Showing 36001 words to 39000 words out of 139192 words
Fadila sunga rayuwa sun Fita a hayyacinsu fuskarsu yazama Baki, a kwana na biyar ne suka samu hanyar fita, saida sukayi murna sosai Dan ganin sun fita a wannan wahalar saura wahala tagaba cewar Fadila, Baby dama ba jikin gashi ta dad'a ramewa sosai idan ka ganta kamar zata karye, Wani Kauyene suka had'u dashi, sun dad'e suna tafiya a halin yanzu su goma ne, rafi suka gani cike da ruwa cikin murna suka nufi rafin sukasha ruwa tareda wanke jinkinsu sai a lokacin sukaji saukin wahalan kwanciya sukayi sukad'an huta sannan suka kara mikewa suka nufi cikin garin dasuka tsinci Kansu, wasu 'yammata suka gani suna tafiya ba takalmi kansu a durkushe, Fadila ce tad'an tsayar dasu tace "bayin Allah Dan Allah nan wani garine?"
Kallonta sukayi d'ayan tace "kije ki tambayi izinin megari idan ya yadda to saikizo muyi magana Dan garinnan ba'ayiwa bako magana"
Suna fad'an haka suka wuce, Fadila kallon 'yan uwanta tayi tace "ikon Allah kunga wani bahagon gari? To idan ba'ayiwa bako magana ba ya za'ayi yasan gidan megari har yanemi izinin magana da 'yan gari"
Suma mamaki abin yabasu Baby tace "saidai muyita tafiya harmu samu gidan megarin"
Haka kuwa sukayi tafiya sukayi tayi suna kallon mutane babu Takalmi sannan Kansu a kasa, Ko magana basuyi musu ba, ganin wani dogari yafito daga wani babban gida yasa Fadila tace "inagafa gacan gidan sarkin" suma ganin dogari yasa suka amince da saurinsu suka karasa suna zuwa suka hango wasu dogare zaune da bulala a hannunsu, Baby dasauri ta b'uya abayan Fadila, dogalen ne sukazo wurin suna tambayarsu ko lafiya? Fadila a taorace tace "mu bakine muna Neman masauki agidan sarki"
Da tsawa yace "idan aka bincika aka gano Ku munafukai ne zakusha suka sosai awurinmu"
Fadila tace "mun yadda" saida yakira wasu 'yammata suka cajesu Tass kafin yace "Ku biyoni muje"
Binshi sukayi suka fara ganin 'yammata acikin gidan ba takalmi suke tafiya, kuma basa kallon mutum, wani babban wuri akace su tsaya tukun sai an nemi izinin sarki, tsayawa sukayi aka nemi izini kafin akace su shiga, wani babban fada aka kaisu suka shiga suka hango sarki wani farine kwance yana kallon sama 'yammata biyu sun durkusa a gabanshi suna mishi tausa, Dogalin ne yayi musu tsawa yace "kuyi sujjada bakwa ganin sarki ne?"
A firgice suka kalleshi jin abinda yafad'a, da karfi yakara cewa "nace kuyi sujjada kada ran sarki ya b'aci"
Fadila kallon 'yan uwanta tayi tayi musu alama dasuyi, sujjada sukayi gaba d'ayansu agaban sarkin, sunfi minti talatin kafin dogali yace "kumike sarki ya amsa"
Mikewa sukayi suma kallon ikon Allah saida suka shafe away d'aya zaune babu Wanda yace musu kala gashi sun gaji basune abin dubawa ba wad'annan 'yammatanne abin dubawa daga ganin alamu sun gaji suna cikin tunanin sukaji ana busa algaita ana cewa "ga yarima" kallon kofa sukayi suka hango wani yana shigowa kanshi akasa, yana zuwa tayi sujjada da sauri sarki yace "Sannu babana" mikewa tayi Fadila da 'yan uwanta kallon Yakima sama ganin wani mutum Wanda za'a iya kirada (readymade) wani gayene dogo chocolate color idonshi manya wannan farine kamar madara Bakinshi wani tsukakke d'an karami ga dogon hanci gashin kanshi a nannad'e daka Ganshi kaga cikakken fulani, Fadila zuba mishi ido tayi tanason tagano wani Abu Wanda ta manta kamar tasan fuskar to amma a ina? ko kallon Inda Suke baiyi ba, da tafiyarshi irin na maza Wanda suka amsa sunansu maza yakarasa wurinsu baban nashi, kwanciya tayi ajikin sarki ya rungumeshi cikin shagwab'a da muryanshi kamar ana busa sarewa yace "Abba nagaji sosai yau"
Taping na bayanahi sarki yayi yace "sannu magaji banso kagaji haka bakasan banaso kashiga damuwa, tashi kaje kayii wanka kasha fura nasa an dama maka ansa a frij ka zab'i 'yammata guda Biyar Wanda zasu d'ibe maka kewa kaji Babana?"
