Showing 48001 words to 51000 words out of 139192 words
biyu"
Dariya sukayi gaba d'ayansu suka tafa, Dan yanzu Fadila ta d'auki Baby kamar kawa sabida Baby tanada jikin girma koba haka bama Baby ta cancanci zama kawarta tako inama, haka sukayi gaba da harkokinsu cikin jin dad'i suma yayansu yashiga musu fad'a, bayan an tashi sun koma gida Abdul yaciro socket na caji, yace kowa ta aje hannunta yayi mata bulala biyar suna ihu harya gama yace "nan gaba zaku kara fad'a a makaranta"
Fadila bataji zafin dukan ba kasancewar ya karb'a mata 'yancinta a gaban mutane, sai Baby datake zabga ihu kamar an yankata, Fadila cikin dariya tace "nikam nayi wayo narufe hannuna da hijabin Jikina ke kuma kika bari yayita zabga miki"
Baby cikin kuka tace "Allah ya isana"
Dariya Fadila tayi.
08144818849
[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸
  *ƘANWATA*
🌸🌸🌸🌸🌸
Na
Jiddah S Mapi
*Chapter 34*
  Â
     ~haka rayuwa take tafiya musu watarana suyita cikin farin ciki watarana kuma sab'anin haka, yau Fadila tacika shekara Biyu a makaranta itada Baby zasuyi Candy tare, shirye shirye ake sosai agidan Alhj Mamman, Fadila yau tagaji sosai sai share zufa take d'ankwalin kantama bata d'aurashi mekyau ba, sunayin cake Wanda zasu yanka gobe a school, Daddy ne leko yace "kuzo ina nemanku a falo"
Fita sukayi sukabar cake d'in wata me aikine takeyi, suna zuwa sukaga Daddy tsaye da makulli guda biyu a hannunshi, mikawa Fadila yafarayi kafin yamikawa Baby yace "wannan shine gift dazan baku motace Marcedes, sannan ke Fadila nayi tunanin kud'in dazan baki tinda kinyi karatun doctor kamata a bud'e miki asibiti da kud'inki idan kinyi shawara nanda kwana uku kimin magana idan kuma kud'in kikafi so saikimin magana shima kinji?"
Fadila hawayene yafara bin fuskarta a hankali ta durkusa kan gwiwowinta tace "Daddy basai kabani kud'iba makarantar dakayimin ma ya isa zan nemi aiki awani wurin"
d'agota yayi yana share mata hawayen yace "kidaina kuka my daughter alkawari nayi kuma insha Allahu saina cika" hannu yamikawa Baby tazo ya rungumesu duka yanajin dad'i a ranshi, Abdul ne yashigo yanzu yanason d'aukan abu a d'aki ganin Daddy yasashi sakar mishi murmushi daddy hannu yamika mishi yana zuwa yahad'a dashi ya rungume, Salati sukaji da tafi a bayansu juyawa sukayi Dan ganin kowaye mommy ce tsaye tana sharan kwalla, cikin kuka tace "Baby kuna gani mahaifinku yana aikata sab'o bazaku hanashi ba? Wannan zankaleliyar yarinyar zai rungume kamar wata matarshi? To wlh yau zatabar gidannan"
Daddy yace "babu inda zataje itama a matsayin 'ya na d'auketa, sabida haka kidaina tunanin wani mumunar abu akanmu"
Mom tace "shifa shaid'an baisan da wannan ba idan yayi niyan zugawa ko 'yar cikinka saiyasa maka shakku"
Da sauri Daddy yakarasa ya zabga mata mari, ido suka waro gaba d'ayansu, Fadila jitayi kafarta yafara rawa, a hankali tasamu wuri ta zauna, Mommy cikin kuka tace "ka mareni akan wannan kucakar? Wannan matsiyaciyar?"
Shima cikin b'acin rai yace "na mareki meyasa kike kaskanta mutane?"
Tace "sabida niba kaskantacciya bace"
Daddy yaji zafin maganar yace "Ke kin manta lokacin Dana Aureki mekuke dashi? Banine na taimakawa mahaifinki ba? Inace tallan goro yakeyi kafin nahad'u dake shine kinsamu wuri har zaki raina wasu?"
