Showing 87001 words to 90000 words out of 139192 words

Chapter 30 - Kanwata Book One Complete Hausa Novel

Jiddah   

27 Sep 2025

876

nazama mara sa'a a rayuwa?"

Kuka take sosai a hankali ajiyar zuciya yafara sauka mata, har saida bacci ɓarawo ya saceta.

         "Wayyo Allah hannuna nashiga uku tin ɗazu ƙonewa nake wannan wani irin bala'i ne? Nasan da agidane can Adamawa da gawayi zansa a kaskon girki nayi girkina hankali kwance, amma wannan sai uban na'u'rori kayita kona hannunka"

Fadila ce take girki a kitchen wacce tasa riga da wando masu faɗi da hula net cap, sai surutu take dan hannunta yanata ƙonewa akan hotplate ɗin, dankali  da ƙwai ta soya da shayi me kauri, jerawa tayi a plate taje ɗakinta ta ajiye nata, sannan taɗau na Baba me gadi takai mishi, kafin tayi wanka ta sauya kaya taɗau na Abdul tayi hanyar ɗakinshi, Abdul daya fito daga wanka yana sauri yaje gida suyi sallama da Kabir, towel ya ɗaura babba da karami yana tsane kanshi, knocking na kofar tayi yace "yes waye?"

Fadila cikin ɗar ɗar tace "nice nakawo maka breakfast"

Ɗan karamar tsaki yaja yace "shigo"

A hanakali ta turo kofar ta mayar, da sauri ta juya baya ganin dagashi sai towel, tsaki yakuma ja yaci gaba da goge jikinshi, da baya baya ta iye mishi plate ɗin tayi hanyar waje, "ke dawo nan"

Muryanshi tajiyo, tsayawa tayi cak bata juyo ba, yace "ba magana nakeyi miki ba?"

A hankali ta juyo tana kallon kasa, matsowa yayi dab da ita yace "oya ki shiryani cikin minti Goma ciki harda breakfast"

Jikinta ne yafara rawa tace "ba..ba..bazan iyaba wlh"

Tsawa ya daka mata wanda yasa ta ɗago kanta da sauri tafara neman inda mai yake, hannunta yana rawa tafara shafa mishi, fuska a haɗe yace "tsaya" cak ta tsaya, saida ya zauna akan sofa yace "oya" shafa mishi tafara hannunta yana rawa harta gama, juyawa tayi zata fita yace "kayan fa?"

Bedroom tawuce ta buɗe wardrobe tarasa me zata fara ɗauka, wani wando tagani jinx me kyau da t shirt takawo mishi, yace "wannan fa? An faɗa miki Gona zanje ne?"

Da sauri ta juya takoma taɗau wani shadda me kyau da hula ta kawo mishi, karɓa yayi yafara sawa, runtse ido tayi yana kallonta harya gama, yace "saura breakfast"

Ɗaukowa tayi tazo gabanshi ta zuba, kafin tafara feeding ɗinshi, saida yakoshi kafin yatashi yace "kafin nadawo ki gyaramin ɗakinayana faɗan haka yafice,

Ajiyar zuciya tasaki tana dafe da kirjinta, "oh Allah ka rabani da sharrin wannan mugun"

Dahaka tafara shirya ɗakin tagama tasa turare tarufe kafin ta tafi.

Jiddah Ce

08144818849

[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸

    *ƘANWATA*

🌸🌸🌸🌸🌸

    Na

Jiddah S Mapi

*Chapter 58*

         ~da gudu da sauri ya iso gidansu ɗakinshi yaje yana knocking da sauri Yarima ya buɗe Abdul be tsaya ba ya rungumeshi da karfi "meyasa ka tafi ka barni jiya? Kuma nazo ina knoking kaki buɗewa?"

Yarima yace "sorry ina dawowa bacci ya ɗaukeni, kaga ɗan sakeni ma irin wannan rungumar ai zaka karyani sai kace wanda mukayi shekaru bamu haɗu ba, kada fa kazo ka karya ƴar mutane"

Abdul tsaki yaja yaɗan sakeshi sannan yace "kaga idan muna magana tsakaninmu ka daina kawomin wata aciki"

Kabir bece komai ba yakoma cikin ɗaki yaci gaba da haɗa kayanshi, Abdul ma yaɗan tayashi har suka gama, Kabir ne ya rungume Abdul yace "ina son in rokeka wata alfarma"

Abdul da jikinshi yayi sanyi da yanayin Kabir yace "kafaɗa koma menene zanyi maka"

Kabir saida ya share guntun hawayen daya zubo mishi sannan yace "please ka kula da matarka sosai yarinyar tanada hankali, kada ka sake ka rabu da ita, bazaka taɓa samun mata irinta ba, kayimin alkawarin zaka riketa amana bazaka daketa ba sannan bazaka ci amanarta ba, koda baka sonta to kayi kokarin koyan santa"

Abdul cikin mamaki yace "meyasa zanyi hakan?"