Kai ya gid'a tareda mikewa ya yafice baiko kalli wurinda su Fadila sukeba.
Jiddah Ce
08144818849
[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸
*ƘANWATA*
🌸🌸🌸🌸🌸
Na
Jiddah S Mapi
*Chapter 24*
~Saida sukayi Awa d'aya da minti talatin kafin sarki yace "meke tafe daku?"
Duk shiru sukayi Dan basusan ta inama zasu fara ba, cikin tsawa Dogali yace "sarki yana magana kuma kunyi shiru zaku bud'e baki kuyi maganane kosai anyi muku hukunci?"
Da sauri Fadila tariko hannun Baby kem bakinta yana rawa tace "mu bakine daga garin Maiduguri Boko Haram ne suka shigo garinmu suna yanka mutane sunsa Bomb ako ina sun kaishe rayuwaka da dama muna gudu muna kallon gawa a kwance babu me binnewa muma da kyar mukasha, shine damuka gudu Allah ya saukemu a garinnan, Muna rokan sarki daya taimaka ya duba Abu akanmu yabamu masauki kafin garinmu yayi lafiya" gaba d'aya ido suka zuba mata suna kallonta wannan karya kamar ta taso agidan Maroka? Kashe musu ido tayi alamar karsuce komai, sarkine yayi gyaran murya yace.
"Naji duk bayananku Kuma na yadda zaku zauna a fada na saidai akwai sharad'i guda biyu na farko zaku zama bayi agidannan na biyu zaku ke wannan" ya nuna Fadila da yatsa yace "Zaki zauna ta b'angaren Yarima kece zakina kula dashi kirinka d'ibe mishi kewa kun Amince?"
Da sauri sukace "mun Amince sarki" Sarki ya kalli 'yammata guda biyu yace "kuje Ku nuna musu masaukin baki"
Durkusawa sukayi sukace an gama ranka ya dad'e, nuna musu masauki akayi Fadila aka nuna mata d'akin Yarima, an kaisu wurin Matan sarki guda uku sunyi nuna Kansu sunyi bayani.
"Amrah saida tagama aiki gaba d'aya kafin tashige d'aki wurin Kamal tanaso ta tadashi yayi sallah, tana shiga ta ganshi yayi nisa sosai da alama baccin yayi mishi dad'i, zama tayi a gefenshi taja blanket d'in a hankali, saida tacire tariko hannunshi tana shafawa ganin bashida niyan tashi yasa ta sunkuya daidai kunnenshi tace "yaya Kamal lokacin sallah yayi"
Shiru taji bai tashiba, kwanciya tayi agefe ta tareda rungumeshi tsam a jikinta a hankali tafara shafa bayanshi, Ido ya bud'e a hankali Yana kallonta itama kallonshi take batareda tacire hannunta a jikinshi ba, murmushi yad'an saki itama ta maida mishi, Shafa fuskarshi tayi a hankali ya lumshe idonshi, tace "Lokacin Sallah yayi" tana fad'a ta mike zata tafi, Fizgota yayi tafad'o jikinshi tana ware ido, idonshi a rufe yace "ina zakije?"
Cikin rawan murya tace "Zanje toilet ne zanyi alwala"
"Okay kiss me before you go"
Waro ido tayi tace "yaya Kamal bazan iyaba gaskiya"
Dad'a lumshe ido yayi yace "Idan kinaso kitashi sai kinyi min"
Shiru tayi tana ganin lokaci yanaja gashi bashida niyar saketa, ganin batada mafita yasa tace "A ina zanyi?"
