Showing 114001 words to 117000 words out of 139192 words

Chapter 39 - Kanwata Book One Complete Hausa Novel

Jiddah   

27 Sep 2025

867

kasance suna neman mata nikuma banayin hakan dan aganina neman mata zai janyomin raini nikuma banason raini, Kabir ne watarana suka bani kwaya acikin Drinks ban saniba nasha suka ɗaukeni a mota suka kaini wani layi wai dan duk in fara neman mata, su aganinsu hakan shine hutu dajin daɗi, ana hadari ina tafiya a titi ban saniba ruwa ya sakko da sauri naje wani kango na zauna, lokacin da Kabir yazo da mota danya ɗaukeni kuma ni nabar wurin, a ranar nayi abinda banaso ina tunawa, wata karamar yarinya nagani tana gudu acikin ruwa da omo a hannunta alamar aikanta akayi, da sauri na tashi naje nariko hannunta, tana ihu na toshe bakinta nashigar da ita cikin kangon, yarinyar tana cemin Yaya kayi hakuri amma bana cikin hayyacina saida nayi mata fyaɗe kafin nadawo hankalina, Fadila? Nayi kuka aranar nayi dana sani, na rasa yacce zanyi da yarinyar danaga bata ko motsi,

Motar Kabir nagani nafara ɗaga mishi hannu, yana ganina yayi parking yana dariya harda rike ciki yace "gaye yasha ruwa an faɗa maka ka rinƙa shan iska a duniya kaki yadda yau gashi munyi maganinka"

A lokacin ina cikin ruɗu bakina yana rawa na nuna mishi kangon nace "tana can"

Kabir yace "wace?"

Hannunshi na janyo nakaishi wurin yarinyar, salati Kabir yayi yace "me kayi mata?"

Ina kuka nace "fyaɗe"

Kabir cikin tashin hankali ya ɗauki yarinyar yakaita asibiti, kasancewar ana tsoronmu sosai hakan yasa babu wanda ya tambiyi meya faru da ita har aka gama treating ɗinta, saida tayi kwana biyu muna dubata muna bata abinci kafin tadawo hayyacinta abin mamaki tana tashi tacemin "yaya? Me nayi maka?"

Kuka nafashe dashi na rungumeta itama tana kuka tace "na yafe ka"

Kabir ne yafitar dani ya ɗauketa yakaita unguwarsu, daga wannan rana kullum saina zauna a wurin kangon naga ko zatazo ta wuce amma ina ban kara ganinta ba, sai watarana na ganta amma dawata a gefenta, hakan yasa nayita bin bayansu harna samo gidansu, Wani abokina muna cemishi K.M nasashi wani babban aiki nace yarinka bibiyan yarinyar duk inda zataje kada yabari ko wani saurayi ya raɓeta harta girma ni zan aureta sabida abinda nayi mata, saide kinsan me? Bayan nagama makaranta nazo gida nasanarwa iyayena zan auri wata a yola sukace ba komai sun yadda indai tanada hankali,  haka kullum muke waya da M.K yana bani information har muka kai shekara shida, number ɗin Km ya ɓatamin bayan yacemin yarinyar sun kaura kuma baisan inda suka koma ba, amma yayimin alkawarin bazai taɓa barin wani saurayi ya raɓeta ba, naje yola dan samun K.M amma ban sameshi ba, gashi soyayyar yarinyar kullum sai azalzalata yake"

Fadila cikin kuka tace "to ya sunanta?"

Abdul yace "Ban sani ba"

Fadila tace "kanada hotonta?"

Abdul yace "Aa hoton lokacin datake tafiya kawai nake dashi"

Wayarshi ya ɗauko yashiga security ya nuna mata hoton wata yarinya tana tafiya kallon hoton tayi sosai amma takasa ganin fuskar gabanta ne yayi mugun faɗuwa ganin hoton, Abdul karɓan wayar yayi yace "yanzu nasan duk inda K.M yake to zai hana kowa zuwa wurinta ita batayi aure ba amma ni nayi na cuci rayuwar yara mata har guda biyu dolene sakayya ya bini"

Fadila tace "nima na tausaya maka amma kasani nima ta sanadiyyar kanwarka na rasa virginity ɗina"

Abdul yace "as how?"

Nan Fadila ta zauna ta zayyana mishi abinda yafaru dasu cikin kuka, Abdul ma kuka yake ya rungume Fadila yace "meyasa baki taɓa faɗan hakan ba?"

Fadila tace "sabida banaso ina tuna baya"

Abdul yace "me sunan wanda ya ɗaukeku kikace?"

