Showing 3001 words to 6000 words out of 139192 words
/>
Shima dariya yayi yace "nima haka tin d'azu sai murna nake, kishirya anjima zamuje wurin shan ice cream"
Fadila "yawwa dama najima banje ba"
Sallama sukayi yace mata "I love you"
Itama Fadila tace "I love you too"
"Adda naji kamar kuna maganar sa rana"
Fadila kallon Amrah tayi cikin farin ciki tace "yau za'azo ayi gaisuwan Aurenmu da Kamal, ina cikin farin ciki Amrah"
Amrah dariya tayi itama cikin farin ciki tace "bari inje kasuwa anjima zan fitarda anko, sabida kawayena dayawa sunce sunaso".
_Jiddah Ce....✍️_
08144818849
[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸
*KANWATA*
🌸🌸🌸🌸🌸
Na
Jiddah S Mapi
*chapter 3*
~"aa Amrah idan kika cire anko yanzu ai zaiyi wuri kibari idan ansa date saiki cire ko?"
Amrah tace "no yau zan cire domin zamu kece raini sabida kawayena 'yan wanka ne kuma 'yan karya, kinga gara nacire musu da wurin"
Fadila tace "shikenan idan hakan zaisaki farin ciki ni ai banida matsala"
Dariya Amrah tayi tace "shiyasa nake sonki kamar yanda kema kike sona"
Dariya kawai Fadila tayi.
"Bayan mangarib saiga iyayen Kamal sunzo ansa date sati uku masu zuwa insha Allah, Fadila ce kwance a d'aki ta d'aura kanta a pillow tana tunanin Kamal, ganin tunanin bazai kareba yasata d'aukan waya ta kirashi, ringing biyu ya kashe saiga kiranshi yana shigowa, ajiyar zuciya ta sauke tanjin wani irin sonshi yanabin duk jikinta, d'aukar wayar tayi cikin sanyin muryanta tace "hello"
Kamal Wanda yake zaune a d'akin Umma ne yace "Fiancy tin d'azu nake tunaninki ji nake kamar lokacin da akasa mana yayi nisa, Wallahi ina matukar bukatarki kusa dani, sau da dama idan naje wurinki muna fira ni kad'ai nasan yanda nakeji a jikina, please fiancy ki fad'awa su Mama a rage kwanakin nan, kinji"
Ajiyar zuciya Fadila ta sauke itama yanda takejin son Kamal a zuciyarta ji takeyi kamar lokacin Aurensu yayi mata nisa, to Amma ta yaya zata fara yiwa Mama wannan maganar?
"Kinyi shiru, fiancy"
Firgigit ta dawo daga tunanin da take, cikin muryanta me sanyi tace "Kamal gobe fa yana saurin zuwa, yanzu zakaga ranar Aurenmu tazo kamar da wasa, Dan Allah ka kara hakuri sannan ka yawaita yin Azumi da fad'in astaghfurullah insha Allah zaka samu sauki, gaggawa fa aikin shaid'an ne"
Da haka sukaci gaba da firansu tana kara kwantar mishi da hankali, sai kusan karfe goma kafin suka hakura kowa yakashe wayarshi dukkanninsu sunajin soyayyar d'an uwansu a zuciyoyinsu, musamman Kamal dayake jin kamar Fadila itace rayuwarshi idan babu Fadila yana ganin shi poster ne bashida anfani, tashi yayi daga d'akin Umma ya tafi d'akinshi, kwanciya yayi tareda janyo filo ya rungume a hankali ya lumshe idonshi yanajin soyayyar Fadila yana kara shiga cikin kirjinshi,
Fadila kuwa suna gama wayar tashiga band'aki tayi Alwala, sallah raka'a biyu tayi kafin ta hau gado ta kwanta a gefen Amra wacce ta zage tun d'azu tana chatting a WhatsApp da kawayenta, suna maganar irin d'inkin da zasuyiwa zanin ankon su, Fadila ce ta wupce wayar a hannunta tana dariya ta b'oye a karkashin filo, Amrah waro manyan idanunta tayi ganin an wupce wayarta, da sauri ta tashi tana kwatan wayar a hannun Fadila, Fadila sai dariya take tana cewa "yaufa bazan baki wayarnan ba so nake muyi fira"
Amrah tana kokarin kwace wayar suka fara damben wasa Amma Fadila tafi karfinta, saida Amrah tayi laushi ta gaji da kwatan wayar yasa tace "Haba my sister nasan zaki bani, Dan Allah kiyi hakuri wallahi message d'aya zan turawa Zee sai in baki"
Fadila waro manyan idonta tayi itama tace "Amrah har yanzu baki daina Kawance da yarinyarnan ba? Kinsan fa ko Mama batason yarinyar batada kunya ko kad'an"
Amrah tace "wallahi nikama na rabu da ita shine tazo tacemin wai ta tuba ta daina bibiyar maza inyi hakuri muci gaba da kawance, shine tabani tausayi shiyasa na yadda muka koma kawance"
Fadila shiru tayi tana nazarin maganar kanwar tata, to Amma tasan Amrah bazatayi mata karya ba, "shikenan ba komai indai ta shiryu ai ba komai kici gaba da bata shawarwari ta gyara rayuwarta"
Amrah murmushi tayiwa Fadila Wanda ya bayyanar da dimple nata, itama Fadila mayar mata da murmushi tayi Tamika mata wayar cikin sakin fuska.