"Bazaka iyamin alfarma ba kenan?"

Cewar Kabir

Abdul yace "nayi maka alkawari zanyi duk abinda kace"

Daɗa rungumeshi yayi sosai, saida sukayi minti goma ahaka kafin ya sakeshi yanayi mishi murmushi, ɗaukan kayanshi yayi yace "to Allah yahaɗamu a haske"

Idanun Abdul ne suka cika da hawaye yayi kokari ya maidasu ɗaukan jakar kayan Abdul yayi suka fita tareda rufe kofa, Parking space sukaje, Dady da Momy suka fito, momy tabashi kwalin dayake hannunta ya karɓa tareda godiya, Dady yaciro bandir ɗin dubu ɗaya sabbi ya mika mishi, dafari yaki karɓa saida suka matsa mishi kafin yayi godiya ya karɓa, Rungume juna sukayi da Abdul yace "i love you dude"

Abdul yace "Luv you too"

Daganan yabuɗe motar, daidai zai rufe marfin ya hango Baby tsaye tana sharan hawaye, a hankali yasa kafarshi yafito, wurinta yanufa tana ganinshi ta juya baya tana share hawayenta, juyo da ita yayi babu zato babu tsammani yayi hugging ɗinta so tied, shiru tayi tana kallon bayanshi, saida yaɗan daɗe haka kafin ya saketa ya share mata hawayen dasuka zubo yace "bye bye sweet sis ki kula da kanki sosai kinji?"

Baby jin yace mata sis yasa ta ɗago manyan idonta ta kalleshi sannan takuma goge hawayenta ta juya tace "bye" daganan ta wuce ɗakinta, ɗan murmushi yayi yajuya ya koma mota, duk abinda akayi akan idon Dady saide shi yaɗau hakan a matsayin Shakuwa, driver ne yazo zasu tafi, motar Nabila ne ya danno kai cikin gidan, Dady yace su tsaya suyi sallam, Kabir badan yaso ba ya tsaya tareda buɗe motar, Nabila datasha dogon wando buɗaɗɗe da wata riga polo jaa da ɗaurin ɗan kwali tasa glass manya tafito daga motar tana yauki harta nufo wurin Dady, rungumarshi tayi tace "good morning Dady"

Dady yace "morning daughter yakike?"

Tace "lafiya" tareda sakinshi ta nufi wurin momy, Rungumeta tayi suka gaisa a haka, daganan tace "Dady zan shiga ciki na manta eirpies ɗina a ɗakin Baby"

Dady yace "okay, tsaya kuyi sallama da Kabir tukun"

Tsayawa tayi tana kallonshi shima kallonta yayi, ganin ze ɓata mata lokaci yasa ta faɗa jikinshi tareda sa takalminta me tsini ta taka kafarshi ta danna, Kabir yanajin zafin takun datayi mishi amma ya daure ya nuna nata shi namiji ne, ya rungumeta sosai kamar zai tsagata biyu, zafi takeji amma tasan ze fita jin zafi shiyasa ta daure, ganin tana cutuwa sosai shikuma be damuba yasa ta raba jikinsu, kin sakinta yayi yakara matseta da iya karfinshi, kamar ta tsala ihu haka takeji, saida yagaji dan kanshi kafin ya saketa tareda yi mata murmushin da shi kaɗai yasan ma'anarshi, itama mayar mishi tayi na karfin hali kafin tace "Bye"

Shima yace "bye"

Dady wani daɗi yaji a ranshi dan sun mugun birgeshi ita kuma momy taga duk abinda sukayi saide tayi shirune sabida kada ace tafiye shishigi, har Kabir yatafi suna ɗagawa juna hannu, Abdul jikinshi a mace ya juya yatafi cikin motarshi ya nufi gida, Fadila ce zaune akan sofa tana karanta wani snacks da aka turo a group, jikinta sanye da dogon riga armless kanta a kunce kuma babu ɗan kwali farin fatarta yakara bayyana sosai, tabada duk hankalinta akan wayarta tana karantawa tana rubutawa awata takadda, sallama yayi jikinshi a mace, ɗago kai tayi ta kalleshi ganin yanayinshi yasa tace "barka da dawowa"

Kasa kasa yace "barka"

