Showing 6001 words to 9000 words out of 139192 words
tsami"
Zee tace "Allah ya huci zuciyarki Amrah, ni bada fad'a nazo ba"
Amrah batayi mata reply ba don ranta ya b'aci matuka.
"Lafiya naga ranki a b'ace Amrah?"
Amrah kallon Fadila tayi da idonta Wanda suka nuna tsantsar b'acin rai tayi murmushi tana kokarin b'oye b'acin ranta tace "babu komai Adda kawai dai na b'ata rai ne Dan hakan yanamin kyau inji yaya Kamal"
Kallonta Fadila tayi tanaso tagano gaskiyar maganar tace "are you sure?"
Amrah tace "yes am sure"
Fadila shiru tayi tafita taci gaba da aikinta ita kuma Amrah kwanciya tayi tanajin haushin maganar da Zee tafad'a mata.
*****************
"Lokaci sai ja yaje yau saura sati biyu Auren Fadila da Kamal, sai shirye shirye suke musamman Amrah wacce take shirin Auren kamar ba gobe, Kamal kuma ce musu yayi duk abinda sukeso sukirashi a waya zaizo suje yasiya musu, Amrah ce kwance akan gado tana chatting da Zee domin a satin nan sun zama cif da Zee kasancewar Zee tace mata ta shiryu bazata kara yin komai ba Wanda babu kyau, Zee tace "Yanzu Amrah maganar dinner kinyiwa mijin yayar naki?"
Amrah tayi reply da "Aa barshi ai Yaya Kamal bashida matsala komai nafad'a mishi to zaice eh"
Zee tace "to Amma kinada tabbacin zai yadda da dinner? Domin fa ba kowani namiji bane yakeson bidi'a"
Amrah tace idan kina tantama bari in kiraki sai shima in kirashi zakiji ta bakinshi ai"
Tana fad'an haka saiga kiran Amrah a wayar Zee, d'aukawa tayi itama Amrah takira Kamal yana d'aukawa tace "bafa kiranka nayi domin kamin girman kaiba, wai Dan zaka zama ango shine harda wani shan kamshi"
Dariya Kamal yayi cikin muryanshi me zaki da sanyi yace "ke meyasa kika kirani? Idan bazakiyi maganaba kashe wayata zanyi in kira babyna muyi firan soyayya"
Tsaki Amrah taja tace "ai itama babyn taka zan iya b'oye wayarta, bama wannan ba Yaya Kamal Dan Allah inason ayi dinner a Aurenku ko Dan kawayena"
Kamal saida yayi shiru kafin yace "baza'ayi ba domin ana d'aura Aure zanzo in d'auke matata mutafi, banason bidi'a"
Amrah sauke murya tayi tace "haba yaya Kamal nasan bazaka ki ba kidan son da kake yiwa Adda Fadila"
Dariya yayi ya kwaikwayi muryanta yace "shikenan za'ayi 'yar Auta"
Godiya tayi mishi tace "bye Allah barka da Adda ta"
"Ameen"
Kashe wayar tayiwa zee magana ta watsapp tace "ya kikaji yanda mukayi da Yaya Kamal? Tuni ya yadda"
Zee tayi reply da "Amrah wani Abu yabani mamaki tsakaninki da Wanda yayarki zata Aura"
Amrah tace "menene ya baki mamaki Zee?"
Zee tace "yanda kuka saba dashi kuma yanda yake sake miki fuska kamar kece budurwarsa? Hiranku ya birgeni har nakeji inama ace kece yake Aura sabida yanda kuke hiran ya birgeni wallahi"
"Ke dakata" cewar Amrah, banason iskanci da iyeyifa Zee, wani irin banzar magana kikeyine? Are you mad? Tayaya zakiyi wannan maganar akaina da Mijin yayata? Ki iya bakinki karki sake kisamin shaid'an a lamarina"
Zee tayi reply da "kiduba kigani maganar danakeyi miki gaskiya ce kuma bazan fasa fad'an gaskiya ba, sabida kece kikace ina fad'an gaskiya akoda yaushe"
Amrah ce tayi saurin kashe Datan wayanta, wurga wayar tayi akan gado ta d'auko filo d'aura a kanta, hannunta tasa a saman filon tafara marin fuskarta, tana tuhumar kanta meyasa takira Yaya Kamal har Zee taji? Gashi tana kokarin kawo mata shaid'an a lamarinta, "Auzubillahi minashaid'anirrajeem"
Shine kad'ai abinda take iya fad'a har ta samu saukin tunanin datakeyi.
