Showing 63001 words to 66000 words out of 139192 words

Chapter 22 - Kanwata Book One Complete Hausa Novel

Jiddah   

27 Sep 2025

877

Wurin aikinshi kirika zuwa kina saminshi.. "

"Kinga da Allah dakata, bazanyi wad'annan abinba Nasan karyane yace zai Auri Adda Fadila Yanzu sabida na haramta aure tsakaninsu to miye zai dameni dashi, Ko Yanzu Nasan Ina cikin zuciyarshi dakanshi zai dawo ya mayar Dani d'akina idan be mayar Dani dan Allah ba ya mayar dani dan kyauna, sabida Haka kidaina Damin kanki kawata kinji"

Zee tace "tom naji na komai"

Kitt Amrah takashe wayar ta tashi tafara gyaran d'aki, Abba ne yashigo bakinshi d'aukeda sallama, cikin girmamawa Amrah ta amsa Tareda durkusawa takarb'i ledan hannunshi, "Sannu Amrah Allah Yayi miki Albarka"

"Ameen Abba"

Kitchen tawuce tá ledan takawo mishi Ruwan Sanyi, Ledan tabud'e taga Fruits Ne aciki yayyankawa tayi tasa Akan plate tanufi falo dashi, lokacin Umma tafito daga d'aki kallon Amrah tayi sosai tana kara kallonta ganin haskenta yafi nada kuma takara Kib'a sosai yasa Mama taji ajikinta anya ba cikine da Amrah ba? Shiru kawai tayi tawuce cikin falon ta zauna agefen Abba, Amrah ajiye Fruits d'in tayi tace "bisimillah"

Kallonta Mama tayi tace "Ke bazakisha bane?"

Yamutsa fuska tayi tace "Wlh ayaban warinta bayamin dadi"

Shiru mama tayi Kafin tace "yaushe rabonki da Al'ada?"

Sunnar dakai tayi kasa dan taji kunyar Abba sosai, cikin jin Kunya tace "kusan wata biyu banyiba"

Mama tace "tashi kije"

Mikewa tayi tana tafiya ido mama tazubawa Bayanta ganin yanda tayi Jiki taciko yasa Mama tace "Kwata Kwata na manta da Batun cikin Amrah saida na Lura da Kyau yau nagano gashi wad'annan mugayen sunce ba cikinsu bane, Mun d'auki kaddara zamu rike komai tahaifa insha Allah"

Abba shiru Yayi yace "gaskiya mutanennan sun wulakantamin 'ya yarinya tun tana surutu harta zama innocent na dole ba komai Allah yashige mana gaba"

Ameen

"Momy durkushe Take takasa Mikewa Allah yasani idan yau Alhaji ya koreta yau bazata iya zaman gidansu ba dan akwai fitina sosai kannenta BA Kunya ne dasuba har dambe zasu iya da ita, Ga Kishiyar mamanta da Shegen mugunta Itakam yau tashiga uku" bata karasa tunanin ba Fadila tafito jikinta sanye da Wani wando wanda aka bud'e saman Kasan kuma aka d'ameshi Kamar na India Wandon Bakine sai riga Pink color da hula Baki me ado, fuskanta fayau takara Haske sosai sakamakon rama datayi, tayi Kyau, Momy kallonta tayi daga sama zuwa kasa Tabbas idan Alhaji ya auri wannan sunanta Sorry, bazama ta hakan yafaruba Koda bayan rantane, Dady ne yace "karaso kizauna"

Mikewa Momy tayi simi simi taje gefen Dady tá zauna, Fadila ma kanta akasa ta samu wuri ta zauna agefen Abdul daya hard'e kafafu yana sanye da wando daidai gwiwa Baki da ganin farin riga, fuakarshi Kamar ta damisa tsabar yanda ya had'e, zuciyar Fadilane yabada Wani sauti ganin irin kallon dayake watsa mata, a hankali ta maida kanta gun baby, wacce tayi Mata signal had'e da murmushi, itama Murmushi tad'anyi takalli momy Asace taga Wani Mugun kallon datake Binta dashi, a hankali ta Maida kanta kasa Tareda zuba dara daran idanuwanta Akan dogayen yatsun kafarta, duk abinda sukeyi Dady yana kallonsu babu abinda be ganiba,