Wucewa yayi be ko kalleta ba, taɓe baki tayi alamar ko ajikinta taci gaba da rubutunta, Abdul yana shiga ɗaki ya cire takalminshi faɗawa yayi kan gado yakwanta rub da ciki, tunani yakeyi sosai wanda ya haifar mishi da zufa kota ina acikin jikinshi, zafi yakeji sosai sanadin wannan tunanin, Fadila ce ta turo kofar ɗakin bakinta ɗauke da sallama, ajiye plate ɗin hannunta tayi tajuya zata fita, "Fadila" sunanta taji yakira a hankali, juyawa tayi tace "na'am"

Hannu yamika mata alamar tazo, a hankali ta sunnar da kai tafara takawa a hankali harta iso ta tsaya a bakin gadon tana kallonshi, hannunshi yasa ya janyota ta zauna a gefenshi, mikewa yayi yazuba mata ido, itama kallonshi tayi sannan ta ɗauke kanta, Batayi zatoba taji ya ɗaura kanshi akan cinyarta, jikinta ne yayi sanyi jin yanda jikinshi yayi zafi, hannunta yariko ya ɗaura akanshi yace "please jikina yana ciwo"

Fadila shiru tayi to miye ma zatayi mishi? Ganin sai kara shigewa jikinta yake yasa taɗan ture kanshi kaɗan muryanta yana rawa tace "to...to ni me zanyi maka?"

Cikin sanyin murya yace "please"

Fadila a hankali ta cusa hannunta cikin sumar kanshi tafara shafawa, lumshe idonshi yayi yana sauke numfashi a hankali, ganin kamar yayi bacci yasa ta sakeshi tareda ɗaura kanshi a filo, a hankali cikin sanɗa ta mike zata tafi, caraf yariko hannunta da karfi, "auch" shine abinda tafaɗa dan taji zafi, janyota yayi a hankali yace "karki tafi please stay with me"

Shiru tayi ta zauna tana wasa da yatsunta, kamo hannunta yayi yakuma ɗaurawa akanshi, kallonshi tayi a hankali ya lumshe mata idonshi, ganin haka yasa tacire hannunta da sauri, kara riko hannun yayi ya ɗaura akanshi yace "kici gaba dan Allah karki kyaleni da  bansan yanda zanyi ba ina cikin matsala"

A hankali tafara shafa sumanshi tanayi tanaɗan bugawa a hankali har bacci ya ɗaukeshi, hamdala tayi zata mike yariko hannunta cikin bacci yaki saki, shiru tayi ta zauna a gefenshi tana kallon yanda yake bacci kamar wani innocent Boy, ɗan murmushi tayi ta janyo filo taɗan ɗaura kanta akai, dahaka itama bacci ya ɗauketa.

           "Amrah saida tayi sabon dole da kuluwa dan matar akwai ɗan karan surutu wane aku, saide duk hiran da zasuyi bata taɓa yadda tafaɗawa Kuluwa sirrinta koda wasa, ahaka sukayi kwana biyar agidan watarana su samu abinda zasuci watarana kuma su hakura dan kayan abincin da Unty Sadiya ta siyo musu yakare kuma basason su dameta, cikin Amrah kuma ya fito yanzu tana bukatar kulawa da samun kayan abinci masu inganci, zaune suke akan tabarma kusada Abba dabaya jin daɗi sosai, Kuluwace tabada kuɗi akaje akayi mishi gwaji an kamashi da hawan jini wanda idan beyi a hankali ba ze iya zama mishi matsala, Mama data zabga tagumi tana kallon kasa Abba yariko hannunta yace "idan kikayi tagumi ita kuma Amrah tayi yay?"

Hawaye Mama tashare tace "na tabbata Amrah tana cikin damuwa da ƴar uwarta tana nan da zasu rinƙa raba damuwan tare amma yanzu harda kaɗaici yana damunta"

Sakin hannunta Abba yayi yajuya baya tareda cewa "banaso kinamin maganar yarinyarnan"

Shiru mama tayi tana share hawaye daganan tace "dolene nayi maganar Fadila sabida ƴarka ce"

Abba mikewa yayi yabar mata wurin mama cigaba tayi da kukanta,

Kulu cikin Mamaki takoma ɗakinta Amrah tace "lafiya Baba kulu? Naganki cikin damuwa"

Kulu taso ta tambayeta waye Fadila amma takasa sabida tana tsoron kada suce tana shige musu sosai, tace "ba komai Amrah naje Abba yafita shiyasa nadawo"

Amrah tace "okay"

Dahaka kowa yaci gaba da aikinshi.