Fadila tace "sunanshi Guyson, na tsaneshi na tsane sunan daya fara da kalmar G"

Abdul yace "to kince yace muku saida dalili yake ɗauke mutum ku wani dalilin yasa ya ɗaukeku dake da Baby?"

Fadila tace "wallahi ban saniba muguntane kawai"

Abdul shafa kanta yake a hankali yace "kiyi hakuri insha Allah, Allah zaibi muku hakkinku"

Fadila tana kuka tace "yanzu ya zakayi da yarinyar daka ɓatawa rayuwa?"

Abdul ya share hawaye shima yace "Ban saniba zanje Yola na nemeta duk inda take, amma bazan iya manta kamanninta ba koda ko ta girma ne dan kullum sai nayi mafarki da ita"

Fadila tayi shiru ta lafe a jikinshi yaji daɗin hakan dan shima zaiso yajishi ajikin mutum a irin wannan lokacin.

Jiddah Ce

08144818849

[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸

    *ƘANWATA*

🌸🌸🌸🌸🌸

    Na

Jiddah S Mapi

*Chapter 74*

         ~Numfashi Fadila taja tace "to idan Ka sameta ni ya zakayi dani Mr Abdul?"

Abdul yace "gaskiya bazan ɓoye miki ba Fadila nafison ta hasalima zan iya rabuwa da kowa dan nazauna da ita"

Wani turkusun bakin cikine ya kamata jin abinda yace haka kawai taji kishi from no where yana taso mata, cireta yayi daga jikinshi yace "jekiyi wanka"

Kamar jira take yayi magana ta shi fuu ta tafi, kallonta yayi da mamaki shima yatashi yashiga toilet ɗinshi.

          "Kamal? Kadainamin wannan tambayar nasha faɗa makahakan amma bakajina sam"

Kamal daya zubawa Umman shi ido yace "Umma idan ban tambiyeki ina dangin mahaifina suke ba, wa kikeso na tambaya?"

Umma ranta a ɓace tace "ka dainamin wannan tambayar nace"

Kamal shima a tsawace yace "dolene nayi miki wannan tambayar, suwaye dangin mahaifina?"

Umma tashi tayi tafita mishi a ɗakin tace "tom sai kayi da jikin bangon ko zai baka amsa"

Kamal yace "idan bazaki faɗamin ba zan nemosu da kaina"

Umma batace komai ba tawuce ta tafi,

Kamal watsi yafarayi da kayan ɗakinshi, saida ya ɓata komai kafin yaɗau makullin mota ya fita idan ka ganshi duk ya rame sai hasken dayayi sosai gashin kanshi sun kara yawa amma baya gyarawa ɓacin rai yake shiga bana wasa ba, da mugun speed yaja motar bai tsaya ko inaba sai cikin wani babban hotel, waya yakira yace "nashigo"

Receiption yaje aka bashi ɗaki da makulli room 104  waya yakara kira yace "ina room 104"

Yana shiga ya cire picap ɗin kanshi ya faɗa kan gado damuwan daniya sun taru sunyi mishi yawa murza goshinshi yake yanajin zafi acikin kirjinshi"

Knocking kofar akayi da sauri yatashi ya buɗe kofar, wani ne jikinshi sanye da bakin kaya fuskarshi rufe da face mask baƙi, ga kanshi dayasa picap baki, gaba ɗaya idan ka ganshi bazaka ganeshi ba, da sauri Kamal ya riko hannunshi ya janyo shi ciki, rufe kofar yayi yace "cire face mask ɗinnan zamuyi magana"

Cire face mask ɗin yayi naga Guyson yana murmushi ya mikawa Kamal hannu,

Kamal yace "ba lokacin gaisuwa bane Guyson ka duba yanda na lalace damuwa da soyayya duk sun addabi rayuwata ina zansa kaina da Soyayyar Fadila? Gashi inajin son cikin jikin Amrah from no where, kasa nayiwa Abokina Abdul karya nace mishi sun kaura nikuma na karya Sim ɗina jna ganinshi ranar dayazo garinnan yana nemana akace mishi bama nan, Ya yadda dani shiyasa yace na duba yarinyar nan, nahana kowa zuwa wurinta gashi yanzu reshe ya juye da mujiya gashi abun akaina yake dawowa"