_jiddah ce...✍️_
08144818849
[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸
*KANWATA*
🌸🌸🌸🌸🌸
Na
Jiddah S Mapi
*Chapter 5*
~Fadila ce tashigo d'akin ganin Amrah bata fitoba har yanzu, "kanwata lafiya baki fito ba?"
Amrah tana jinta Amma tayi shiru kamar me bacci, d'an bubbuga bayanta Fadila tayi takara cewa "bacci kikene kanwata?"
Har yanzu taji shiru, murmushi tayi taja bargo ta lullub'ata zama tayi a gefenta tasa hannunta a gashin kanta tana shafawa a hankali tanajin son kanwar tata yanabin duk jikinta, saida taga Amrah tana bacci cikin jin dad'i kafin ta tashi ta rage mata gudun fanka tafita a d'akin, Amrah bacci ne ya d'auketa a lokacin da bata shirya yinshi ba, jin yanda yayarta take kula da ita yasa ta cire komai a ranta tayi baccinta cikin kwanciyar hankali.
Koda ta tashi lokacin ta manta komai,
"Kin tashi ne kanwata?"
Amrah mutitsika ido tayi cikin muryan baccin da bai gama saketa ba tace "eh Adda na tashi kuma inajin yunwa"
"To waye zai dafa miki abinci yabaki kinje kin kwanta a d'aki waye sa'anki"
Cewar Mama wacce take zaune akan tabarma tana gyaran farcenta,
Amrah baki ta turo gaba tace "Mama dad'ina dakefa kina yawan shiga tsakanina da yayata, yanzu haka haushina kikeji sabida jiya banyi wanke wanke ba, ni gidannan ma ya isheni sabida bakya sona"
Mama tace "ni bake bace banaso halinki shine banaso, keda Fadila wace babba? Dazaki zo kice mata kinajin yunwa, ai kamata itace zatace miki tanajin yunwa kikawo mata abinci koda shike ba laifinki bane laifin ita Fadilarce, kuje kunfi kusa"
"Haba Mama don tace tanajin yunwa shine yazama abin magana? Kibarta mana ai yarintane"
Mama shiru tayi batace komai ba don idan ta bud'i baki babu shakka sai tayi zagi garadai tayi shirun, Inna Falmata ce tayi sallama wata kawar Mamace dasuke makwabta dasu, tare suka Amsa saidai Amrah ce kad'ai bata Amsa ba, had'a rai tayi domin taki jinin inna Falmata a rayuwarta matar tana shige mata lamari sosai tashi tayi ta shige kitchen koba komai zata zauna a ciki har Inna Falmata ta tafi, Gaisawa su Mama sukayi da Inna Falmata ta zauna akan tabarma gefen mama suka fara hira, Fadila ma tana zaune a gefe d'aya tana danna wayarta, Inna Falmata ce tace "Wai ina Amrah ne ban ganta ba?"
Amrah datake b'oye a kitchen cikin zuciyarta tace "me kuma zatayimin datake tambayata"
Fadila tace "Amrah tana kitchen"
Inna Falmata tace "Dama shine aikin ai, nifa tun wuri na fad'awa Mamanku ta nemawa Amrah taimako ga malamai dayawa a gari, yarinya babu Wanda yatab'a zuwa wurinta da sunan So balle ayi maganar Aure, duk yanda akayi akwai Jinnu ko kuma dasa hannun makiyanta"
Mama murmushi tayi tace "Inna kidaina fad'an haka zato zunubi ne, kuma dududu shekarar Amrah nawane? Shemaranta fa goma sha bakwai, kuma tana makaranta har yanzu sai wani ahekara zata kammala ai babu abin damuwa anan"
Inna Falmata tace "Hmmm bazaki ganeba Karima ita yarinya idan ta balaga babu Wanda yace yanaso to akwai abun dubawa ko irin soyayyarnan ta yara itafa batayi, ni abun yana damina sosai bana fad'a mikine sabida kada hankalinki ya tashi"
Mama shiru tayi domin tasan maganar Inna gaskiyace to amma idan harta amince akan gaskiyane Amrah tana jinsu a kitchen hankalinta zai tashi, dariyan da bai kai har zuciba tayi tace "abar maganarnan Inna ayi maganar data kamata"
"Karima abinnan bazai dameki yanzu ba sai kinga Amrah tayi shekara talatin a gida zakisan gaskiya nake fad'a"
