Showing 105001 words to 108000 words out of 139192 words
tata, "Allah ka shiryamin yayata koda me takeyi bazan iya daina sonta ba wannan soyayar a jini take".
Jiddah Ce
08144818849
[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: *ƘANWATA*
🌸🌸🌸🌸🌸
Na
Jiddah S Mapi
*Chapter 68*
~Abdul ne yashiga ɗakin Fadila ganin bata cikin falo yasa yakarasa Bedroom ganin batanan yasashi zama a bakin gado yana jiran shigowarta, Hannunshi rikeda kwalin waya me kyau kirar i phone11pro surprise yakeso yayi mata dan yasan zataji daɗi kuma zata rage tunani dukda tanada wayar amma yasan wannan tafi na hannunta tsada, Fadila wanka take acikin toilet sai nurza sabulai masu kamshi take ajikinta tana kwance acikin bathtube ɗin, tunani take hankalinta kwance, saida tagaji sannan ta kunna shower yafara sauka a jikinta dakuma kanta, bayan tagama wankan ta ɗauko wata karamar towel wanda ya tsaya daidai cinyarta sannan duk rabin kirjinta a waje, kanta a jike bata goge ba ta, murɗa handle tayi tafice zuwa Bedroom ɗinta, tanaɗan waka kaɗan kaɗan tana yarfa gashin kanta ruwan yana ɗiga zuwa kasa, hankalinta bai kai wurin gado ba ta nufi wurin Dressing mirror, zama tayi akan karamar stool ta ɗauko karamar towel goge kanta kafin ta kunna drayer tafara busar da kanta, saida tagama sannan ta kurawa gashinta ido cikin madubin ɗan turo baki tayi tace "ɓingel fulbe amma gashinta yake karyewa haka? Jibi yanda gashina yatafi wayyo Allah"
Mai ta ɗakko tafara shafawa a hankali saida tashafe duk jikinta sannan ta feshe turare, tamike tana kallon jikinta kara turo baki tayi tace "jibi yanda na rame?" tsaki taɗan ja kafin ta juya zuwa wurin wardrobe kaya taciro wani simple gown tana kokarin sawa taɗan juya tana kallon mirror ido huɗu sukayi da Abdul wanda yayi suman zaune, kallonta yake da idonshi daya fara canja kala, ihu Fadila tayi tabuɗe wardrobe ɗin tana kokarin shiga ta rike towel ɗin gam, Abdul firgigit yadawo hayyacinshi yace "sorry" tashi yayi yafice ita kuma Fadila sai kakkare jikinta take idonta a rufe batasan yafita ba tace "dan Allah kafita, dan Allah" ɗan buɗe idonta tayi jin shiru taga bayanan, ajiyar zuciya ta sauke tana dafe da kirji,
Abdul kuma yana fita yayi hanyar ɗakinshi direct bedroom yawuce yafaɗa kan gado zuciyarshi tana bugawa da sauri sauri ganin suranta yasa yafita daga hayyacinshi hakan ya tuna mishi da abubuwa dayawa a rayuwarshi, filo ya ɗauko yasa fuskarshi a ciki yana sauke numfashi da karfi, kwalin wayar ya ajiye a gefenshi gaba ɗaya rayuwarshi na baya yafara dawo mishi sabo, atake yafara ɗiban zufa jikinshi yafara rawa, hannu yakai yana kokarin kunna fanka amma yakasa, ganin haka yasa ya mirgina zuwa kasa da kyar yana jan jiki harya kunna fanka dahaka yakoma kan gado, ganin fanka bazaiyi mishi komai ba yasa ya koma ya kunna Ac, sanyi ne kuma yafara zubo mishi yanaso yatashi yakashe Ac ɗin amma yakasa, zuciyarshi ya dafe yanajin ciwo sosai, Blanket yaja ya rufe jikinshi, Zazzaɓi ne ya taso mishi me karfin gaske,
Fadila zama tayi a bakin gado tace "Allah na yaushe ya shigo? Meya shigo dashi?"
Ganin batada amsa yasa ta mike tasa rigan tareda kara fesa turare kafin ta fice zuwa kitchen, abinci ta ɗauko takaiwa Baba me gadi sannan ta dawo ciki taɗau nashi dukda tanajin kunya amma tasan zuwa yanzu yafara jin yunwa, a hankali ta buɗe kofarshi ganin baya falo yasa ta ajiye plate ɗin ta zauna tana jiran fitowarshi, minti ɗaya zuwa goma taga be fito ba, mikewa tayi tagyara ɗaurin kanta kafin tashiga bedroom ɗin haɗeda yin sallama, bai amsa ba cikin tsoro tsoro tashiga ciki, ganinshi nannaɗe cikin bargo gawani sanyi daya zagaya ɗakin yasa ta karasa kan gadon tana kiranshi "frnd!! Frnd!!"