Jiddah Ce

08144818849

[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸

    *ƘANWATA*

🌸🌸🌸🌸🌸

    Na

Jiddah S Mapi

*Chapter 59*

         ~Abdul da Fadila tun daga wannan ranar basu kara haɗuwa da juna ba, kowa yana ɓangarenshi yana harkan gabanshi, Fadila tafara zuwa aiki tun ranar litinin daya wuce, Dady yasa musu ma'aikata mata babu namiji a Asibitin, Baby ma tana zuwa dukda bata cikin yanayi me daɗi amma tana daurewa tayi alakarta da Fadila yanda suka saba, rayuwa me ɗaukeda ban sha'awa sukeyi, Yau yakama alhamis Fadila ce kwance akan gado tana murkususu sakamakon ciwon ciki daya galabaitar da ita tin jiya dare, Riga da wando na bacci ne a jikinta da hula net cap tsabar wahalar datake sha batasan lokacin data cire hulan ba, wayarta ce tafara ruri, dafari ta share saide kira ake babu kakkautawa, Da kyar tasa hannu ta ɗauko wayar tana cize baki, sabuwar number tagani ta ɗaga tareda cewa "hello"

"Barka da warhaka Doctor Fadila muna nemanki cikin gaggawa idan baze zama matsala ba mun kawo patients ne kuma tana bukatar taimako na gaggawa ki taimaka mana dan Allah"

Fadila tace "zan tura maka number yanzu ka kira Baby nikam banida lafiya"

"Nagode Doctor Fadila"

Fadila katsewa tayi tashiga duba number ɗin Baby harta tura mishi kafin takoma ta kwanta.

Abdul dayake kwance a ɗaki kanshi yana kallon sama tunani yakeyi sosai ga yunwa yafara sashi agaba kuma yaje dining bega komai ba, cikinshi ne yafara ɗan murɗawa a hankali yasa hannu ya shafa lumshe ido yayi yace "sorry yanzu zaka samu abinci"

Tashi yayi yafara tafiya a hankali, zuciyarshi tana raya mishi yaje ya sameta yace yanajin yunwa, wani ɓangaren kuma yana faɗa mishi yaje kitchen da kanshi, kitchen ya nufa yafara dafa indomie soya kwai yayi ya ɗaura ruwan zafi, madaran ruwa yasa tareda sugar dakuma coffe saida suka tafasa kafin ya sauke ya tace a ƴar karamar cup, zama yayi asaman drawer dake kitchen ɗin yafara ci, saida ya koshi kafin yafara tunanin to meyasa Fadila bata fito ba har yanzu?

Ɗan tsaki yaja yace "iskanci ne kawai dan taga ina damuwa da abincinta shiyasa"

Wani ɓangaren kuma yace mishi kaje de ka duba meya hanata fitowa, a hankali ya dirko daga saman yanufi ɓangarenta, this is the first term daya fara shiga ɗakinta, wani ƙamshi yaji ya buga mishi hanci ga wani sanyi dayaji ya ratsa cikin jikinshi, kallon falon yayi komai a kimtse a gyare, dubawa yayi be ganta ba, hakan yasa ya nufi hanyar bedroom ɗinta, murɗa handle ɗin yayi a hankali bakinshi ɗauke da sallama, "Ke" shine abinda yafaɗa ganinta nannaɗe acikin bargo tana bacci kuma da alama ko salla batayi ba, cikin tsawa yakuma cewa "ke"

Fadila data samu bacci ya ɗauketa da kyar, taji muryanshi a hankali tafara buɗe idonta harta saukesu akanshi, kara maidawa tayi ta rufe, a zafafe yace "ba magana nakeyi miki ba?"

Fadila yatsina fuska tayi ta mike a hankali tana cize baki tace "kayi hakuri"

Kallon yanayinta yayi yace "kinyi salla?"

Girgiza kai tayi alamar aa

Cikin ɓacin rai yace "kina ƴar musulma amma har yanzu bakiyi sallan asuba ba? Me kike jira? Kinzo kin kwanta kina bacci kamar wata ƴar maye tashi da Allah kije kiyi salla"

Hawayene yafara zuba a idonta tace "banayi"

"Ba kyayin me?"

Tace "sallah"

"Oh ayya sannu Kafira kinji?"

Fadila tayi shiru, nufota yayi cikin zafi yace "yanzu zaki farayi"

Fadila dataga kamar belt yake cirewa ze daketa cikin sauri tace "wallahi cikina ne yake ciwo bana sallah tin jiya da dare"

Kara rike cikinta tayi tana kuka, jikinshi ne yayi mugun sanyi yace "okay kimsha magani?"