Mommy cikin kuka tace "Tallan Goron ma ai Sana'a ce, dama badan Allah ka taimaka mana ba kuma akan wannan kake min gori Allah ya isa damarin dakaimin"
Hannu ya d'auka zai kara zabga mata wani Marin da sauri Baby tarike cikin kuka tace "meyasa? Meyasa bazaku shiga d'aki kuyi fad'arku a can ba? Dolene sai kinyi a gabanmu? Ko kuma kunaso mud'auki d'abi'ar banzane? Kunsan fad'an iyaye agaban yaransu meyake janyowa kuwa? To idan Baku sani ba bari yau na fad'a muku, fad'an iyaye agaban yaransu yana janyo abubuwa guda biyu, na farko yanasa yara suji sun tsani babansu domin kowani lokaci zasuji kamar shine da laifi kuma maza sunada saurin hannu da wuya kaga mace ta mari mijinta saidai namiji ya mari matarshi to anan yara zasu fara kallon Babansu a matsayin mugu, sannan na biyu yanasa yara su koyi fad'a a waje bazasuji kunyar fad'awa babba magana ba sabida mamansu tana fad'awa Babansu kuma sunsan ya girmeta, wallahi idan baku gyara ba yaranku ne zai zamo musu matsala" tana fad'an haka tasaki hannun Daddy tareda Barin wurin gaba d'aya d'aki tashige tafad'a kan gado batun yau ba dama asali daddy da mommy suna yawan fad'a kuma a in harda duka yanzune sukad'an daina ita mommy batada hakuri shikuma daddy yanada zuciya idan suna fad'ar sai Abdul yatafi d'aki yasa earpiece ko magana bayayi sai Baby ce take zama tana basu hakuri, Fadila takasa mikewa jikinta yayi sanyi sosai sai hawaye take zubarwa itafa ta tsani rayuwarta yanzu akantane suke fad'a "innalillahi wa inna ilaihiraji'un" sai maimaita Kalmar take, Mommy wani harara ta banka mata kafin tabar d'akin, Daddy ma fita yayi a zuciye, Abdul ne ya karaso wurinta ya durkusa yana kallon fuskarta da sanyin muryanshi yace "kinyi daidai da kika had'a mata da miji fad'a, nasan yanzu kinajin dad'i a ranki, keep enjoying dear"
Yana fad'an haka ya mike yabar wurin, wani kuka ne yazowa Fadila Wanda babu alamun yin shiru, kuka take tsakani da Allah tana kara tuno rayuwarta na baya tajima batayi wannan tunanin ba sai yau, yau taji kewan Umma fiyeda tsammani, saida kanta yafara kokarin rabewa biyu kafin ta sarara kukan, mikewa tayi ta tafi d'aki lokacin Baby tana kwance tajuya baya itama tana kuka, batayi mata magana ba tashiga toilet tayi wanka tana fitowa tasa wani dogon rigan atamfa purple da mayafinshi purple fuskarta tayi fayau idonta ya fad'a sosai gashi yayi jaa, kayanta ta d'iba tasa awata karamar akwati wayarta ta d'auko da karamar jaka Wanda tasa kud'i aciki tad'auko flat shoe tasa sai lokacin tayi magana tana kallon Baby tace "Baby nagode da taimakon da kikayimin nasan kin soni kuma kin nunan gata Allah yabiyaki da aljanna shima Daddy zanyita mishi Adddu'a Allah yabashi a Aljannatul Firdaus, nasan rayuwata ta b'aci ta sanadiyyar KANWATA, Baby banida wani mafita yanzu bazan iya zama in b'atawa iyayenki Aurensu ba, baki cancanci haka daga wurina ba yaya Abdul ma bai cancanci haka ba, karo na farko a rayuwa Wanda yafara karb'amin 'yancina shine yaya Abdul kina ganin zan manta dashine? Mommy nasan Kishine yake damunta data d'aukeni a matsayin 'ya wlh bazatayi wannan tunanin ba amma zama da zargi bazai yiwu ba, domin watarana kema zakiyi zargina kuma bazanso hakan ba, nabarki lafiya idan Aurenki yazo please kifad'amin koda ta wayane insha Allahu zanzo" share hawaye tayi taja akwatin zuwa waje, bataso tajuya takalli fuskar Baby sabida tasan dolene ta karaya, hawaye yanabin fuskarta tanajan akwati, Baby dake kwance jitayi kamar mafarki take, da sauri ta dira akan gado batako d'auki d'ankwali ba, da gudu tabi bayan Fadila tariko jakanta tanaja, Fadila ganin haka yasa ta sakar mata jakar takama hanyar waje, da ihu Baby take kiran sunanta Amma batako juya ba, Karo Fadila taci da Abdul Wanda yataso daga rakiyan abokinshi, kallonta yayi daga sama har kasa yace "ina zaki?" Saida zuciyarta tabada sautin dum domin Abdul yana mata kwarjini sosai, tsawa ya daka mata saida jikinta yafara rawa "ina zakije nace!!!?"