Gyaran murya Yayi yace "yau talata ni amatsayina na babba acikin gidannan wanda zai fad'a ayi Aiki dashi, Ina me sanar muku ranar Jumma'a da misalin karfe 2:30 za'a d'aura Auren 'yata Fadila dakuma d'ana Abdul Akan sadaki naira Dubu d'ari" d'ago Kai Abdul Yayi a rikice yace "Dady... " hannu Dady ya d'aga mishi, alamar Yayi shiru, itama Fadila d'ago Kai tayi zatayi magana Dady Yakuma d'aga mata hannu,

"sannan Ina me sanar muku asibitin danasa aginashi Angama na danka amanarshi a hannun Fadila dakuma Mamana wato Baby, zamu had'a walimar aurensu dana bud'e asibiti"

"Kai Abdul Nabaka damar kayi magana amma kada ka kuskura kacemin bakason auren"

Abdul yama rasa me Zece Dady ya d'aureshi da jijiyoyinshi cikin in Ina yace "w wa Wlh Dady Inada wacce nakeso Dady ka taimakeni Wlh Inasonta idan ban auretaba zan iya rasa raina"

Dakatar dashi Dady yayi yace "Nikuma nazab'a maka Fadila, Ke Fadila Kiyi maganarki, Kema banaso kicemin bakison Auren"

Fadila kuka tafara cikin Muryan kuka tace "na d'aukeka a matsayin Uba Bazan bijire Makaba na yadda da zab'in dakaimin amma Ina rokon alfarma, ka taimaka kabar Yaya Abdul ya auri wacce yakeso Koda rana d'aya zai had'a ya auremu"

Kallonta Abdul Yayi yana karanto Wani abu a fuskarta amma yakasa karancewa, Dady yace "na amince amma sai bayan ya aureki Kafin ta auro ita wacce yakeso d'in"

Milena Yayi yabar falon bê kara cewa komai ba, Momy ce tace "Yayi miki dadi Ko 'yammata? "

Fadila shiru Tayi tana kallon kasa, mikewa Momy tayi tabar falon itama, Baby ganin haka yasa itama tamike da murnarta tabar Wurin, yarage daga Fadila sai Abdul, Abdul Tashin hankali yahanashi tashi ita kuma Fadila Tsoro yasa takasa tashi, sai murza yatsun kafarta Take, shikuma Abdul yazuba mata ido Kamar yayi ajiya a fuskarta, saida taga kallon yaki karewa yasa tamike sumsum zata tafi "tsaya" shine abinda Abdul yafad'a, cak tá tsaya tana kallon gefe, mikewa yayi da takunshi ya iso warinta kallonta Yayi daga sama har kasa, a hankali yafara matsowa Kamar zai shiga jikinta baya baya tafara yana Binta tana baya harta had'u da jikin bango, waro manyan idanunta tayi tana kallonshi bakinta har rawa rawa Yake, lips nata yazubawa ido yana kallon fuskarta, hannunshi yasa ajikin bangon duka biyu sai gata a tsakiya, so take tayi Salati amma takasa sai waro ido take lips nata yana rawa, yatsanshi d'aya yasa yafara zagaye lips d'in dashi, jikintane yafara rawa, a hankali yafara Kokarin Kai bakinshi kan nata, da sauri ta juyar dakanta gefe, murmushin mugunta Yayi cikin sanyin murya yace "juyo mana"