Tace "Aa"

Toilet nata ya nufa a wata ƴar karamar roba yafito da ruwan zafi da towel a hannunshi, zama yayi a gefen gadon yace "cire rigan nan"

Waro ido tayi dukda tana cikin ciwo be hana ta cewa "me zakayi" ba, matsowa yayi dab ita a hankali ya riko hannunta fuskarshi a ɗaure gam babu alamar dariya, igiyar rigan yafara kwancewa a hankali, Fadila shiru tayi ta runtse ido, saida yacire rigan sannan ya kurawa bayanta ido, jin yayi shiru sosai yasa taɗan juya ganin yanda yake kallon bayanta yasa taɗan rufe da hannunta, ɗago kai yayi ya kalleta kafin yaɗau towel ɗin yasa a ruwan dayake hayaki tsabar zafi, riko hannunshi tayi ya kwace yajuyo da ita tana facing ɗinshi, towel ɗin yasa akan cikinta daidai inda take rikewa, ihu tayi tsabar zafin azaba dataji "shiiiiii" shine abinda yafaɗa tareda ɗaura yatsa akan bakinshi alamar tayi shiru, shirun tayi ta lafe a jikinshi,haka ya rinƙa sa towel ɗin yana sawa akan cikinta har taji sauki sauki kafin ya zameta a hankali ya ɗagata yace "canja kayan"

Tashi tayi taje wurin wardrob ta ɗauko wani dogon riga mara nauyi sannan ta juya tana kallonshi, roban da towel ɗin ya ɗauka yanufi toilet saida ta canja kayan kafin yafito, kwanciya tayi akan gado ya rufata da blanket sannan yaje kitchen yahaɗa mata breakfast yazo yabata, fita yayi a ɗakin yafaɗa ɗakinshi tareda cewa "Alhamdulillah ina kula dake kamar yacce nayiwa Dude na alkawarin zan kula dake"

      "Niko Amrah inada tambayar danakeso nayi miki amma ina tsoron yacce zaki fahimci zancen"

Cewar kuluwa datake toya kosai Amrah tana sawa a leda, Amrah tace "mun riga mun zama ɗaya kiyi tambayarki kawai ba komai"

Kuluwa tace "tom shikenan Dan Allah Amrah Wacece Fadila?"

Sakin Ledan hannunta tayi kosan ciki yazube mikewa tayi batace komai ba tayi hanyar tafiya gida ranta idan yayi dubu to ya ɓaci batasan wannan tambayar ce Kulu zatayi mata ba da yau bazama ta fito ba,

Da sauri Kulu ta rikota tace "dan Allah kiyi hakuri saida na tambayeki fa kikace mun zama ɗaya"

Amrah cikin ɓacin rai tace "bansan kina bibiyar rayuwarmu har haka ba, bansan zaki tambayeni wacece Fadila ba, ni bansan wata wai Fadila ba sannan koda na santa to na manta da ita dan Allah kada ki tuno min da ita na manta ta"

Kulu tace "shikenan daga yau bazan kuma tambayarki ba, amma ki koma kici gaba dasa kosa"

Amrah tace "Aa kaina yanaɗan ciwo saikin dawo kawai"

Tana faɗan haka ta wuce batako saurari abinda Kulu zata faɗa ba, tafiya take amma tunani yayi mata yawa batasan meyasa idan akayi mata maganar Fadila ranta yake saurin ɓaci ba, hannu tasa ta share hawayen da suka zubo mata, ɗit ɗit wani me mota yake tayi a bayanta tsabar tunani batama jishi ba, parking yayi yafito cikin tsawa yace "ke anayi miki horn kina yiwa mutane iskanci, zan wanka miki mari wallahi"

Amrah ma cikin ɓacin rai tace "idan baka mareni ba baka tabbata mara kunya ba"

Cikin hasala ya nufo wurinta kamar ze mareta Amrah tariko hannunshi tace "idan ka sake ka mareni to kasa a ranka ka mari rayuwarka dan saika gwammaci baka fito yau ba koda abinda yafitar dakai me daraja ne"

Cikin ɓacin rai ya janye hannunshi yace "kinsan meya fitar dani dakike min wannan rainin hankalin?"

"Kaima kasan meyasa nake tunani akan hanya?"

Ganin yarinyar baza'ayi mata ta kyale ba gashi har mutane sun fara taruwa yasa yace "muje gefe idan ba matsala"

Amrah a hankali ta bishi wurin motarshi yace "baiwar Allah niba mafaɗaci bane wallahi yauma dalili ne, daga Abuja nake amma nazo hutu nan, yanzu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login