Dakewa tayi tace "gidanmu zanje"
Wani harara ya zabga mata ya nuna mata yatsa alamun takoma, cikin kuka tace "Yaya Abdul wlh bazan iya zama a gidannan ba mommy ta tsaneni"
"Dama na tambayeki zaki iya zama ko bazaki iya bane?" Girgiza kai tayi yace "koma"
Kuka takeyi soai yanzu shima tausayi tabashi Dan bayason ganin tana kuka gashi gobene ranar farin cikinsu domin gobe zasuyi Candy, hannunta yariko cikin sanyi yace "kiyi hakuri kizauna idan kin samu aiki kin fara d'iban albashi saiki tafi kinga lokacin zaki iya kula da kanki amma yanzu idan kika tafi akwai b'arayi akwai masu yankan kai kinaso su yankaki ne?"
Waro manyan idonta tayi tace "Aa"
Abdul yace "to mu koma ciki duk abinda Mommy zatayi miki karki kulata kibari dakin fara aiki kin d'ibi albashi saiki tafi kinji?"
Gida kai tayi ta sakar mishi murmushi Dan gaskiya yabata shawara me kyau yanzu zata share mommy idan ta fara aiki saita tafi, hannunta yaja suka fara tafiya zuwa cikin gida, wani murmushin farin ciki Baby tayi Wanda hawaye yakebin bayanshi, Daddy ma murmushi yayi Dan yafito tun lokacin da Baby tafara ihu, ganin Abdul yashawo kanta yasashi jin dad'i sosai, Jakarta ta karb'a a hannun Baby, Abdul yakawo bakinshi daidai kunnenta yace "karki fad'awa Baby fa"
Tana murmushi tace "to"
Itada Baby suka koma ciki lokacin Mom tana zaune akan sofa kallon Fadila nayi tace "nazata macury zakije ai mayya"
Jiddah Ce
08144818849
[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸
  *ƘANWATA*
🌸🌸🌸🌸🌸
Na
Jiddah S Mapi
*Chapter 35*
   .  ~Washe gari Fadila da Baby ne suka tashi da sassafe wanka sukayi kowacce tana saurin taje makaranta domin yau show za'ayi bana wasaba, wani tsaddaden leshi sukasa anko bakaramin kyau sukayi ba Fadila tayi kwalliya Babyma haka idan ka gansu kamar ka sace ka gudu, Fadila jikinta har rawa yake Dan taga tayi kyau (kunsan idan mutum yayi kyau jiyake kamar yatashi sama) Cake dasukayi suka d'auka, fita sukayi da sauri Dan sunyi latti Daddy yana ganinsu yace "Kai kunyi kyau yarana Allah ya rayamin Ku"
Sukace "Ameen"
Mommy ce tafito tana mutsika ido alamar daga bacci ta tashi waro ido tayi ganin yanda sukayi kyau tab'e baki tayi tace "Babyna kinyi kyau sosai" Baby tace "mun gode mommy"
Mommy cikin had'a fuska tace "kun gode keda wa? Cewafa nayi kinyi kyau"
Fadila bataji komai a ranta ba Dan tad'au shawaran Abdul, Baby tace "to Mommy Sai kunzo mukam mun tafi"
Mommy tace "tom"
Abdul ne yashigo d'akin yana kallon agogon hannunshi yayi kyau sosai cikin shadda brown color kanshi da hula irin na 'yan Maiduguri, sai faman yamutsa fuska yake yana tsaki, kallon Daddy yayi ya shagwab'e fuska yace "Daddy wlh banida lafiya" Daddy dariya yayi yace "my son idan baka kai kannenka ba wa zaka kai a motarka?"
Shiru yayi yana turo baki, Mommy tace "ai badan kowa zakayi ba Dan kanwarka zakayi uwa d'aya uba d'aya ba wasaba"
Da Sauri Fadila ta kalleta jin abinda tafad'a idonta ne yacika da hawaye, carab sukayi ido hud'u da Abdul girgiza mata kai yayi alamar kar tayi kuka, da sauri ta mayar da hawayen ta hanyar kif kifta ido, Abdul yace "muje kar muyi latti"
Da sauri Fadila tayi gaba Dan tana Allah Allah tabar gidan kada mommy takara yab'a mata magana, tare suka jera da Abdul Baby tanabin bayansu, makullin motar hannunta tamikawa Abdul tace "Yaya Abdul ga makullin motar da Daddy yabani nikam ban iya mota ba, garama Baby naga ta iya"
Kallonta yayi yace "me kikeso nayi miki to yanzu?"
