah jikinta sai ɓari yake cikinta sai murɗawa yake tayi haske sosai, ahaka har suka kai dare, Kaka taki yadda aje asibiti dan tasan halin likitocin zasuce zasuyi ma tiyata, washe gari da asuba Amrah tafara ihu tana rike ciki, Ahmad ne yashigo ɗakin jikinshi duk yana rawa ganin yanda take yasa yace sutafi asibiti, nan suka kwasu dukka ƴan gidan harda Minal da Bilal, Amrah tafita a hayyacinta, Ahmad yana gudu yace "wani asibiti zamuje?"

Kaka tace "muje Wanda zasu kula damu ba wanda zasubar yarinya ta galabaita ba"

Ahmad asibitin da ake kira Fadilat Hospital ya nufa dan yanzu babu asibitin da ake kula patient kamar shi.

          "Baby hijabi tasa ta ɗaukko nikap tasa daganan tafice ta baya dan bataso kowa ya ganta, ganin motar Kabir yasa taje ta buɗe, baiyi magana ba yaja motar, Baby tace "lafiya kam?"

Kabir shiru yayi, saida yayi parking tana kokarin fitowa yayi sauri ya ɗauketa, kallonshi take da mamaki taga ya ɗauke kanshi, cikin bedroom ya sauketa kwanciya yayi ya janyota tafaɗa a ruwan cikinshi, riketa yayi yace "i need your Help"

Da sauri tace "meya faru?"

Hannu yasa yacire hijabin jikinta yace "Babyna bazan iya daurewa har a ɗaura auren ba wallahi ina cikin matsala"

Baby data tsorata tace "me zanyi maka?"

Hannunta yariko yasa akan maranshi yace "ciwo yakemin"

da sauri ta zame hannunta ta mike tace "gaskiya bazan iya ba kabari idan an ɗaura auren"

Kallonta yayi yace "please"

Dira tayi daga kan gadon tace "badani ba aikata wannan haramcin ko yanzu kataɓani hukuncin masu zina yahau kanmu domin ba'a ɗaura auren ba"

Baice komai ba yamike tareda cire rigan jikinshi matsowa wurinta yayi yace "please romance me"

Da sauri ta koma baya tace "Aa yaya Abdul ya faɗamin haramcin hakan"

Jin tace Abdul ne yahanata yasa yaji daɗi a ranshi koba komai zataji maganarshi idan sunyi aure, juya bayanshi yayi da sauri ta waro ido ta matso wurinshi hannu tasa tana shafa bayanshi, a hankali yace "is okay stop it"

Da sauri tace "Yaya tattoo nagani a bayanka ka rubutu farin sunanka dashi, haramun nefa ranar tashin alkiyama da wuta za'a kankare maka"

Juyowa yayi ya kalleta, yace "ba tattoo bane haka aka haifeni dashi"

Baby tace "laa ashe kai ɗan baiwa ne"

Sa riganshi yayi yace "muje na ajiyeki"

Hannunta yariko suka fita ya maidata gida, saida zata fita ta juya ta kalleshi tace "Kayi hakuri"

Murmushi yayi mata yace "ba komai"

Fita tayi taje cikin sanɗa tashige ɗakinta, Nabila da Pinky suna zaune suna cin abinci Fadila kuwa ta zauna ta buga tagumi gaba ɗaya jitake zazzaɓi yana shirin kamata saide bataso sugane dan yau ranar auren Baby ne, Baby tace "Adda Fadila lafiya?"

Kakalo murmushi tayi tace "eh" daganan ta kwanta danji take jiri yana ɗibanta,

Da karfe biyu aka ɗaura auren Kabir da Baby me martaba da kannen Kabir yau suna cikin garin Abuja kuma tare dasu aka ɗaura auren,

Wayar Fadila ce tayi ringing gakuma mutane dasuke cikin ɗakin, ɗauka tayi tace "hello Mary"

Ɗayan ɓangaren akace "Madam am sorry nasan yau kuna biki ammafa an kawo wata me haihuwa abun ba kyaun gani gaba ɗaya bata hayyacinta munyi iya bakin kokarinmu amma mun kasa, idan ba matsala muna neman taimakonki"