Kin juyowa tayi yasa hannunshi da karfi ya juyo fuskarta, kallon lips nata Yayi sosai ganinshi Pink color gashi tashafa lip Balm me kamshin chocolate yasa Yayi saurin had'e bakinshi da nata, tsotsa Yake Kamar yasamu Sweet a hankali Yake saukar da numfashi, Kokarin kwace bakinta take tana hawaye dan zafi takeji sosai, shikuma ganin tana kuka yasa yaki sakinta Saida yaga numfashinta yana neman d'aukewa Kafin ta saketa tareda tureta Yabar falon, Baby ce Tsaye abayan Kofa tana kallon abinda yafi zare tsayi, taso tá gudu tun d'azu amma kafarta Yayi Nauyi, dama ganin Fadila bata shigo bane yasa taje su taho tare amma tana zuwa idanunta sukayi mumunar gani, yayanta me hankali da nutsuwa tagani yanashan bakin Addanta me Kamun Kai da sauri Kai dakuma hakuri, da kyar taja kafarta takoma d'aki a hankali taja blanket tarufe kanta dashi tana kara kallon hoton yanayin a zuciyarta,

Fadila saida ta juya taga Ba kowa Kafin tajuya taja kafarta zuwa d'akinsu a bakin Kofa ta tsaya ta goge fuskarta da bakinta Kafin tayi sallama a hankali tashiga, Ganin Baby tana bacci yasa tawuce toilet saida tasha kukanta Kafin ta Wanke fuskarta had'eda yin Alwala tafito, salla tayi tashafa mai Kafin taje Wurin Baby tana tashinta, Kamar da Gaske Baby tamike tace "Adda Fadila "

Fadila kanta tá d'auke d'an batason Baby tagane komai, "kitashi Kiyi sallah"

Tashi Baby tayi tawuce toilet, tana fitowa taga Fadila da madubi tana kuka Ga bakinta daya d'an kumbura kad'an she cant emergin wai yayanta ne Yayi wannan abin, karasawa tayi Wurinta tá zauna a gefenta tareda riko hannunta tace "Adda Meya sami ankonki? "

Cikin kuka da b'acin rai Fadila tace "ba yayanki bane yamin"

Abin ya baiwa Baby Dariya amma ta dake tace "me Yayi miki"

Fadila tace "gashi kina gani"

Baby tace "Awww nagane Kice yafara nuna miki abinda zakiyi mishi idan ya aureki, yanaso kisaba kikuma zama expert tawannan harkan, shikuma besan raguwa bace ke, daga Kiss harkin fice a hayyacinki fuska dukya kumbura? Kice akwai Aiki, zan gaya mishi saiya dage sosai"

"ni kike fad'awa Haka Baby?"

Baby tace "bayanke akwai Watace Anan? " tayi Mata alama da hannu,

Filo Fadila ta d'auko tafara maka Mata Baby sai Kokarin kwacewa take, fad'awa sukayi kan gadon suka fara dambe Kamar wasu kananan yara, Baby sai Dariya take ita kuma Fadila ta zage tana buga mata filo, ganin dariyan Baby Kamar wata 'yar shekara biyu sai kyalkyalewa take yasa itama Tafara dariyan.

Jiddah Ce

08144818849

[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸

    *K'ANWATA*

  🌸🌸🌸🌸🌸

    Na

Jiddah S Mapi

*Chapter 46*

         ~Washe gari Umma ce zaune Akan sofa Sanye take da bakin dogon Riga hijab hannunta rikeda waya sai karkad'a kafa take da alama ranta a b'ace sosai, ringing wayarta tayi da sauri ta d'aga Tareda karawa a kunnenta cikin masifa tace "Ina kiranka tun safiya bazaka d'agaba Kasan yanda mutanennan suka haukatamin yaro? Tun jiya sambatu Yake wai nakawo mishi Fadila Kai kuma Dan shashanci kaki d'aga kirana"

Hakuri meshi yayita bata daganan Yayi Mata bayanin komai, "ka nemomin number wanda ya saida musu gidan daga nan zuwa karfe 4"

Kitt ta katse wayar Tanajin Wani haushin 'yan gidansu Amrah Tareda kudira aniyar d'aukan fansa.