Turo baki tayi tace "Yaya siyarwa mana"
Yace "amma ina ganinki kamar kinada hankali Ashe dakikiyace ke, yanzu mutum yabaki kyauta ai yanaso yaga kina amfani dashi ne idan kika siyar kina ganin zaiji dad'i?"
Shiru tayi tana tunani daga baya tace "gaskiya nefa nafasa"
Yace "kuma idan kika fara aiki a motar wa zakina zuwa?"
Kallonshi tayi da manyan idonta tace "motarka mana"
"Sa'ankine ni ko driver d'inki"
Fadila ganin ya had'a rai yasa tayi shiru har suka shiga mota, Baby ce ta zauna a gaba ya dalla mata harara yace "koma baya, ai kina ganina bakiyimin magana ba sai yanzu zakizo nan kizauna"
Fita tayi tana gunguni Fadila ce takoma gaba tanad'an murmushi harara itama ya dalla mata yace "kema ki koma baya kinzo kin zauna harda wani murmushi motarkice?"
Sum sum takoma baya, jansu yayi ya kaisu cikin makaranta lokacin har an fara program, da sauri suka shiga shima Abdul yashiga 'yammata sai kallonshi suke shifa har sun fara bashi haushi, dasun had'a ido da mace sai had'e fuska yaja tsaki, 'yammata dayawa sun fita sunyi godiya wa shugaban makaranta da malamansu, su Daddy da Mommy sun karaso kusan 12, lokacin Ana wa'azi, shugaban ne ya karb'i speaker yace Fadila tafito tayi musu wa'azi, Family nasu Baby suna zaune a wuri d'aya Abdul yana gefen Daddy sai yamutsa face yake, Fadila jikinta yana rawa Dan batason cikin mutane ko kad'an, Da sallama ta fara daganan tad'au hanya, wa'azi take akan ranar tashin alkiyama inda daga karshe tana kuka tace "ranar da d'an uwa zai guji d'an uwanshi, ranar da masu kud'i zasuji kamar su dawo duniya suyi sadaka da dukiyoyinsu, ranar da uwa zata manta da d'anta, ranar da jariri zaiyi furfura tsabar wahala, ranar da mugaye da maciya Amana wad'anda sukaci amanar 'yan uwansu zasu ciji d'an yatsansu harsai ya karye tsabar nadama, jama'a mutuba mubi Allah, zunabanmu sunayin yawa badan Annabi ya roki ubangiji akan kada a hallaka mutanenshi ba da tuni an hallakamu, domin duk zunuban da mutanen da sukeyi mu mun tara gaba d'aya muna aikatasu, shirka anayi sata anayi, Zina anayi, shan giya anayi, caca anayi, Mad'igo anayi, luwad'i anayi, ina zamu zauna lafiya?, mugyara halinmu sai Allah yaji tausayinmu, a wannan zamanin d'an uwanka shine zai cutar dakai Wanda kuka fito ciki d'aya shine zai cuceka...." Kukane yaci karfinta harta kasa magana, kowa a wurin sai share hawaye yake jikinsu ya mutu da wannan wa'azin, Abdul kwantar da kanshi yayi jikin benci yana kuka tun Daddy yana ganin kukan na tausayi ne har abun yafarayin yawa, kuka yake tsakaninshi da Allah kamar Wanda akayiwa mutuwa, Baby ma kuka take sosai tana tuna rayuwar da sukayi a Sudan, da kyar Baby ta janye Fadila a wurin speaker sabida kukan yafi karfinta tana tuna rayuwarta da Amrah, mutanen wurin basuci wani abun kirki ba Dan yau jikinsu ya mutu, Daddy ne yajuya wurin Abdul yariko kafad'arshi tareda d'agoshi ya share mishi hawayen fuskarshi yace "my son kukan me kakeyi?" Wani kukan yakara fashewa dashi yafad'a jikin Daddy mommy ma jikinta yayi sanyi, cikin kuka Abdul yace "ba komai Daddy ba komai.." Sai kuka, a daddafe aka baiwa su Fadila result nasu, jikinsu a sanyaye suka koma gida, mommy ma bakinta yayi shiru Dan batayi tsammanin haka Fadila takeba.
     "Amrah kwance take Akan gado yau da zazzab'i ta tashi jikinta sai rawan d'ari yake, Kamal ne yafito daga toilet ya d'aura Towel a jikinshi karami kuma a kanshi yana gogewa kallon Amrah yayi ya watsar yanufi wurin dressing mirror ya shafa mai da turare yasa kaya tareda d'aukan makullin mota yanufi hanyar fita, Amrah da muryanta baya fita tace "Yaya Kamal ina zakaje kana ganin banida lafiya?"