Rass rass gaban Fadila ya rinka faɗiwa batasan lokacin datace ina zuwa ba, kashe wayar tayi taje ɗaki cikin dabara ta shirya taɗau hanyar asibitinta batareda tabar kowa ya ganta ba, a hanya sai salati take tana furta "innalillahi wa inna ilaihi raji'un"

So take kawai taganta a asibiti tarasa meyasa,

Tana isa tafito da sauri ganinta yasa su Kaka dasu Ahmad sukayi kanta suna rokan ta taimaka ta ceci ƴar uwarsu, Fadila hannu tasa ajikin Kulu wacce taga tafi kowa ruɗewa tace "calm down ƴar uwarki zata sauka lafiya da yaddan Allah amma kusa a ranku bamu likitoci ne zamu bata lafiya ko musa ta sauka lafiya ba, Ubangiji Allah shine zai saketa lafiya, kunji"

Kulu cikin kuka tace "ki taimaka mata doctor tana burika da yawa wanda bata cikasu ba"

Fadila jikinta yayi sanyi da sauri ta karɓi rigan doctor da wata nurse ta miko mata, sawa tayi tacire gyallen kanta tasa karamar farin hijabi, waya takira tace "ku shirya komai yanzu zan shigo afara aiki"

Tana faɗan haka tawuce labour Room gabanta yana mugun faɗuwa.

*Jiddah Ce*

08144818849

[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸

*ƘANWATA*

🌸🌸🌸🌸🌸



Na

Jiddah S Mapi

*Chapter 80*

~Abakin kofa ta tsaya saida tayi addu'a ta shafe jikinta dashi kafin ta buɗe kofar bakinta ɗauke da sallama, suna ganinta suka fara kai mata gaisuwa "lafiya" kawai tace, nan suka kwasu zuwa cikin ɗakin inda Amrah take kwance duk tafice a hayyacinta sai salati take, Fadila jikinta ne yafara rawa ganin me nakudan ta juya baya, da kyar dai ta daure ta matso wurin, suma nurse ɗin matsowa sukayi, Hannu Fadila tasa ta juyo da Amrah, Da sauri tayi baya baya zata faɗi, Mary ce ta riketa ta faɗo a hannunta, cikin gigita tafara nuna Amrah bakinta yana rawa tace "kan..kan..kan.."

Mary tace "calm down zata haihu"

Fadila tace "kan...kanwata ce"

Da mamaki suka fara kallon Fadila, da karfi ta kwace jikinta tayi kan Amrah wani wawan runguma tayi mata da karfin gaske, girgizata tayi tace "Amrah!!! Zaki haihu in Allah ya yadda" da tsawa tace "me kuke jira?"

Duk sun tsorata suka matso wurin, sunyi iya bakin kokarinsu naganin ta haihu da kanta amma abu yaci tura, Fadila tana kuka tace "dole muyi mata aiki"

Nan aka tada inji suka shiga tiyata room, Amrah tana kallon Fadila amma bazata iya magana ba sai hawayen wahala dasuke sauka daga idonta, ga hannun Fadila data damka taki saki, Fadila tana kuka tana cewa "zaki haihu"

Alluran kashe jiki sukayi mata, daganan tafara bacci suka shiga aiki, sunyi nasaran ciro yarinya mace kyakkyawa fara, da jinin Fadila ta rungume yarinyar, nurse ɗin kokarin karɓan yarinyar suke su gyarata amma Fadila taki sakinta, jikinta dukya ɓaci da jini, gashi bata hayyacinta tazama kamar zautacciya, Mary tace "madam Fadila ki kawota ayi mata wanka, maman nata zata farka nanda awa ɗaya"

Fadila hana yarinyar tayi da kyar suka kwace yarinyar a hannunta daganan tayi kan Amrah tana girgizata, "kitashi!!"