"Washe gari wata matace wacce suke kira da unty Sadiya (Unty Sadiya Ta d'auki Amrah da Fadila kamar kannenta wanda suka fito ciki d'aya, saidai tafi shiri da Fadila sabida hakurinta, Unty Sadiya tanada miji da yara guda biyu, Aisha da Nabil, tana garin Yola itama a unguwar Jambutu)
Itace tazo domin duba su Fadila da Amrah, ganin Unty Sadiya ba karamin murna sukayi ba domin duk lokacin datazo saita koya musu girki sannan tabasu shawarwari, itama murnar ganinsu tayi, shiga tayi suka gaisa da Mama tace "to tinda mun gaisa da mama sai kuzo muje d'akinku domin yau akwai lecture"
Mama kallonsu tayi tace "aikin kenan dama sai kuje kuji dashi"
Dariya sukayi gaba d'ayansu suka tafi d'akinsu, d'alewa gado sukayi Amrah ta saki kunnuwa ta zubawa Unty Sadiya ido tana jiran taji bayani, unty Sadiya tace "Amrah yau fa ba maganarki bace, Maganar Amare ne, sabida ita Fadila ta kusan Aure kinsan saida lectures"
Amrah had'a rai tayi tace "wallahi babu inda zani saidai a fad'i komai a idona"
Fadila ganin idan Amrah batanan kamar ran Amrahn zai b'aci yasa tace "Unty Sadiya ai Amrah ma wata rana zata zama Amarya ko?"
Dariya Unty Sadiya tayi tace "hakane to inaso Ku bud'e kunnuwanku kujini da kyau, musamman ma ke Fadila keda kike shirin shiga d'akin miji"
Gyara zama sukayi sukace "muna jinki Untyn mu"
Unty Sadiya tace "da farko zan fara yi muku bayanai akan girke girke".
*Girki*
"shi wannan girki da kukeji ana fad'a bawai ki d'ibo ruwa ki hura wuta ki dafa abinci ake nufi ba, idan ance girki ana nufin ki kwantar da hankalinki kiyi girki me dad'i Wanda duk Wanda ya d'ana Saiya tambaya wayayi girkin nan, ki kasance kin iya sarrafa abubuwa da dama da kanki, girki yana daga cikin abubuwan da yakesa miji yaji yana kara son matarshi, ya kasance kin iya girki na gargajiya da kuma na zamani, shi girki na zamani wani lokacin zaki iya kirkiran Abu da kanki kiyi kuma kiga yayi dad'i, ki kasance kin iya snacks da kuma yin drinks da kanki kamarsu (banana juice, Apple juice, Mango juice, da sauran kayan itatuwa) su wad'annan anaso yazamana kinada blander abun zaizo miki da sauki, ki kasance idan kinji ana maganar girki to kiyi kokari ki koya kuma ki gwada da haka ake kwarewa"
Sai kuma Abu na biyu, shine.
*Tsafta*
"Shi tsafta abune me girma idan kinada tsafta to komai zaizo miki da sauki, ki kasance kin iya tsaftace jikinki da kuma gidanki sai uwa uba yaranki"
Sai Abu na Uku shine.