Guyson wani murmushi yayi yakalli Kamal sosai sannan yace "nima ai abokin naka ne? Sannan kasan Abinda Abdul yayimin a rayuwa nabashi auren ƘANWATA amma ya wulakantani ranar da aka kashesu na kirashi ya kashemin waya hakan baya rasa nasaba da yanada hannu a mutuwarsu inaso in kuntatawa rayuwarshi, wannan kanwar tashi Baby nice nayi sanadiyyar saceta nayi dana sanin barinta a raye danayi dana sani da kasheta nayi yaji kwatankwacin zafin danaji a rayuwata, sannan na raba abota da Abdul na tsaneshi kuma har yanzu bazan daina bibiyar rayuwarshi ba"

Kamal yace "wannan ku ta shafa nikam babu ruwana na cire hannuna a wannan maganar ku barni da abinda yake damuna"

Guyson yace "Come On Dude ya kake sarewa da wuri ne? To yanzu ita Fadilar ka aureta mana"

Kamal yace "to basai idan tana nan zan aureta ba? Rayuwa ta canja kaddara ta sauya nariga na auri Kanwarta gashi naci amanan Abokina gaskiya na raba hannu dakai daga yau"

Guyson yace "kana ɗaya daga cikin waɗan da bazan manta dasu ba a rayuwata ma'ana waɗanda suka taimakawa rayuwata nagode sosai banida hanyar taimaka maka dana taimaka, amma zanci gaba dayi maka addu'a Allah ya kawo sauki cikin lamuranka"

Kamal da hawaye yacika idonshi baisan lokacin daya rungumi Guyson yafara kuka ba, Guyson bubbuga bayanshi yayi yace "be a man kada ka rinka kuka yana raunana zuciya kaji?"

Kamal yace "nagode Allah ya haɗamu a haske"

Guyson wani bakin jaka ya ciro yamikawa Kamal yace "ga wannan nasan kanada kuɗi amma wannan kyauta ce daga gareni"

Kamal karɓa yayi ya buɗe wasu diamonds farare yagani da sauri ya cire ɗaya ya ɗaga sama yana kallo, ganin original ne yasa yace "ina kasamu diamonds haka?"

Guyson yace "A sudan nasamu sauran nakai bank a ɓoyemin"

Kamal yace "nagode amma yakamata kayi aure kodan ka rage damuwan dayake cikin zuciyarka"

Guyson hawaye ya share yace "bazanyi aure yanzu ba saina samu yarinyar dazan maidata kamar kwai ni zan zama driver ɗinta nizan rika bata abinci abaki bazanyi nesa da itaba balle har asamu daman kasheta"

Kamal yace "ba komai Allah yabaka"

Guyson yace "Ameen nagode Dude Allah ya haɗamu a haske"

Nan sukayi musabiha sannan kowa yafita daga hotel ɗin amma sun raba hanya dan Guyson fuskarshi a rufe.

  

          "Me martaba ne yakira Kabir yace "Kabir kanada niyyan yin aure acikin wannan shekaran?"

Kabir cikin jin kunya yace "eh Abba"

Me martaba dariya yayi kaɗan yace "to yanzu mukayi waya da Alhaji yace yayi maka ginin gida a Abuja kaje ranar Monday mukuma zamuje ranar Alhamis sai ayi maganar aurenka ko?"

Gaban Kabir ne ya faɗi da sauri yace "wa zan aura?"

Me martaba yace "sunanta Nabila wai ko me?"

Kabir yace "Abba banason wannan Nabilar"

"To wa kakeso?"

Kabir shiru yayi, Abba yace "Alhaji yariga yayiwa Baban yarinyar magana kayi hakuri Kabir nima banso ka auri wacce bakaso ba to amma ya za'ayi mutuminnan yayimin abinda baka zato a rayuwata kayi mishi biyayya kaji?"

Kabir badan yaso ba yace "to Abba" nan yatashi ranshi a jagule yabar gidan ma gaba ɗaya,

Cikin mota yashiga ya zauna yunanin Fadila yana hanashi sakat a rayuwarshi yarasa me yasa,shi sam bayason Nabila ɗinnan.