Murmushi yayi a hankali yacire hannunshi d'aya daga jikinta yanuna mata bakinshi, ido takara warowa tace "wallahi bazan iyaba" shiru yayi mata, itama tayi shiru tana kallonshi, ganin bazatayi ba yasashi Nuna mata gefen fuskarshi yace "yimin anan"
A hankali tafara kai bakinta daidai fuskarshi lumshe ido sukayi atare, Bakinta ta d'aura a kumatunshi tayi mishi Peck, dagudu tamike yakara fizgota ba tareda ya bud'e Ido ba ya nuna mata d'ayan gefen fuskarshi, murmushi ta saki tareda yimishi deep kiss a wurin, mikewa tayi tashige toilet da gudu, Kamal kallonta yayi yana dariya a hankali shima ya mike yanufi toilet d'in knocking na kofar yayi, Amrah tana jinshi tayi shiru saida tayi Alwala kafin tabud'e, ganinshi tayi tsaye ya nad'e hannunshi a kirji yana sakar mata murmushi, gefenshi ta rab'e zata wuce yariko hannunta, juyawa tayi tana kallonshi amma shiba kallonta yakeba, kokarin janye hannunta take amma takasa, saida yagaji da kanshi kafin yasake mata hannun yashige toilet.
"Fadila wanka sukayi aka basu kaya irinna bayi sukasa, abinci aka basu sukaci sannan Fadila ta nufi b'angeren yarima, Tana zuwa ta tsaya a bakin kofa, batasan ya zata kayaba idan tashiga, daurewa tayi ta bud'e kofar a hankali ta Shiga, kayataccen falone taci karo dashi, kallon cikin falon takeyi kamar tasamu television, d'aga kanta tayi sama tana kallon wutar da yake canja color (disco light) abun yayi mata kyau matuka, tafiya take tana kallon sama batasan ina zata shigaba, karo tayi da Abu a gabanta da sauri tadawo cikin hankalinta tana kallon meta buge, Yarima tagani tsaye ya hard'e hannu a kirji fuskarshi a d'aure tamau yana kallonta, da sauri taja baya ta durkusa cikin tsoro tace " ka gafirceni ranka shidad'e bada sanina nayi hakan ba" kallon fuskarta kawai yakeyi yanajin yanda take magana kamar batason yi, Fadila jikinta ne yake rawa ganin yanda yake kallonta, matsowa yayi dab da ita da sauri tayi baya, yakara matsawa takarayin baya, binta yake tana gudu bataso ya tab'a ta, saida takai jikin bango kafin ta tsaya tareda dafe kirji tanajin mugun tsoronshi, Yarima kallon fuskarta yayi tareda sakin murmushi yasa yatsanshi a daidai bakinta yana zagayawa, Janye fuskarta tayi da sauri ta buge hannunshi, dariya yayi yace "Fadila ko? Hmmm nayi mamakin yanda kikazo gidanmu Neman taimako, kuma nayi mamakin yanda kina nuna baki sanni ba, har a fara tunanin ko dai ke MAKUNIYA CE idan baki tunaba yau zan tuna miki, nine Wanda naje wurinki kanwarki tafito bayan ta koma kema kika fito, kika watsamin kud'i a fuska tareda yimin wulakanci, bazan manta da wannan rana ba domin shine rana ta farko da akayi min wulakanci, na dad'e ina tunanin yanda zan d'au Fansa sai gashi kin kawo kanki da kanki har gidanmu, sunana Kabeer Wanda akafi sanida Yarima, dafatan kin gane?"
"Tunda yafara magana ta zuba mishi ido jikinta ya saki, dama tunda taganshi tayi tunanin akwai Inda ta tab'a ganinshi, hawayene yafara bin kumatunta, bakinta yana rawa ta rasa me zatace mishi, Hanki yaciro daga aljihunshi yakai daidai fuskarta yana kokarin share mata hawaye ta buge hannunshi cikin b'acin rai ta had'a hannunta biyu wuri d'aya alamar roko tace "Stay away from me please, banason damuwa kayi duk abinda kasa a ranka zakayi ni kam dama rayuwata tariga ta b'aci, Saidai kawai nabaka hakuri akan abinda nayi maka amma bazan hanaka yin abinda kayi niyaba"
Yarima kallonta kawai yakeyi shi sai yanzuma yagano yanda ta b'aci tayi baka, juyawa yayi yafice daga d'akin yabarta tsaye tana kuka "Kanwata ce tasani a wannan halin Amrah ke muguwa ce Allah ya isa tsakanina dake"
Saida tagaji kafin tamike tareda share d'akin da Taimakon wata baiwa, turare me kamshi tasa sannan taja kofar tafice, Yarima tagani tsaye yana yiwa wani magana bata tsaya ba ta dukar dakai tareda cire takalmi yanda taga sauran mutane nayi "ke waya baki izinin tafiya" ta tsainci muryanshi, juyawa tayi tana kallonshi sai taga hankalinshi yanakan mutumin dasuke magana, tsayawa tayi kawai tana jiran ya gama, saida yagama maganar ya juya zai tafi da sauri ta tare mishi hanya tace "me zanyi maka? Inace magana duk aikin da akace nayi, to me kuma yarage?"