Shiru taji ganin kamar yana bacci yasa ta rage Ac ta kashe fankan, wurinshi taje takara gyara mishi blanket ɗin, juyawa tayi zata tafi, caraf taji yariko hannunta, juyawa tayi ganin idonshi a rufe yasa ta janye zata tafi, kara riko hannunta yayi gam yaki saki, dawowa tayi ta zauna a gefenshi a hankali tasa hannunta a wuyarshi, jin zafi sosai yasa tace "meya sameka?"
Janyota yayi jikinshi ya rungumeta kem, cikin zafin ciwo yace "help me"
Fadila ta tsorata dajin muryanshi tace "lafiyanka?"
Kuka yafashe dashi yace "please help me i love her"
Wani tukukin bakin cikine ya turnike Fadila jin yana kiran wata, zame jikinta tafara ya kankameta yana kuka yace "my frnd dan Allah nasan bata mutu ba shima be mutu ba ki taimaka min bata mutu ba"
Da wannan kalmar taji yayi shiru, da mamaki ta kalleshi ganin yayi bacci yasa tace "to meyake faruwa? Wace ta mutu?"
Zame jikinta takeson yi amma yayi mata riko sosai, da kyar ta janye jikinta ta rufashi da blanket kafin ta tafi zuwa ɗakinta, waya ta ɗauko tayi dialing number ɗin datayi saving da Darlin, "hello" cewar Baby cikin muryan bacci, Fadila tace "ke tashi inaso muyi magana"
Baby tace "Uhmm kibari mana sai gobe Adda wallahi bacci nakeji da kyar fa nasamu nayi baccin saida Kabir yakirani yaɗan lallaɓani ka...." da sauri ta rufe bakinta, Fadila tace "umhum ina jinki kafin me?"
Baby data dawo zuwa hayyacinta tace "oh mafarki nakefa"
Fadila tace "anyway inaso muyi wata magana me muhimmanci kuma banaso ki ɓoyemin gaskiya sabida yanzu mun zama ɗaya"
Baby tace "tom"
Fadila tace "me yasamu Abdul ne wace da waye suka mutu da naji yana maganarsu yau kuma baya cikin hayyacinshi meya sameshi?"
Baby da sauri tacire wayar daga kunnenta takalli screen ɗin hankalinta ya tashi bakinta yana rawa tace "ba..babu komai, kidai kula dashi sosai dan Allah kada kibarshi a wannan halin ke macece kisan yanda zakiyi dan Allah kinji?"
Fadila tace "ba yanda zaki koyamin kula dashi na tambaya ba tambayarki nayj meya sameshi waya mutu?"
Baby tace "dan Allah kije wurinshi ki kula dashi a wannan halin ba'a barinshi shi kaɗai kije dan Kaunar dayake tsakaninmu dan Allah"
Fadila tace "nifa.."
Baby katseta tayi tace "idan bazakije ba ki faɗamin ni zanzo inason Yayana"
Fadila da mamaki tace "Baby dama nace miki bakyason yayanki ne?"
Baby da karfi tace "me kike jira to? Kinsan baya cikin hayyacinshi kuma kika tafi kika barshi?"
Da sauri Fadila ta kashe wayar, mamaki take sosai, a hankali jikinta a mace ta nufi ɗakin Abdul, ganin har yatashi yana rawan ɗari yasa ta karasa kan gadon, rikeshi tayi ta kwantar dashi, riko hannunta a hankali tahau gadon itama ta rufasu da blanket, matsowa tayi kusa dashi sosai ta rugumeshi ajiyar zuciya ya sauke sannan ya kankameta, bakinta takai kunnenshi tace "ba tafiya zanyi ba ɗan sassauta riƙon kaɗan"
Ɗan saketa yayi kaɗan, hannu tasa tafara shafa kanshi shiru yayi yana jinta sai hawaye dayake zuba daga idonshi, Fadila tace "ka daina kuka"
Kamar jira yake tafaɗa a hankali yasa hannu ya goge fuskarshi sannan ya kuma riketa, ita kuma Fadila tafaɗa duniyar tunani.