*iya magana*
"Wallahi rashin iya magana yana kawo rashin zaman lafiya a tsakanin kawaye ma balle mata da miji, idan kazauna da wasu mutanen zakaji sun shiga zuciyarka meyake kawo hakan? Shine iya magana, wasu mutanen kuma idan kuka zauna dasu maganar dazai fito a bakinsu wane maganar dabbobi tsabar rashin iya rashin magana, an samu wani mutum a zamanin Annabi Muhammad (S A W)
Mutumin yanada rowa sosai, sai ranar yana zaune a wani wuri yanacin (Tufa) Apple kenan, wasu mutane sukazo wurin sukace kad'an mana, mutumin yarasa yanda zaiyi sai yace, ana rabawa a gidan sarki, mutanen dasukaji haka sai suka kwasa da gudu sai gidan sarki, shima ganin sun tafi yasashi wani tunani yace kai karfa suje kuma abasu da gaske, shima kawai saiya bisu da gudu, suna zuwa sarki yace me yake faruwa? Sukace wai aance ana raba Tufa a gidanka, shikuma sarki ganin yafi karfin yace ba'a rabawa sai yasa fadawa suka fara raba musu, shima wancan marowacin saida ya samu, to kunga anan ai iya maganar shine ya jawo mishi, sabida haka iya magana ba karamin gudumawa yake baiwa mutum a rayuwarshi ba".
"Sai Abu na hud'u wannan kuma sai an d'aura Aurenki kafin nafad'a miki, sabida su Amrah sun sake kunnuwa sunaji, yanzu kutashi muje kitchen akwai wasu kalolin abinci dazan koyar muku"
"Idan tayi tsami ai Nima zanji ko?"
Cewar Amrah wacce taso ayi maganar gaba d'aya a gabanta,
Unty Sadiya tayi dariya tace "Ku tashi muje nikam muyi cake da coconut rice sai coconut juice"
Mikewa sukayi duka suka shige kitchen, Amrah da wayarta ta shige kitchen d'in tana chatting nata, unty Sadiya ce tace "ba lokacin chatting bane yanzu lokacin aiki ne, mutum d'aya zan ragawa tad'au waya itace Fadila sabida Sweethert nata zai kirata maybe"
Amrah ganin komai sai ace Fadila yasa tace "dad'in abun ai nima macece kuma watarana zanyi saurayin"
Unty Sadiya cikin wasa tace "Ke ai banga samarai suna rububinki ba duk da kinfi Fadila kyau da class Amma ita hakurinta yasa tana samun maza kamar ruwan sama"
Maganar ta konawa Amrah rai jitayi bazata iya zama a kitchen d'in ba, fita tayi a fusace tana jin ranta yana kara b'aci.
_Jiddah Ce...✍️_
08144818849
[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸
*KANWATA*
🌸🌸🌸🌸🌸
Na
Jiddah S Mapi
*chapter 4*
~Amrah d'aki tafad'a ranta a b'ace, Unty Sadiya ta kona mata rai da wad'annan maganganun, duk da dai da wasa tafad'a mata Amma wani lokacin cikin wasa ake fad'awa mutum magana, runtse idonta tayi tana kara tunanin maganar Unty Sadiya (duk da kinfi Fadila kyau Amma ai tafiki farin jini)
Kenan ni banida farin jini? Meyasa maza basayimin maganar soyayya? To kodai gaskiya Unty Sadiya tafad'ane tinda nake ban tab'aji ko ganin namiji yamin magana da sunan soyayya ba, tashi tashi ta zauna ta d'auko filo ta matse a cinyarta tanason tuno me hakan yake nufi? Tana cikin tunani Fadila tashigo d'akin riko hannunta tayi tace "Dan Allah ki rabu da Unty Sadiya kinsanta da wasa ai, ita tanada yawan wasa, kuma kinsan banson ranki ya b'aci"
Amrah d'ago manyan idonta tayi ta zubawa Fadila, kallon cikin idonta takeyi batada niyar d'auke kanta, Fadila ce ta kawar da kanta ganin damuwa karara a cikin idon kanwar tata, cikin kakkausar murya Amrah tace "Fadila da gaskene banida farin jini?"
Fadila janyota tayi a jikinta tace "me kike fad'ane Amrah kanwata? Keda kike secondary school ina maganar Bakida farin jini anan?"
Amrah wacce idonta ya kada yayi ja tace "Fadila ban tab'aji wani yace yana sona ba, bakya ganin kamar gaskiya Unty Sadiya tafad'a?"