Kamal yace "Wurin Ubale zanje" (ubale yana nufin Ubanki)
Hawayene yafara bin fuskarta tace "yaya Kamal please kabani kud'i zanje asibiti a dubani daganan zanje gidansu Mama inyi kwana biyu kozan huta a can"
Hararanta yayi yace "ban hanaki zuwa gidanku ba amma banida kud'in dakike nema hasalima bazan baiwa Karuwa kud'ina ba"
Amrah tace "niba karuwa bace..." Kafin takarasa maganar yafice, rufe bakinta tayi da blanket tana kuka mara sauti sai shesheka take kamar ranta zai fita "na shiga uku na lalace meyake faruwa danine?" Saida taji d'an sauki kafin tamike tayi wanna tasa wani dogon riga roba roba Wanda ya fito da ramanta a fili, sai kasusuwa da idanunta dasuka fad'a, kallon madubi tayi tashare hawayen dasuka zubo mata, hijabi tasa tad'auki wani naira d'ari data b'oye tafice, tana kallon Umma tsaye abakin kofa amma batace komai ba ta tafi, Napep takama zuwa ganye road unguwarsu kenan.
Jiddah Ce
08144818849
[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸
  *ƘANWATA*
🌸🌸🌸🌸🌸
Na
Jiddah S Mapi
*Chapter 36*
     ~Fadila suna zuwa gida tawuce toilet kullewa tayi tahad'a kanta da jikin bango tafara kuka me tsuma zuciya cikin kuka tace "Kanwata kin cuceni kin rabani da iyayena kin rabani da masoyina, bazan yafe miki ba Amrah wallahi bazan yafe ba" Babyma tashigo d'akin jikinta a sanyaye ganin Fadila bata d'aki yasa tayi tunanin wanka take, fita tayi a d'akin tanufi d'akin Mommy, Mommy da Daddy ne sukasa Abdul a gaba saiya fad'a musu abinda yake daminshi, Abdul yace "ba komai nafad'a muku ba wani Abu" daddy yace "to idan har ba wani Abu meyasa kake kuka haka?"
Abdul shiru yayi yana Kallon Amrah wacce ta lab'e a bayan kofa tanason jin kwakwaf, yace "Daddy ba komai wa'azin ne yasani haka" Daddy yace "to Allah yasa hakanne" fita Abdul yayi yana Kallon Baby ta kwasa da gudu bai kulata ba yawuce d'akinshi, fad'awa yayi akan lallausan gadonshi, rufe manyan idonshi yayi Wanda yake d'auke da Zara zaran gashin ido, dafe kirjinshi yayi da hannunshi mai tsayi "ya Allah kaciremin wannan damuwar a raina ko hankalin iyayena zai kwanta" hawayene yafara bin fuskarshi yana gogewa wasu suna karabin fuskar, wayarshi ce tafara ruri, tsaki yaja kafin yamika hannu ya d'aga new number ne saida ya yanke aka kara kira kafin yadanna Kore, karawa yayi a kunnenshi baice komai ba, ta d'ayan b'angaren akace "barka da dare ranka yadad'e sunana Aisha daga nan Abuja naga hotonka a wayar wani abokina shine na roki number d'inka da fatan zan samu karb'uwa a wurinka" wani bakin cikine ya kamashi cikin jin haushi yace "kina mace kina kiran namiji a waya babu ko Jan aji? Wannan wani irin lalacewa ne? Sannan kina fad'amin wai abokinki dama akwai abota tsakanin mace da miji ne? Kinga dallah kiyi hakuri inada wacce nakeso" d'it yakashe wayarshi dan yaji haushin yarinyar sosai harda kashe mishi murya chewww, tashi yayi yashiga toilet yayi Wanka tareda alwala yafito d'aure da towel, wurin mirror yaje yashafa mai da turare rigan daba nauyi yasa da wando yakwanta akan gado yaci gaba da tunaninshi kamar yanda ya saba, bai dad'e da kwanciya ba bacci ya d'aukeshi.
    "Fadila saida tayi kuka harta gaji kafin ta wanke fuskarta, madubin cikin toilet d'in ta kalla tana kallonshi yanda idonta ya kumbura goge idon tayi dan batason agane tayi kuka, fita tayi ta zauna abakin gado da sauri ta mike Dan wani tunani datayi, wurin kayanta tanufa ta sakko dawani akwati Wanda sarki yabasu, bud'ewa tayi ta fara dube dube farin paper da Yarima yabata taciro wani farin cikine ya