Jiddah Ce
08144818849
[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸
*ƘANWATA*
🌸🌸🌸🌸🌸
Na
Jiddah S Mapi
*Chapter 69*
~Ajiyar zuciya yayita saukewa cikin baccin, Fadila sai kallon fuskarshi take, sajenshi ya kwanta lub a hankali yake sauke numfashi, hannu tasa taɗan shafa fuskarshi tace "ya Allah ka kawo sauki cikin lamuranmu"
Cire hannun tayi taji ya kamo hannunta ya mayar kan fuskarshi, shiru tayi tana kallonshi daganan tagara tunanin to meyasa Baby takeyi mata tsawa? Koba komai ai ta girmeta, ɗan janye jikinta tayi tamike tabar ɗakin, ɗakinta ta nufa tace "meyake faruwa ne wace ta mutu? Kuma waye ya mutu? Tabbas saina nemo dalilin wannan damuwar da Abdul yashiga daga ganina da Towel sai rikicewa sai kuma zazzaɓi daganan sai kiran sunan wata? Tabbas akwai abinda yake ɓoye a rayuwar Abdul kuma saina nemo koda ko Baby bata faɗamin ba saina san yanda zanyi nagano gaskiya, da wannan tunanin ta kwanta bacci,
Abdul saida yayi bacci me isarshi sannan ya mike yana kallon ɗakin ɗaya bayan ɗaya, a hankali yafara tuno abinda yafaru dashi, tashi yayi jiki a sanyaye yaje wurin drawer ɗinshi makulli ya ɗauka ya buɗe drawer ɗin wani hoto ya ɗauko yana kallo yana kuka, rungume hoton yayi a kirjinshi yana fitar da hawaye, saida yayi kuka me isarshi kafin ya maida hoton yakara kulle drawer ɗin ya mike zuwa toilet, wanka yayi yasa kaya marasa nauyi sannan yaɗau wasu takaddu yanufi falo, rubutu yake yana duba files a zuciyarshi yace "ina Fadila?"
Taɓe baki yayi alamar oho, nan yaci gaba da aikinshi.
"Washe gari Amrah ce tagama shirya kayanta tsaf gefe guda kuma Kuluwa ta haɗa kayanta itama, jikin Amrah a mugun mace jitake kamar ma tafasa tafiyan dan haka kawai takejin kanta somehow, Mama datake tsaye abakin kofa ta kurawa Amrah ido ganin yanda jikinta yake amace yasa tace "Amrah zonan"
Amrah wurin Mama taje ta zauna tace "gani Mama"
Mama dafa kanta tayi tace "idan akwai abinda kikeji gameda tafiyannan to ki barshi kawai sabida ba'aso ana tafiya da shakku, duk abinda kasa a ranka idan zakayi tafiya to hakan ne zai faru"
Amrah tace "hakane Mama"
Mama tace "tashi kiyi shiri da zuciya ɗaya"
Tashi tayi suka gama shirinsu Ahmad ne yayi sallama, yagaida Mama tareda ce mata zasu tafi, Mama tace "nabaka amanansu Allah ya kiyaye hanya"
Ameen yafada, daganan Amrah ta rungume Mama tana kuka, Mama ma zuciyarta ta karye amma ta daure ta ɗago Amrah tareda ce mata "Allah ya kiyaye hanya yakuma baki ikon cika alkawarinki"
Amrah cikin kuka tace "Ameen Mama"
Nan suka shiga mota itace agaba sai kulu abaya, ɗagawa Mama hannu suke har suka bar layin, Amrah ce tace "rayuwa kuma ta canja dama haka rayuwa ke bakasan aina zaka gama taka ba, hakanne yasa akeson ka zauna lafiya da mutane domin mutane rahama ne"
Share hawayenta tayi Ahmad yana kallonta bece komai ba.
"Fadila tana cikin asibiti sai tunani take akan matsalar Abdul, "dolema nagano wannan matsalar ni ai macece kota halin yaya saina gano kuma sainayi mishi maganin matsalarshi"
Baby ce tayi parking ɗin motarta Fadila tana kallonta batayi mata magana ba saima ɗauke kai datayi kamar bata ganta ba, ɗan murmushi Baby tayi ta fito daga motar a hankali take tafiya tana kallon Fadila saida takaraso ta dafa ta tace "am sorry Adda, ina kwana?"
Fadila tashi tayi zata tafi tace "morning"
Baby rikota tayi tace "fishi kike dani?"
Fadila tace "tsawa fa kikayimin awaya to meyasa bazanyi fishi dake ba? Ni ai yayarki ce koda ranki ya ɓaci zaki iya controlling ɗin kanki"
Baby tace "hakane am sorry amma dan Allah kada ki tambayeni meya samu Yaya Abdul"
Fadila tace "Abdul fa mijina ne yanzu nafiki kusanci dashi idan ban gano matsalarshi ba waye zai gano?"