       "Adda Fadila Momy na kiranki" da sauri Fadila ta sauko daga gadon ta dafe kirji cikin Tsoro tace "me Nayi kuma? "

Baby tace "Kiyi a hankali babu abinda Kikayi Mata, kawai tace Nakiraki" dogon hijabi Fadila ta d'auko tazira Akan Wandon dayake jikinta wanda ya d'ameta sosai, flat shoe tasa da sauri ta murd'a handle tafice,  addu'a take a zuciyarta Allah yasa ba Wani abin tayi ba,  da sallama tashiga ciki,  ganin momy zaune tana taunar cingum yasa ta durkusa kasa ta gaidata, abin mamaki sai momy ta amsa,  Tareda cewa "kinyi break fast?" da mamaki Fadila tace "Eh nayi"

Murmushi momy tayi tareda Ciro wasu magunguna guda uku a Jakarta biyu a gora Ruwa ruwa sai d'ayan kuma satches ne, b'allawa tayi tamikawa Fadila tace "karb'i wannan Ki had'iye" da sauri Fadila takarb'a tamike "Ina zaki? "

Fadila tace "ruwa zan d'auko"

Momy tace "Ga ruwa nan neman gajiyar da Kai kawai"

Dawowa tayi ta durkusa tareda had'iye maganin ta Kora ruwa akai, murmushi momy tayi sannan tabata na goran tace "sha Marfi Bibbiyu, tsumine shikuma Wancan Supplement ne, kirika zuwa kina karb'a kowani safiya bayan kinyi breakfast, sannan wannan Maganar ta Matan aurece Ko wacce takusa aure kada kifad'awa Baby balle wasu awaje kinji"

Fadila murmushi tayi tace "to momy na gode"

Momy tace "tashi kije"

Mikewa Fadila tayi tafice a d'akin Tanajin dad'i momy tafara Sonta,  Momy kallon Bayanta tayi tace "a zahiri Kamar me wayo ashe dakikiya ce zaki aureshi amma zanga yacce zaki haihu harki samu gindin zama nonsense"

Fadila tana zuwa d'aki Baby tace "wai mmeyafaru?"

Murmushi Fadila tayi tace "tsakaninmu ne ba'aso yara suji"

Tab'e Baki Baby tayi "intayi tsami maji"

"Barama tayi tsami ba insha Allah" babu wacce takara magana acikinsu.

       "Meyasa Dady zemin Haka?  Tabbas an Cuceni an Cuci rayuwata Wlh Dady zai shiga hakkina idan aka auramin wannan yarinyar ya zanyi da soyayyar danayi dakonshi shekara da shekaru" Abdul sai juyi Yake Akan gado idanunshi yana zubda hawaye,  yasan koda ya auri Fadila hakkinta kawai zai shiga Dan Tabbas gangar jikinshi ta aura amma zuciyarshi bata Wurinta, tin jiya beyi bacci ba har yau Jiyayi jikinshi Yana zafi alamar zabzab'i zai kamashi, juyi yakarayi Akan makeken gadonshi yana Tino wai ranar Jumma'a zasuyi mishi aure, wani Sabon hawayene yakara zubowa daga idanunshi, mikewa yayi zuwa Wurin drower Wani magani ya d'auka ya b'are, Wurin frij yanufa da maganin a hannunshi, ruwan gora ya d'auka yasa maganin abakinshi Yamutsa fuska yayi yahad'iye da kyar Dan yatsani had'iye magani a rayuwarshi, komawa Yayi kan gadon ya kwanta tareda rufe Kanshi da blanket.