          "Amrah yau cikinta yakama wata shida saura wata biyu ta haihu da yaddan Allah, bakin ciki da damuwa sai karuwa suke a zuciyarta ta wurin kuɗi kuma tana kan tarawa kuma Allah yana sa mata albarka, asusu ta nemo babba tana zuba kuɗinta aciki,Kaka tana yawan bata kyauta koda zani aka bata bata ɗaurawa saita siyar tasa kuɗin a asusu dan ta kudiri aniyar tana haihuwa zata kwashe kuɗin tarabawa ƴan jarida da gidajen redio su nema mata ƴan uwanta, Baba Kulu sai wanka take ɗauka tana canja kayeki idan ka ganta zakace asali agidan take harma tafi Ruky zakewa dan da Ruky taga Kulu tafi karfinta atake ta dawo wurin kulu tana shige mata, kulu kuwa abin nema yasamu shawara take bata kullum na ɗaukan wanka da kwalliya kala kala, Wani lokacin Amrah tana jinsu amma batasa baki, wani lokacin kuma tanaɗan sa baki kaɗan, duk tazama shiru shiru bata yawan magana, musamman idan Ahmad yana wuri saita zauna kamar kurma, shikuma yayita zabga mata harara kenan, Umar ya shiryu yana baiwa Amrah girma sosai wani lokaci yana zuwa kitchen ya sameta suyita hira har tambayanta yake meyasa yanzu basa wani magana da Yayanshi, Amrah shiru tayi sannan tace "ba komai Umar kawai de ɗan faɗane wanda ba'a rasawa"

Dariya Umar yayi yace "Unty Amrah idan kika auri yaya nima zanyi aure vary soon dan a mugun takure nake"

Amrah datake wanke plate da sauri tasa hannu ta rufe bakinta dan maganar yabata kunya sosai shikuma Umar ko ajikinshi, hira sukeyi sosai Kwanon tace taliya Amrah take wankewa bata ankara ba taji ya tsaga mata hannu, ɗan kara tayi tana yarfa hannu, da sauri Umar ya diro daga kan drawer yace "sannu Unty mugani"

Mika mishi hannun tayi da sauri ya ɗauko kyalle yafara ɗaure wurin da jini yake zuba, tsunkuyawa yayi yana ɗaurewa tareda hura mata iska a hannun, Ahmad ne yashigo kitchen ɗin hannunshi rikeda cup ɗin kunun Kaka, da sauri ya koma baya ganinsu ahaka yasa yaji kirjinshi ya buga baice komai ba ya ajiye cup ɗin abakin kofa sannan ya juya ya koma ɗakinshi, Umar saida ya ɗaure mata yace "sorry Unty kawo nagama ki kaiwa yaya breakfast ɗinshi na manta ashe yafaɗamin tsabar hira na manta"

Amrah tashi tayi tace "kabari idan nazo zan gama"

Wankewa yafara tana dariya taɗau breakfast ɗin tayi hanyar ɗakin Ahmad, sallama tayi sau uku ba'a amsa ba, Shiga tayi ta ajiye plate ɗin zata fita taga Ashema yana cikin ɗakin ya rungume hannunshi a kirji yana zirga zirga a ɗakin, Amrah tace "ashe kana na kuma kana jina baka amsa ba koba komai ai amsa sallama Farilla ne"

Da wani irin matsifa ya juyo yace "ke kinsan farilla ne dama? Ban san na ɗauko annoba da kaina na kawo gida ba sai yau, haba Amrah Umar fa yaro ne be kamata ki ɓata mishi rayuwa ba"

"Enough" cewar Amrah data ɗaga mishi hannu, atake bakinta da jikinta suka fara rawa tace "Mr Ahmad kada bakinka yakara furta wannan kalmar akaina dan niba yanda kake zato bane"

Ahmad ma ranshi a ɓace yace "da idona fa nake ganinku yazaki rainamin hankali..."

"Dan Allah ya isa, ya isa haka nace!!! Bakinka ya sari guntun kashi, ai dama hausawa sunce me hankali shike gane furfurar farar tinkiya, mara hankali bazai taɓa ganewa ba"

Juyawa tayi zata tafi ya riko hannunta ya juyo da ita da karfi, Kwace hannunta tayi tace "How dare you? Ni matarka ce? Dazaka rikemin hannu"

Ahmad dariyan rainin hankali yayi yace "oh sorry Baby bakiso na rikeki ta wannan sigan bako? Saide kash am sorry niba Mr Romantic bane saikin koyar dani yanda naga kina koyar da Umar bro"

Wani wawan mari Amrah ta sauke mishi a fuska, rike kunci yayi yana dariya yace "kinci zafi ne? To haka nima nakeji idan naganki da Kanina please get out"

Yafaɗa yana nuna mata hanya, Amrah buɗe baki tayi zatayi magana yace "i say get out"

Fita tayi tsabar ɓacin rai yasa zuciyarta ya bushe hawaye ma kin fitowa sukayi sai a lokacin tasan cewa fitar hawaye ma rahama ne, Minal ce tazo da gudu ta rungume ta tace "Momy tin ɗazu nake nemanki kibani tea yunwa nakeji Kaka batada lafiya"