Baby ɗan murmushi tayi sannan tace "shiyasa banaso nafaɗa miki nafiso ki gano da kanki"
Daganan suka shiga ciki suka duba marasa lafiya, saida suka gama kafin Fadila taje office tayi rubuce rubuce ta manna sunayen masu duty da dare kafin ta tafi gida, tana shiga lokacin Abdul shima yashigo bata kalleshi ba tawuce ɗaki, saida tayi wanka tasa wani wando daga sama ya ɗameta daga kasa kuma pencil, wani yololon riga tasa me hannun vest rigan yana showing ɗin duk jikinta, hula tasa me adon duwatsu ajiki, turare ta fara fesawa jikinta kala kala masu kamshi, saida taɗanyi light makeup sannan ta kalli kanta a madubi, tsayawa tayi tana kara kallon kanta yanda tayi kyau saide ta bayyana tsiraici sosai, baki taɗan taɓe tace "ba komai indai zan gano wannan sirrin ai babu matsala"
Wayarta ta ɗauka sannan tanufi hanyar fita, tafiya take amma duk jikinta yana motsi, falo taje bataga Abdul ba, daganan tanufi ɗakinshi abakin kofa ta tsiya tanajin kunyan shiga da kyar dai ta daure tashiga kirjinta yanaɗan bugawa, sallama tayi taji shiru, saida tayi sau uku sannan ta buɗe kofar tashiga, ganin baya ɗakin yasa ta zauna a gefen gadon, wani game tagani ta ɗauka tana bugawa, Abdul daya gama wanka yafito yana goge kanshi da karamar towel, ganinta yasa yayi sauri zai koma da sauri itama tace "Yaya"
Cak ya tsaya amma be juyo ba, a hankali ta tashi taje wurinshi towel ɗin hanunshi ta karɓa tafara goge mishi gashin, juyo dashi tayi tanaɗan sakar mishi murmushi, mutum mutumi yazama yana kallonta da sama har kasa, Fadila ganin haka yasa taɗan juya baya, Abdul ido ya zuba mata yana kallon bayanta, kara juyowa tayi cikin shagwaɓa tace "My frnd zan iya tayaka?"
Babu bakin magana yasa yaɗan girgiza mata kai alamar "eh"
Hannunshi tariko tajashi zuwa kan stool agaban madubin tafara shafa mishi mai tana kallon yanda ya zuba mata ido tacikin madubi, iska taɗan hura mishi tace "kallon fa?"
Firgigit yaɗan dawo hankalinshi, ɗan murmushi tayi sannan taci gaba da shafa mishi man, saida ta gama sannan ta ɗauko turare ta fesa mishi tana fesawa tana zagayeshi kamar karamar yarinya, Abdul hannu yasa ya janyota tafaɗa kan cinyarshi, kallonta yake sosai, Fadila ɗan kwaɓe fuska tayi tace "sakeni"
Cakulkuli yafarayi mata dariya take tana zillewa, cikin dariya tace "please cikina zeyi ciwo"
An tsakaitawa yayi bece komai ba kuma be saketa ba, hannu tasa ta zagaye wuyarshi dashi tace "frnd?"
"Ummm"
Shine abinda yace, tanaso tayi mishi tambaya amma takasa kawai tace "shikenan"
Shima be damuba yace "umhum"
Kallonshi tayi ko zai canja amma taga har yanzu bai canja ba, a zuciyarta tace "dolema nasan meyake faruwa"
"Tashi kasa kaya"
Baice komai ba kuma be daina kallonta ba, cikin shagwaɓa ta turo baki tace "tashi kasa kaya nace"
Ido ya zuba mata sosai, a hankali ta zuba mishi ido nan taga kamar hawayene suka taru a idon nashi, da sauri ta sauka daga jikinshi tace "sorry bansan ranka zai ɓaci ba" tafiya tafara taji ya riko hannunta, bata juyoba, tashi yayi ya rungumeta ta baya yasa kanshi a wuyanta yana kallon fuskarta, hannu yasa ya zagaye cikinta dashi a hankali ya juyo da ita suna kallon madubi, ido ta zuba mishi tacikin madubi shima haka ko kiftawa bayayi, a hankali ta janye idonta, yatsanshi ɗaya yasa yafara zagaye fuskarta dashi, jikin Fadila ne yaɗan fara rawa, leko fuskarta yayi batayi zato ba taji ya sakar mata kiss a kumatu, da sauri ta juya tana kallonshi, kwace jikinta tafara shikuma ya riketa gam, da in ina tace "bari natafi saika shirya"
Yace "no Baby ba shiryani kikazo yi ba? Go ahead"
Waro ido tayi ganin yanda yake shigewa jikinta, da sauri tace "aa nikam"
Yace "saifa kinyi abinda ya kawo kin"
Fadila kokarin gudu tafara ya riketa gam, ta ɓangaren Abdul yanason ya danne damuwarshi bayaso ya nuna mata halinda yashiga sam, amma zuciyarshi sai bugawa take rayuwarshi na baya sai dawo mishi yake kawai daurewa yake yana biye mata, ɓangaren Fadila kuma tana mugun tsoron yanda yake shige mata tazo dan su ɗan saba su shaku da juna sosai yanda bazai iya ɓoye mata sirrinshi ba amma tsoro da kunya zasu hanata samun nasarawa a zuciyarta takuma cewa "i have to fight this two things tsoro dakuma kunya dan samun biyan bukatata"
Abdul sakinta yayi yace "okay zauna to na shirya"
Kamar jira take ta zauna daɓas tana kallonshi harya gama shiri cikin kananan kaya, kallonta yayi yamata signal tareda cewa "kallon fa?" ɗan kawar dakai tayi tace "bakai nake kallo ba"
Abdul yace "okay shi kike kallo?"