Da sauri Amrah ta dirko daga saman Kantar data zauna, Durkusawa tayi a kasa tana sauraron maganar Inna Falmata, Hawayene yafara sauka a idonta zuciyarta tanayi mata zafi, dafe kirjinta tayi daidai saitin zuciyarta tanajin yanda yake bugawa, runtse idonta tayi gam tana tunanin "to idan maganar Inna Falmata ta kasance gaskiya fa? Yaya zanyi? Da gaskene zan iya kai shekara Talatin babu Wanda yace yana sona? Kai karya ne" tafad'a tana goge hawayenta tashi tayi tafara bin jikinta da kallo ganin bata kallo me kyau yasata fita a kitchen d'in da gudu ta nufi d'aki ko kallon inda suke batayi ba, Fadila ce ta tashi tabita, tana zuwa tacire d'an kwalin kanta tsayawa tayi a gaban mirror tana kallon fuskarta da kuma jikinta gaba d'aya kurawa fuskarta ido tayi tana kallon manya manyan idanunta da karamin bakinta me kalar pink, kallon gashin kanta tayi Wanda ta kameshi wuri d'aya, kwance ribon d'in tayi ta baza gashin har zuwa fuskarta, kara hargitsa kanta tayi kamar mahaukaciya cikin ni irin murya tace "Inna Falmata kinyi karya inada kyau inada gashi kuma inada ilimi na boko Dana islamiyya, menene a jikina Wanda maza basa so? Ko wani namiji zaiyi burin samuna a matsayin mata, to Amma meyasa basa cewa suna sona?" Ta kara fad'a tana zubda hawaye, durkusuwa tayi har kasa tahad'a kanta da jikin bango tana kuka me cin zuciya, Fadila share hawayenta tayi tanajin tausayin kanwarta karasawa tayi cikin d'akin, d'ago Amrah tayi tana goge mata hawayenta, Amrah d'ago kanta tayi tana kallon Fadila da idanunta Wanda suka rine suka zama ja, bud'e baki tayi zatayi magana Fadila tayi saurin rufe bakinta da hannu a hankali ta girgiza mata kai tayi idonta yana zubar da hawaye, cikin muryar kuka tace "banaso kice komai a halin yanzu, kibari sai idan zuciyarki tasamu nitsuwa"
Amrah shiru tayi batace komai ba Kuma idanunta basu daina zubar da hawaye masu d'umi ba, janye jikinta tayi daga na Fadila hawa gado tayi ta kwanta tareda janyo bargo ta lullub'e jikinta harda kanta, shiru tayi kamar me bacci amma ita kad'ai tasan me takeji a zuciyarta, Fadila ganin Amrah ta kwanta kuma alamar ta huce yasatayin murmushi tafita a d'akin.
"Washe gari Kamal ne yazo gidansu Fadila baifi minti Biyar ba saiga Fadila tafito jikinta sanye da leshi Ash colour da Ash na hijabi tashafa jambaki maroon fuskarta tayi kyau sosai, Kamal yana ganinta yafara murmushi itama murmushi ta sakar mishi me tsada, Bud'e mata marfin mota yayi yace " bismillah Amaryar Kamal"
Farfar tayi da manyan idonta ta juya mishi baya alamar bazata Shiga ba, Fitowa yayi daga motar cikin mamaki yace "lafiya my Dila, kince zakisha icecream gashi kuma Nazo akan lokaci shine zaki b'ata rai so kike wannan kwalliyar ta b'aci ne?"
Fadila cikin shagwab'a tace "meyasa baka tambayi Amrah ba kuma kasan da ita zamuje"
Kamal rike kunnenshi yayi da hannayenshi yace "Am sorry yayar Kanwarta"
Dariya tayi tace "gashima tafito"
Juyawa yayi ya kalli Amrah wacce ta had'a rai kamar tana zuwa, Jikinta sanye da bakar dogon riga tasa jan hijabi bakinta tashafa mishi jambaki Ja sai Jan flat shoe datasa a kafarta ta rataya Jan jaka karami a left hand side nata, ba karya tayi kyau kuma kamarsu tafito sosai da Fadila, Tana zuwa ta kalli Kamal sau d'aya ta d'auke kai kamar batason magana tace "Yaya Kamal lafiya kuka tsaya kaida Amaryarka kuna kallona kamar kun samu talabijin?"