Kallonta yayi sannan yace "Tausa yarage, kowane rana anamin tausa sau uku, safe rana dare, idan kuma bazakiyiba sai inji"
Kallonshi tayi da mamaki fuskarshi bai nuna haka yake ba, she innocent ne a fuska batayi tsammanin zaiyi haka ba "tayaya zan d'aura hannuna a jikin wani kato Shiva mijina ba?"
"nine katon? Ya tambaya ranshi a b'ace, itama rai b'ace tace "Eh mana kaiba kato bane? Yarone kai?"
_Dan Allah ku sani a addu'a, duk wacce ta karanta tamin addu'a_
Jiddah Ce
08144818849
[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸
*ƘANWATA*
🌸🌸🌸🌸🌸
Na
Jiddah S Mapi
*Chapter 26*
~Abba ne yashigo gidan cikin zafi da tsawa ya nuna Mama da yatsa tareda cewa "Kinsan Allah idan kika kara ambatar sunan Fadila agidannan abakin Aurenki, ba ni taso ta kunyata ba? To taje gata ga duniya, kuma duk ranar Dana ga ta d'ibo kafa tazo sainayi mata abinda bata tab'a zata ba"
Yana fad'an haka yawuce d'aki tareda banko kofar har saida sukaji tsoro, Amrah sai rarraba ido takeyi tana Kallon Mama, babu shakka tana cikin tashin hankali, jitake kamar tafad'a mata gaskiya to amma idan tafad'a zasu rabata da Kamal nata, Mama tana kuka Amrah ma ta fashe da kuka, saida suka gaji Dan Kansu kafin sukayi shiru.
"Fadila yau za'ayi meeting agidan sarki Dan haka aka tara bayi da matar sarki kowa yazauna a fada, saida sukayi sujjada kafin suka zauna, sarki yayi gyaran murya tareda cewa "Barka maza da mata, a matsayina na sarki yau zan hallata muku abu guda uku agidannan sabida naga akwai anfani hakan, na hallatawa mata surinka jan sallah sannan na hallata muku sa takalmi kuma na hallata ayiwa Yarima sujjada bayanni, idan akwai me magana yanada magana to nabashi izini"
Fadila ce ta d'aga hannunta sama alamar tanada magana, sarki kallonta yayi yace "zaki iya zuwa nan kitsaya kiyi maganarki"
Fadila takawa tayi ta iso wurinda sarki yake mutane sai kallonta suke kamar sun samu Film, haka ta daure ta iso wurin Yarima Ido yazuba mata yana ganin irin jajircewar yarinyar, saida ta iso ta gaida sarki sannan tafara magana kamar haka "da sunan Allah me rahma me jin kai, ina mika gaisuwata ga d'aukakin jama'ar wannan fada, Sunana Fadila ni musulmace, dafarko munzo garinnane da sunan a taimaka mana sai naga 'yan garin suke Neman taimakonmu, Allah yana cewa kusanni kafin Ku bautamin dolene kunemi sanina kafin Ku bautamin, Allah ne kad'ai yake hallata abu ba mutum ba, sannan Allah shi kad'aine akeyiwa sujjada bayan shi babu wani mahalukin dayakai ayi mishi sujjada, wani abu daya bani mamaki shine wai baza ayiwa bako magana ba to Ai Allah yana cewa (Man kana yu'uminu billahi wal yaumil akhiri fal yukrim daifahu) yana nufin duk Wanda ya kasance yayi imani da Allah da rana ta karshe wato ranar kiyama to ya girmama bakonsa kunga anan an nuna bako yanada muhimmanci domin wani bakasan dame yazo ba, sannan naga matanku suna yawo babu hijabi sunasa wani sarka a kafarsu to manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yana cewa (sinfani min ahalin nar lam arahuma kaumun siyad'in ka'azna bil bakarati yadribuna bihannas wanisa'un kasiyatun asiyatun ma'ilatun mumilatun ru'usuhunna ka'asnimatil bughti la yadkhulul jannata wala yajidna rihaha fa inna rihaha layujadu min maseerati kaza wa kaza) manzon Allah yana cewa nau'i biyu daga cikin wuta banga kamansuba wasu mutanene atare dasu akwai bulalai kamar kunnuwan shanaye suna dukan mutane dashi da wad'ansu mata da tufafinsu amma tsiraru ne masu tafiya suna karkato da hankalin jama'a izuwa Kansu da kawunansu kamar tozon rakumi bazasu shiga aljanna ba bazasuji kamshinta ba domin ana samun kamshinta daga tafiyar kaza izuwa kaza, anan matanku babu hijabi suke yawo, idan basu gyara ba zasu kasance acikin wad'ancan matan dasuke shan duka, sannan Babu saduwa Atsakanin Wanda basuyi Aureba saidai sarki idan ya kasance yana da bayi anan ance kwarkwara itama matar sarki ce, to amma Yarima bai hallata a had'ashi da mata su d'ibe mishi kewa ba, zaku iya Neman malamai sukara fahimtar daku, sarki a gafarceni idan nayi kuskure amma nikam nasan banyi kuskureba domin fad'in Allah ne da manzon shi" Fadila tana fad'an haka ta juya zata tafi sarki yace "dakata" Baby dake zaune agefe guda jikinta sai rawa yake tasan yau babu me kwatarsu awurin sarki, harta fara hango dukan dazasu sha yau, Su Fatima ma sai addu'a suke Allah ya kub'utar dasu.