Tashi tayi tace "muje kaci abinci" bin bayanta yayi har zuwa dining daganan tayi serving ɗinshi, sai kallonta yake dressing ɗin ya mugun tafiya dashi musamman rigan, kallonshi tayi tace "frnd bismillah"
Firgigit yayi sannan yafara cin abincin.
Jiddah Ce
08144818849
[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸
*ƘANWATA*
🌸🌸🌸🌸🌸
Na
Jiddah S Mapi
*Chapter 70*
~Amrah sun iso Abuja lafiya, Gidansu Ahmad Babban gidane me kyaun gaske dagashi sai yaranshi guda biyu ɗaya mace ɗaya namiji sai kakarsu da kuma kaninshi babba Sai kanwarshi, shiga sukayi wurin Kakarshi suka gaidata nan tace "sune ƴan aikin?"
Ahmad yace "eh"
Kaka tace "to kafaɗa musu banaso ana taɓamin jikoki kaga Minal da Bilal yarane kanana banaso naji kukansu koda kaɗan ne"
Nan yace "nayi musu Kaka"
Kaka tace "ka karadai sanar musu ehen idan mutum yasamin jikoki kuka naci mutuncinshi na zauna"
Amrah kallon Kulu tayi itama kulu ta kalleta ɗan waro ido Amrah tayi alamar zamu iya kuwa? Kulu taɗan taɓe baki alamar ba komai, nan Ahmad yanuna musu ɗakinsu, Kanwar Ahmad tazo tayi musu bayanin komai cikin fitsara da rashin kunya yarinyar batada kunya sunanta Ruky, a yau suka fara aiki suna Ahmad ya baiwa Amrah hakuri yace suyi hakuri da halin Kaka dakuma kaninshi Umar yaron bayaji sosai, Nan sukace ba komai, da dare Umar ɗin yashigo daka ganshi zakasan bayaji ɗin da gaske dan wani banzan askine akanshi da wani wando ya sauke saman wai ass down, kallo Amrah ya tsaya yanayi sosai, Amrah saida ta tsargu tace "lafiya?" matsowa yafara yana kara kallonta tace "miye haka malam?"
Dariyan ƴan bariki yayi yace "oh Baby Doll ya da ihu haka? Kinada kyau yarinya"
Amrah ranta ne ya ɓaci tace "bakada hankali ne ko baka ganina da ci..."
Da sauri tayi shiru tinawa da idan tayi mishi rashin kunya zai faɗawa kakar tasu kuma zata iya koransu to daga lokacin kuma zancen cika alkawari ya tsaya, Umar ɗin yace "Baby Doll kina magana ina jinki"
Tsaki taja taci gaba da aikinta, dariyan ƴan bariki yayi sannan ya wuce yana waka yana kaɗa kai, Amrah da sauri taje wurin Kulu tace "anya Ahmad fa yayi mana karya dayawa be faɗa mana yanayin gidan nasu ba"
Kulu tace "shit kada kisake kisa musu ido mufa bakine kuma keba aurenshi zakiyi ba ina ruwanki da Yanayin gidansu? Muyi abinda yake gabanmu"
Amrah tace "tom"
Dahaka sukaci gaba da zama agidan Minal da Ahmad yarane masu hankali da nutsuwa daga gani uwarsu tanada halin kirki hakan yasa Amrah take son yaran, ita kuma Kaka ganin yanda Amrah taja yaran jiki itama tafara