Kamal tsaki yaja cikin wasa yace "Allah ya kiyaye mu tsaya kallon me karamin baki da manyan Ido"
"Shiyasa naga kun zubamin ido ai"
Cewar Amrah
Fadila tana jinsu tayi shiru domin inda sabo tariga tasaba da halin Nasu, bud'e motar sukayi dukansu suka shige, basu tsaya ako inaba sai wurin shan ice cream na Imburu garden, wurin ya k'ayatu sosai akwai sanyin ni'ima na bishiyoyi masu kamshi ga grass karpet dake gefe shima yasha gyara, Kamal ne yajawo musu kujera yace "kowa ya zauna"
Zama sukayi gaba d'ayansu aka kawo musu ice cream a tsakiyar kujera aka aje musu, Amrah wayarta taciro tana kallon hotunan kawayenta dariya wasun suka sata wasun kuma suka birgeta, Kamal d'ibo ice cream yayi a cokalin yakai bakin ido tazuba mishi tana kallon cikin idonshi cikin so da kauna, daidai lokacin Amrah ta d'ago kai zata nunawa Fadila wani hoton daya sata dariya ganinsu a haka yasata sunkuyar da kanta taci gaba da danna wayarta, Fadila bud'i bakinta tayi Kamal yasa mata ice cream d'in a hankali yake bata saida yayi rabi kafin ta kawar da kanta, karb'an spoon d'in tayi ta d'ibo tanufi bakinshi, bud'e bakinshi yayi tayi sama tasa mishi a saman hanci da gefen kumatunshi, Dariya tafara tana nunashi, Kamal Ciro wayanshi yayi yana kallon fuskarshi ganin yanda ta b'ata mishi yasashi d'ibowa shima yanaso yashafa mata, ihu tayi tafara kokarin gudu, Binta yafarayi shima suna zagaye wurin, Amrah danna wayarta kawai takeyi tanashan ice cream d'in a hankali, Fadila ce tazo da gudu ta b'uya a bayan Amrah Kamal ma da gudu yazo da ice cream a hannunshi, Daidai fuskar Fadila ya nufa dashi saita tura Amrah ice cream d'in ya b'atawa Amrah fuska, Turo baki tayi tace "ni banyi komai ba gashi kun b'atamin fuska"
Dariya Fadila tafarayi tana nunasu, waya taciro tafara d'aukansu photo, Itama shiga tayi sukayi selfie Kamal da Amrah suna tsaye a bayanta suna dariya itama tana dariya sukayi tayin hoto har suka gaji, saida yamma tayi likis Kafin ya maidasu Gida, suna fita a motar Amrah tace "Yaya Kamal anjima zansa hotunan duka a status"
Kamal tab'e baki yayi yace "ina ruwana"
Murgud'a mishi baki tayi ta wuce cikin Gida.
_jiddah ce....✍️_
08144818849
[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸
*KNAWATA*
🌸🌸🌸🌸🌸
Na
Jiddah S Mapi
*Chapter 6*
~Fadila kallonshi tayi takai bakinta daidai kunnenshi tace "ina sonka Yaya Kamal, kayi mafarkina"
Tana fad'an haka tashiga Gida da gudu, Kamal murmushi yayi yanajin soyayyarta tana raza jini da b'argon shi, daidai zata shiga gida yace "nima kiyi mafarkina"
Juyawa tayi ta sakar mishi murmushi kafin ta wuce gida tana cikin farin ciki,
Mama ce zaune a cikin gida tanacin Abinci had'a rai tayi data gansu, Fadila ce tad'an tab'a Amrah, Amrah kallonta tayi da ido tayi mata alamar suyiwa mama magana, Karasawa wurin mama sukayi, suna zuwa sukace "mama mun dawo"
Kallonsu tayi d'aya bayan d'aya tace "ai na ganku, kunyi daidai da kuka kai mangariba kuma babanku zai dawo sai kun fad'a mishi a ina kuka tsaya"
Fadila ce ta waro ido tace "Dan Allah mama kirufa mana Asiri nice na tsayar damu ita Amrah tin karfe Uku tace mudawo nikuma naki"
Amrah juyawa tayi tana kallonta jin karyan data zabga, ido ta kashe mata alamar tayi shiru, Amrah shirun tayi, Mama tace "Tinda ke kikasa Ku yin dare saiki tashi kiyi wanke wanke da shara ki goge varanda sannan ki wanke bayan gida ki d'aura ruwan zafin flask"
Fadila tace "to Mama"
Amrah tashi tayi ta shige d'aki tana chatting har Fadila tagama aikin" tana zuwa ta kwanta akan gado gefen Amrah tace "nima bari nabud'e Data na"
Amrah batace komai ba, Fadila tana bud'e Data taga Amrah tazuba status, bud'ewa tayi tana murmushi hoton data d'aukesu da Kamal shi tasa with my abokin fad'a, Murmushi Fadila takumayi tayi mata reply da "kunyi kyau"
Amrah bud'e message d'in tayi sai a lokacin ta tunada batasa nasu da Fadila ba, Dafe kirji tayi dasauri ta d'aura nata da Fadila da Kamal tarubuta "With my partners"
Fadila data bud'e tayi dariya kawai batayi reply ba.