"Abun mamaki saiga sarki yana share hawaye hanki yaciro yafara goge fuskarshi dashi, mutane ganin sarki yana kuka suma sai kuka, sarki cikin muryan kuka yace "baiwar Allah suwaye iyayenki Dan Allah, inaso in nemawa Yarima d'ana na cikina Aurenki" Fadila tace "sarki ansa ranar Aurena nariga nayi alkawari dawani shikuma alkawari yazama wajibi mutum yacikashi idan ya d'auka" sarki yace "dafari naji labarin duk abinda yafaru akanku nasa anyimin bincike kuma nayi niyan ind'au mataki kwakkwara akanku saidai yau naji kunshiga zuciyata kuma nayi alkawarin zan had'aku da dogalai na sukaiku gida har gaban iyayenku"
Murna Baby sukayi sunajin dad'i lalle Fadila ta dabance, ta taimaka musu, tashi sukayi suka rungumeta suna murna harda hawaye Fadila ma murna takeyi, Yarima ne ya mike yana kallonsu yace "to idan kun gama nima akwai kyautar dazan baku" Fadila kallonshi tayi tace "bamaso kariki abunka na sarki ma ya ishemu" dariya yayi suma sukayi dariya, daganan sarki yace aje asiyo kaya da hijabai arabawa bayi da mutanen gari, sannan a haramta mata suja maza sallah saidai mata suja mata idan ya kasance babu maza a wurin, sannan duk bakon dayazo gari a bashi masauki sannan aji damuwarshi, atakaice dai gidan sarki yazama wurn ibada sarki yace afara Gina masallaci a kofar gidanshi, sannan babu Wanda za'a yiwa sujjada idan ba Allah ba, Allah shine Wanda za'ayiwa sujjada, Abinci aka dafa masu yawa da kyau agidan sarki mutanen gari sunci kuma sunyiwa Fadila godiya, da dare sarki yasa akira Su Fadila, bayan sunje sarki yace yaushe sukeso sukoma gida?
Fadila tace "ko Jibi zamu koma ranka shidad'e" sarki yace "ba komai Allah yakaimu"
Duk sukace "Ameen"
Suna shiga d'akin da aka basu matsayin masauki, Baby ta rungume Fadila suma sauran suka taru suka rungumeta sunata murna, Baby tace "yanzu jibi zanga Momy da Daddy da Yayana?" Hawayene yafara bin idanunta, da sauri Fadila ta goge mata tana murmushi saida tayi shiru Fadila ta tunada Amrah da Kamal jitayi takasa tsayawa zama tayi agefen Katifa ta dafe kanta dayake sarawa "nasan Kamal bazai Auri Amrah ba, nasani nikad'ai yakeso kuma zan dawo in Aureshi, to Amma idan ya Aureta fa? Yaya zanyi? zan kasheta bazan iya jure ganin Kamal dawata ba"
Baby da Fatima ne suka dafata tareda kwantar mata da hankali akan tayi addu'a Allah yasa basuyi Aureba, share hawayenta tayi Dan sai yanzu takejin wani irin d'aci a ranta jitake kamar kartaje gida, Dan batasan mezata Tarar ba.
"Amrah sai lallab'a Mama takeyi hartayi shiru, girki tayi musu sukaci sukayi sallah, bayan isha Kamal yayi horn saida ta kara baiwar Mama hakuri akan sud'auki kaddara kafin tafice Mama tana Samata Albarka, bud'e mortar tayi tashiga Kamal yana zaune yana waya, tana shiga ya katse kiran da sauri