      "Baby Ina tsoron kasancewa sirika awurin momy kada tazo taci zalina Kiyi hakuri bawai Ina Zagin mahaifiyarki bane Ina fad'an abinda zai iya faruwa ne"

Dafata Baby tayi tace "Ko Wani d'an Adam danashi kaddarar Wani yazo mishi da sauki Wani kuma yazo mishi da wahala addu'a zakiyi Allah ya canja miki kaddararki da Mafi alkhairi, Addu'a yana canja kaddara, idan kika tafi Ina zakije? Gida?  Ko yawon duniya?  Kinada nutsuwa Adda Fadila, agida kuma kanwarki tariga ta b'ataki a idon kowa babu me ganinki da mutunci"

Shiru Fadila tayi sai daga baya tace "hakane Baby Kanwata tayimin abinda Bazan tab'a mantawa ba, Wlh ba tsani Amrah banason jin sunanta duk wani Wahala danasha a duniya ta sanadinta ne sannan idan da nice bazanyi Mata Haka ba, Amrah ta cutar dani kuma Ina rokan Allah ya cutar da ita kwatankwacin yanda ta cutar dani"

"kidaina yimata Mugun Baki addu'a zakiyi Mata Allah ya shiryata"

"babu addu'a tsakanina da Amrah idan kinji Nayi Mata addu'a to tabbas Saide na b'atanci Badai na shirya ba Wlh"

Shiru Baby tayi Dan tasan Fadila tana maganane cikin b'acin rai da Kunar zuci.

        "Wlh koda ya auri Abdul Nayi alkawarin bazata haihu ba idan ya haihu Saide bayan Raina sai idan Bana numfashi, yarinya tazama min annoba acikin gida ta kwakwayemin iyalai Kowa Sonta Yake acikin gida to Wlh ta Tsaya iya aure amma banda tara zuri'a, maganin dana bata na lalata mahaifa ne mahaifanta ya b'aci kenan ya tashi a Aiki, dani take zancen"

Momy ce da kawarta a d'aki tana fad'a Mata maganganun, shiru kawar tayi sannan tace "garada kika dau mataki tun wuri kibarta ta aureshi amma da kafanta zata gudu idan taga ba alamar haihuwa"

shewa sukayi suka tafa tareda fara hirarsu ta yaushe gamo.

          "Amrah ce kwance Akan cinyar momy a kwanakin nan tana laulayi sosai jikinta babu dadi samsam, da d'an Wahala tace "Umma idan na haifi namiji zansa takwaran Baba idan Macece kuma zansa takwararki"

Shafa kanta mama tayi tace addu'a zakiyi Allah ya saukeki lafiya cikin har nawa Yake dazaki fara wannan lissafin?"

Murmushi Amrah tayi tace "yaufa da gobe babu wuya awurin Allah"

Sallaman Abbane ya katseta "Sannu da zuwa Abba"

"yawwa"

Abba yafad'a jikinshi a sanyaye, Mama kallonshi tayi da Kyau tace "lafiya Kuwa?"

"lafiya"

Jikin Amrah ne Yayi Sanyi Dan bata tab'a ganin Abba a wannan yanayin ba tashi tayi tabasu wuri itama jikinta a mace, Mama ce tayi Matso tace "ba lafiya ba akwai Matsala"

Shiru Abba Yayi baice komiba,

Mama hankalinta yatashi tace "Dan Allah ka sanarmin Meyake faruwa Kodai Fadilace? "

"ba Fadila baace kuma Nasha fad'a miki kidaina kawomin zancenta agidannan,  an koreni awurin Aiki batareda Wani Dalili ba sannan sunamin Maganar Wani nasiyi gidana ba Akan tsari ba"

"Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un Meyake shirin faruwa damu?"

"Karki sanarwa Amrah gudun damuwa kinsan ciki bayason damuwa"

"to Allah ma yasa sukiraka gobe"

"Ameen"

Da sauri Amrah tana Wurin ganin Mama tana shirin tashi, jin jikinta tayi Yayi Nauyi wani irin masifane wannan? Me zasuci idan Abba baya Aiki? Innalillahi shine take maimatawa"

Kwanciya tayi Akan gado tadafe kirjinta dayake bugu"