Fadila shiru tayi domin itama abun yana d'aure mata kai, ace yarinya kamar Amrah ga kyau ga ilimi ga kuma iya wanka wai babu Wanda yatab'a zuwa kofar gidansu da sunan yana sonta
"Kinyi shiru Adda"
Cewar Amrah
Fadila da muryar lallashi tace "Ai mazan suna ganin kamar kina makaranta shiyasa basa miki magana yanzu suna jira ki gama tukun"
Sai a lokacin hankalin Amrah ya kwanta d'an kwalinta ta d'aura cikin jin dad'in maganar yayar tata tace "yawwa hankalina ya kwanta muje muyi girkin"
Dariya Fadila tayi mata tace "yawwa Kanwata"
Tashi sukayi sukaje kitchen d'in suka cigaba dayin aikinsu saida Unty Sadiya taga duk sun koya kafin tayi musu sallama dasunan tafiya domin mijinta yazo d'aukanta, rakata sukayi gaba d'ayansu suka d'aga mata hannu harta tafi.
"Kamal yana kwance yaji wayarshi tayi ringing d'auka yayi baice komai ba, d'ayan b'angaren akace "KM baka gane me magana bako?"
Kamal yace "eh"
"Guyson ne"
Kamal tashi yayi akan gadon yace "guyson dama kana raye baka mutu ba?"
Dariya akayi sannan akace "dama kun zata na mutu ko? To ban mutu ba ina raye ina garin Kaduna unguwar Sarki ina sana'ar saida gold"
Kamal da yake ganin Kamar a mafarki mikewa yayi yace "guyson meyasa baka nemeni ba kabarni da tunanin ka mutu?"
Wani irin dariya me sauti guyson yayi yace "ada nayi Alkawarin bazan kara koda nemanku ba, Amma a yanzu na sauke Alkawarin, na hakura nayafewa kowa, ina so muci gaba da rayuwa kamar na da"
Ajiyar zuciya Kamal ya sauke yace "guyson banyi tsammanin zan kara jin muryanka ba, sai kuma gashi najishi kuma cikin sanyi da alamun ka sauka daga fushin da kakeyi damu, nagode daka yafe mana"
Guyson yace "ba komai KM kayi Aurene?"
Kamal yace "Aa banyi Aure ba Amma saura 3weeks in zama ango"
Guyson yace "wow congratulations, nikam yanzu yarana biyu, Amrita da Neenah"
Kamal yace "wow Ashe uwar gida takara haihuwa kai Allah yaraya mana su"
Guyson yace "Ameen, Ya harkan Kuma? Kanayine ko kuma ka daina?"
Kamal dariya yayi yace "me za'a fasa ai bazan iya dainawa ba, kaima nasan baka daina ba domin ba'a dainawa" yafad'a yana kara yin dariya.
"To ai ni dama bance zan daina ba, Kaine dai kayi gwaninta"
Dariya kamal yakarayi yace "Nima ai barazana ne"
Shima Guyson dariya yayi yace "hakane dama nasani ai"
Haka sukaci gaba da hiransu da kuma tuna lokacin yarintarsu har suka kashe wayar kowa yana jin dad'in had'uwa da d'an uwanshi.
"Yau takama litinin, Amrah ce tashirya cikin kayan Uniform tana saurin taci Abinci domin tayi latti kuma sunada test, Fadila tace "kici a hankali mana Amrah ta"
Amrah kallonta tayi ta kara d'auke kanta taci gaba da cin abincin duk da yana kona mata baki, Fadila ce ta d'auko mafuci tafara fifita mata abincin tana d'ibowa a cokali saita fura kafin ta bata a baki, Saida Amrah ta koshi kafin ta d'auko Jakarta na zuwa makaranta ta rataya a gefe tace "to Adda na tafi"
Fadila tashi tayi tace "muje na rakaki ko?"
Tafiya sukeyi suna sauri domin Amrah tayi latti sosai, Daidai bakin kwalta wata bakar mota tayi parking a gabansu, Me motarne ya sauke glass yace "yammata kuahigo na rage muku hanya"
Fadila kallonshi tayi tace "bamuda bukata malam"
Amrah ce tayi wup tace "haba Adda kina ganinfa nayi latti za'amin dukan latti idan naje kuma kice bama bukata, ai taimako ne"
Fadila jin zasu daki kanwarta yasata shiga cikin motar itama Amrah tashiga suka tafi, a hanya mutumin yace "yaya sunanki 'yanmata?"
"Sunana Amrah"
Mutumin yace "Aa bake ba shiru shirun"
Amrah shiru tayi batace komai ba sai daga baya tace "sunanta Fadila ita yayata ce kuma anyi baikonta"
Mutumin dariya yayi yace "to ai ba Aure take dashi ba ko?"