"Washe gari bayan Amrah tadawo daga makaranta Fadila tace mata suje gidan Unty Sadiya, Amrah dama tanason yawo, shiri sukayi kowa da kalar kayanta Fadila yellow Amrah blue, Sallama sukayiwa Mama kafin suka tafi, Taku suke akan hanya cikin nitsuwa suna fira, Wasu samarai guda biyune suka fara biyosu "yammata jimana"
Amrah tace "Adda idan bamu tsaya bafa samaran nan bazasu daina binmu ba, gara mu tsaya mu sallamesu"
Fadila tsayawa tayi cak tace "Amma kinsan Kamal bazai yadda in rika tsayawa da maza bako? Sabida yanada kishi sosai"
Amrah tace "to ai rashin tsayawar yanzu shizai sa suyita binmu harya gansu"
Daidai lokacin samaran suka iso"
"Yammata Dan Allah numbarki zaki taimaka mana dashi"
Suka fad'a suna kallon Fadila, Fadila wayarta taciro tabasu numbar suka juya zasu tafi sai Amrah tajiyo d'ayan yana cewa "ka karb'i na kanwartan mana, bazata hanaba"
Shikuma yace "kai wallahi batamin ba kwata kwata"
'Dayan yace "Ammafa kyakkyawa ce"
Shima yace "to nikuma duk kyaunta bata shiga raina ba, hasalima tsoro tsoro take bani"
Amrah jin haka taji numfashinta yafara yankewa, Fadila tana jinsu amma ta share don bataso Kanwarta taji batasanma Amrah taji ba,
Amrah kallon samaran tayi taga sun tafi, juyawa tayi tafara gudu idanunta suna zubar da hawaye, tana gudu tana gogewa da gefen hijabinta l, masu mota sai horn sukeyi mata amma Sam bata jinsu burinta kawai taganta a gida, Fadila ganin Amrah tana gudu itama tafara binta tana kiran "Amrah!!! Amrah!!! Ki tsaya"
Amrah sai kara gudu takeyi batako juyawa saida tagaji ta kwanta a karkashin wani bishiya tana kuka me ratsa zuciya, Fadila ma da kyar ta iso wurin tana haki domin ta gaji, riko hannun Amrah tayi tace "bakida hankaline Amrah? Yanzu idan mota ya bugeki fa, ya kikeson nayi da rayuwata? Dan Allah kidaina irin wannan kidaina biyewa samaran nan baki gansu zubin 'yan kwaya bane? Nifa nabasu number ne domin murabu cikin sauki suna kirana zansa a black list, ki share hawayenki ki daina biyewa mutane shi Aure lokacine idan kinga bakiyi ba to lokacinkine baizo ba, yanda kikasan markad'e haka yake, idan layinki baizo ba babu Wanda zaiyi miki, watama tana iya yin Aure da Wanda bata saniba, wasu babu soyayya zakiga sunyi Aure, kicire abinnan a ranki shi soyayya a waje bashine Aure ba, mutane nawa suke soyayya kusan shekara uku basuyi aureba sai kiga wasu sun had'u sati Uku sunyi Aure, please banason ganinki cikin damuwa kinji?"
"Adda Yaya zanyi ne? Kinajin abinda Inna Falmata tafad'a jiya yau kuma nagani da idon, Yaya zanyi da rayuwata idan kikayi Aure na tabbata zan daina fita sabida tsangwama da Neman tsokana da habaici da zasu rinka yimin"
Hawayen idonta ta goge tace "Aa nasanma kafin nagama makaranta zan samu me sona Wanda zaijini a cikin zuciyarshi, Adda kice Ameen"
Fadila hawayen tausayi ta share cikin muryan kuka tace "Ameen Kanwata"
Tashi Amrah tayi ta karkad'e riganta tace "muje"
Itama Fadila mikewa tayi suka kama hanyar gidan Unty Sadiya, shiru sukayi kowa yana sake sake a ranshi,
Har suka iso gidan.
"Unty Sadiyace zaune a gefen mijinta suna hira, Tana bashi labari sai dariya yakeyi, Sallamar su Fadila ce ya katsesu, Cikin jin dad'in ganinsu ta mike ta rungumesu dukkansu, tace "yau Ashe inada Manyan baki"
Fadila tayi dariya tace "kwarai kuwa unty Sadiya tace "ya naga Amrah kamar tayi kuka?"
Amrah d'auke kanta tayi don bataso