Janyeta nurse ɗin sukayi suka fita da ita zuwa ɗakin hutu, Awa ɗaya zuwa biyu zuwa uku zuwa huɗu bata farfaɗo ba, Fadila data fita a hayyacinta ganin hakan yasa tace "Kuyi mata allura ta farka mana"

Mary tace "haba Madam tayaya za'ayi mata alluran farkawa? Kinsan dai ai babu"

Fadila fita tayi hijabin jikinta ma yafita, ɗakin da aka kwantar da Amrah taje ta zauna a gefen gadon ta rike hannun Amrah, hawayene suka fara sauka daga idonta ganin yanda Amrah ta rame tayi haske kashin wuya ya fito mata, wayarta ne yafara ringing tana ɗagawa taga Baby ce, so take tace tana asibiti amma tasan abin da zafi, saide ya zatayi da kanwarta? Uwa ɗaya uba ɗayafa ba wasaba, koma meya faru be kamata ta guji ƴar uwarta a wannan yanayin ba, karo na farko data dannawa Baby dismiss kenan, Baby kira take amma Fadila sai kashewa take, Abdul ma yakirata har taso ta ɗauka sai kuma ta danna dismiss, kashe wayar tayi gaba ɗaya tasa a jakarta, kamar da wasa Amrah bata farka ba, hankalin Fadila duk ya tashi takasa zama ga jaririyar a hannunta sai tsala ihu take, rungume yarinyar tayi tafashe da kuka, kallon Mary tayi tace "zan iya bata nono?"

Mary tace "ga uwarta mezesa kibata nono madam? Kidawo hankalinki mana"

Fadila tace "nima uwarta ce dan nida uwarta uwa ɗaya muke kuma uba ɗaya"

Mary tace "kidai hakura"

Rungume yarinyar tayi tana yawo da ita, sai bayan mangrib Amrah tafara buɗe ido, motsi tafara da bakinta a hankali take furata "Adda Fadila!!!"

Fadila datake zaune a gefenta tariko hannunta tace "Ganinan"

Amrah bakinta yana rawa tace "Ki yafemin"

Fadila hawaye ta share tace "zakiyi lafiya insha Allahu ki daina wannan maganar na yafe miki"

Buɗe kofar akayi da sauri ta dago kai taga Baby dasu Abdul da Kabir ne suka shigo hankalinsu tashe, kawar Baby ce tace musu taga Fadila a asibiti hakan yasa suka ɗibu dukkansu sukazo sun zata ba lafiya ba,

Baby ce ta matso tace "lafiya?"

Fadila da hankalinta yake kan Amrah tace "kanwata ce"

Shigowa sukayi dukkansu suka zauna a cikin ɗakin, Amrah tariko hannun Fadila muryanta baya fita tace "Sune sabbin dangin ki?"

Fadila share hawaye tayi tace "Eh sune"

Nuna Abdul tayi tace "ga mijina"

Abdul murmushi yayi yace "nine" tunda yashigo yake kallon Amrah jiyayi zuciyarshi ta buga gani yake kamar akwai wani connection tsakaninsu, hannu Amrah tamika mishi tana murmushi, shima mika mata yayi sukayi musabiha, hannun Fadila tariko tahaɗa da nashi tace "ga amanar yayata ka riketa amana mahaifinmu ya rasu"

A gigice Fadila ta kalleta tace "What!!! Ya mutu? Yaushe"

Baby ce ta matso ta rike Fadila tace "calm down"

Kuka Fadila tafara tana shesheka, Amrah tace "ba kuka ba addu'a zqkiyi mana gaba ɗaya, akwai abinda nakeso nafada miki amma ke kaɗai nakeson kisani"

Fadila tace "kifaɗa a idonsu waɗannan sun zamemin kamar ƴan uwa"

Amrah muryanta baya fita sosai tace "Abba yacemin munada yaya namiji wanda ya auri mamanshi a Saudi sunanshi Khalil a bayanshi akwai kalmar K wanda aka rubuta da bakin abu kitaima ki nemoshi dan ya ɓata tun yana yaro"

Da sauri Baby takalli Amrah ta matso wurinta tace "da baki aka rubuta K?"

Amrah giɗa mata kai tayi dan batason yin magana maganar wahala yake bata wannan ma daurewa take tanayi, Baby kallon Kabir tayi ta janyo hannunshi tace "yaya Kabir cire riganka"

Kabir da mamaki yace "ban gane ba meyake faruwa ne?"

Baby tace "Naga K a bayanka jiya"

Kabir yace "nawa tabon sarauta ne duk gidanmu sunada tabon kowa da inda aka rubuta nashi"

Amrah tace "kayi hakuri ka cire"

Cire

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login