Amrah shiru tayi, yace "Ni kuma sunana Guyson ni d'an Asalin garinnan ne, ina ganin yayarki naji tashiga raina domin nutsuwarta"
Amrah tace "to Amma ai nafad'a maka anyi baikonta ko? Saika hakura ai"
Fadila tace "barshi Amrah karki gajar da bakinki domin ba yadda zaiyi ba"
Motar be tad'au shiru kowa da abunda yake sakawa a ranshi,
Daidai kofar makarantar yayi parking dukka suka fito sukayi mishi godiya, suna zuwa bakin gate sajent yace saiya yiwa Amrah dukan Latti, Fadila ce tayi ta bashi hakuri Amma Sam yaki yadda, saida taga ba zai yadda ba, tace ayi mata dukan ita abar Amrah ta wuce, Amrah dama tsoron bulala take da sauri ta karasa bayan Fadila ta b'uya, Fadila tsayawa tayi akayi mata bulala Goma lafiyayyu a bayanta, dukda zafin datake ji baisa ta nuna ba, Ana gama mata tacewa Amrah "kitafi class saikin dawo"
Amrah rungumeta tayi tace "Allah yabarmin ke Adda na"
Fadila tace "ki tafi class karkiyi missing na test kinji?"
Amrah juyawa tayi tanayi mata bye bye harta shiga class,
Fadila murmushi tayi ganin ba'a daki Amrah ba, juyawa tayi zata tafi sai taga mutumin har yanzu bai tafi ba, tsaki taja tazo ta wuceshi, fita yayi a motar yace "baiwar Allah kitaimaka ki tsaya, nifa taimakonki zanyi..."
Fadila Napep ta kama tashige ko juyawa batayi ba.
"Amrah tadawo daga makaranta tana murnar tasamu test, Fadila ce kwance akan gado tana waya da Kamal sai shagwab'a take zuba mishi wai yace zaiyi tafiya ita kuma tace babu inda zaije, kamal ne yace "to fiancy na hakura da tafiyan dama maganar office ne Amma tinda bakyaso zanyi aika kawai hakan yayi miki dad'i?"
Cikin muryar shagwab'a tace "eh har naji dad'i"
Amrah ce tashigo d'akin tafad'a kan Fadila da karfi tace "Adda Fadila yau nasamu test kuma naje latti"
Fadila tace "to tashi a kaina karki karyani"
Tashi tayi tace "waya kike da wannan me girman kan ko?"
Kamal ne yayi dariya Dan yasan da Gangan tafad'i hakan, Fadila tasa wayar a hands free Kamal yace "eh na yadda inada girman kai ke kuma kinada girman ciki"
Amrah dariya ta kwashe dashi tace "wayaga katon ciki, kanadai jin haushi nafi matarka kyau, nima dai bazan Auri miji irinka ba me shegen had'a face idan zaiyi magana ga yanga kamar mace Allah dai ya tsare"
Kamal yace "idan na kamaki zaki fad'i bakinki ai"
Haka sukaci gaba da hira ita da Kamal Fadila kuma sai dariyan fad'an nasu takeyi data gajima tashi tayi taje tanata aikinta a cikin gida, ita kuma Amrah sai bala'i sukeyi itada Kamal saida ta gaji kafin ta katse wayar, d'aukan wayarta tayi tafara chatting itada Zee, sunata labarin yanda school ya kasance yau, Zee ce tace "ke Amrah akwai wani group dasu Khady suka sani kinga group d'in kuwa"
Amrah tace "haba dai Zee? Ana koyar da kwalliya a ciki?"
Zee wata siririyar murmushi tayi tace "Kefa dad'ina dake bakya shiga gari, group ne Wanda za'a had'aki da manyan Alhazozi Kishigo gari zasu baki kud'i kici duniyarki da tsinke"
"Auzubillahi minki"
Allah ya tsareni Dake Zee, dama baki canja hali ba? Har yanzu kina kan bakanki? To ni gaskiya zan fad'a miki yayata zatamin fad'a idan taji har yanzu ina tare dake kuma baki canja hali ba, ranta zai b'aci sosai kuma bazanso hakan ba"
Zee ce tayi wani shu'umin dariya tace "hmm Amrah kenan yanda kike Golding girl ai saikin had'a da Golding Guy's, ita yayar taki kinsan me take aikatawa a b'oye?"
"Short up Zee, karki sake kiyi maganar banza akan Yayata, sabida na yadda da ita hundred percent akanta zamu iya yin kaca kaca da ke kuma kinsan halina tsarai sabida haka ki iya bakinki ko kuma jiki yayi