Amrah hannu tasa ta janye yarinyar daga jikinta tana kallon hanya tana tafiya ko kallon Minal ɗin batayi ba, Minal takara zuwa da gudu ta rungumeta tace "Momy inajin yunwa fa"

Da karfi ta janyeta sannan ta wullata kasa da karfi tace "zanci ubanki idan kika kara taɓamin jiki kije ubanku yabaki mana nifa karuwace kuje me tsabta ya baku"

Kaka data fito daga ɗaki tace "lafiyanki ƴannan? Me tayi miki kika wullata kasa haka? Kodan kinga inayi miki dariyane?"

Amrah batace komai ba ta wuce ɗakin da aka saukesu tana shiga ta au key ta kulle ta kashe wutan ɗakin gaba ɗaya sannan ta hau gado ta cusa kanta cikin filo tunano rayuwarta take so take kawai tayi kuka koda kaɗan ne amma ina kuka yaki zuwa, kulu ce tazo tana buga kofa tareda kiran sunan Amrah Amma Amrah tayi banza da ita, Kaka ma tazo tana kiranta dasu Umar dasu Bilal da Minal duk babu wanda tayi mishi magana, kirjinta tarike tanajin kamar zai fito, bata anakara ba tafarajin amai tanayi tana jin zafin a kirjinta, saida taga zata hallaka yasa ta mike ta kunna wuta, jini tagani dayawa a jikinta wanda ta amayar.

*Jiddah Ce...✍️*

08144818849

[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸

    *ƘANWATA*

🌸🌸🌸🌸🌸

    Na

Jiddah S Mapi

*Chapter 75*

         ~Amrah dan Allah ki buɗe ɗakinnan kada ki halaka kanki"

Amrah data zubawa jikinta ido a hankali hawaye yafara bin kuncinta aman jini?

Saida tayi kuka kafin ta tashi jiki a sanyaye ta buɗe ɗakin, Da sauri Kulu ta rungumeta tace "lafiyanki dai ko?"

Amrah shiru tayi ta lafe ajikin Kulu, ɗagota Kulu tayi tana kallon jikinta ganin jini yasa jikinta yana rawa tace "meya sameki?" duk tabi ta ruɗe kaka ma matsowa tayi tace "lafiyanki?"

Minal data rakuɓe agefe ta leko Amrah tace "sannu Momy"

Amrah ko kallonsu batayi ba tasaki Kulu sannan ta koma ɗaki, Kulu ce ta bita ta wanke mata jikinta tareda bata magani ta kwanta, Umar daya dawo yaji labarin Amrah ba lafiya, duk yaji ba daɗi, ɗakinta yaje yazauna a gefenta yace "Unty meya sameki?"

Amrah batayi magana ba tayi mishi murmushi kawai, ɗago kai tayi ta hango Ahmad yana laɓe a bakin kofa, Amrah ganin haka ya mugun ɓata mata rai taji zafi sosai kuma ao take ta baiwa Ahmad ɗinma haushi a hankali tacewa Umar "Come closer"

Umar yace "na'am"

Da sauri tace "come closer i said"

da mamaki ya matso wurinta a hankali tace "ka ɗaukomin magani a cikin drawer, da sauri Ahmad ya matsa ganinsu kusa kusa yasa ya tabbatar da zarginshi zuciyarshi har wani zafi take, Amrah ganin ya tafi yasa taɗanji daɗi a ranta koba komai shima zaiji zafi kamar yacce yasata taji, Umar tana kawo mata yace "Unty Allah yakawo sauki nikam zanje ɗaki"

Amrah tace "To Umar nagode".

             "Kabir ranar Monday yafara shirin tafiya Abuja gaba ɗaya ya haɗe fuska baya dariya, me martaba ne yace "Kabir bakason tafiya ne?"

Turo baki Kabir yayi yace "to ni nafaɗa ne?"

Me martaba dariya yayi kaɗan yasan halin Kabir idan baiso abu ba to haka yakeyi saide yayita tura baki yana gunguni, Yace "Haba Yarima me jiran gado kayi hakuri kayi wannan tafiyar na tabbata ze ɗebe maka kewa sosai musamman idan kayi aure"

Kabir yace "ai bazanso najira gadon ba sabida nasan kasheni zasuyi idan sukaga nahau kujerar sarki, shiyasa kullum nake addu'ar ubangiji yakaraa maka nisan kwana"

Me martaba shiru yayi, gaba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login