_Jiddah Ce....✍️_

08144818849

[16/09, 10:01 pm] Jiddah S Mapi: 🌸🌸🌸🌸🌸

    *K'ANWATA*

  🌸🌸🌸🌸🌸

    Na

Jiddah S Mapi

*Chapter 47*

         ~shirye shiryen Biki ake sosai agidansu Abdul Dady ne yake bada kud'in duk Wani abu da ake bukata ta b'angaren Amarya da ango, Yanda momy ta sake Jiki tana shiri zakace ta saduda ne Tamika Kai amma ita kad'ai tasan abinda Yake zuciyarta, Amarya da ango kuma basu kara had'uwa ba tin ranar da suka hadu a falo kowa sabgar gabanshi Yake musamman Abdul da Bayama zama agida sai can dare yake dawowa, itama Fadila hakan take tana Gama Aikin cikin gida zata shige d'aki taita bacci Hakan yasa tayi Jiki kad'an fatarta tayi laushi sosai tin batayi dilki ba jikinta ya canja balle ace tayi Dilki musamman ma idan Unty Amina ce tayi Mata Dilki Ai magana ta Kare (Unty Amina ba iya Dilki ba Harda Gyaran Amare tanayi tana anfani da turaruka masu Kanshi Wurin kawata amare, Abunka da 'yar Maiduguri Ai dolema Kiyi Kyau idan kika shiga hannunta gyara daga ciki har waje, Ina sonki Unty Amina)

Baby ce tashigo d'aki tana tura Baki, buga Fadila tayi tace "Adda kitashi wai muyi cake"

Fadila Salati tayi tana Mika jikinta yazama na ajebo sosai takara Haske Ga gashinta dayake a tsefe ya Bazo fuskarta tayi Kyau sosai a yanayin, Baby tayi murmushi, Fadila tace "murmushin Me kike? "

Baby tace "hmm yacce kika tashi a baccinnan na tabbata da yayane ya tadaki Ko Baiyi niyaba saiya rungumeki tsabar yacce Kikayi kyau"

Dirowa Fadila tayi Akan gadon tad'auko filo tafara makawa Baby, sai ihu Baby take tana kiran Momy, kwace filon tayi Fadila ta tureta Akan gadon ta rikota suka fara kokawa Kamar yara, Baby ce ta Danne Fadila tace "Kin zata kinfini karfi Ko?  Bakisan barinki nakeba? Fadila sai waro Ido take Dan batayi Zaton Baby tanada karfi hakaba,  "kicemin sorry Kafin na sakeki"

"Wayyo ataimakeni"

Shine abinda Fadila take fad'a, Abdul daya tashi a dakin dady ranshi a b'ace Dan Dady Yagama tsigeleshi yaji Muryan Fadila tana cewa a taimaketa, tsaki yaja yaje ya bud'e kofar waro Ido yayi ganin Baby Akan Fadila tana Dariya Itakuma Fadila sai zazzare Ido take, "Ke!!!" yafad'a da karfi, juyowa baby tayi, ganinshi yasa tasauka da sauri, Fadila Ko Dirowa tayi agadon tarikeshi tana Haki, kallonta Yayi daga sama zuwa kasa ganinta a hargitse yasashi Jan tsaki cikin Tsawa yace "Yanzu waye Mara hankali cikinku? Kece babba amna kece raguwa?  Yarinyarnan karamar ne zata hau Kanki bazaki Zaneta ba?" waro Ido Fadila tayi, yace "dalla kidaina kallona da wannan idon naki mema yahad'aku fad'an?"

Kallon Kallo suka fara Baby takalli Fadila, Fadila takalli Baby, "bazaku fad'aba Keban?"

Baby tace "um dama" sai tayi shiru Fadila ma kame kame tafara ganin haka yace "Kubiyoni"

Cikin Tsoro suka fara bin bayanshi d'akinshi yaje dasu yabud'e wardrobe wasu Uban Kaya suka Gani masu yawa yace "oya Ku Matso" Fadila ce tafara matsowa yace "kucire kayannan dukka kushiga toilet Ku Wanke kada kuyi anfanida washing machine da hannunku zakuyi dama Rashin Aikinyi Ke damunku"

Kallon Kayan Baby tayi sannan takalli Fadila, Fadila dukar da kanta tayi sannan tasa Hannu tafara divan kayan, Babyma matsowa tayi ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login